Showing 96001 words to 99000 words out of 287295 words
/>
kon Allah, toh Allah ya rufa asiri. Amma wasu irin mutane ne su da irin haka zata faru ba zasu sanar mana ba tun da ai yanzu mun zama abu guda?" Abban ya sake fa
ɗ
a. Anty Labiba da ta zabga wa Mu'azzam harara ta ce
"In ma da gaske ne ba komai ya ja masa ba
illah haƙƙin iyalin sa da baya saukewa kaga an wasu can a banza sun ƙwata ta ƙarfi ai, Allah ya ƙara"
"Haba Labiba ya kuma da irin wannan maganar? Idan da abun ya zo da tsautsayi fa suka hallaka shi ko suka masa wata illar da za'a gwammaci ma mutuwa ya
yi fa? Wannan al'amari na masu ƙwacen waya da mashin dai ya fara yawa se dai fatan Allah ya shirye su kawai" Mama ta fa
ɗ
a cikin jimami.
"Bari na gani idan na fita se mu biya mu duba shi" Abba ya fa
ɗ
a yana miƙewa, kafin ya zaro ku
ɗ
i a aljihun sa ya miƙa
wa Anty Labiba yana cewa
"Gashi se ku ƙara kayan, kin san yanzu lissafi ya canza aboki ne kuma takwara. Ke ma ya kama ta ki ware akwatin ki daban; idan kuma kin barwa su Fauziyya auren shikenan" ya ƙarasa cikin sigar raha. Ta kar
ɓ
i ku
ɗ
in ta na
ɗ
an murmush
i Mama kuma ta taka masa zuwa gurin mota.
"Dama ai son zuciya da kwa
ɗ
ayin abin da Abban ze masa ne ya saka ya yi masa takwarar ba wai saboda cancanta ya yi ba. Bilal kuma, ai se dai ya
cuci wanda be san shi ba wlh amma ni nan kar na ke kallon su" Cewar
Anty Labiba bayan Mama ta dawo falon. Mu'azzam yayi dariya ya ce
"Wlh kin gano shi Anty. Tsabar son zuciya ne kawai. Ban da haka ina nasa uban ya mutu? Ba se ya yi masa takwarar ba ko mun ce masa muna so ne?"
"Ai dai zan ga abin da Bilal ze yi ya muk
u gwanin ta kai da Labiba, ka tashi kaje gidan Hajiya Larai ka amso mun saƙon da ka ce se yau zaka je, ke kuma muje ciki ki duba kayan se muga abin da ya kamata a ƙara. Yau na cewa yan gidan su Abban su su zo su gani idan ya so go be kwana biyar se aje a k
ai musu ko?" Cewar Mama. Labiba ta ta
ɓ
e baki ta ce
"Ba dai zaki haƙura da wannan al'adar
ɗ
aukar maganar ba? Meye wani abin zuwa a gani a kayan barka se kace lefe? Kuma da zaki gayya to su suzo kai kayan kin dai san can gidan su Bilal bana zaton ko ƙyalle
sun tana da da zasu gabatar a matsayin kayan da suka yiwa yaron nan. So kike a maimaita ta lefe ko a sake samun abun da za'a yi ta terere dashi a dangi, ai shikenan".
"Toh Labiba ya kike so na yi? Kin dai san haka suke al'adar su, yanzu idan ba'a kira s
u ba se ki ji ya zama abin magana" Maman ta fa
ɗ
a. Labiban bata sake ce mata komai ba ta wuce
ɗ
akin da suka ajiye siyayyar kayan barkar da suka yi ta shiga fito dasu. Cikin akwati set me uku da kit
ɗ
in sa ta shiga shirya kayan. Kaya masu kyau da tsadar gask
e suka siya. Kusan duk wani abu da za'a buƙata na jego sun siya mata, har da set
ɗ
in feeding bottle da bath set komi basu manta ba duk da ana siya Anty Labiba na mitar mijin ta ya kamata ya siya mata amma kuma itan ce me sake zaƙulo wasu abubuwan a siya ha
r da gado ta basu na minal
ɗ
in ta a pre order ta siye shi kafin yazo har yarinyar ta fara tafiya se kawai ta ajiye shi yanzu kuma ya zama rabon su Halima.
Mama dai na tsaye tana kallon ta har ta gama jera na yaron a babbar akwati da ta uku kafin ta shig
a zuba na Halima a ta biyun wanda duk an
ɗ
inka su. Kala shida ne Atamfa uku lace biyu da shadda
ɗ
aya se mayafi harda takalmi da jaka set bibbiyu. Sauran tarkacen undies har da body sprays da body mist duk ta zuba a kit
ɗ
in, ta tayar da su tsaye kafin ta ka
lli Mama tace
"Tsakani da Allah ko mu muka mata cikin iya wa
ɗ
annan kayan sun isa".
