Showing 162001 words to 165000 words out of 287295 words
da
ɗ
aukar nauyinta harda ƙanwarta Jidda, wata uku kenan daya siya musu wannan gidan da suke ciki watansu biyu da tareqa kuma a ciki mahaifinsu ya rasu.
Rashin samun ha
ɗ
in kan Hajja ne ya hana shi ya auri Zulaihan tun bayan
data kammala secondary domin Hajjan tace babu yanda za'ayi ya auro mata yar Allah baku mu samu, da wanne zaiji? Nauyinta dana yan uwansa ko kuwa na matarsa da danginta tunda kaf ahalinsu a binciken da aka mata an gaya mata babu mai samun cikakken ci uku a
rana, ko hidimar da yakeyiwa su Zulaihan a lokacin a
ɓ
oye yakeyi domin ya san muddin ta sani toh fa ba zata bari ba shiyasa ko da ta hana shi aurenta a lokacin bai matsa ba domin shi da kansa yana so ya aureta a sanda yake da damar bata kalar rayuwar da ya
ke mafarkin sama mata saboda yanda yake tausayinta a ransa.
Yana son Halima har ransa saboda ita
ɗ
in tsarinsa ce sannan kuma tana masa son da ya yarda da wahala ya samu qata mace da zata kwatanta masa irin sa sai dai kuma soyayyarta a zuciyar sa bata k
o kama ƙafar yanda yake jin Zulaiha a ransa ba. Kusan kwatankwacin irin son da take masa ne shi kuma yakeyiwa Zulaiha har ga Allah kuma da ace ya samu irin damar da yake fata kafin ya aureta da Zulaihan zai aura ba ita ba. Sai dai a yanzu da al'amura suka
kasance ba yanda ya so faruwarsu ba Allah ya ƙaddara ita Haliman ce matar sa ta farko ga kuma rabon da yake a tsakaninsu ya san ba zai samu matsala da ita ba idan ya auri Zulaihan daga baya. Toh amma yanzu komai ya lalace ya tashi daga yanda yayi hasashen
faruwar sa kansa kuma ya kulle ya rasa ta ina zai fara gyarowa.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_U
mmu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biy
a naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 37*
HALIMA
Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce na
yi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halaka
ni. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce,
"Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki kalli yayanki da har yanzu basu san ina suka dosa a rayuwarsu ba idan kika bari damuwar wani can ta kasheki su kika
yiwa asara domin tun kina raye dai kinga alamar cewa dake da babu a gurinda duk
ɗ
aya tunda tun bayan da aka kawoki banga wani da aka nuna mun a matsayin shine mijin ki kuma nasan kina da aure dan haka kiwa kanki karatu Halima ki san mai ya kamace ki idan m
a zaki mutu ki mutu akan abinda kike da daraja a gareshi".
Daga lokacin na fara ƙarfafar kaina domin dagaske na yarda idan na mutu iyayena da yayana suke kan gaba gurin asara yanda kuma suke zagaye dani kullum cikin nuna kulawarsu idan na cigaba da
ɗ
aur
a musu damuwata na sani Allah zai iya kamani da haƙƙinsu. An sallameni da tarin garga
ɗ
i akan abubuwan da zan kiyaye, muka koma gida na sake bu
ɗ
e sabon babin zaman
ɗ
aki domin bana son kowacce hayaniya yan dubiya da suke zirga zirga a gidan kuma takuramun su
keyi shiyasa na za
ɓ
i da inyi zamana a
ɗ
aki ko na samu damar yin tunanin da likita yace in daina amma ba zan iya ba ya zama tamkar maha
ɗ
in rayuwata ne tunda ba zan iya bu
ɗ
e baki in fa
ɗ
awa kowa damuwata ba sai dai nayi ta tattaunata tsakanin ƙwaƙwalwata da Z
uciyata.
Ranar da nayi kwana uku da fitowa daga Asibiti har lokacin tsakanina da Mama tsantsar kulawa ce tamkar zata mayar dani ciki ta sake haifoni haka take ji dani, duk sanda na kalleta tana mun hidima na tuna furucin Bilal sai naji wani abu tamkar
dutse ya danne mun ƙirji. Kamar kullum bayan ta taimakamun nayi wanka na shirya ta fita ta dawo da try data
ɗ
ora mun breakfast, haka ta zauna tana tausata har saida naci da yawa kafin ta
ɗ
auke ta sake dawowa da ruwa ta fito da magunguna na ta bani na sha s
annan ta
ɗ
akko mun wayata da jona mun a caji ta ajiye a kusada ni tana cewa
"Ga wayarki nan tayi caji sai ki kunna dan ƙila ana ta nemanki ba'a samu". Kaina yana ƙasa bance komai ba naja wayar na turata ƙasan filo, damuwa zan ƙarawa kaina idan na kunnat
a dan haka gara tayi ta zama a kashe kawai.
