Showing 255001 words to 258000 words out of 287295 words
na zare jin abinda ta fa
ɗ
a na ce
"Kuma ya rasa ranar da zai zo sai yau da nake d
a uzuri? Tun fa last week aka ce zai zo?" Tana gyara fuskarta da powder ta ce
"Ai kuwa dai sai yau kuma wlh har wa
ɗ
anda basu da duty yau gashi can Dr Sa'id yace a kirasu a waya duk kuma wanda bai zo ba ya ce babu ruwansa dan haka kiyi haƙuri kawai ki ji
ra na san ba jimawa zaiyi ba".
Kamar zanyi kuka haka na koma office na zauna, tun last week aka ce zai zo Dr Sa'id kuma ya jaddada har ranakun da bamu da duty mu kasance cikin shiri za'a iya cewa mu fito saboda yace yana so ya gana da duka staffs ne ida
n ya zo. Ina duba agogo ina zabga tsaki, mutumin da aka ce an
ɗ
akko daga Airport tun 12 gashi har
ɗ
aya ta gota basu iso ba ko dai dama basu taso daga can Abujar bane lokacin da aka tafi
ɗ
akko shin sai Allah. Da wannan mitar na tashi nayo alwalawa ganin zam
an ba zai fissheni ba nayi sallah, ina addu'a Dr Sulaiman ya shigo office
ɗ
in yana ganina ya ce na fito da sauri dan haka na shafa na miƙe shaf na manta ban mayar da Lab coat
ɗ
in ba na fita da Abayar dana saka nayi sallah.
A reception na tarar da duka
staffs harda cleaners anyi layi na tafi inda naga sa'annina da alama tsayuwar matsayi aka bi, yanda kasan wa
ɗ
anda zasu tari wani Gwamna ko Shugaban ƙasa haka muka nutsu muna kallon ƙofa kusan minti uku kafin suka shigo, Dr Sa'id ne a gaba sai wasu mutum bi
yu da ban sansu ba da alama tare suka zo da CEO
ɗ
in sai kuma shi Dr SALMAN ABDULLAHI AGI da wasu mutum biyun a bayan sa,
ɗ
aya daga gani PA
ɗ
in sa ne sai kuma
ɗ
ayan da yayi kama da security.
Fuska ba yabo ba fallasa ya ringa kallonmu suna tayi masa sann
u da zuwa banda ni dana zuba masa ido ina ƙare masa kallo kamar mai neman wani abu a jikinsa. Duk yawan shekarunsa ba zasu kai 40 ba yanzun ne na sake tabbatar da haka dana ganshi a zahiri. Dogo ne sosai dan har ranƙwafawa yayi, a kallo
ɗ
aya kuma dukda sui
t ce a jikinsa zaka fahimci yana da kirar ƙarfi irinta masu
ɗ
aga ƙarfe.
Bashi da wani shahararren kyau kuma baƙi ne mai ƙananan ido amma akwai wani abu a tattare da idanuwansa da bai zai barka kayi masa kallo
ɗ
aya ba tareda ka ƙara ba, gayu da iya
ɗ
auka
r wanka ya saka ya ƙaƙalo kyawun a dole amma ba dan asalinsa mai kyau
ɗ
in bane irin su Bilal da aka haife su da kyan su, amma maganar gaskiya a ture duk wani ƙaƙale-ƙaƙale, Dr Salman ya ha
ɗ
u; ga kuma tarin ilimi abin ba'a cewa komai.
Yanda nake kallons
a shima haka ya tsayar da idonsa a kaina sanda ya kallo
ɓ
angarenmu, naga sanda la
ɓɓ
ansa suka motsa alamar magana yayi amma kunnuwana basu jiye mun sautin mai ya fa
ɗ
a ba ganin kuma mun ha
ɗ
a ido ya saka nayi saurin sadda kaina ƙasa ina jin haushin irin kallo
n ƙurillar daya kamani ina yi masa. Juwairiyya ta zungureni na kalleta da son jin ƙarin bayani, da ido ta nuna mun CEO
ɗ
in da har sannan ashe ni yake kallo na zare masa ido cikin rashin fahimtar dalilin kallon da yake yi mun.