Mama tayi murmushi kawai tana kallon ta, Labiba akwai daru. Ƙarara take adawa da lamarin Bilal da Halima amma yanda ta zage ta kashe ku
ɗ
i a sabgar auren Halima zuwa hai
huwar ta ba zaka yarda bata son auren ba.
Ku
ɗ
in da Abba ya bata ta ciro daga aljihun rigar jikin ta ta shiga ware su, ta miƙawa Mama wani kaso ta ce
"Gashi nan ki rage asara wannan kuma zan ha
ɗ
a akwai ku
ɗ
in ta tun na barkonon da muka ta
ɓ
a siya zan ha
ɗ
a
su na siya mata sarƙa ta samu ta fitar suna". Mama na dariya wai ta rage asara ta kar
ɓ
i ku
ɗ
in tana juya su tace
"Da kika ce ba zaku yi taro ba"
"To ko babu taro ai dai zatayi kwalliya na san kuma yan uwan sa ba zasu ƙi zuwa ba ƙila su zasu yi sunan; Al
lah dai ya kaimu gobe muga zubin su, ko zasu mata ƙauri ma oho" cewar Anty Labiba. Sai Mama ta bata amsa da cewa
"Ke ma da neman magana kike Labiba, cewa fa tayi har account
ɗ
in sa sun yashe komai wa
ɗ
anda suka ƙwace masa waya. Idan ya samu sararin yin h
aƙiƙa ma ai yayi"
"Idan ma ƙarya ya ke Allah ya biya bakin sa ya sa a kwashe
ɗ
in" Anty Labiba ta fa
ɗ
a daga nan ta zura Hijabin ra tayi wa Mama sallama akan zata je kasuwar rimi ta dawo.
*******************
Cike da walwala na ƙare yinin ranar ban da
ma zuwan Hajja da ta so ta
ɓ
ata mana farin cikin mu amma ban bari maganganun ta sunyi tasiri a raina ba. Dab da la'asar Abba tare da Baba Salahu da Baba Munzali suka zo duba Bilal, tun aure na zuwan Abba na farko kenan gida na. Na ji kunya ta yanda ko ruw
an robar da zan basu babu a gidan balle a je ga lemo ko wani abu se pure water na juye musu a Jug duk su ukun ma babu wanda ya sha basu jima ba kuma suma tafi.
Basu jima da tafiya ba Hajja ta zo tare wasu ƙawayen ta da suka zo dubiya da kuma barka. Ina
ɗ
aki ina shiryawa dan gama wanka na kenan Abba na kuma yana hannun Bilal yana masa wasa dan shi Anty Amina ta fara yi wa wankan kafin tayi mun.
"Wato kinga gurin zama har da kafa murhu" Hajja ta fa
ɗ
a bayan da na fito ba tare da ta ko amsa gaisuwar da
nake musu ba. Lanti, ƙawar ta ta ce
"Zancen da na ke yi a raina kenan na ce ita haihuwar farin ma ba zata tafi gida tayi wanka ba?"
"Ke ko jaraba irin ta yayan zamani mana. Nan na ke gaya miki jikar Saude ba yanda uwar ba tayi akan ta tafi gida tayi wan
ka ba taƙi wai da wa zata bar mijin ta? Na ce Allah ya yafe mana mu da zamanin mu ake arba'in biyu"
ɗ
ayar ƙawar ta ta da ban san ta ba ta fa
ɗ
a. Shikenan ta samu fili ta fara zazzaga har tana cewa tsabar mugun ta tasa naƙi tafiya.
"Duk ibtila'in daya fa
ɗ
awa yaron nan amma saboda rashin tausayi ace ki zauna ki yi jego a gidan nan; ai se ki zauna kici uwar da zaki ci" take ta maimaitawa. Ni se ta bani dariya ma na koma
ɗ
aki na barsu ina jiyo Bilal na mata magana akan ta yi shiru amma se ƙara volume ta ke L
anti tana taya ta. To wace uwa kuwa zanci wadda ban saba ci ba? Tun ma da na dawo
ɗ
in me Bilal
ɗ
in ya yi mun da har zata ce ba'a jin tausayin sa? Ni yanda yayi mirsisi be tambaye ni in da aka samo kayan da ake sakawa yaron ba ma shi ya fi bani mamaki tun d
a dai dubu goma ce ta gifta tsakani na dashi akan sabgar haihuwa haka ko da wasa be yi zancen asibiti ba balle ya tambayi waye ya biya ku
ɗ
in.
