Showing 9001 words to 12000 words out of 287295 words

Chapter 4 - KURA A RUMBU COMPLETE

ma naji wayar a kashe. Wannan ya

ɓ

ata mun rai

ban ko tsaya jira a gama watsewa ba nabi yan unguwar mu a Adaidaita muka tafi.

A ƙofar gida na tarar da Bilal tareda abokinsa Nura, duk da naji haushin ƙin zuwan da yayi gurin bikin amma ganin dana masa se naji zuciyata tayi sanyi. Light blue

ɗ

in shadd

a ya saka data dace da atamfar ankon da mukayi me ruwan dark blue da ratsin fari da light blue

ɗ

in. Na isa inda suke Ina ha

ɗ

e fuska a son na nuna masa

ɓ

acin raina amma na kasa musamman da Nura ya fara zolayarmu wai munyi too match dama mun ha

ɗ

a baki ne amm

a gamu nan tamkar ranar auran mu. Haka na lalace a tsaye yana tsarani har seda Abba ya dawo kafin na wuce ciki su kuma suka tafi bayan sun gaisa dashi.

Ina tsaka da sallar magriba da isha'i da suka ha

ɗ

e mun Amirah ta shiga

ɗ

akin tana fa

ɗ

in nazo inji Ab

ba. Bayan na shafa addu'a na fita falo, Abba ma zaune yana kallon labaran ƙarfe tara. Seda aka tafi hutun rabin lokaci kafin ya juya kaina yana murmushi yace

"Hali dubu" haka yake tsokanata. Sunan babbar yayarsa ne kuma mafi soyuwa a gare shi cikin yan uw

ansa. Kwanana uku a duniya ta rasu seya ha

ɗ

a soyayyar ta data kasancewata yar da ya fara samu duk yake mun.

Murmushi nayi kaina yana ƙasa na gaishe shi yana amsa yana tambayata biki kafin ya

ɗ

ora da cewa

"Yaya Salahu ya gaya mun sunyi magana da kawun

Bilal yace ze kirashi duk yanda ake ciki

ɗ

azu yake sake ce mun kimanin sati biyu kenan har yanzu beji daga gare su ba". Sena rasa abinda zance masa, ina ji yaci gaba da cewa

"Ɗazun har zan tsaya nayi masa magana da kaina se kuma sai nace bari na fara jin

ta bakinki ko dai saƙon be iske shi ne". Daƙyar nace

"Eh Abba ya gaya masa. Dama maganar albashinsa da be fara samu bace ta dakatar dashi" se Abba yace

"Aa, har yanzu dama wannan matsalar bata kau ba? Na zata dana ha

ɗ

ashi da Malam Mansur yace mun an gyar

a komai tun last two or three months kenan da mukayi maganar.

"Eh Abba an gyara amma salaryn ne wai se wannan watan sannan suka sa masa na wata uku" na fa

ɗ

a masa iya abinda na sani, se yayi shiru kafin yace

"Ikon Allah, to barka tunda an gyata

ɗ

in. Ya

nzu ina kuka tsaya kenan a maganar?"

"Yace zuwa ƙarshen watan nan zasu zo" na fa

ɗ

a ya amsa mun da

"Toh Allah ya nuna mana. Yaya Salahu ya damu, kin san fa babu sanda zamu ha

ɗ

u ba tareda yayi mun mitar ƙin aurar dake ba. Kullum se yace ga Bishira nan da

yaya biyu bayan rana

ɗ

aya aka haife ku"

"To ita Abba ai muna gama secondary aka mata aure bata cigaba da karatu ba" na fa

ɗ

a cikin shagwa

ɓ

a yayi dariya yace

"Haka ne amma dai da kema anyi miki ta tatan da yanzu kin fara tara mana masu samu bari bari a gi

dan nan ai". Sena rufe fuska ta da hijabi ina cewa

"Haba Abba ni yar yarinya dani ai dama ban isa aure ba har yanzu"