"Tambaya yayi wai baƙuwa ak
ayi?" Juwairiyya ta ra
ɗ
a mun a kunne, still ban fahimci kan zancen ba sai da Dr Sulaiman ya ce
"Sallah tayi garin sauri kuma ta manta ta fito a haka". Sai lokacin na lura ashe ni ka
ɗ
ai ce a gurin babu lab coat a jikina cikin yan Lab, nayi ƙasa da kai ina
kallon takalman ƙafarsa kafin na
ɗ
aga kai a hankali jin yana cewa kowa ya gabatar da kansa. Sai kace za'a gudu ba zai bari aje a zauna ba tukunna. Da
ɗ
ai-
ɗ
aki kowa ya ringa gabatar da kansa da kuma position
ɗ
in sa har aka zo kan coppers mune kuma ƙarshe, J
uwairiyya dake kusa da ni tayi tana gamawa na bu
ɗ
e baki zan fara magana wayarsa tayi ƙara sai ya
ɗ
aga mun hannu alamar na dakata ya kar
ɓ
i wayar daga hannun PA ya amsa kafin ya fara tafiya suka shige Elevator shida muƙarrabansa suka barmu a tsaye musammani,
ni ce fa ka
ɗ
ai na rage banyi introducing kaina ba maimakon ya bari nayi sai su wuce gaba
ɗ
aya yanzu ko mai yake nufi sai Allah, zamu tsaya ne yaje ya dawo ko kuwa shikenan taron ya watse? Wai dama iya dalilin daya saka aka tsayar damu kenan ko da saura?
Dr Sa'id ne ya dawo ya ce zamu iya tafiya wai amma gobe kowa ƙarfe takwas tayi masa a gurin za'ayi meeting. Haka muka fita ina mita ga rana ta take babu lallai kuma na tarar da masu clearance
ɗ
in suma tunda ƙarfe biyu ta rigada tayi amma haka nan na biya
tunda idan na ce na bari gobe Friday kuma ban san sai ƙarfe nawa zai sake mu ba. Da haushin rashin samun clearance
ɗ
in na wuce gida dan munyi waya da Anty Labiba tace mun suna gidan Mama.
Ban san
ɗ
aya matar da muka hau Adaidaita tare cikin unguwa za'a
shigar da ita ba tunda tace Sabon titi kawai na
ɗ
auka a bakin hanya zata sauka ni kuma ya wuce dani sai da muka je naga yana ƙoƙarin shiga layin Gidan Ƙanƙara layin su Bilal kafin nayi masa magana.
"Ba ciki sosai bane Hajiya kuma kan hanya ne inda zata s
auka sai mu fita ta baya Hajiya" mai Adaidaitan ya bani amsa. Ƙoƙarin mayar da kaina kan wayata da nake dannawa nayi amma na kasa sai na zurata cikin jaka na shiga kallon hanya ina tuna zuwana gurin na ƙarshe ranar da muka zo duba Hajja bayan mun dawo daga
gidansu Duniyarsa.
A kan layinsu Bilal ya tsaya, na leƙa ina hango ƙofar gidansu daya sha sabon fenti ga mata suna ta shige da fice kamar ana wata hidima a gidan,
"Ko mai akeyi sai Allah" na fa
ɗ
a a fili kafin na
ɗ
auke kai na koma kallon mai Adaidaitan
dake irgawa matar data sauka canji.
