Showing 156001 words to 159000 words out of 287295 words

Chapter 53 - KURA A RUMBU COMPLETE

dan Allah king

a halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena kuka kinji?"

"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuw

ar" likita ya fa

ɗ

a. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse

ɗ

in da Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya kar

ɓ

a ya fara ha

ɗ

awa, zai zare ruwan dake h

annuna Abba ya dakatar dashi yace

"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"

"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya girgiza masa kai yace

"Na sani amma ka

ɗ

anyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". T

sayawa yayi kamar ba zai fita ba kafin ya juya, Nurse

ɗ

in da ta yiwa Mama magana

ɗ

azun ta bu

ɗ

e baki zata sake magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.

Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya

ɗ

ago kaina daga kafa

ɗ

ar sa yace

"Kukan ya isa

haka Halima kiyi shiru kinji"

"Tsoro nakeji Abba" na fa

ɗ

a daƙyar kafin na kama hannunsa na

ɗ

ora saitin zuciyata da nakejin ciwo tamkar an hura mun wuta nace

"Zuciyata zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"

"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji

ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu salama kinji?"

Kai na

ɗ

aga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a ha

nkali na fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya

ɗ

auke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci, sai da ya

ɗ

auke ƙwallar data zubo masa k

afin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lullu

ɓ

a mun bargo sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.

Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu da

ɗ

i gaba

ɗ

aya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida da sassafe haka da kuma

yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta fa

ɗ

a mata wani abu amma kuma baya son yaji abinda zai

ɗ

aga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi Lagos

ɗ

in. Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magrib

a lokacin sun tashi gaba

ɗ

aya ya shiga hotel room

ɗ

in sa kafin ya bu

ɗ

e wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita kuma saƙon Mama ya fa

ɗ

o tana gaya masa Halina na Asibiti sun sameta a sume a

ɗ

aki har lokacin kuma dukda bai san ƙarfe nawa ta t

ura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi magana.

Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan haka ya mayar da akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu

ɗ

aya ya

ɗ

auka kuma yanda ya jishi da

bayanin da ya masa akan yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa

ɗ

aya a Lagos

ɗ

in ba duk kuwa da bai kammala uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano suka kwana cikin tashin ha

nkali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayiwa likita magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a

gaya mata kawai saboda tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara ta sani in mutuwa tayi ta

ɗ

auki dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.

Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya ga

ya masa kawai zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial stroke da tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti goma a zaune kafin ya iya bu

ɗ

e baki yayi mag

ana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?

Dr ne ya ringa kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar

numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya fa

ɗ

a mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta ka

ɗ

a ta raya tayi kukan duk a banza yaƙi fa

ɗ

a mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu ka

ɗ

an

ce akan ya sanar mata da ainihin halin da Haliman take ciki.

Bu

ɗ

e ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya daga bakin ƙofar yana cewa

"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurar

eka" sai ya miƙe yana cewa

"Wacece"

"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita da sauri dan dama tunda ya dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi ba ranar da

aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal zata tafi idan ma bata same shi ba sai ta saka an

ɗ

aure Hajja ai dole ya fito duk ma ind

a ya shiga ya musu bayanin abinda yayiwa Halima.

Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna kallonsu, ta fashe da kuka tace

"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu

ya samu Halima wlh sai na

ɗ

aukar mata fansa akansa". Cikin fa

ɗ

a Abba yace

"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan Allah ba zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi

ma ku wuce gida kawai tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su amma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi da

i babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka nan duk wanda yazo ya tafi zai ha

ɗ

a nasa kalar labarin da ciwon da zai

ɗ

ora mata, amma dai maganar data fi ƙarfi ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacc

e ta fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin

ɗ

aya daga cikin ƙannen Bilal.

BILAL

Bayan daya sauke su kai tsaye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare dashi. Tsakani

n sa Allah tun waccen ranar da Halima ta banka

ɗ

o sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a

ɓ

oye. Koda da yake nuna tamkar komai ba komai bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi ka

ɗ

ai yasan kalar ku

nya da nadamar da yake ciki a yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya

ɗ

akko ba saboda yasan Halima bata da

ɗ

abi'ar bibiyar masa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da wayar sa balle yanzu daya kulle

ta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya bu

ɗ

ewa koda ace ma tayi niyyar hakan.

A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace

"Yawwa gashi nan ma yazo ai" Hajja tace

"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka a

msa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa fa tuntuni nace ka bata ku

ɗ

in motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar farko sai tayi jira wata ta cika".

Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera ha

ɗ

i da daf

e kansa da hannu biyu, Hajja ta shiga tana cewa

"Au ina magana shine zaka shige

ɗ

aki ko ka amsa ni?"

"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya fa

ɗ

a yana gyara zama, sai ta zauna itama tana cewa

"Saboda me?"

"Mun

ɗ

an samu matsala ne da Halima ta

tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke ka

ɗ

ai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace

"Kaji yar abu ta kazan uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"

"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saur

in katseta, Fadila tayi tsugul tace

"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take kamar na ubanta bata so kowa ya shiga sai ita da danginta".

"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya fa

ɗ

a yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta taso masa itama tana cewa

"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta fa

ɗ

a, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi tunda haka ta za

ɓ

a to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai t

ayi zama mai lasisi kai kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye komai da anyi magana kace Halima to yanzu ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin gidanka ya isa kuma haka a canz

a sheƙa".

Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san ainihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?

Miƙewa yayi a a sanyaye yana cewa

"Idan

ta huce dai na san zata dawo"

"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na

ɗ

auka dangin arziƙi ne ashe duk shigo shigo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to kuwa ba zata dawo b

a kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".

