Showing 153001 words to 156000 words out of 287295 words
ta sani in mutuwa tayi ta
ɗ
auki dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.
Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya gaya masa kawai zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial stroke da tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya
gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti goma a zaune kafin ya iya bu
ɗ
e baki yayi magana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?
Dr ne ya ringa
kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya fa
ɗ
a mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta ka
ɗ
a ta ra
ya tayi kukan duk a banza yaƙi fa
ɗ
a mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu ka
ɗ
an ce akan ya sanar mata da ainihin halin da Haliman take ciki.
Bu
ɗ
e ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya
daga bakin ƙofar yana cewa
"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurareka" sai ya miƙe yana cewa
"Wacece"
"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita da sauri dan dama tunda ya
dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi ba ranar da aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal
zata tafi idan ma bata same shi ba sai ta saka an
ɗ
aure Hajja ai dole ya fito duk ma inda ya shiga ya musu bayanin abinda yayiwa Halima.
Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna kallonsu, ta fashe da
kuka tace
"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu ya samu Halima wlh sai na
ɗ
aukar mata fansa akansa". Cikin fa
ɗ
a Abba yace
"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan
Allah ba zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi ma ku wuce gida kawai tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su am
ma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi dai babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka nan duk wanda yazo ya tafi zai ha
ɗ
a nasa kalar labarin da ciwon da zai
ɗ
ora mata, amma dai maganar data fi ƙarfi
ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacce ta fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin
ɗ
aya daga cikin ƙannen Bilal.
BILAL
Bayan daya sauke su kai t
saye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare dashi. Tsakanin sa Allah tun waccen ranar da Halima ta banka
ɗ
o sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a
ɓ
oye. Koda da yake nuna tamkar
komai ba komai bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi ka
ɗ
ai yasan kalar kunya da nadamar da yake ciki a yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya
ɗ
akko ba saboda yasan Halima bata da
ɗ
abi'ar bibiyar ma
sa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da wayar sa balle yanzu daya kulleta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya bu
ɗ
ewa koda ace ma tayi niyyar hakan.
A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace
"Yawwa ga
shi nan ma yazo ai" Hajja tace
"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka amsa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa fa tuntuni nace ka bata ku
ɗ
in motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar farko sai tayi jira wata t
a cika".
Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera ha
ɗ
i da dafe kansa da hannu biyu, Hajja ta shiga tana cewa
"Au ina magana shine zaka shige
ɗ
aki ko ka amsa ni?"
"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya fa
ɗ
a yana gyara
zama, sai ta zauna itama tana cewa
"Saboda me?"
"Mun
ɗ
an samu matsala ne da Halima ta tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke ka
ɗ
ai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace
"Kaji yar abu ta kaz
an uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"
"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saurin katseta, Fadila tayi tsugul tace
"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take kamar na ubanta bata so kowa ya sh
iga sai ita da danginta".
"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya fa
ɗ
a yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta taso masa itama tana cewa
"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta fa
ɗ
a, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi
tunda haka ta za
ɓ
a to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai tayi zama mai lasisi kai kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye komai da anyi magana kace Halima to yanzu
ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin gidanka ya isa kuma haka a canza sheƙa".
Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san a
inihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?
Miƙewa yayi a a sanyaye yana cewa
"Idan ta huce dai na san zata dawo"
"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na
ɗ
auka dangin arziƙi ne ashe duk shigo s
higo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to kuwa ba zata dawo ba kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".
Da wata sabuwar da
muwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife kansa jikin sitiyari ya tafi tunanin ha
ɗ
uwar sa da Jalila.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *
Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki
hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 35*
Amirah ta
ɗ
aga Sharifa data saka kuka
daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Toh lafiya dai?"
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye kan kujera
ya kwanta alamar baccin sa zai cigaba, sai ta juya kitchen ba tareda tace komai ba amma zuciyarta cike da saƙe saƙe.
Kan gado na fa
ɗ
a bayan dana shiga
ɗ
akin dafe da ƙirjina da nake ji tamkar an
ɗ
aure ni da igiya, daƙyar nake fuzgar numfashi, na ringa
juyi a kan gado ni ka
ɗ
ai tsayin lokaci kafin ubangiji ya kawo mun rangwamen abinda nakeji ta hanyar rabani da numfashina na wani lokaci.