Ganin ta gyara zama tana kallona yasa naji zuciyata ta shiga bugawa da sauri dan na san da wahala idan ba zancen Bilal zata mun ba. A tsayin sati biyun da nayi a kwance ko bisa kuskure banji wani ya ambaci sunan
sa ba, na san kuma bai zo ba babu kuma wani nasa da yazo na san kuma dama babu yanda za'ayi su cigaba da yi mun shiru dole akwai lokacin da zasu tambayeni dalilin zuwana gida da kuma dalilin ciwo na amma bana zaton ina da amsar da zan bayar a nan kusa ko a
gaba.
"Ta yaya zan fa
ɗ
a musu alaƙar banza na kama Bilal yanayi da wata mace a waje? Da wanne ido zasu cigaba da kallonsa? Ba shi ba ina zaton har yayana sai martabar su ta ta
ɓ
u idan wannan maganar ta fita shiyasa nayiwa kaina alƙawarin shanye baƙin cik
i na ni ka
ɗ
ai ba zan ta
ɓ
a fa
ɗ
awa kowa komai ba tunda dama damuwata tace bai kamata kuma naci gaba da raba baƙin ciki na dasu ba.
"Halima magana nake so muyi" ta fa
ɗ
a hakan kuma ya saka bugun zuciyata ƙara gudu, na kalleta kafin na sakw sadda kaina ƙasa
ina ji tayi murmushi mai sauti kafin ta kamo hannuna cikin nata tace
"Mai ya faru Halima?"
Nayi kamar ban fahimci mai take nufi ba hakan ya saka ta sakw cewa
"Ina nufin mai ya faru tsakaninki da Bilal?"
Jimm nayi amsoshi da yawa suna yawo a raina
amma na rasa wacce ta dace da in bata, yanda take kallona kuma nasan koma me zan fa
ɗ
a da yake akasin gaskiya zata amma kuma dole inyi mata ƙarya domin wannan gaskiyar ba mai fa
ɗ
uwa bace. Cikin in ina nace
"Babu komai Mama"
"Babu komai kika ce?, babu k
omai ya kawo ki gida ƙarfe bakwai na safe kuma tunda ya tafi bai sake waiwayarki ba?" Ta fa
ɗ
a tana tsareni da ido. Na
ɗ
auke kaina gefe nace
"Tafiya zaiyi ai shiyasa ya kawo mu gida". Shiru tayi dan har saida na sace kallonta naga itama ni take kallo da
alama ta rasa abun fa
ɗ
a ne shiyasa tayi shiru tana kallona, can taja numfashi tace
"Ba wasa nakeyi ba Halima ki fa
ɗ
a mun wace damuwa gareki a aurenki da har take barazana ga rayuwarki?"
Ɓ
ata fuska nayi kamar zan fashe da kuka nace
"Na fa
ɗ
a miki babu k
omai Mama idan da akwai ai kin san ba zan
ɓ
oye miki ba zan gaya miki ko?" Shirun ta sakeyi kafin ta miƙe a sanyaye tana cewa
"Shikenan" daga haka ta fice daga
ɗ
akin na bita da kallo jiki a sanyaye ina jin kamar na tashi na bita na fa
ɗ
a mata amma kuma baza
n iya ba. Cusa kaina nayi cikin pillow na fashe da kuka.
Tun daga ranar kuma Mama ta janye mun duk wata hidima da take mun da kanta ta saki sai Zainab ce takeyi ko kuma inyiwa kaina hakan kuma ba ƙaramin ƙara mun damuwa yayi akan wacce nake ciki ba duk
gidan sai ya mun ba da
ɗ
i, Abba ya koma Lagos, Amirah ta koma makaranta Al'amin dama tun da aka kwantar dani Anty Labiba ta tafi dashi gidanta har ta sakashi makarantar su Inaayah ya fara zuwa Sharifa ma kuma Mama Fauziyya ta
ɗ
auke ta da muka dawo saboda n
a huta karta ringa damuna da rigima dan haka dagani sai Mama da Zainab sai kuma su Suraj a bakin Gate duk sai gidan ya mun fa
ɗ
i babu da
ɗ
i tarairayar da nake samu an janye mun tallafi kusan magana ma sai ta zama dole sannan take mun.