"Baki isa aure ba amma kin iya dafawa gardi abinci" Mu'azzam daya shigo falon ya fa

ɗ

a, na galla masa harara ina cewa

"Abba ka mana tsak

ani dashi"

"Se dai in ce ya dena tsokanarki amma babu batun na miki tsakani da

ɗ

an uwanki" Abban ya fa

ɗ

a nace

"To ka gaya masa ya fita daga sabgata"

"Gaskiya ce bakya so kuma se an fa

ɗ

a, har gulmarki ake a unguwa da anga yara da kula za'a ce daga gida

n nan ne" Mu'azzam

ɗ

in ya sake fa

ɗ

a kafin nace wani abu Abba yace

"Arziƙi ne ai kai baka san ladan ciyarwa ba ko?"

"Ciyar da mabuƙata ba. Kai kake bin bayanta Alhaji shiyasa kullum take sake shiga daji maimakon ta dawo hanya" Umma data fito daga

ɗ

akinta

ta fa

ɗ

a sena miƙe na sulalae

ɗ

aki na barsu inaji Abban na kareni yana fa

ɗ

in ai ba laifi bane idan na bashi da babu ai ba za'a masa ba.

Washe gari akayi

ɗ

aurin auran Zainab a ranar kuma muka rakata gidanta mw kyau acan sabuwar gandu. Mijinta matashin

ɗ

an kasuwa ne yayi ƙoƙari sosai a gininsa iyayenta ma sunyi namijin ƙoƙari gurin yi mata kaya da suka sake ƙawata gidan muka fito munata santi da yiwa juna shaƙiyancin wacece next. Duk su uku da ranar su ni ka

ɗ

ai ce amma dukda haka a jikina inajin sena riga

su amarcewa domin dai nasu samarin a yanda suke ko yau akace a fito ayi aure kowanne yana da abin yin auren amma sun tsaya suna jan lokaci har da Hansa'u da zataje a ta hu

ɗ

u.

Kusan sati uku da suka biyo baya ina ta juya yanda zan sake ma Bilal magana g

anin bamu da

ɗ

e dayi ba kuma ha uzurin daya bani se naji dama Abban ya amsa maganar da kansa kawai dan harga Allah yanzu dana gama

makaranta bana komai hankalina ya fara komawa akan nima nayi aure na tafi nawa gidan. Safiyar litinin Anty Labiba ta haihu, in

a bacci Mama ta tashe ni wai zamuje asibiti daga can kuma bayan an sallameta muka wuce gida Mama tace in zauna mata kwana biyu, ban so ba amma babu yanda na iya haka na tafi gida na ha

ɗ

o kayan da zanyi amfani dasu na kira Bilal ya mayar dani.

Seda nayi

mata sati biyu, dake morata takeyi bata damu da zaryar da Bilal ya ringayi ba kullum se yaje anan zeci abincin dare ko kuma yazo da yamma idan ya taso daga aiki mu

ɗ

anyi hira ya kar

ɓ

i abinci ya tafi, duk zuwan da yakeyi kuma sau

ɗ

aya ya samu ya shiga ya y

iwa Anty Labiba barka dan kusan duk sanda zezo tana da baƙi yan barka dake ta kwana biyu bata haihu ba tsakanin Amir da Inayah shekara

ɗ

aya da rabi ita kuma ta bawa Sadis shekara biyu tun nan kuma seda ta shekara bakwai yanzu ta haifi Amina takwarar Mama.

Ba ƙaramar kunya naji ba sanda Bilal ya gama zamansa a falon Antyn ya tafi ba tareda ya bada ko sisin kwabo da sunan barka ba. Dama tun kafin suna dana ke masa hirar me ya kamata mu siya na takwarar da akawa Mama ya fara kawo zancen wata yazo ƙarshe har ya

nzu ba'a fara salary, a zato na ze bada wani abu amma se gashi ya tashi ko asi dukda uban naman suna da abincin da na jibga masa har yan gidansu seda suka ci.