"Gadon ƙaya" muryarsa ta sauka a kunnena tamkar dirar aradu kafin ƙamshin turarensa da tunda na sanshi bai ta
ɓ
a canzashi ba ya mamaye iskar da take yawo yawo a gurin, na
ɗ
ago; har ya zauna a gefena. Dukda na razana
da ganinsa amma ban bayyanar da hakan a kan fuskata ba sai na mayar da hankali na kan mai Adaidaitan na ce
"Malam drop fa na
ɗ
auke ka, itama saboda naga hanya
ɗ
aya zamuyi kuma abin hawan yana wahala shiyasa na bari ka
ɗ
auketa"
"Kiyi haƙuri Hajiya, Mal
am yi haƙuri ka sauka ba can zamuyi ba" mai Adaidaitan ya fa
ɗ
a, sai lokacin Bilal ya kalleni idan kuma nayi rantsuwa na san ba zanyi kaffara ba tsabar wulaƙanci ne ƙarya yakeyi ya ce bai san ni bace a ciki sai a lokacin.
"Halima" ya fa
ɗ
a muryarsa da ida
nuwansa suna bayyanar da mamaki, na
ɗ
auke kai a raina ina cewa
"Ƙaryar banza wlh ka san ni ce" kafin kuma na saita fuskata na kalle shi da irin yanayinsa na ce
"Au Bilal, kai ne?"
"Kun san juna ma ashe? Toh mu
ɗ
auke shi ko zai sauka?" Mai Adaidaita d
ake kallonmu ta cikin mudubi ya fa
ɗ
a, shiru nayi dan har ga Allah ƙarfin hali kawai nakeyi sai Bilal
ɗ
in ne ya ce masa
"Bari sai na sauka a titi tunda ciki zaku shiga" ya tayar da mashin ya juya sai lokacin na ƙaƙalo murmushi ganin yana kallona na ce
"
Ya su Hajja?"
"Amma baki fa
ɗ
a mun zaki ringa fita wani guri ba, ko kin manta har yanzu ina da iko akanki tunda kina cikin iddatah?" Ya fa
ɗ
a yana kallona cikin sauti mai kama da ra
ɗ
a dan nima ba dan shi nake kallo ba bai zama lallai na ji abinda ya fa
ɗ
a
ɗ
in ba. Na saki murmushin irin na tura takaici wanda ni kaina ban san na iya ba kafin nima na sauke murya yanda yayi na ce
"Da alama amarci ya sa ka faa manta lissafi, ko dai in saka ayi maka babbar calendar da zaka ringa duba watanni da ranaku saboda gu
dun manta abubuwa masu muhimmanci irin haka?"
"I'm serious Halima, 28th of this month ya kamata ki fara cycle
ɗ
in ki na uku" ya sake fa
ɗ
a, ganin mum kawo kan titi mai Adaidaitan na neman cigaba da tafiya ya saka nace masa
"Ya sauka a nan" sai ya dak
ata, na kalli Bilal da shima ni yake kallo kafin na ce
"An zo titi Malam", kallona yakeyi kamar wanda yaga wata halitta ta daban dan haka na ka
ɗ
a yatsuna akan fuskarsa ina sake maimaita masa cewar an zo titi,
"Ki fara shiri, na mayar dake
ɗ
akin ki" ya
fa
ɗ
a yana sauka daga Adaidaitan, bansan lokacin dana fashe da dariyar da har mai siyar da ƙanƙara a inda kuka tsaya da mutanen dake gurin saida suka kallemu ba, da hannu na nuna kaina ina cewa
"Da alama kayi hauka ko?"
Ya miƙawa mai Adaidaitan gudar
dubu
ɗ
aya yana cewa
"Za'a ga wanda yake hauka tsakanin ni da ke" ya wuce ya tsayar da wani Adaidaitan ba tareda ya tsaya kar
ɓ
ar canjinsa ba, abun nasa yayi bala'in bani dariya; lallai bansan Bilal mahaukaci bane sai yanzu. Wato shi yana can yana mun lissa
fin Iddah kenan? To da bai ha
ɗ
u dani ba yanzu wa zai aikowa da saƙon ya mayar dani
ɗ
in?
