Showing 72001 words to 75000 words out of 287295 words
aka zo aka bu
ɗ
e, yanda kasan gidan su haka Bilal ya ringa jefa ƙafa ni kuma ina bin sa a baya, se da muka zauna kan w
asu kujeru masu azabar kyau da laushi kafin na fahimci gidan Abokin sa Hafiz muka dalilin hoton su shida matar sa dake kafe jikin bango. A raina na raya ashe dai ba ƙarya Bilal yake ba idan yana santin irin arziƙin da Hafiz
ɗ
in suke dashi, na ayyana yana d
a ku
ɗ
i haka ko me ya kaishi aikin gomnati kuma bama wani shahararre ba irin su CBN ko Oil ko porth authority naga can aka fi samun yayan manyan ƙasar a ciki.
Tun zuwan da suka mana ni na manta ma da babin su har idan ba shi ya
ɗ
akko zancen su ba, matar
ma da mukayi exchanging number sau
ɗ
aya ta ta
ɓ
a kirana tace sisters
ɗ
in ta sun ji ƙamshin turaren wutar dana bata suna so na ha
ɗ
a ta da me siyarwar (08033950747, kina neman turaren wuta me asalin ƙamshi da kama guri wanda duk wanda ya shaƙa seya tambayi i
n da kika samo shi? Ki tuntu
ɓ
e ta) shikenan bamu sake magana ba. Da ina
ɗ
an ganin ta a whatsapp daga baya kuma na dena ganin ta ma na zata yanda ta sake dani
sanda suka zo zamu yi doguwar mu'amala kamar yanda Bilal yake fata toh kuma hakan bata kasance ba.
Se da mukayi jiran kusan wasu minti goman har seda Bilal ya kira maigidan a waya kafin suka fito yana sa
ɓ
e da baby tana bin sa a baya. Na ringa hasaso sanda suka je mana ni dai bangan ta da ciki ba ko kuma lura ne banyi ba oho dai gashi nan ta haihu. F
arat farat kamar karon farko muka gaisa, tace mun
"Baki da kirki Halima, na rasa number ki ke kuma ko sau
ɗ
aya baki ce kinji ni shiru bari ki ta
ɓ
o ni kiji ya nake ba ko dai zumunchin ne bakya so muyi?"
Kafin na bata amsa Bilal yayi caraf yace
"Ai itama
wayar ta ta lalace ne, tuntuni kuma tace na kar
ɓ
o mata number gurin yalla
ɓ
ai se in manta" Hafiz yace
"Kai dai kace zaka kare ta kawai amma zuwan ka nawa gidan nan kuna ha
ɗ
uwa ai ko ka manta ya kamata ace idan ka ganta ko sau
ɗ
aya ka tuna saƙon da aka baka
". Ni dai sakin baki da hanci kawai nayi ina kallon Bilal jin wannan gingimemiyar ƙarya daya shirga an kuma kama shi. Na sha mamakin jin wai yana zuwa gidan ashe, lallai se a bar Bilal. Ashe shi yasa ba'a ko tambaye mu daga ina ba aka bar mu muka shigo, ko
me yake zuwa yi se Allah.
Mita Suhaila taci gaba dayi ni dai na bita da ban haƙuri ina riƙe da kyakykyawan babyn ta me suna Muhammad Sani sunan babanta suna kiran sa Na'im. Duk tarin kayan ciye ciyen da aka cika mu dasu ruwa ka
ɗ
ai na iya sha a ciki, s
e da muka shiga
ɗ
akin ta ta dame ni da se na fa
ɗ
i abin da nake ra'ayi an mun tunda ta lura ba ni ka
ɗ
ai bace baze yuwu na zo gidan banci komai ba. Dankali nace a soya mun dan na kwana biyu ban ci ba tun azumi. Se bayan sallar Isha'i muka tafi gida shaƙe da
kayan arziƙi harda naman suna kusan cikin ƙaramin bokiti a haka ma tace wai ya ƙare ne haihuwar kusan kwana talatin ni dai nace an gaida masu ku
ɗ
i ko raguna nawa suka yanka se Allah ko kuma dan basu da yan uwa da yawa a Kano ne tunda mu na gidan su Bilal
ma ko hanji ban gani ba cewa akayi mutane sunyi yawa akan naman ya ƙare dama kuma dabbar ƙarama ce batayi auki ba.
