Showing 18001 words to 21000 words out of 287295 words
yana sakin numfashi ban san lokacin dana fashe da kuka ina cewa
"Haba dan Allah kar ka mun haka, kana
ina yanzu? Kaje asibiti ko kana gida?"
"Ina gida Halims bazan je asibiti ba tun da na fahimci rayuwa ta ki ke nema gara kawai na sauƙaƙa miki in bar miki duniyar se ki fi jin da
ɗ
i kamar yanda kika ce na fita daga rayuwar ki". Ban tsaya sake jin abin da z
e fa
ɗ
a ba na kashe wayar na figi jaka ta dake kan gado nayi ƙofa, Hansa'u ta biyo ni tana tambaya ta lafiya amma ban tsaya ba na nufi get se kawai ta biyo ni. Se da muka hau adaidaita kafin cikin kukan da nake na gaya mata Bilal ne bashi da lafiya. Bata iy
a riƙe kanta ba ta zabga tsaki tace
"Bilal bashi da lafiya Halima shine kika riki ce haka kina kuka?"
"Ban gane na riki ce ba? In ce miki mijin da zan aura bashi da lafiya har ki tambayi ba a sin rikicewa ta ko kuka?" Na hayayyaƙo mata. Se ta sake yin t
saki tace
"Wlh ƙarya yake, yanzun nan daga gidansu Maryam Abdullahi nake har gaisawa mukayi yana ƙofar gidansu suna hira da Abokanan sa".
Nayi mata banza ina ci gaba da share hawaye tun da ba son sa take ba ai dama komai ma daya shafe shi zata ce ƙarya
ne. Ban ko tsaya kar
ɓ
ar canjin adaidaitan ba na wuce ƙofar
ɗ
akin sa na shiga bubbugawa. Abubakar ƙaninsa ya fito daga cikin gida gani na yasa ya tsaya.
"Yaya Bilal
ɗ
in ne bashi da lafiya?" Ya tambayeni cikin mamaki bayan dana tambaye shi ina Bilal. Se na
ciro wayata na shiga kiran layin sa, Nasiru ne ya amsa yace suna asibiti jikin nasa ne ya riki ce"
"Subhanallahi, babu jimawa fa Yaya Nasirun ya kira shi duk muna tare a cikin gida bari na shiga na gayawa Hajja se nazo muje asibitin" Abubakar ya fa
ɗ
a yan
a komawa cikin gida.
Nasan kara kawai Hansa'u ta mun ta bini asibitin, na ringa rusa kuka ganin Bilal kwance da robar ƙarin ruwa a ido na se naga ya rame yayi baƙi Abubakar da Hajjansu nata jimamin to me ya same shi tun da su dai lafiya lau ya fita dag
a gida se Nasiru ne yace musu dama kwana biyu yana masa ƙorafin ciwon kai da ƙirji shine suna zaune suna hira wai kawai suma. A
asibitin na wuni sur har sallar isha'i se da Abba suka zo tare da su Mu'azzam kafin na bishi muka tafi gida Hansa'u dama ko mint
i goma bata yi ba da mukaje tace mun zata wuce. A hanya Abba yake ce mun wai typhoid da malaria ne suka kwantar dashi lokaci
ɗ
aya kamar yanda likitan daya tambaya ya fa
ɗ
a masa. Nayi shiru a raina na raya ƙila basa so a fa
ɗ
i ainihin abinda yake damunsa ne d
an ni likitan ce mun yayi zuciyar sa ce ta kumbura, wai dama yana da matsalar zuciya amma duk tsayin zaman mu shine ya
ɓ
oye bai ta
ɓ
a gaya mun.
Na share hawayen daya gangaro mun ta gefen ido na sanadin tunanin wai Bilal na da matsalar zuciya da nayi. In
da na sani ina zan masa boren da nayi waccen ranar har in share sati ba tare da na amsa wayar sa ko na bari mun ha
ɗ
u ba. Ko kallon in da nake Mama bata yi ba da muka koma gidan, ban iya bacci da kyau ba cikin dare duk motsi na hankali na yana kan Bilal ga
wayarsa dama tun ina can Nasiru ya kashe a dafe na kai safiya tun farar asuba kuwa na shiga kitchen na fara ha
ɗ
a masa kunun gya
ɗ
a da alala na ha
ɗ
a masa da farfesun kayan ciki. Saboda kar Mama tayi fa
ɗ
a na duka gida nayi kan bakwai na gama na shirya wanda z
an kai masa na ware na gida sannan na wuce wanka a gurguje. Ina fitowa naji Mama na fa
ɗ
a
"Saboda jiya ban ce mata komai ba shine yau zata
ɗ
ibar mun kaya tayi girki ba tare da ta sanar mun ba to babu in da za'a kai abuncin nan" na jiyo tana fa
ɗ
a. Nayi sau
rin zura doguwar riga ba tare da na shafa komai a jiki na ba na saka hijabi na fita. Daga ne sa na gaishe ta ta galla mun harara tana cewa
"Wato bakya jin magana ko Halima?"