Ranar dana cika sati
ɗ
aya da dawowa daga Asibiti wanda ya kama sati uku kenan da barowata gidan Bilal ina zaune a falo na zubawa Tv ido, gajiya nayi da zaman
ɗ
aki na fito ina zama kuma Mama ta tashi ta fita can tsakar gida ta fara aikin da bansan na menene ba, ni dai na fahim
ci kawai zama tareda ni
ɗ
in ne bata so, har nayi kamar na bita sai kuma na fasa na zauna, dama tunda Anty Labiba tazo jiya naga tana wani hararata na san sai ta sake zugata ilai kuwa gashinan.
Ina nan zaune a zahiri Tv nake kallo amma a ba
ɗ
ini nayi zur
fi cikin tunani. Ni da kaina na san na zama wata iri, nayi rama mara fasali duk da yanda Mama take matsamun kan cin abinci amma tamkar yana bin rariya yana tsiyayewa ne dan babu abinda yake nunawa a jikina azabar tunani da ƙuncin daya cunkushe mun zuciya s
u suka hana sassan jikina kar
ɓ
ar abincin su sarrafa shi yanda ya kamata.
Daga waje na ringa jiyo kamar muryar Hansa'u suna gaisawa da Mama, ba zan iya tuna rabon da nayi magana da ita ba dan an
ɗ
auki lokaci mai yawan gaske tun kafin na haifi Sharifa wa
ni zuwa da tayi taje gidana ta tarar da abincin da Bilal ya auna mun zan dafa tayi mun magana akan kada na kuskura na fara rayuwar da a gaba zanzo ina kuka da kaina har tayi iƙirarin zata gayawa Mama halin da nake ciki a sannan haka na rufe ido na gaya mat
a maganganu son raina kuma nace ta fita a duk wata sabgatar gidan aurena ko da take
ɗ
aga kafa
ɗ
a tana iyayi ai sai dai idan ba zata fa
ɗ
i gaskiya ba amma itama tana da nata matsalar ƙila ma halin da take ciki yafi nawa dan haka kowa yaji da kansa idan gulma
zata ringa kawota ni na yafe kada ta sake zuwa in da nake.
Haka muka rabu dutse a hannun riga ta kuma
ɗ
aukar mun alƙawarin ba zan sake ganin ƙafarta a gida na ba dama kuma duk cikin ƙawayen mu ita ka
ɗ
ai ce take har sannan dan su Baby su Zainab mun da
ɗ
e
da yin uwaka ubanka tun bayan haihuwar Al'amin da suka sameni har gida zasu gaya mun maganar banza akan wai labari ya baza gari komai daga gidanmu aka mun nan ma na musus tatas nace nagodewa Allah inada gatan da za'a mun a gidan namu su dai da suke taƙama
da miji randa bai musu ba sai in ga ina zasu kama shikenan mukayi baran baran suka fita harkata.
Idona akan ƙofa harta shigo falon cikin kyakkyawar shigar Abaya data matuƙar kar
ɓ
ar ta. Ko dan na jima ban ganta ba sai naga ta ƙara wani kyau da kwarjini
ta sake zama bababar mace kana kallonta ba sai an gaya maka nutsuwa da kwanciyar hankali sun bi jikinta ba. Da sauri ta ƙaraso in da nake tana kallona kafin ta rungume ni lokaci
ɗ
aya ta fashe da kuka wanda tamkar nima ina jira na fashe da kukan da na da
ɗ
e
ina so nayi amma damuwar Mama ta saka nake ha
ɗ
iye shi. Rungume da juna muna kukan kamar ƙananan yara muka shiga
ɗ
aki na, kan gado muka zauna muka cigaba da kukan zuwa wani lokaci kafin ta sassauta nata ta fara rarrashi na wanda daƙyar mukayi shiru a ƙarsh
e.