"Ki san a Egypt ta haihu se ranar idi suka dawo yace baya so azo ayi ta jagwalgwala masa yaro shiya sa suka yi zaman su se da ya
ɗ
an yi ƙ
wari. Yan gidan su can a Kaduna sukayi suna na zata ma da suka dawo gida zata wuce wai su basa haka ashe ba'a zuwa wankan gida" Bilal ya fa
ɗ
a bayan da muka hau titi. Na gya
ɗ
a kai tare da cewa
"Allah sarki, zuwa wankan gida dama ai ra'ayi ne kuma ma yanzu
duk an dena ai kowa a gidan ta take zama tayi jegon ta"
"Wanda suka de na dai sun dena mu kuwa a dangin mu kwana sittin ma akeyi ba arba'in ba" ya sake fa
ɗ
a, se da juya na kalleshi da mamaki nace
"Wato kwana sittin ma? Kai yanzu idan na haihu se ka yar
da na tafi gida nayi har kwana sittin bana tare da kai?"
Ido
ɗ
aya ya kashe mun kafin yace
"Nasan dai zan azabtu da missing
ɗ
in ki amma ya zanyi da abin da al'ada ta gindaya. Kwana sittin
ɗ
in ma fa bayan an haihu ne wannan lissafin naga matan su Yaya Su
leiman da haihuwar fari da cikin su ya shiga wata tara suke tafiya gida. Kinga kamar Anty Mariya da take ba yar gari ba ina ga se da tayi wata uku ma ita sannan ta dawo ai to ke tun da a kusa kike da
kafin haihuwar zuwa bayan haihuwar se kije kiyi arba'in
biyu kawai, wai ma wata nawa ne cikin yanzu?" Ya ƙarasa yana
ɗ
ora hannun sa akan cikina.
Al'ajabi da mamaki suka sa na kasa cewa komai se bin sa da ido dana ringayi ya kuma yi mirsisi abin sa yaci gaba da tuƙi yana soko mun wata hirar. Mamakin nawa biy
u ya kasu, na farko wai ashe ma ya tabbatar ina da ciki amma ko da wasa ban ga wata murna ko zumu
ɗ
i a tattare dashi ba sannan kuma yanzu lissafi yake idan na tashi haihuwa gidan mu zan yafi nayi arba'in har biyu wato lallai bani da wani muhimmanci a gurin
Bilal. Ji nayi raina ya
ɓ
aci take hawaye ya fara cika mun ido, jin nayi shiru bana amsa hirar da yakeyi yasa ya kamo hannu na yana cewa
"Bacci kika yi ne ina ta magana kinyi shiru?" Aiko kamar ina jira se hawaye shaaa suka
ɓ
alle mun, "subhanallahi Halima
me kuma ya faru?" Ya fa
ɗ
a yana gangarewa gefen titi. Ha
ɗ
e kai nayi da guiwa na shiga rera kuka kamar wadda aka daka.
A karon farko tun auren mu naga rikicewar gaske tattare da Bilal akan
ɓ
acin raina. Fita yayi ya zagayo ta in da nake na durƙusa kamar z
eyi kukan shima yana roƙon na gaya masa mene ne. Se da nayi me isata kafin nace
"Yanzu saboda baka farin ciki da kyautar da Allah yayi mana shi yasa ko a fuska baka nuna mun ka sani ba, ni ka
ɗ
ai nake shirme na kai ko a jikin ka" na sake fashewa da kuka. S
e ya dafa kai kafin ya miƙe yana murmushi ya koma mazaunin sa.
"Na lura so kike kiyi surprising
ɗ
ina shiyasa nake acting along kar na
ɓ
ata miki shiri amma da na san ranki ze
ɓ
aci akan haka da tun sanda na gane nayi magana. Kuma Allah ba wani da
ɗ
ewa akayi
ba, ranar da kika ce na siyo miki mangwaro ne shine nayi suspecting kuma dama na lura ba kiyi period da azumi ba. Nasan akwai shirin da kike yi da ya sa baki gaya mun ba kar nayi magana kuma na lalata miki" yayi maganar ta sigar da ko ba gaskiya ya fa
ɗ
a b
a dole na yarda da abin da yace. Har kaza ya siya mun ƙatuwa da yoghurt me sanyi, da muka isa gida kuwa a hannu ya
ɗ
auke ni har da yi mun rawa wai dan na yarda yana murna da ƙaruwar da muka samu.
Baki san yanda nake son yara bane Halims, ko da kika ga
ina yi kamar ban damu ba tun da mukayi aure bana so na ringa magana ne hankalin ki ya tashi bayan kuma bamu zamu bawa kanmu haihuwar ba amma ban ta
ɓ
a zaton zamu tsallake watan farko na auren mu baki
ɗ
auki ciki ba ke baki ga irin ƙoƙarin da nake yi ba?" Ya
fa
ɗ
a yana kashe mun ido. Da hannu biyu na rufe fuskata ina murmushi, daren ya shiga cikin dararen farin ciki na a gidan Bilal, washe gari da yamma muka je asibiti, an sake mun scanning cikin har yayi wata uku yana shirin shiga na hu
ɗ
u, a hanya bayan mun fi
to daga asibitin yake cemun
"Naga da file
ɗ
in ki na gida kikayi amfani, kuma na san kai tsaye daga account
ɗ
in Abba ake cire ku
ɗ
in magani babu matsala?"
