Showing 87001 words to 90000 words out of 287295 words

Chapter 30 - KURA A RUMBU COMPLETE

/>
Gida Bilal ya juya, yana shiga ya tarar da Hajja na saka hijabi; da mamaki ya kalle ta yace

"Unguwa zaki je ne Hajja?"

"Yanzu Fainusa tayo waya tace mana Halima ta haihu s

hine zamu je mu gano su" ta bashi amsa. Se ya wani

ɓ

ata fuska yace

"Yanzu an kira ki ne an gaya miki haihuwar balle ki

ɗ

auki ƙafa ki tafi? Ke da Fainusa waya fi zama a haƙƙu da su kira? To ki koma

ɗ

aki kiyi zamanki ko ni da nake uban

ɗ

an basu kira sun gay

a mun ba nima a wai wai naji a gari dan haka babu in da zamu je, idan sunga muna da muhimmanci sun san inda zasu same mu ai zasu zo" ya fa

ɗ

a yana shigewa

ɗ

akin Hajjan.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fict

ional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yard

a wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*

1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 20*

Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na

cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo duba mu ya

ɗ

auki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm. Nan

da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shai

ɗ

an da saƙe saƙe tuni har na fara hasaso wai babyn ma mutuwa zeyi. Ina kwance nake wannan tunanin se kawai na tsinci kaina da fashewa da kuka kamar har abun ya fa

ru ne.

Gwaggo, ƙanwar Abbanmu ta taso da sauri ta iskeni tana cewa

"Lafiya Yaya? Ko ciwon ciki ne?" Nan hankalin sauran mutanen

ɗ

akin ya dawo kaina duk suka shiga jera tambayar meya same ni? Ko wani gurin ke yi mun ciwo ni kuwa kamar suna tunzura ni n

a samu guri na cigaba da Sheƙa kuka ba ji ba gani.

"Ku rabu da ita babu inda yake mata ciwo baze wuce akan wancan mijin nata da be san daraja da ƙimar ta ba take wannan kukan. Ace ka haihu gari

ɗ

aya ba wai daga wata nisan duniya ba miji ya kasa zuwa ya du

ba halin da kake ciki ko abinda ka haifa ba? Ko da yake ita ta jawa kanta ba wani da dan haka namu ido".

Maganganun ta suka bu

ɗ

e musu fili kowa ta shiga tofa albarkacin bakinta dukdai be wuce zagin Bilal da Ahalin sa ba.

"Ai wlh ko a wata jaha suke da

ga dai haihuwar ta tun jira da yamma zuwa yanzu azahar yaci ace ko mutum biyu sun taso sun zo amma ce gari

ɗ

aya ko shi uban cikin be zo ba balle wani nasa yayi kara shima yazo? To Alla ya rufa asiri, duk irin abunda aka ringa hango mata kenan soyayya ta ru

fe mata ido shima Yaya Aminu ya biyewa Yaya Salamatu, dan kai ka auri mace ka mata halacci se aka ce yarka ma idan tayi irin auren zata dace? Tsabar lalacewa ma fa ase daidai da ginin gidan shi ya bashi maƙudan ku

ɗ

a

ɗ

e ya ƙarasa duk a shawarar Yaya Salamatu

. Wannan yaron yace mun a gurin sa aka siyi ƙofofi da wundunan gidan yace saboda samun guri wanda ma sukayi magana da Yaya Aminun za'a bashi da yaje se cewa yayi basu yake so ba ya nuna wasu daban kuma Yayan yace a bayar. Abun nan ya da

ɗ

e yana cimun rai ka

wai nayi shiru ne dan kar ace a baki na magana ta fito".

Murmushi kawai Anty Labiba ta ringa yi tana gya

ɗ

a kai irin abun ya mata da

ɗ

i, Anty Rakiya wadda yayan maza suke da su Abba tace

"Kuma shine saboda su

ɗ

in ba gadon arziƙi bane yayi mata lefe a led

a; wato bata kai ko a cikin ku

ɗ

in da uban nata ya bashi ya ragi wani abun ya siya mata akwati ba"

"Ke kuwa idan suka zubo a akwati ai abun tsiyar ƙara yawa zeyi, yo ina abun zubawa a akwatin ma banda abinki Rakiya? An dai cuci yarinya kawai an kaita an ba

ro" Gwaggo Hajiyayye ta fa

ɗ

a. Se Anty Labiba tayi caraf tace

"Ta dai cuci kanta waya mata dole a auren sa?"