"Yanzu Amina ba zan ce magana ta wuce ki barta haka ba se kin sake tadawa?" A
bba ya katse ta, se ta juya kansa tace
"Dama ai kai baka ganin rashin dacewar duk abinda takeyi a gidan nan. Yanzu mutunchi ne ace ta tafi ta tare a asibiti tun hantsi ina ga da baku je ba ma a can tayi niyyar ta kwana ko? Sannan yanzu kaga uban abincin d
a tayi zata kai musu kan ta aka fara soyayya ko kuwa da zata ringa abu kamar mara cikakken saiti. Badai namiji bane, ka bishi a sannu ma ya ka ƙare balle ka nuna masa ba zaka rayu idan babu shi ba"
"Ni da kika nuna mun ba zaki rayu idan babu ni ba nayi
miki butulci ne Amina da har zaki fara kafa hujja da halin Maza?" Abba ya fa
ɗ
a, tuni na sulale nayi kitchen jin maganar na neman canza salo. Na bi ta ƙofar baya na fice ina zagayowa muka ci karo da Mama ta kuwa falla mun marin da da wayo na bazan iya tuna
sanda ta dake ni ba.
"Har idan na isa dake Halima umarni nake miki ba shawara ba ki fita daga sabgar yaron nan, ban yarda ba kuma ban amince da cigaban tarayyarki dashi ba" Mama ta fa
ɗ
a cikin fushin da ban san tana da shi ba. Hankalina ya tashi matuƙa,
na aje kwandon hannuna na fashe da kuka ina cewa
"Mama me yasa zaki ce haka me Bilal yayi miki?"
"Ba abin da ya mun amma ina kallo bazan bari ki tura kanki a rami ba. In sha Allahu idan ma da ƙulumboto ya nemi soyayyar ki zan ci gaba da kaiwa Allah kuka
na ya warware komai ya raba ki dashi. Na gaji, wannan wane irin bala'i ne? Bilal se kace na billahillazi bakya ji bakya gani akansa? To ba dani ba ko kina so ko bakya so dole ki barshi tun da ba hauka akeyi ba".
Kuka na fasa harda kururuwa Abba ya fito
cikin
ɓ
acin rai yace
"Baki ji ba kenan?"
Ta wuce ciki ba tare da ta amsa masa ba tana jaddada mun wallahi na fita se na sha mamakinta yau.
"Dan Allah Abba ka bata haƙuri na fa
ɗ
a ina kama ƙafarsa, seya
ɗ
ago ni yana cewa
"Ya isa, ki koma ciki tunda tac
e karki fita bari na taso Ibrahim se yaje ya kai musu abincin". Yanda kasan wadda aka wa mutuwa haka na shiga
ɗ
aki na ringa kuka akan hanani komawa dubo masoyi na da akayi. Wuni sur ban fito daga
ɗ
aki ba ko abinci ban iya kaiwa baki na ba seda mukayi waya
da Bilal ya gaya mun an sallame shi se lokacin na tsagaitawa kaina har na fita na nemi shayi na sha.
"Ba wasa nakeyi ba bana son auren nan Alhaji kwata kwata abin yaƙi kwanta mun a rai. Wlh ba ƙaramar murna nayi ba da ya
ɗ
auke ƙafarsa ya dena zuwa itama
naga ta fita a batunsa, ni da ka sani da suka ce zasu zo kawai ku ce musu an mata miji tun da dama tun asali ai ba ku
ɗ
i suka kawo ba magana kawai akayi" Hajiya Amina ta fa
ɗ
a bayan da suka zauna da Alhaji Aminu yayi mata magana akan rashin dacewar abin da
tayi a ganinsa.
"Me yasa zaki ringa fa
ɗ
ar haka Amina? Ban ta
ɓ
a zaton zaki shiga layin wa
ɗ
anda basa son ha
ɗ
i tsakanin Halima da yaron nan Bilal ba. A duk sanda na kalle su rayuwarsu ta kan tuna mun a yanda muka fara tamu tarayyar" se tayi saurin katse sh
i tace
"Karka fara ha
ɗ
a rayuwar mu da tasu domin akwai banbanci"
"Wane banbanci? Irin son da kika nuna mun? Wace irin sadaukarwa ce baki mun ba Amina? A sanda na nemi auren ki ban ko kama ƙafar Bilal rufin asiri ba. Bana manta ƙanin da yan gidanku suka
mun me riga
ɗ
aya. Kin ciyar dani, kin tufatar dani kin kuma zauna dani cikin halin matsi har muka kawo yau menene banbanci cikin abinda yake faruwa a rayuwar Halima yanzu?" Alhaji Aminu ya fa
ɗ
a cikin kwantar da murya.