Ni ka
ɗ
ai na ringa dariya mai Adaidaita dai sai satar kallona yakeyi da alama magana ce fal bakinsa amma ya kasa furtawa har ya saukeni ƙofar gida nayi wucewara tund
a Bilal ya biya mun, lallai yau kam za'ayi ruwan sama harda ƙanƙara Bilal ya biya mun ku
ɗ
in mota.
❤
️
*ƊANLARABAWA INVESTMENT! Kyau Da Ƙima A Hannunku!*
❤
️
*Ku sauka lafiya zuwa masarautar ƙayatarwa!*
👑
*ƊANLARABAWA INVESTMENT* na kawo muku:
*Atamfofi masu kyau na zamani*
*Shaddodi da Laces masu
ɗ
aukar ido*
*Takalma & Jakunkuna masu ladabi da ƙima*
*Hijabai, mayafai da dogwayen riguna masu salon zamani*
*Yari da sarƙa da kayan ado masu ban sha’awa*
*Akwatuna masu kyau don tafiya ko ha
ɗ
a lefe*
*Turaruka masu ƙamshi da kayan kwalliya na garari*
*Nau'in kayan kicin na alfarma da kayan
ɗ
aki*
*Zannuwan gado da labulaye na kashe kala*
*Da dai sauran su*
*Muna tura kayanmu ko'ina a fadin Nijeriya da ƙasashen ƙetare. Cikin mutuntaka d
a cika alƙawari in sha Allah*
*Location: Kano, Ƙofar Waika, Layin Malam Sani Shawus.*
*Lambar waya domin tuntu
ɓ
a*: 08080049548
*Ko ku shiga zaurenmu na manhajar WatsApp ta wannan link kamar haka:*
https://chat.whatsapp.com/Loht5sGuLJO3LXYE9Okq
Ns
*Za ku more da kallon kayayyaki na ƙawa bisa ingantaccen farashi da rahusa mai kama da kyauta. Sayen nagari, mayar da ku
ɗ
i gida.*
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun
da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 57*
BILAL
Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan
da za'ayi tuwon
ɗ
aurin auren Fadila da za'a
ɗ
aura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu, Yayan Hajja ne da suke
uba
ɗ
aya da yake mutum ne mara
ɗ
aukar raini shiyasa duk rashin mutunchin Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal
ɗ
in yaje ya samu ya gaya masa zancen auren Fadilan da yanda ita da Hajja suke shirya komai ba
su saka kowa a ciki ba.
Kawu Ɗayyabun ya ringa fa
ɗ
a yana cewa
"Wane irin rashin hankali ne haka? Ita Hajara wai sai yaushe zata girma ta fara abu irin na mutane masu hankali? Dama mace ta ta
ɓ
a aurar da kanta ne ko kuwa uwa ce take bayar da auren yarta
? Daga ku har uwar taku sai a rasa wayafi wani tunani, kaima nan zancen ya iskeni ance ka saki uwargidanka dama kuma duk ina jin labarin irin
ɗ
iban albarkar da kai da uwarka da yan uwanka kuka ringayi mata, toh hausawa dai suka ce duk wanda bai yi sharar k
asuwa ba zaiyi ta masallaci dan haka tun wuri in dai da gyara ina baka shawarar ka dawo da matarka dan ba zaka gane illar da kayiwa kanka ba sai a gaba. Ita kuma Hajara zan kirata" akan haka suka rabu.
Washe gari kuwa ya kira Hajjan yace taje gida ta s
ameshi yana son magana da ita ba musu kuma ta shirya ta tafi yayi mata tatas sannan yace su dakatar da duk wani shiri da sukeyi Fadila ta gayawa yaron yaje ya gaida iyayenta maza tukunna idan sukayi bincike sukaga bashida wani aibu sannan su bashi lokacin
da zai turo ayi magana.