Dana gaji da sauraron cin mutunchin da suke mun se kawai na tashi daga kan gadon na shige ban

ɗ

aki. Tunani nake dagaske Abba ne ya bawa Bilal ku

ɗ

in daya ƙarasa ginin sa ko dai surutun su ne kawai?

Da ace Anty Labiba ce ta fa

ɗ

a zan iya cewa duk cikin son ta cusa mun tsanar Bilal ne amma kuma banga hujjar da ze saka Anty Rakiya tayi ƙarya cikin wannan maganar ba, a karon farko naji haushin Bilal h

ar zuciyata. Idan har ta tabbata dagaske Abba ne ya bashi ku

ɗ

in nan amma har ya iya bu

ɗ

e baki ya kira ni da yar matsiyata ba sau

ɗ

aya ba sau biyu ba lallai Bilal ban ma san a wane aji ya kamata na ajiye shi ba. Kuka na se ya canza salo, dama

ɗ

azu na jin da

ɗ

i ne yanzu ko dana samu dalili me ƙarfi se na shiga kukan tausayin kaina. Bubbuga ƙofar ban

ɗ

akin da akayi yasa na wanke fuskata na fito.

Abba, Baba Salahu se abokin Abba Baba Lawan ne suka zo, ban yarda mun ha

ɗ

a ido ba na gaishe su Baba Salahu ya shiga

tambayar meya same ni ido na ya kumbura ba kunya Anty Labiba tace wai kumburin haihuwa ne.

"Shine haka har ido kamar wadda tasha kuka?" Baba Lawan ya tambaya. Ni dai shiru nayi bance komai ba, basu jima ba suka tafi. Haka yinin ranar ya doshi ƙarewa har

la'asar banga Bilal ba ban kuma ga wani daga

ɓ

angaren sa yazo ba.

Zuwa lokacin har na rasa wane tunani zanyi akan ma'anar abinda Bilal

ɗ

in yayi mun. Da kunne na naji Abba yana fa

ɗ

ar ya kirashi be amasa ba kuma ya tura masa da saƙo tun sanda aka kawo ni

asibiti; sannan ni ma da kai na na kira shi da wayar Anty Labiba be amsa ba. Nama rasa wane tunani zanyi, shin yana sane yaƙi amsa wayoyin kuma yaƙi zuwa ko kuwa akwai wani al'amari daban da bamu sani ba?

Haka muka sake kwana; ƙarfe goma na safiyar was

he gari aka sallame mu. Gidan mu aka wuce dani, a

ɗ

akin Mama na kwanta dan na shiga tsohon

ɗ

aki na in da yake na Amirah a yanzu ganin kayan ta a barbaje yasa na fahimci ba a nan zamu zauna ba ƙila ko

ɗ

akin baƙi za'a gyara mun.

Mama Fauziyya ce tayi mun

wanka, nasha kuka amma kuma naji da

ɗ

in jiki na duk gajiyar dake tare dani ta warware. Se da naci abinci kafin na kwanta, bacci nake so nayi se dai tunanin daya cunkushe mun zuciya ya hanani.

Gaba

ɗ

aya zuciyata babu da

ɗ

i, kwanaki biyu daya kamata su zama

mafiya farin cikin a rayuwata sun juye zuwa na akasin haka. Ace na haihu har kwana biyu uban

ɗ

an yana raye amma be iya zuwa in da muke ba, idan wani ne ya gaya mun haka zata iya kasancewa tabbas bazan yarda ba se gashi ni da kaina na shaida hakan. Amma da

na tafi lissafin baya tun daga goyon cikin da yanda sam ban shida irin

ɗ

oki da farin cikin da ƙawaye na suke bani labarin mazajen su na yi ba a lokacin da suka samu ƙaruwa se banyi mamaki da abinda ya aikata mana a yanzun ba.

Na tuna sanda Hansa'u ta h

aihu, yar da a haifa ita ce ta goma sha biyu a jerin yayan mijinta amma hakanan ya baro abin da yake yi a Dubai in da yake kasuwancin sa ya taho a ranar ya duba su sannan ya juya ya tafi. Irin soyayyar da nayi tunanin a gurin yaro matashi sabon jini ka

ɗ

ai

ake samun ta se gashi rayuwar Hansa'u da Mijin ta ta ƙaryata tunani na.