Kwananta goma sha shida da haihuwa na koma gida saboda wata ƙanwar Mijinta bazawara data zo d

aga zaria, sena fake da zanje na maida kaya na na

ɗ

ebo wasu daga nan na fece ba komai ya saka hakan ba kuma illah Munir dake neman takura rayuwata yana kuma ha

ɗ

a ni fa

ɗ

a da Bilal. Ranar talata na koma gida Bilal baya gari yaje Jos mijin ƙanwar Hajjan su ne

ya rasu babban mutum ne sosai shine duk suka tafi. Ranar alhamis zasu dawo tunda suka tafi kullum mukayi waya kwana uku kacal amma ya ringa mitar yayi missing Kano yayi missing abincin Kano ze kace wanda ya tafi wata ƙasar ta daban. Ran da ze dawo tun saf

e na tashi da shirin yi masa girki, na yi da

ɗ

an yawa tunda duka tare da Hajja da yayyensa mata biyu da ƙaninsa

ɗ

aya suka tafi se matar wansa nasna kuma duka a gidan Hajjan zasu sauka kan kowa ta tafi gidansu. Ina aikin Mama namun tsiyar da sakani tayi se

nayi ƙorafin abincin yayi yawa amma dake na Bilal ne na zage inayi sedai kawai nayi murmushi har na gama na shirya komai nayi wanka a Adaidaita na

ɗ

auki Amirah muka tafi gidan bayan munyi waya ya gaya mun sun dawo.

Ba wannan ne zuwa na na farko gidansu

Bilal ba, badan ma Mama ta kafta mun warning ba da haka nan ko fa

ɗ

a mukayi na kirashi a waya be amsa ba zan zari jiki in tafi, tun Hansa'u na rakani har ta dena yanzun ko nasan ko giyar wake nasha bazan cw tazo muje ba shiyasa ma naja Amirah ko Maman ce m

ata nayi Aliyu me Adaidaita zan bawa ya kai musu ni kuma zan wuce gidan kitso badan ba nasan ba zata bari in kai abincin da kaina ba. A kuyance muka gaisa da yan gidan nasu suna ta nan nan dani kamar su goyani ban wani jima ba nayi musu sallama muka fita s

e da muka fito waje kafin naga Bilal dan sanda muka je ance yana

ɗ

akinsa yana wanka. Se naga kamar ya rame a kwana ukun da ban ganshi ba, ya jingina jikin bango yana kashe ni da kallon so yace

"Ashe dagaske kike zaki zo"

"Oh da ka

ɗ

auka da wasa nakeyi

? Ai na gaya maka zanzo nawa Hajja gaisuwa dama" na bashi amsa seta miƙe tsaye sosai yana cewa

"Kin kyauta, kuma naji da

ɗ

i sosai". Ya shafa cikinsa yace

"Kin san ruwan tea ka

ɗ

ai nasha muka kamo hanya, ina kwanukan kuma na ganki ke ka

ɗ

ai?"

"Suna cikin g

ida na bashi amsa" se ya wani kalleni yace

"Cikin gida kuma? Abincin nawa kika kai mun cikin gida Halims? Maimakon ki buga mun ƙofa ki ajiye a nan kafin ki shiga?"

Se naji abun wani iri amma na kanne nace

"To banda abinka dama abincin ai ba kai ka

ɗ

ai

nayiwa ba kuma yana da yawa zasu

ɗ

iba nasu su rage maka"

"Ragowar wasu zanci kenan?" Ya fa

ɗ

a kamar a fusace, se kuma yayi shiru na tsaida idona akansa ina karantar yanayin fuskarsa, se kuma yayi murmushi yace

"To an gode My Halims Allah ya bada lada. Bar

i na shiga ciki muyi sallama da Yaya Zubaida nasan yanzu zata wuce se nazo na raka ku". Gefe muka tsaya kusan minti biyar ya fito kamar ransa a

ɓ

ace, Adaidaita ya tare mana muka shiga ganin ya tsaya be shiga ba yasa na kalle shi nace

"Ka fasa raka mu ne k

uma?"