Da wata sabuwar damuwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife kansa j

ikin sitiyari ya tafi tunanin ha

ɗ

uwar sa da Jalila.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir No

vels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800,

biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 36*

Ƙ

addara da kwa

ɗ

ayi ha

ɗ

i da son zuciya irin nasa ya janyo masa fa

ɗ

awa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin

samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake

ɗ

abi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun

ɗ

auki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zi

na ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da ji

ɓ

i da ita. Da yawan su sun

ɗ

auki hakan a matsayin ƙaramin zunubi domin wasu basu ma yarda cewa dasu da wanda ya keta haddin macen da ba halalinsa basu da banbancin zunubi.

Su kan manta ita kanta Zina ta kasu kashi da yawa, a ciki akwai Zinar idanu da kuma ta baki da kunnuwa wadda suke aikatawa domin kuwa suna kallon haram, su saurari haram su kuma furta haram da bakunan su wanda illolin hakan dai dai suke da wanda yayi fasi

ƙ

anci da mace a zahiri.

Ko farkon ha

ɗ

uwar sa da Halima ya so ya gabatar mata da irin wannan soyayyar sai dai bata bashi fuskar hakan ba shima kuma bai takura mata ba daga baya ma kuma ya tuba ya bari har zuwa lokacin da sukayi aure kafin lokaci

ɗ

aya Ja

lila ta fa

ɗ

o rayuwarsa ta wargaza komai ta sake jansa ruwa har ta kaishi da aikata abubawan da suka zarce wa

ɗ

anda yake aikatawa a baya.

Silar Hafiz ya ha

ɗ

u da Jalila, ita

ɗ

in tsohuwar budurwar Hafiz ce tare sukayi karatu a London dan har an saka musu r

anar aure ya rage saura watanni aka fasa sakamakon ganinta da mahaifinsa yayi tareda wani abokinsa a France sunje wani taron kasuwanci ita kuma tayiwa Abokin nasa rakiya wanda ya kasance Sugar Dadynta.

Hafiz bai ta

ɓ

a sanin ba

ɗ

inin Jalila ba, dukda ya s

an macece me rawar kai dan shi yake tsawatar mata abubuwa da yawa saboda son da take masa kuma take ragewa kuma da yake shi

ɗ

in bai zo mata da fuskar da zasuyi irin rayuwar da takeyi a bayan idonsa ba sai ta

ɓ

oye masa zahirinta, ko da wasa bai ta

ɓ

a sanin i

rin rashin jin da takeyi ba sai bayan da mahaifin ya kirashi ya gaya masa babu maganar aure a tsakaninsa da ita ya nemo wata matar yar gidan mutunchi tunda wuri. Koda Dady ya sanar masa sa abinda idon sa ya gani ma da farko har ransa bai yarda ba dukda ya

san babu wani dalili da zai saka Dady ya masa ƙarya ko ya hanshi aurenta. Sai sa ya ringa bibiyar takunta a hankali komai ya fito ya gane zahirin wacece ita ya mata kaca kaca suka raba hanya a lokacin har kusan rataye kanta tayi saboda yanda take masifar S

on sa, tayi rantsuwa da yi masa alƙawarin zata daina duk wani abu da takeyi in har zai aureta amma yace la la, in taga dama ta tuba saboda Allah amma ba dan shi ba domin ba zai ta

ɓ

a aurenta ba bayan yasan wacece ita.

Haka nan tayi naci, Tun tana bibiya

rsa harta haƙura ta ƙyale shi tana ji tana gani ya fara soyayya da Yasmin har suka yi aure daga ƙarshe ma ya bar Abuja ya dawo aiki a Kano. A hankali bayan wani lokaci da naci da bin binin da take masa ya fara sauraronta suna gaisawa a matsayin abokai kam

ar yanda suka faro tun asali kafin soyayya ta shiga tsakanin su, har ranta tana fatan a hankali ta shawo ya amince ko a ta biyun ne ya aure ta bata damu ba dan tana tsananin son Hafiz sai dai shi clearly ya gaya mata kada ta yaudari kanta domin ba zai ta

ɓ

a

aurenta ba. Ko da ya ke sauraronta a yanzu ma saboda yaga alamun ta kintsune saboda ya rage mata ra

ɗ

a

ɗ

in takunkumin da iyayenta suka saka mata tun bayanfallasar asirinta da fasa aurensu yake yake sauraronta yana Kuma ƙara yi mata nasiha da nusar da ita ga

skiya.

Jalila bata rasa komai ba domin mahaifinta hamshaƙin mai ku

ɗ

i ne haka mahaifiyar ta data kasance Balarabiya itama mai ku

ɗ

in kanta ce. Babu abinda suka rageta dashi a rayuwa kusan ma gatan da ya mata yawa yana da nasaba da silar lalacewarta. Tun

tana secondary school take riƙe manyan ku

ɗ

a

ɗ

en da suka shallake shekarunta tafiyarta Turai karatu kuma ya sake bata yanci a nan ta ha

ɗ

u da ƙawayen da suka bu

ɗ

e mata ido da maza, da ku

ɗ

in ta take amfani ta mallaki duk saurayin da yayi mata idan ta gama yayi

nsa ta sallame shi ta

ɗ

akko wani kusan Abokin Dadyn Hafiz shi ka

ɗ

ai ne saurayin da ta ta

ɓ

a yi babba kuma mai ku

ɗ

in kansa wanda shima wayewar sa da yanda ya iya soyayya irin wacce take so ta jata harta biye masa suke fita ƙasashe tare har hakan ya zamo sila

r tonuwar asirinta.

Yanda suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login