Sau tari har bana son bu

ɗ

e status

ɗ

in ta saboda abubuwan da nake cin karo dasu da suke sosa mun zuciya har nake jin kamar da gayya ma take

ɗ

orawa saboda na gani. Duk da shekarun mi

jinta baya kunyar su fita tare su je guraren Shaƙatawa a ciki da wajen ƙasar nan suyi hotunan da kana kallo baka buƙatar a fa

ɗ

a maka su

ɗ

in masoya ne dake cike da farin ciki. Tun da na auri Bilal sau

ɗ

aya zan ce mun ta

ɓ

a zuwa wani guri shima ba wai haka na

n ba dalili ne ya kaimu birthday budurwar wani abokin aikin sa Patrick da akayi a wani garden. Duk sanda na roƙe shi da mu fita wani guri ko da gidan zoo ne mu sha iska se yace ba yanzu ba.

"Yanzu ke ba zaki ji wani iri ba na

ɗ

auke ki a mashin kawai muj

e kowa suna zuwa a manyan motoci masu aji?" Abin da yake fa

ɗ

a mun kenan duk sanda na masa maganar. Na kan yawan tunasar dashi akan

"Shi farin ciki babu ruwan sa da wadata. Shi yasa ma nake ce maka muje irin guraren da nasan munfi da yawan wa

ɗ

an da zamu ta

rar wadata ƙila mu zama abin kallo ma a gurin su da bayar da sha'awa. Sannan duk ma inda muka ga damar zuwa ina ruwan mu da masu zuwa a motoci? Se ta yuwu muje mu kashe dubu

ɗ

aya wanda yazo a ƙatuwar motar se dai kawai yayi zagaye ya tafi ba tare da ya kas

he ko sisi ba ni ban san me yasa kake yawan damuwa da maganaganun mutane ba ko kallon da mutane zasu maka. A baya da kake

ɗ

auka ta a mashin

ɗ

in muke zuwa me yasa baka ta

ɓ

a tuna za'a raina ka ba se yanzu?"

Duk sanda mukayi haka daga ƙarshe abin rigima ma

ganar take komawa yace na raina ƙoƙarin sa ina hangen rayuwar da wasu sukeyi; idan nayi haƙuri nima wata rana zamu taka matsayin fa nake hange hangen shi kenan se ya

ɗ

auki fushi idan ba'a yi sa'a ba se anyi kwana biyu ina bin sa da rarrashi da ban baki kaf

in ya sakko muci gaba da walwala a gidan.

Ƙ

arfe biyar bayan nayi wankan yamma babyn ma anyi masa ina zaune ina cin gasassun yan shilan da Anty Labiba ta ajiye mun Mama ta shigo

ɗ

akin.

"Kiyi sauri ki ƙarasa kada magriba tayi ku samu ku tafi" ta fa

ɗ

a da

ga tsayen da take.

Kallon ta nayi da rashin fahimtar abinda maganar ta take nufi. Kamar ta fahimce ni fuska babu walwala tace

"Abban ku yace ki koma can gidan ki". Se na ture kwanon gabana na fuskance ta da kyau nace

"Me yasa Mama?"

"Saboda haka y

aga dama". Ta bani amsa, take hawaye ya

ɓ

alle mun dan dama ba nisa sukayi ba, na karanci akwai tausayi na akan fusakar ta amma ta dake tace

"Tun farko abinda na gudar miki kenan Halima amma kika kasa ganewa. Se kije kiyi ta haƙuri, ita dama rayuwa haka ta

ke kowa da kalar nasa ƙalubalen" daga haka ta fita ta barni na ha

ɗ

a kai da guiwa na shiga kuka kamar wadda aka doka. Tuntuni dama dashi da iyayen sa kullum cikin yi mun

shagu

ɓ

en na tafi gida na haihu sukeyi yanzu kuma se ace na koma bayan ko da na haihun m

a basu zo ba alamar basu damu da ƙaruwar da muka samu ba kenan.

Kukan dana ringayi be hana Mama Fauziyya da Anty Labiba mayar dani gidan Bilal ba. A hanya suna ta hira abun su ni ko na ha

ɗ

a kai da window ina share hawaye. Gaskiya ba'a kyauta mun ba, an

ma nuna neman kai kawai akeyi dani shi yasa za'a tattarani kwana biyu da haihuwa ace za'a mayar dani gidan miji. Da muƙulli na sukayi amfani suka bu

ɗ

e gidan. Compound

ɗ

in kamar ya shekara babu mutum a ciki ƙura da ganyayyekin bishiya kasancewar sanyi ya f

ara kankama. Yanayin dana ga gidan yasa na fara shakkar anya kuwa Bilal na gari? Domin Bilal

ɗ

in dana sani in dai ba sharafa yakeyi ba babu yanda za'a yi ya bar muhallin da yake zaune ciki a haka.