"Zanzo kawai anjima, yanzu zanje gidan gidan Muslim ne naga ko zan samu abinda zanci dan yunwa nake ji sosai wlh". Da mamaki nace

"Wannan abincin kuma fa?" Ya

ɗ

auke kai gefe yace

"Sun cinye, kin san duk bamu wani tsaya munci abinci ba muka taho sh

iyasa dama da a gurina kika ajiye na

ɗ

iba nawa se na kai musu sauran".

Harga Allah seda naji wata kunta ta kamani amma kuma yunwar da yace yanaji ita ce a gabana yanzu dan haka nace

"Amma basu kyauta ba, to ko muje gida se na dafa maka ko indomie ce. M

atar Muslim dake fama da kanta babu lallai ai tayi girki ma". Seda yayi jimm kafin yace

"Amma ba zaki wahala ba? Kin gama wannan girkin ki sake yin wani?"

"Dafa maka abinda zaka ci kake kira da wahala?" Na fa

ɗ

a ina langwa

ɓ

ar da kaina ina kallonsa. Me Ada

idaitan ya kalla kafin yace

"Shikenan nan, kuje bari na canza kaya se na taho" ya ciro

ɗ

ari biyar daga aljihunsa ya bawa me Adaidaitan, seda ya kar

ɓ

i canji kafin ya koma cikin gidan mu kuma muka wuce. Kallona kawai Mama tayi sanda nake gaya mata zan sake

dafawa Bilal abinci wancan da aka kai musu ya ƙare,

"Wato gidansu kika je? Ke wace irin yarinya ce mara jin magana anya Halima kina son ki siyawa kanki ƙima da mutunchi a idon dangin Bilal kuwa? Banda ke sakarya ce a ina kika ta

ɓ

a ganin mace na zirgilli

irin haka akan namiji?" Mama ta fa

ɗ

a cikin

ɓ

acin rai, nayi ƙasa da kaina kawai na kasa ce mata komai ta cigaba da bambamin fa

ɗ

a kafin ta wuce

ɗ

aki, seda ta kullo ƙofa sannan na wuce kitchen jiki na rawa na

ɗ

ora masa Indomin. Kaji biyu na saka a abincin da

na musu

ɗ

azu, dubu biyar Abba ya bani yace nayi cefane harda lemo katan

ɗ

aya da ruwa shima katan na siya musu. Seda na duba freezer babu sauran nam se kifi, Bilal baya son kifi dan haka kawai na daga masa ita da karas da kabeji na soya masa ƙwai guda hu

ɗ

u

. A falon Abba na shirya komai, seda na fita tsakar gida zan wanke kayan da nayi amfani dasu dan famfon cikin kitchen

ɗ

in ya lalace se na gashi tsugunne gaban Abba suna magana.

Ban sam me suka tattauna ba na koma ciki bayan ya shigo seda ya cinye indom

in tas yasha lemo kafin ya kalleni yana murmushi yace

"Se yanzu na fara gane kaina"

"Dole ai, ka sha tafiya ga yunwa kuma ai kayi ƙoƙari ma" na fa

ɗ

a ina murmushi se yace

"Yanzu Abba yake mun magana. Ai ma zata ma kin gaya masa abinda na sanar dake se y

ace mun wai kin ce masa ƙarshen wata za'a zo gashi watan ya mutu wani ya kama shima harya ƙare shiru me yasa zaki masa ƙarya?"