"Halima mai ya faru? Mai yayi zafi a duniyar nan kika mayar da kanki haka Halima kina kallon mudubi kuwa?" Ta fa
ɗ
a tana
ɗ
auke sabbin hawayen da suka far zubo mata. Na kwantar da kaina a kafa
ɗ
ar ta nace
"Hansa'u ƙirji na zafi yake mun zuciyata ina j
in tamkar zata fashe"
"Me kika aje a zuciyar? Ki amayar da koma menene Halima zaki samu sauƙi duk wani nauyi da kika ji zai sauka" ta fa
ɗ
a tana
ɗ
agoni daga jikinta. Nayi shiru ina kallonta, tabbatas ina da buƙatar fitar da abinda yake ci mun zuciya tun
bai gama yi mun illar da ba zata gyaru ba, na bu
ɗ
e baki da niyyar magana sautin muryar Bilal ya shiga yawo a kunnena sanda yake cewa
"Kafin su zageni sai sun fara yi miki dariya sunce Allah ya ƙara Halima duk wanda kika fa
ɗ
awa aibu na laifinki zai gani b
a ni ba" tuna hakan y aka na rufe bakina ba tareda na ce komai ba na zame daga riƙon da ta mun na kwanta ina ajiyar numfashi. A hankali tace
"Bazan miki dole akan ki fa
ɗ
a mun abinda yake damunki ba amma ki sani barin kashi a ciki baya ta
ɓ
a maganin yunwa
Halima. Meye ribarki ki rayu cikin fushin iyaye Halima? Ace da ki fa
ɗ
i damuwarki wacce kulawa ce ma har ta saka aka damu da aji domin a nema miki mafita amma ke kin gwammace ki ƙara jefa kanki cikin wani bala'in ta hanyar shiga fushin iyaye?
Ni dai ban
sanki a haka ba ban kuma san mai ya canza ki ba shiyasa ko da nayi fushi dake nace zan fita a sabgarki bana iyawa saboda nasan ke
ɗ
in a yanzu ba Halimar dana sani a baya bace kuma kina da buƙatar mu domin idonki ya bu
ɗ
e ki gane gaskiya a yanda take ki fit
a daga iziyar zaton da kike ciki amma kuma duk yanda muka so da mutaimakeki har idan baki so ba babu hali tunda ba zamu miki dole ba, amma ina so ki sani rai
ɗ
aya ne kuma a duniyar nan babu wani namiji daya cancanci sadaukarwar rayuwa domin a yau kika mutu
a gobe zai samu madadinki na sani kuma ko a yanzu kinga izina da ranki baki mutu ba to kiyi hasashen makomar yayanki a bayan ba ranki sai ki yiwa kanki Hisabi kan abinda ya kamata kiyi" ta ƙarasa tana miƙewa ha
ɗ
i da
ɗ
aukar jakarta.
Da sauri na ruƙota
ina juya kai lokaci
ɗ
aya hawaye ya
ɓ
alle mun nace
"Bazan iya gayawa Mama ba Hansa'u"
"Anty Labiba fa?" Ta fa
ɗ
a sai nayi saurin girgiza kai nace
"Gara kowa akanta". Murmushi tayi ta koma ta zauna ta dafa kafa
ɗ
ata tace
"Ban sani ba ko har yanzu kina
ɗ
aukata a irin matsayin da kike dashi a gurina". Nayi shiru ina kokawa da muryar Bilal dake nanata mun kaina zan tozarta idan na tona asirinsa. Da hannu biyu na toshe kunne na kafin na fizgo maganar da ƙarfi nace
"Matan banza yake bi Hansa'u" wannan magana
r kuma tasa naji tamkar na bu
ɗ
e wata ƙofa cikin zuciyata dan haka tiryan tiryan na shiga koro mata bayani tun daga aurena da Bilal duk wani abu da na ha
ɗ
iye saida ya samu hanya ya fito da kansa na furtawa Hansa'u shi harda furucin da yayi akan Mama ban rag
e ba saida na amayar mata. Haka muka rungume juna ni kuka ita kuka babu mai rarrashin wani, mun da
ɗ
e a cikin yanayin kafin ta miƙe tana cewa
"Zanje na dawo Halima idan na zauna yanzu ina kallonki bazan samu ƙarfin guiwar ce miki komai ba zanje gida amma
komai dare zan dawo". Ban
ɗ
ago na kalleta ba na
ɗ
aga mata kai alamar "Toh".
Bayan tafiyar ta ji na ringayi kamar an kwashe mun wani
ɓ
angare na jikina, tsabar yanda nauyin da ƙirji na yake mun ya ragu ina tsaka da kukan bacci ya kwashe ni dana farka ku
ma sai na ringa ji kamar bani ba, babu wannan abun da nake ji yana mun yawo tsakanin ƙirji da maƙogaro, haka na ƙarasa yinin ranar, har na fitar da rai da dawowar Hansa'u sai gata lokacin ƙarfe tara harta gota. Fuskarta duk ta tashi da alama bayan tafiyart
a kuka ta cigaba dayi, a
ɗ
aki muka sake ƙulewa, ta fa
ɗ
a mun maganganu da sukayi tasiri sosai cikin ƙwaƙwalwata. Abu uku da na fi riƙewa cikin maganganunta tunatarwar da tayi mun akan addu'a.
"Halima tun ba yau ba na sani kina da sakaci gurin addu'a. Ki
sani Allah yana fushi da bawan da baya roƙonsa. Ko da ace