Basu jima sosai ba suka tafi, ina
ɗ
akin Anty Amina ta leƙo ta ce mun zasu tafi itama zata bi su taje gida ta d
awo, a da ina ganin kamar tafi kowa zafi cikin yan gidan su Bilal amma a yanzu kam na tabbata duk ta fisu kirki domin tayi mun abun da ko jini na ce iya kaci kenan. Daga bakin ƙofa nayi musu sallama na koma ciki, se da na ji Bilal na kira na kafin na fita
na koma falon.
"Ki bani aron wayar ki zan yi kira" ya fa
ɗ
a se na koma
ɗ
aki na
ɗ
akko masa wayar na bashi sannan ya ce na
ɗ
akko masa wani littafi a can
ɗ
akin sa. Numbobin abokanan sa wa
ɗ
an da ya rubuta ya ringa sakawa yana kira ya sanar musu da an masa
haihuwa. Hafiz ya kira a ƙarshe bayan sun gama
magana ya bani muka gaisa yayi mun barka tare da ƙorafin me yasa ban kira Matar sa na gaya mata ba? Haƙuri kawai na bashi kafin na mayar wa da Bilal wayar na tashi saboda Abba na daya fara ƙananan kuka.
"Ki
n ji me oga Hafiz yake cewa?" Bilal ya fa
ɗ
a bayan daya gama bige bigen wayar, na girgiza masa kai ya yi yar dariya ya ce
"Wai amma shi za'a yi wa takwara".
"Se kace masa me?" Na fa
ɗ
a ina kallon sa tare da tuno maganganun da suka yi,
"Nace masa Dady ak
a saka, kin san surname
ɗ
in ku
ɗ
aya. Baki ji yanda ya ringa murna ba ina ga ma yau zasu zo duk da yace suna Abuja ama jirgin 6 zasu biyo zuwa Kano dama".
Kallon sa kawai na ringa yi, yanzu shi Hafiz
ɗ
in idan ba soko ba ne da ze yarda a wace dangantakar
Bilal ze yi masa takwara balle har ya saka sunan mahaifin sa ma?
"Kin san ya so ya sakawa yaron sa sunan Dadyn ne amma matar ta ce sunan mahaifin ta za'a saka shi yasa yaji da
ɗ
i sosai yanzu dana ce masa sunan Dadyn na saka" Bilal ya sake fa
ɗ
a yana ruƙo
hannu na.
Duk yan da na so na ci gaba da murmushin da nake yi amma na kasa, ina
ɗ
aki
ɗ
azun na tsinci maganar Hajja sanda take Lanti take tambayar sunan yaron ta ce mata Aminu, ina ji ta ce "lallai, baban ta aka wa takwara kenan?" Ita kuma Hajjan ta ce
mata
"Baban uban gidan sa dai". Dake nesa nake jiyo maganar se na ji kamar ta ce "Babban ubangidan sa" har ina dariya na ce wato Abban ne kuma ya zama uban gidan Bilal ashe Baban ubangidan sa ta ce.
Wani abu naji ya tsaya mun a wuya, na bu
ɗ
e baki amma
na kasa ce masa komai se kawai na zame hannu na daya riƙe na wuce
ɗ
aki ina jin sa yana kira na amma ban tsaya ba. Kwanciya nayi akan gado ina kokawa da abin da ya tsaya mun a wuya, amma ko har idan ta tabbata uban Hafiz Bilal ya yiwa takwara tabbas ya gam
a raina mun hankali ya kuma mayar da ni shashasha da ban san abun da na ke yi ba. Ina jin sa ya shigo
ɗ
akin na rufe ido na, duk yanda ya ringa kira na da tambayar menene na yi masa banza har ya yi fushi ya fi ce ya barni. Kuka na fashe da shi mara sauti.
Bayan magriba Nasir da matar sa suka zo, ina
ɗ
aki har sannan duk shige da ficen da Bilal yake ta yi duk be sake mun magana ba ni ma ban kula shi ba se da suka zo sannan ya shiga ya mun magana. A hannun kujera na zauna muka gaisa da Nasir
ɗ
in kafin na cew
a Aisha mu je ciki taga babyn. Kusan ƙawata ce tare muka yi islamiyya duk da dai ƙawancen namu bai wuce na gaisuwa ba idan ta kama ayi hirar duniya ko yanzun da na auri Bilal aminin mijin ta zumunchin mu be sauya daga yan da yake a da ba dan ya fi maraba d
a alaƙa ta da matar Hafiz akan Aishar Nasir da suka tashi tare.
Ina zaune na jingina kaina da gado na yi zurfi cikin tunani sam ban ji duk maganar da take ta mun ba har se da ta ta
ɓ
a ni sannan na farga.