Ta koma gida ta saukewa Bilal tijarar da batayi a gaban Kawu Ɗayyabun ba tunda shi ya kai masa gulmar amma kuma dole tayi abinda yace ta kira Baba Sani yaƙi
ɗ
auka sai a wayar matarsa ta sameshi shima daƙyar ya kar
ɓ
a sukayi magan
a tana gaya masa dalilin kiran kuma yace babu shi a cikin wannan magana
"Kin manta kashedin da kika mun akan yayanki Hajara? Ai ko ni na kawo rashin zuciya duniya ba zan sake tsoma baki cikin abinda ya shafeku ba, bani ka
ɗ
ai bane
ɗ
an uwan ubansu ai muna d
a yawa ki nemi wani" ya bata amsa daga haka kuma ya katse wayar. Daga ƙarshe dai sai babban yayansu Bilal
ɗ
in Alhaji Salisu ta taka har gida ta samu dan Kawunnansu duk wanda ta kira sai yace yana Aa dan kowa nada labarin
ɗ
ibar albarkar da tayiwa Baba Sani
da Aminu akan zancen Bilal.
Fadilan ce ta raka shi gurin Yayan nasu akayi sa'a ashe ma sun san juna akwai hul
ɗ
a ta cinikayya tsakaninsu, kamar yanda ya cewa Hajja a tsayin lokacin daya san Alhaji Ahlan saurayin Fadilan ya san mutumin kirki ne kuma yayi
tambaya akansa an tabbatar masa da mutumin kirki be kuma yana da asali mai kyau dan Babansa nada sarauta acan Zarian ma. Ya ta
ɓ
a aure sau biyu, ta farkon rasuwa tayi suna da yara biyu Mace da Namiji ta biyun kuma rabuwa sukayi, shikenan aka cigaba da shi
rin biki, maza sunzo sun sake kawo ku
ɗ
in aure da Sadaki bayan wanda ya rigada ya bata.
Bayan ya gama sauke musu kayan miyan a tsaitsaye suka gaisa ya wuce saboda zaije ya
ɗ
akko Jalilah ne a airport.
Motarsa ce taƙi tashi, ganin zata
ɓ
ata masa lokaci y
a barta ya kira wani abokinsa dake siyar da motoci a Gadon ƙaya yace zaizo ya kar
ɓ
i mota yanzu, da wannan saurin ya fa
ɗ
a Adaidaitan daya gani a bakin layin ashe rabon su ha
ɗ
u da Halima ne.
Harga Allah har ya zauna bai san ita bace a ciki dan hankalinsa
na kan wayarsa sai da tayi magana kafin yaji muryarta ya kuma yi mamaki matuƙa amma bai nuna hakan ba har ransa kuma sai yaji rashin da
ɗ
i da bai san dalilin sa musamman ganin da yayi mata ta canza tayi wani kyau fatarta har wani ƙyalli takeyi baka buƙatar
a fa
ɗ
a maka ta samu hutu da kwanciyar hankali. Shi da yake nan yana tunanin tana can cikin halin ƙaƙanikayi soyayyarsa ta hanata sakata ko wacce daƙiƙa cikin dakon kiranta yakeyi domin ya tabbatar ba zata ta
ɓ
a iya rayuwa mai ma'ana ba tareda dashi ba.
Da
ɗ
ewar da akayi yanzun ma bata waiwayeshi ba ya sani cikin biyu, ko dai an ƙwace wayarta ne tunda kowa nata ba son su tare yakeyi ba ya san zasu iya ƙwacewa dan kar ta kirashi kuma a hanata fita idan kuma ba haka ba toh bata da lafiya, yana kuma lissafe
da kwanaki jira yakeyi sai ya rage saura kwanaki ta fara period
ɗ
in ta na ƙarshe sannan zaije ya mayar da ita sai dai su mutu da baƙin ciki a lissafi kuma yau saura kwana goma sha biyu ya aiwatar da shirinsa tunda saura kwana sha biyar a