Hawayen da suka tarar mata a ido ne
suka fara sauka, ta saka gefen hijabinta ta share tana cewa
"Ko da na so ka na so ka ne a matsayin ka na Aminu kai ma ka so ni a Amina. Babu son rai ko so. zuciya a tarayyar mu. Baka dashi amma kowa ya shaida kai me zuciya ne kuma kana kan tafarkin nema.
Baka ta
ɓ
a roƙo na nayi maka abu ba kuma na sani a duk sanda na maka abu kana kar
ɓ
a ne saboda ka faranta mun kuma a duk sanda Allah ya baka dama ka kan kwatanta kyautata mun kaina daidai yanda zaka iya. Mahaifi na ya fa
ɗ
a mun ya baka aure na saboda ya yard
a da kai ya kuma yarda da nagartarka ya kuma san akwai da babu ba zaka wulaƙanta masa ni ba saboda ya yarda tsakani da Allah kake so na. Wace madogara kake da ita da har ka yarda zaka bawa wancan yaron auren yarka?
Ban ce baya son ta ba amma son da tak
e yi masa ya kere wanda yake mata nesa ba kusa ba, kai namiji ne. Be zama lallai ka hango illar dake tattare da irin wannan tarayyar ba. Bance a duk in da son mace yafi yawa yana kasan cewa matsala ba amma muna amfani da abinda yafi faruwa musamman a irin
al'umar da muke ciki yanzu. Yanzu ka kalli abubuwan da Halima takeyi, akan Bilal bata ji bata gani ba kuma ta shakkar
ɓ
atawa da kowa. Har ta kai yanzu bata shakkar
ɓ
acin rai na akan duk abinda ze faranta ran Bilal. Tun be aure ta ba take haka ina ga kuma s
un zauna me kake tunanin zata zama? Ni dai gaskiya ina jiye mata tsoro domin zuciyata
ta kasa nutsuwa akan al'amarin nan mafi sauƙi a haƙura mu cigaba dayi mata addu'a Allah ya fito mata da wanda ya fishi alkhairi".
Shiru Alhaji Aminu yayi kawai, sam ya
kasa ganin abinda take kira da matsala cikin al'amarin Halima da Bilal. A iya binciken sa ba'a samu yaron da wani halin banza ko shashanci ba. An san asalinsa, yana da sana'a ga yarinya tana son sa to me ake nema? Sau tari shi ma ya kanga kamar Haliman ta
zurma da yawa amma yanayin ta ne a haka tun tana yar yarinya ta kan tsananta son abu, ko cikin kayan wasan ta ta kan tattala tare da kulawa da wanda ta fi so bata ta
ɓ
a fitar dashi idan suna wasa ta sa'anninta shiyasa yakan mata uzuri akan abubuwa da yawa
nata haryar kenan ta bayyar da soyayya. Cikin nutsuwa ya ringa kwantarwa da matar tasa da hankali tare da nunar mata da babu komai. Kamar yanda yasan tana wa yaranta addu'a karta gaza, taci gaba da yiwa Halima in sha Allahu duk ma hasashen da wasu sukeyi b
aze yi tasiri ba.
"Yanzu haka nan da wace hujja zamu ce zamu hana shi aurenta? Go be fa suka ce zasu zo saka rana naga da ƙorafin ki ya tsaya wasa ba aure zeyi ba yanzu kuma ya yunƙuro se ki zo da wata magana daban Amina ban fa san ki da haka ba na kuma
san ba kowa yake zugeki ba illah Labiba kuma zan kirata. Ita dai tunda Halima taƙi ƙanin Alhaji Saleh shikenan ta tsangwami zancen auren ta Bilal" Abban ya fa
ɗ
a. Seta girgiza kai tace
"Babu ruwan Labiba wlh, kuma ko da taƙi al'amarin tana da hujjoji da
ababen dubawa ne ai kuma son da takewa Halima yasa har take adawa da abinda take ganin ze iya zaka matsala a rayuwarta dan dai ka sani ko ni da na haifi Halima dan dai soyayyar uwa da abin cikin ta daban ce amma bazan ce nafi Labiba ƙaunar Halima a zahiri
ba" Mama ta fa
ɗ
a. Se yayi murmushi yace
"Bana in kari da ƙaunar dake tsakanin Labiba da Halima wani ha
ɗ
i ne daga ubangiji wannan na kuma san duk abinda zatayi akanta zatayi ne don ganin rayuwarta ta in ganta. Ƙaramar uwa da yarta, ai babu me shiga tsaka
ninsu dan idan aka juyo ta wani fannin muna nan za ta iya baki kunya kuma ta juya tabi bayan yarta. Ni dai abin da zan ci gaba da fa
ɗ
a miki shine ki ci gaba da yi mata addu'a kawai in sha Allahu e mun ce gara da akayi ba kuma zamuyi nadamar wannan tarayyar
ba" da maganganun daya danneta kenan harta sakko tabi ta tasa taci gaba da addu'ar da dama kullum cikinta take.