Kallonsa nayi jin abinda ya fa

ɗ

a wai nayiwa Abba ƙarya, bance masa komai ba na maida kaina ƙasa ina jan zaren mayafin jikina

ina jinsa yana cewa

"Kin kasa fahimtar abinda nake gaya miki Halima. Bawai bana son azo maganar saka ranar nan bane aa ina duba abubuwan da suke gabana daya kamata na kammala kafin ace an fara maganar aure. Yanzu idan akayi sa rana kowa ze tada hankalinsa

ne da son jin yaushe za'ayi biki, da zarar an

ɗ

an samu akasi an

ɗ

aga daga sanda aka fa

ɗ

a se kiji maganganu su kansu iyaye zakiga sun

ɗ

auka kamar mutum ya shigo da shiririta cikin abun. Ni yanzu babban abinda yafi tsayamun shine na kammala gini na kin san

kuma dai gini abu ne me buƙatar tana di da lokaci dan ko da ku

ɗ

in a zube kin san aikin gaggawa baya ƙarko"

"Haka ne" na fa

ɗ

a ina kallonsa ƙwaƙwalwata na son bawa maganganun sa ajin daya dace dasu. Yaci gaba da cewa

"Kin san ina da taste, akwai plan

ɗ

in

dana tsarowa gini na da idan yanzu nace na katse ko na canza da wani abu daban baze bada yanda ake so ba. Kinga ginin nan shi ka

ɗ

ai ne nake so ace na kammala duk wata sauran hidima za'ayi abinda ya samu ne na sani lefe ma zaki iya yafe mun ko My Halims tu

nda dama ke ai kullum cikin sababbin sutura kike ko wa

ɗ

annan na jikinki ma ai ban ta

ɓ

a ganinki dasu ba" ya ƙarasa yana wata dariyar data ƙular dani, kafin nace wani abu ya tareni yana cewa

"Wannan bayanin nake so kiyiwa Abba nasan zw fahimce ni tunda ina

da hujja me ƙarfi ko shi Baba Salahun idan aka fahimtar dashi ze gane".

"To amma Bilal me ze hana ka kama haya mana ko da na shekara

ɗ

aya ne pending ka ƙarasa ginin naka? Na fa

ɗ

a bayan dana gama jin nasa uzurin, seya wani kalleni kamar wadda na fa

ɗ

a ma

sa mugun abu yace

"Haya? In kama haya fa kike cewa Halims? Yanzu ke ba zakiji kunya ace gidan haya aka kaiki ba?"

"Wace irin kunya kuma Bilal mutane nawa suke rayuwa a gidan haya? Ita kanta hayar ai se wanda ya isa ne ma yake da hali ze kama naga wasu s

edai su nemi a basu aro" na bashi amsa ina

ɓ

ata fuska seya girgiza kai yace

"No Halims wace irin haya ana zaune ƙalau se kace matsiyaci. Mu gama zagin abokananmu saboda rashin zuciya sun kasa mallakar gidan kansu se kuma kawai nima na ƙare a haya bayan Al

lah ya rufa mun asiri ina da yanda zanyi"

"Oh ashe ma kana da yanda zakayin niyya ce kawai bakayi ba ko kuma nace auren nawa baka shiryawa ba. Da kuma zaka ce tsiya ce take sakawa ayi haya har kana zaginsu wasu da hakan shi muhalli tamkar rabon haihuwa

da silar mutuwa Allah ke saukar dasu don yanda kaso da faruwar su ko kauce musu baka da wayo baka da dabara akai kuma idan Allah yaso ya nuna maka iyakarka seya jarabce ka kaima duk arziƙin ka ya hanaka mallakar gidan kan naka. Mutane nawa keda rufin asir

i amma har suka mutu suka ƙare rayuwar su a gidan haya? Ka fito fili kawai ka fa

ɗ

a mun abinda yake ranka game dani domin na fara gajiya da uzurin ka da basa ƙarewa kullum da wanda zaka zo dashi to kawai ka fa

ɗ

a mun matsayar maganar mun, idan yi yi

idan bar

i bari kawai nagaji da sa banga ƙaho ba Bilal" na fa

ɗ

a ina miƙewa tsaye.

[5/18, 13:07] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login