Yanayin falon ya tabbatar mun da zargina na Bilal baya

nan, hatta da fasassun tangaran da taliyar daya zubar tun shekaran jiyan suna nan ba'a kwashe ba. Ɗaki Mu'azzam ya shigar mana da kayayyakin baby wanda duk a gidan mu aka siya tunda ko abun susar kunne banje dashi ba. Anty Labiba da Mama Fauziyya suka gyar

a gidan tas, kafin a kira Magriba har tsakar gidan an nemo almajirai sun share sun wanke. Har bayan sallar isha'i kafin sukayi mun sallama zasu tafi, na fashe da kuka ina cewa

"Yanzu tafiya zakuyi ku barni ni ka

ɗ

ai?"

"To zama kike so muyi Halima? Da c

an dawa kike zaune ba ke da mijinki bane?" Mama Fauziyya ta fa

ɗ

a. Na girgiza kai ina cigaba da kukan nace

"To ai yanzu baya nan Mama, kuma ko yana nan da da yanzu ai ba

ɗ

aya ba ni ban ma san yanda zan kula da yaron nan ba kuka yakeyi cikin dare Anty Labib

a ce take goya shi kuma idan safiya tayi ya zan masa wanka nima ya zanyi?" Na ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa. Shiru suka yi da alamu kukan nawa ya ta

ɓ

a su. Mama Fauziyya ta zauna kusa dani ta jani jikin ta cikin rarrashi tace

"Mijinki bashi da k

irki Halima. Ta yaya za'ayi ace ki haihu har kwana biyu amma be zo ba wani nasa be zo ba a gari

ɗ

aya ba wai can nisan duniya ba? Kin fi kowa sanin sauƙin kai irin na mahaifin ki amma tunda har yayi fushin da yace ki dawo gidan ki tabbatas abun ya

ɓ

ata masa

rai. Da kansa ya kira Bilal ba wai wani ya saka ya kira shi ba amma be amsa wayar sa ba har yanzun nan kuma be biyo sahun kiran ba, dama ai ga akan yanda kuka rabu har kika tafi gida ko? Kiyi haƙuri ki jira shi ya dawo duk yanda kuka yi ki kira waya domin

mahaifin ki yace ba zaki koma ki zauna masa a gida ba har se da dalili, wato idan sakin ki yayi".

Da sauri na kalle ta jin abunda ta fa

ɗ

a daga ƙarshe, wai Bilal ya sake ni. Baki na har rawa yakeyi nace

"Mama y sake ni kuma?"

"Yanzu bayan wannan kora

da halin daya miki har kina tunanin cigaba da zama dashi ne Halima?" Mama Fauziyya ta fa

ɗ

a kusan da mamaki, se na shiga girgiza mata kai nace

"Bafa fa

ɗ

a mukayi ba Mama, kuma ni jiki na ma yana bani ba lafiya Bilal yake ba ai dai kunga gidan nan beyi kama

da wanda mutum yake zaune a cikin sa ba tun da har can

ɗ

akin sa kun duba duk babu alamar yana kwana a gidan nan. Ni tsoro nakeyi koma wani mugun abu ne ya same shi" na ƙarashe cikin sabon kuka.

Yanda Mama Fauziyya ta bu

ɗ

e baki ze baka tabbacin ta rasa a

bin fa

ɗ

a ne, a fusace Anty Labiba tace

"Dan ubanki ai se ki bazama ki binciko in da ya shiga. Ki tashi mu tafi idan kuma baki gaji da kwasar takaicin bane se ki zauna ki taya ta kwana ni dai nayi nan" daga haka ta nufi ƙofa itama Mama Fauziyyar ta miƙe ta

bita ganin haka yasa na rufa musu baya ina fashewa da sabon kuka nace

"Ni wlh bazan iya zama ni ka

ɗ

ai ba gida zan tafi"

"Ai kin san hanta maza tafi amma karki kuskura naga ƙafar ki kusa da motar mu ki jira idan muka tafi se ki biyo bayan mu" cewar Mama

Fauziyya. A bakin ƙofa na durƙusa bayan fitar su na ringa rusa kuka baji ba gani, se da baby na ya fara kuka kafin na tashi daga gurin na

ɗ

auke shi daga kan kujerar da yake kwance na zura masa ido ina kallon sa hawayen dake saukar mun suna

ɗ

isa akan fuskar

sa. Rungume shi nayi ina cigaba da kukan. Ban ma san me ya kamata nayi ba, an shiga an fita tsakanina da Abba na kawai dan ba abinda za'a gaya mun na yarda wai shi yace a dawo dani gidan nan.

Jin yaƙi yin shiru yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login