A daren ta kira Anty Labiba ta gaya mata zancen zuwa sa ranar a take kuma tace a cireta ciki bata cike da iskancin Bilal da Halima. Tun dai
taji ta gani ai shikenan mai Allah ya tabbatar da alkhairi. Dariya kawai Maman tayi ta kira Yayarta Hajiya Rumana kawai tace zata yiwa Matar Yayansu Lawan Anty Laure magana tun da taga ta fara harkar snacks na biki, duk da ba'a gidan zasu zo saka ranar ba
amma zatayi abin tukuici akai can gidan Baba Salahun.
Washe gari lahadi ƙarfe hu
ɗ
u na rana Kawunnan Bilal biyu da Aminin mahaifinsa
ɗ
aya suka je saka ranar auren mu gidan Baba Salahu. Kusan a kowanne
ɓ
angare ana al'ada, wasu su kan yi tsohuwar da aka
saba akai akwati da kayan sa rana. Wanda suka zamanantar da abun kuma ku
ɗ
i suke badawa wa
ɗ
an su kuma a sanda aka kai ku
ɗ
in aure ake ha
ɗ
awa da na sa ranar ko kuma a ha
ɗ
o kayan tare da lefe to su dai su Bilal bamu san wanne zasuyi a ciki ba, dama sanda akayi
tambaya basu bada komai ba Abba yace
baya buƙatar wani ku
ɗ
in na gani ina so ko na aure yanzun ma haka nan suka zo da saka rana shekara
ɗ
aya se dai Baba Salahu yayi tsallen albarka yace basu san zance ba.
Watanni shida shine abin da suka yanke zasu aur
ar da yar su, bayan duk dogon zaman jiran sa da aka sha har idan suna ganin hakan ya musu gajarta to fa suyi haƙuri kawai domin a cikin dangi akwai wanda dama suka ci burin ha
ɗ
a ta dashi. Aminin mahaifin Bilal ne yace ba za'a yi haka kuma tabbas kam iya lo
kaci an basu domin be manta ba an tafi shekara ta uku kenan da sukayi tambayar auren kuma shi kansa be san ranar har ta shekara suka shiryo ba da tun kan su zo dama ze gaya musu yayi yawa musamman dama ga bikin ƙanwar Bilal
ɗ
in da za'a yi duk lissafin sa t
are zasu ha
ɗ
e. Haka dai aka rabu, duk sauƙin kai da rashin
ɗ
aukar duniya da zafi irin na Baba Salahun bayan sun tafi se da ya kira Abba yayi masa mitar mutanen fa ko goro basu zo dashi ba balle wani abu na al'ada. Abban yace babu komai.
Irin murnar dan
a shiga bayan da na samu labarin a watanni shida masu zuwa zan zama mallakin Bilal ba me fa
ɗ
uwa bace. Har party na ha
ɗ
a, cikin sa'a washe garin ranar tayi daidai da ranar zagayowar haihuwata dama dan haka na roƙi Mama da muke hi hi yanzu akan zanje gidan A
nty Labiba. Bata hanani ba, dama na gayawa Hansa'u da su Baby zamu je gidan zoo ranar birthday na Baby na bawa ku
ɗ
i ta yi mana kayan ta
ɓ
awa na siyi cake da a jiki aka rubuta mun Happy engagement Mrs Bilal to be ban sanar ma Bilal
ɗ
in bama se da na samu na
bar gida haka ko suka je shi da abokanansa biyu muka sha hotuna muka ci snacks muka yanka cake bamu ji ma ba na wuce gidan Anty Labiba dan kar zance ya tashi tace ban je ba. Na dai sha zagi a gunta amma ban damu ba, tace kayan gado yan goron dutse zasu mun
duk tarin da Mama takeyi a saboda aure na ba zata bari ta
ɓ
arna tar da ku
ɗ
in ta ba har kayan kitchen da take siya da wanda itama ta siya mun Amirah zasu ajiyewa nace duk naji.
Shikenan rayuwa ta dawo mun sabuwa, soyayya da shaƙuwar mu da Bilal se abin
da ya sake gaba. Na samu ƙatuwar takadda na zana calender ta wata shida kullum da safe na tashi zan soke ranar ki nake yi tamkar na janyo lokaci ni dai buri na da fata na kawai na zama matar Bilal.
Wata Juma'a sati biyu kenan da yin sa ranar mu watann
i biyar