"Tunanin me kike yi haka Halima?" Ta fa
ɗ
a ta na
kallo na. Na ƙirƙiri murmushi ina gyara zama na na ce
"Ba tunani na ke yi ba bacci nake ji wlh".
"Ai fa se a hankali zaki saba hala yana muku kukan dare?" Da kai na amsa mata alamar eh se ta ce
"Yaya Bilal ne ya ke kiran ki". Hijabin da na cire na may
ar sannan na fita. Daga gefe na tsaya ba tare da na kalle shi ba na ce "gani".
Nasir ya ce
"Hajiya Halima wai me ya faru ne tun da muka shigo na lura akwai yar damuwa a gidan".
"Babu komai Yaya Nasir" na bashi amsa ba tare da na
ɗ
aga kai na ba, Bilal ya
ce
"Wai yanzu kamar Halima bata san wasa ba? Daga fa munyi waya da Oga Hafiz na ce masa Dadyn sa na yiwa takwara bayan mun gama na gaya mata shikenan fa ta fara kumburi har da shiga
ɗ
aki tayi kuka".
Sauti a sama na ce
"Ai tun jiya ya kamata ka gaya m
un sunan Baban abokin ka ka saka ba na mahaifi na ba kaga da be sha wahalar takowa har gidan nan ya duba ka ba"
"Au dama ba dan Allah ya zo duba ni ba saboda na yi masa takwara ne?" Ya taso mun shi ma. Se Nasir ya yi saurin katse shi ya na cewa
"Meye h
aka Bilal? Wace irin maganar shirme ka ke yi?" Ya juyo kaina ganin na miƙe ya ce
"Dawo ki zauna Halima". Kai dan kar ya ce na masa rashin mutunchi ya sa na koma na zauna na ja hijabi na rufe fuska ta.
"Yanzu saboda Allah abun da be kai ya kawo ba kuke s
o ku bawa shai
ɗ
an ƙofa ya hadda sa sa
ɓ
ani a tsakanin ku. Yanzu kai menene na cewa sunan wani can baban abokin ka ka saka masa?"
"Ni fa ba haka na ce mata ba; waya muka yi da Hafiz ya ce amma shi zan yi wa takwara ni kuma na ce masa aa sunan Dady aka sak
a saboda nasan sunan su
ɗ
aya da Abban Halima. Shi kan sa ai yasan wasa ne ba wai dagaske Dadyn nasa ma saka ba amma ai ze ji da
ɗ
i ita kuma dan na bata labari meye abin
ɗ
aukar zafi a ciki saboda Allah?" Bilal ya fa
ɗ
a se na ce
"Saboda na san halin ka ne k
uma ba abun mamaki ba ne dan ka saka sunan Baban Hafiz
ɗ
in. Tun da na
ɗ
auki ciki safa baka ta
ɓ
a siya ka kawo gidan nan ka ce na ajiye ba har zuwa yanzun dana haihu kallon ka kawai na ke yi amma da matar Hafiz
ɗ
in ta haihu ka kashe ku
ɗ
i ka cika leda da kaya
ka kai musu kaga ko ai sun fi ni muhimmanci dan haka ba wani abun mamaki bane idan ka saka sunan Baban sa tun da kuna da wata alaƙa da bani da masaniya".
"Kar ki kuskura ki ce zaki zage ni ko ki mun rashin kunya Halima" ya fa
ɗ
a cikin hasala yana miƙewa
tsaye duk da Nasir na riƙe shi amma be fasa cewa
"Na kai musu kayan da ku
ɗ
in ki na siya balle kiyi baƙin ciki? Ban siya miki
ɗ
in ba kuma ba zan siya ba idan ki na da ƙarfi se ki ƙwata mu ga ni"
"Wlh na fi ƙarfin na yi baƙin ciki akan abin duniya Bilal d
uk abin da kake zaton zaka yi ko ka yiwa wani nafi ƙarfin sa, idan da na ina saka ido na akan abubuwan da kake yi da bamu kawo yanzu ba. Kuma ko ka siya wa
ɗ
an ka ko karka siya kai ta shafa dan idan da ina tsammatar kayi mun wani abu da ban
ɗ
auki cikin ba
ma. Idan ka ga dama ka sauke haƙƙi kan ka ka taimaka ba wani ba" na ƙarasa ina shigewa
ɗ
aki har ina ture Aisha da hayaniyar mu ta fito da ita.
Ina jiyo yan da ya kw bambami kamar ze kama da wuta Nasir na tare shi da alama
ɗ
akin ze biyo ni, a yanda rain
a yake suya duk