"Ka jika da wata magana kuma wace irin matsala? Duk yan gidan mu kasan asibitin da muke zuwa kenan
nasan idan ma na canza wani ƙarshe hakan ne ze zama laifi shiyasa ban ma yi maka maganar ku
ɗ
in asibiti ba ko wani abu, da har ma na bu
ɗ
e file a wannan asibitin na gaban mu dan can na fara zuwa ma kuma da naga dai nan
ɗ
in ya fi sun kuma fi ma'aikata da kay
an aiki shiyasa ban koma can
ɗ
in ba" na bashi amsa.
Da dare se ga kiran Mama, tun da na jiyo muryar Anty Labiba a background dama nasan wani abun ta ƙulla ilai kuwa bayan mun gaisa Mama tace
"Ɗazu an turowa da Abban ku bill na ku
ɗ
in antinatal shine na
kira naji shi uban cikin ne yace ba ze
ɗ
auki nauyin sa ba ko kuwa kalar naki sanin ya kamatan ne yasa zaki
ɗ
orawa Abbanki haƙƙin da ba nasa ba?"
Nayi shiru na kasa ce mata komai, bata damu ba taci gaba da cewa
"To baze biya ba, idan kina so kici gab
a da awo a nan ki gayawa mijin ki ya yankar muku kati idan kuma yana da wani gurin da yake ganin yafi masa ki koma can tunda kin san dai tsare tsaren su da cin ku
ɗ
i kar ki kuskura ki
ɗ
ora masa abin da kika san baze iya ba" bata ma jira na amsa ba ta mun sa
llama ta kashe wayar ta. Ni dai kacokam na
ɗ
ora laifi kan Anty Labiba nasan ita ta zugata dan dai Abba baze ce baze biya mun ku
ɗ
in asibiti ba ita ma Maman a ra'ayin kanta ba zata hana ba se dai idan mazuga irin su Anty Labiba da Mu'azzam sun shiga lamarin.
Rasa ta in da zan farawa Bilal magana nayi, batun ya biya mun ku
ɗ
in awo a wannan asibitin ma be taso ba dan tsakani da Allah a matsayin da yake kai yanzu services
ɗ
in su sun masa tsada dama dai ace bashi da hidimar kowa ne se tawa da abin da zamu haifa ba
lle ma nasan Bilal a yanda baya maraba da duk harkar kashe ku
ɗ
i bana zaton ko yana da sararin ma ze biya dan da an fara maganar asibiti dama ze ce shi yafi gane aje Aminu Kano ko Murtala sun fi manayan likitoci da kayan aiki privet
ɗ
in nan duk kame kame ne
.
Ganin a sati hu
ɗ
un da aka
ɗ
ibar mun na komawa awo saura kwana biyar yasa nayi ƙundumbalar tarar sa safiyar wata asabar na fa
ɗ
a masa Abba yace ya kamata mu bu
ɗ
e file namu na kanmu ba naci gaba da amfani da na gidan mu ba. Bece komai ba amma fuskar sa
ka
ɗ
ai na kalla na gane sam hakan be masa ba, ranar litinin kuwa be fita aiki ba yace ma shirya muje asibiti a bu
ɗ
e file
ɗ
in, na
ɗ
auka ma zamuje na nan unguwar dana fara zuwa tun farko ina kuma shakkar na masa maganar dan tun ranar asabar
ɗ
in ya shiga
ɗ
aure
fuska be dai tafi hutun kulani daya saba idan munyi fa
ɗ
a ba amma dai magana ma se wadda ta zama dole ce zeyi mun ba sakin fuska ba walwalar da muka saba.
Asibitin Murtala muka je, dama tun da naga mun
ɗ
auki hanya jiki na ya bani amma ban ce komai ba,
dake akwai wata cousin sister su dake aiki a gurin se gashi nan da nan an mun komai har an bani ranar zuwa awo muka juya gida. Gidan su ya sauke ni yace se da yamma zezo mu tafi, tun sunan Fadila zuwana biyu suma a tsaitsaye tare muke zuwa mu tafi tare se
yau ne ze ajiye ni ya tafi tun kuma daga yanda Hajja ta amsa mun gaisuwa nasha jinin jiki na shi yasa yana tafiya na shige
ɗ
akin da Fadila da har sannan bata koma gidan ta ba take na zauna a can. Na fito alwalar sallar azahar na tarar da Hajjan da Mama Usa
ina ƙanwar ta suna zaune a falo suna hira, ban san asalin zancen da sukeyi ba amma yanda suka canza magana da gani na se naji kakaryda gayya sukayi dan naji.
"Allah na tuba a zamanin nan lafiyar
ɗ
an ka ma ace se kayiwa kanka mugunta, yan da haihuwar na
n ta zama se addu'a kana ji kana gani a son ku
ɗ
i se ka kai
ɗ
an ka in da za'a halaka shi kwanan sa be ƙare ba" Mama Usaina ta fa
ɗ
a. Hajja ta karkace tace
"Kema dai kya fa
ɗ
a, shi yasa kika ga nayi tsaye kan wannan yarinyar nace ta taho gida in da mun biye t
a tasu suman da
ɗ
an nan yayi aka fasa kukan mutuwa da can a gurin su take ai da tuni an binne shi wlh. Yana nan kullum yana zarya ta koma nace aa se tayi arba'in biyu tukun ta murmure
ba zata koma da
ɗ
anyan yanka a cuce ni ba. Su dai wanda suka sallamawa d
uniya nasu yayan ai shikenan se yanda suka gani".
Ina alwalar ina jiyo zantukan nasu se suka ma bani dariya, da zamu tafi Fadila take ce mun se sunzo, na
ɗ
auka yawon arba'in take nufi kwana biyu da yin haka ina kwance da hantsi aka buga gida in bu
ɗ
e se
ganin ta nayi sa
ɓ
e da babyn ta ga Abubakar da ƙatuwar akwatin kayan su. Da mamaki na basu hanya suka shiga, se da na basu ruwa da lemo muka gaisa kafin take ce mun
"Kin ganmu se yau ko?, se
ɗ
azu su Hajjan suka tafi jiya ruwa ya hana tafiyar se yau ina ga
ma yanzu sun sauka ai" Abubakar ya duba agogon hannun sa yace
"Ah ya kamata sun isa yanzu ina Kano ina Jos musamman kuma motar gida ai har hutawa ma sun yi yanzu kam, bari naje Anty se Anjima" yayi mana sallama ya fita.
Ni dai ban fahimci kan zancen n
asu ba, bana girki da rana tun da Bilal na gurin aiki amma zuwan Fadila dole na tashi na
ɗ
ora mana. Da wuri Bilal ya dawo ranar, Fadila tayi
ɗ
ai
ɗ
ai a falo yanda kasan sun shekara da zuwa duk inda ka duba kayan
ɗ
an ta gashi da kuka masha Allah tun da suka
zo kunne na be huta ba tun ina mata kawaici ƙarshe na koma
ɗ
aki nayi kwanciya ta ina jiran Yayan ta ya dawo naji ba'asin zuwan su. Yana shigowa kuwa ya fara hargagi, nayi saurin shafa addu'a dan na idar da la'asar kenan na fito na tarar dashi yana mata fa
ɗ
a kamar ze mare ta, ashe kashi yaron yayi akan kujera ta kwantar dashi babu ko zani balle aje batun diaper ko napkin ina doso falon ƙarnin da ban san ko na menene ba ya fara hargitsamun zuciya.
Be amsa sannu da zuwan da na masa ba ya shige
ɗ
aki se na b
i bayan sa ina shiga kuwa ya rufe ni da fa
ɗ
a kamar ni na kwantar da yaron.
"Toh ni yanzu menene nawa a ciki? Ka gaya mun zata zo ne balle na san tanadin da zanyi musu?" Na fa
ɗ
a ina ha
ɗ
e fuska, tsaki yayi, se a lokacin yake ce mun wai Hajja ce ta tafi Jos
gidan ƙanwar ta zata yi sati biyu shine tace Fadilan ta taho nan gidan.
"Se da nace mata kar ta zo ta nemi gurin da zata zauna ko ta koma gidan ta amma taƙi ji to wlh ba zata zauna mun da wannan muguwar ƙazantar tata ba, ni mejego ko wadda ta zamar mun
dole ma se naga kamun ludayin ta kafin nasan zaman da zanyi da ita balle Fadila da duk wanda ya zauna tare da ita se ya gane ƙazama ce ta bugawa a jarida. Ji yanda ta mayar da falon nan se kace na mahaukata toh wlh in kina son ganin farin ciki na tun kafi
n na fito daga wanka ki sallame ta ta kama gaban ta" ya fa
ɗ
a yana wani ka
ɗ
a yatsa kafin ya shige ban
ɗ
aki.
"Lallai ma" na fa