A waya Mama ta kira Abba, tambayar sa tayi ko Bilal yace masa wani abu ne tunda ance tare muka zo sai ya ce mata
"
Bai tsaya ba yana sauke musu kayan su ya juya ko gaisawa bamuyi ba"
"Ikon Allah, to mai ya faru?" Ta sake tambaya cikin jimami. Daga can yace
"Ni kam ina zan sani ne Amina? Ba gata nan a cikin gidan ki tambayeta mana", jin kamar ya fara fusata ua saka t
ace
"Toh shikenan sai ka dawo" ba tareda ya bata amsa ba ya katse wayar dan ransa y sosu matuƙa da ko in kulan da Bilal ya musu. Sosai yaji ba da
ɗ
i sanda Alhaji Bala da suke tsaye yace masa
"Wannan ba Mijin Halima bane naga yaja mota bai ko tsaya ya gaid
a mu ba? Koda yake yanda ta shige itama kamar dai akwai matsala dan na lura bata ma ga tsayuwarmu ba, amma shi ai idan
ɗ
an arziƙi ne yaci ko matsala suka samu ya tsaya nan ya maka bayani ba yaja mota ya tafi ba".
Wannan maganar ta dame shi har ta saka ya
fasa komawa cikin gidan da yayi niyya ya sallami Alhaji Balan kawai ya wuce inda zashi ya a tafe kuma yana tunanin dalilin zuwan Halima da sassafen nan.
Sai gurin ƙarfe tara Mama tace Amirah ta shiga ta kirawo Halima ta karya lokacin har tayiwa su Al'
amin wanka sun ƙoshi sun shiga sabgogin su, ihun da Amirah ta fasa bayan shigar ta
ɗ
akin ya saka Maman tashi da sauri tamkar zata hantsila ta shiga
ɗ
akin, gabanta ya yanke ya fa
ɗ
i ganin Amirah tsugunne kan Halima tana girgiza ta haditda kiran sunanta amma
ko gezau bata motsa ba, cikin tashin hankali ta isa gaban gadon ta
ɗ
agota jikinta ta shiga jijjigata da ƙarfi amma bata koyi alamar zata farka ba.
"Ta mutu innalillahi mun shiga uku Yaya Halima ta mutu" Amirah ta fa
ɗ
a hannu biyu akai cikin matsanancin
kuka Mama dake rungume da Halima ta
ɗ
aga mata hannu tana cewa
"Bata mutu ba fita ki kira Mu'azzam, kiyi sauri dan Allah yazo mu kaita asibiti" ta ƙarasa tana ƙoƙarin bu
ɗ
e idanun Haliman. Da gudu Amirah ta nufi ƙofa sai kuma ta juyo cikin kuka tace
"Kin m
anta ya tafi makaranta tun
ɗ
azu yana da exam yau?"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Amirah ki fita kowa kika gani ki kira mu kaita Asibiti" Mama ta fa
ɗ
a tana fashewa da kuka itama. Tareda Samari biyu Amirah ta dawo wanda a waje ta taresu sun taho a
mota su suka
ɗ
auki Haliman suka fito da ita daga Mama har Amiran babu wanda ya tsaya neman koda Takalmi suka biyo su Zainab na kuka riƙe da Sharifa haka Al'amin dukda ba wai sanin mai yake faruwa yayi ba kawai ganin sunayi ya saka shima ya kama. Suna ƙoƙa
rin sakata a motarsu Suraj ya iso ƙofar gidan dan dama tare suka fita da Abba ya kaishi Airport zai tafi Lagos, motar sa Mama tace su sakata suka shiga ita da Amirah ya ja motar da gudun gaske suka nufi asibiti.
Bayan tsayin lokacin dana
ɗ
auka tsakanin
mutuwa da rayuwa na farka, na bu
ɗ
e idanuwana da naji tamkar an manne mun su da super glue daƙyar na iya bu
ɗ
e su na kalli in da nake saidai ban fahimci komai ba hakan ya saka na sake mayar da idanuwan nawa na kulle ina jin sautuka sama sama kamar daga can
nesa. Mama dake zaune kan kujerar dake kusa dani ta miƙe da sauri saboda ƙafata dana motsa, ta kira sunana, dukda ba wai na fahimci mai ta fa
ɗ
a ba sautin da naji ya saka na sake bu
ɗ
e idona na sauke akan fuskarta. Ta kama hannuna hawaye na ziraro mata tace
"Kin farka Halima?" A hankali tamkar mai koyon magana na kira sunanta a rarrabe "Ma..ma" ha
ɗ
i da matsa hannunta data riƙe nawa dashi. Cikin kuka mai ha
ɗ
e da dariya ta amsa da
"Na'am Halima kin farka? Alhamdulillah". Ji nayi maganganunta suna hau mun k
ai sai na sake mayar da idona na rufe tayi azamar kamo fuskata tana cewa
"Ki tashi dan Allah kada ki sake komawa Halima dan Allah ki bu
ɗ
e idonki ko hankalina zai kwanta" ta ƙarasa cikin kuka. Na sake bu
ɗ
e idona na kalleta, tabbas naga ƙauna mai tsanani ha
ɗ
i da tausayi cikin ƙwayar idanunta dake tsiyayar da hawaye, kalaman Bilal da ya ce "Da uwarki nayi zina" suka dirar mun tamkar saukar mashi take wani abu ya taso ya sake tokare mun maƙogaro, ban iya yin abinda ta buƙata ba na sake mayar da idanuna ruf na
rufe su sai ta saki hannuna ta nufi ƙofa kusan da gudu ta fice daga
ɗ
akin ba jimawa suka dawo tareda likita da Nurses biyu. Sai da ya gama dubani kafin ya kalleta cikin kalaman kwantar da hankali yace
"Kiyi haƙuri Hajiya na fa
ɗ
a miki jikinta yana da buƙ
atar hutu sosai zata farka idan lokacin hakan yayi in sha Allahu ki daina damuwa zata samu lafiya da yardar Allah"
"Likita ta farka fa, ta bu
ɗ
e idonta har magana tayi mun kafin ta sake komawa dan Allah likita kayi wani abun yarinya ta ta farka kaifa ka
ce mun awanni ka
ɗ
an amma gashi kwana biyu kenan bata farka ba". Kwana biyun data ambata ya saka na sake bu
ɗ
e idona na kalle su, hannu biyu ta
ɗ
aga tana cewa
"Alhamdulillah, ka gani ko idonta biyu". Ganin tana ƙoƙarin
ɗ
ago ni ya saka ya dakatar da ita, a h
ankali ya kira sunana na kalle shi yace
"Kina jina Halima?" Nayi shiru badan bana jin sa ba sai dan bansan ta yanda zan amsa masa ba. Bakina yayi mun nauyi tamkar an
ɗ
aure mun harshe. Cikin taushi ya sake kiran sunana da maimaita tambaya ina jinsa amma
na kasa amsawa. Mama ta fashe da kuka tana cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr mai ya samu yarinyata dan Allah kayi mun bayani ni Musulma ce koma menene zanyi haƙuri na kar
ɓ
i ƙaddarar data samemu".
"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iy
a shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi tsammanin nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da
kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take"
ɗ
aya
ɗ
aga cikin Nurses
ɗ
in ta fa
ɗ
a a hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so in tsayar da ita amma kuma banida ikon yin hakan.
Wata yar fitila likitan ya kunna ya
shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lumshe idona kafin na bu
ɗ
e nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa
"Yawwa H
alima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi jimm dan kwata kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, s
ai da ya sake maimaitawa kafin na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu. Hamdala yayi kafin ya kar
ɓ
i folder dake hannun Nurse yayi rubutu ya bata yace taje ph
armacy ta kar
ɓ
o abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.
Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba
ɗ
ayan su kallo
ɗ
aya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina
nayi karfin halin tattaro kalmomi na ha
ɗ
a na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gya
ɗ
a masa kai lokaci
ɗ
aya kuka ya kwace mun Abba ya rungume ni yana cewa
"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru