Showing 306001 words to 309000 words out of 641791 words
God sake ba don ya aureta ba, tausayinta ne yayi leading har yaji zai aureta, kuma
idan ba auren tayi ba tsohon mijinta will keep on hunting her" Mai martaba yace "Kuma duk zuwa biyun da nayi Amurka tare nake ganin ka da yarinyar a maimakon Jawwad din ae" Ajay ya kallesa, sai kuma ya sauke kansa yace "I helped him with some responsibilit
ies too" Mai martaba yace "Then why were you trying to cover that up? Kace komai shi yayi" Ajay yace "I am not hiding it sir, we were all protecting her from her Ex differently, shi yasa har kake zuwa kake samunta a gidan..." Mai martaba yace "Duk yanda za
ka kare kanka you are very good at that Junaid, shi kuma Jawwad always take the Consequences no matter how deep it is for you" Ajay yayi shiru trying to understand what his dad meant, after some seconds Mai martaba yace "Shikenan.... Kai ya batun naka maga
nar auren?" Ajay yayi shiru bai ce komai ba don shi kansa ya gaji da tsara new excuse kullum, Mai martaba ya
ɗ
an yi murmushi yace "Karyar taka ta kare kenan?" Ajay dai bai ce komai ba. Ranan laraba Nenne ta gama hada kayanta a er jakar da Aunty Farida ta a
ra mata don a buhu ta so saka kayan nata tun daga Kano, Nenne na kallon Aunty Farida tace "Kar fa su zo su yi ta jiranmu Parida kiyi da jiki" Ita dai Khaleesat na zaune ta jingina da bango a dakin Aunty Murja idonta yayi jajir saboda kuka, Nenne tace "Ke d
a naga har kin saba da yaran unguwar, baki bishiyar mangwaro baki bishiyar Amburela ke da yara kuna tsinkar 'ya yan itatuwa, to me zai dameki don ance ki zauna kiyi sati biyu ayi maki magani ayi maki gyara yanda ya kamata, kin zata gidan sarauta gidan banz
a ne da za mu bari ki shiga kamar gantalalliya kai tsaye, miliyan biyu sarki ya bada a bamu da Parida amma haka nan na kashe kusan dubu
ɗ
ari biyu akan ki ina nema maki taimako saboda Allah, sannan ga gyaran jiki da za ayi maki tunda ba wani lokaci me tsayi
aka saka na auren ba, Ina laifina a nan daga abun arziki?? So kike mu kwashe ki mu koma Kano Awdul din ya ji dadin sungume ki mu shiga uku, babu abincin da yaron nan Ahamad bai ajiye maki ba a gidan nan na jin dadin rayuwa, gashi shi da
ɗ
an uwansa suna zu
wa ganin ki, har wata panka me tsada ya siya maki saboda zafi da daddare yarinyar nan ke kadai kike saita pankan dai dai inda kike kwanciya mu kuma zafi ya kashe mu, to me kike so da ya wuce haka? Ai gwara tun yanxu ki fara sabawa da zaman Bauchi tunda nan
aure zai kawo ki, Kano da zan koma cikin gaggawa duk domin ki ne inje asan shirye shiryen da za ayi na biki tunda ga damin kudi har dubu dari takwas a lalita ta, ki fa ji tsoron Allah Khaleesah" Aunty Farida dai ko kallon Khaleesat bata yi ba don dama a r
anta tace bazata sake lallabata ba tunda kamar tunzurata ake kara yi in ana lallabata, ita ai duk tunaninta tun bayan da Abdul ya koya mata rayuwa ta ajiye wani shagwaba da iskanci a gefe ta canza hali, ashe ba haka bane waje ne bata samu ba kukan banzan n
a nan har yanxu, a haka su Jay suka iso za su kai Nenne da Aunty Farida park, Ba Ajay kadai ba hatta Jay sai da yayi shock da Khaleesat a kofar gidan don tara masu jama'ar anguwan tayi da kuka da ruri a kofar shiga gidansu Aunty Murja ita baza a tafi a bar
ta ba, Aunty Murja na aikin lallashinta, Nenne ta dinga kauda kai tana daura gyale a kai tana rufe fuska tsabar kunya, Aunty Farida dama tuni ta shiga mota don bata da lokacinta, Jay dai ya kasa cewa komai don bai san lamarinta ya kai haka ba, can ya kall
i Aunty Farida yace "Aunty ko dai kawai ta dauko kayanta ku tafi" Aunty Farida tace "Ai babu inda zata je sai tayi kwanakin da aka ce tayi a gidan nan tunda gidan kanwar Babanta ce" kiris ya rage Ajay bai yi dariya ba a front seat yana kallon Khaleesat, ba
kin ciki kamar ya kashe Nenne don Khaleesah ta gama kunyatasu gaban surkai, Jay ya bude driver seat ya sauka ya nufeta, tana ganinsa ta bar wajen da sauri alamar bata ma son jin abinda zai ce mata kuma bata fasa rusa kukan da take ba, Nenne ta kalli Ajay c
ikin sanyin murya tace "Kaga mu yarinyar nan zata kunyata ta tona mana asiri a unguwan mutane ko? Gudun wancan yaron Awdul ya sa fa nace ta zauna nan ko na sati biyu ne shi ne take mana wannan tijara haka kamar mun ajiyeta wajen yankan kai" Ajay dai yayi m
urmushi kawai ya bude motar ya sauka ya koma driver seat ya zauna, da su Nenne basa wajen tsaf babu abinda zai hanasa korata da dorinar gaban motar, ya danna ma Jay horn alamar ya shigo su wuce, Nenne tace "Madallah, gwara ya kyaleta da halinta ya shigo mu
wuce don ba sauraronsa zata yi ba" Da kyar Aunty Murja ta shiga cikin gida da Khaleesat, Jay ya dawo ya bude front seat ya shiga, Nenne tace "Mu bamu san har yanxu bata dena wannan shagwabar ba wallahi, ko kanninta basa mana wannan iskancin mu dai" Duk ba
yan sati hudu zuwa shidda ake shirya meeting a fadan dake bangaren sarki, wanda kusan kowa na family din ke halartan wannan meeting din barin wa enda ke gari har ma wasu da ba gari suke ba kuma suna da sararin zuwa, tun daga jikoki, 'ya ya, kanni, yayyi, c
ousins da dai sauransu, akwai kuma meeting da ake yi bayan wata uku amma ba na kowa da kowa ba, duk meeting din da za ayi Mami bata ta
ɓ
a halartan ko daya, don ko tana gari bata zaman meeting din, rabonta da zama ayi meeting da ita zai fi shekara goma, sai
dai daga baya a gaya mata me aka yi wajen meeting din, duk aka yi mamakin ganinta a wajen ranan, shi kansa Jay was surprise seeing her at the meeting, sai da ta jira aka gama meeting lafiya sannan daga karshe tace tana da magana, Sarki na kallonta ya bata
daman magana, Aunty ta gyara zama don duk tare suka shirya komai, Kai tsaye Mami ta fara magana tace "Ranka shi dade, duk da ni dai nasan bani da matsayin da za a sanar min abinda aka zartar kan Jawwad, amma dai na samu labarin har an kai kudin aurensa Kan
o, to ni duk wannan ba matsalata bace don yawanci duk abinda ya shafesa dama sai an zartar nake sani, to babban abun tambaya a nan shi ne haka aka je neman auren babu bincike kenan ranka shi dade?" Wata cousin sister din Mai martaba wanda duk ta girme ma m
atan dake zaune gun meeting din cikin fushi tace "Ki kula Fulani da sarki fa kike magana, ya kamata ki tausasa kalamanki ki kuma san abinda ke fitowa bakin ki" Mami ta wani kalleta daga sama har kasa, shi dai Mai martaba kallon Mami kawai yake, Ajay ya kal
li Jay dake kallon Maminsa shi ma with shock, Mami ta ci gaba da maganarta babu yabo babu fallasa tace "To idan kuwa haka aka je neman auren yarinyar nan babu bincike ya kamata a koma ayi bincike kasan wacece kake kokarin hada
ɗ
an
ɗ
an uwanka aure da, ni da
ya zame min dole tunda
ɗ
a na ne shi nayi iya binciken da zan yi ban ga ta inda aure zai kullu tsakanin Jawwad da yarinyar nan ba, don kuwa shi din ba sa'an aurenta bane ta ko ina...." Bayan kusan minti daya Mai martaba yace "Fulani, no one is in the right
ful place to question my decision in this palace, duk abinda na zartar hakan zai kasance in sha Allah, babu me canza hakan har ke da kike mahaifiyar Ahmad...." Mami tace "Kana nufin ka zartar da hukuncin Jawwad ya auri bazawara mara cikakken asali sannan e
r kananan mutane?" Tsawa Hajiya Shafa'atu da ta fara yi ma Mami magana tun farko a parlon ta sake yi mata tace "Kina cikin hayyacin ki kuwa Fulani? Shi Mai martaban kike furta ma wa ennan kalaman? Menene wannan ya same ki?" Rai bace Mami tace "In dai akan
Jawwad ne baza a ta
ɓ
a samuna cikin hayyacina ba, yau in uban Jawwad na da rai zai yarje ma Jawwad auren bazawara mara asali? Bazawara fa? Anya an duba ma uban Jawwad da ƙasa ta rufe ma ido kuwa? Yau don babu shi a duniya sai ayi ma
ɗ
an sa haka?" Kowa dake
zaune a fadan was speechless and shock at Mami's action banda Aunty, Mami ta ci gaba kanta tsaye babu ko shakka tace "In lamarin gaskiya ne a aura ma Junaid da ko macen auren bashi da ita har yanxu mana, sai Jawwad da kowa yasan da maganarsa da Hadiyah?" M
ai martaba ya
ɗ
an yi murmushi, abubuwa da yawa suka sa yake raga ma Mami kuma zai ci gaba da raga mata saboda abubuwan nan, bazai ta
ɓ
a daukan mataki akan ta ba, with calmness yace "Ai Junaid bai kawo min ita yace yana so ba Fulani, don haka shi Jawwad din
da ya ganta yace yana so shi din dai zai aureta ko ki amince ko kar ki amince, idan kuma da inda aka haramta auren bazawara a addininmu Enlighten us" Yana kai wa nan ya mike, Hajiya Shafa'atu ta fara basa hakuri cikin girmamawa tana jero masa kirari, Jay c
ouldn't believe all what his Mami was saying, he was just shock and weak, Mai martaba na barin fadan Ajay ya mike shi ma zai fita, cikin fushi Aunty da Mami suka hada baki wajen cewa "Munafiki, me mugun nufi, duk kai ka hada wannan tuggun...." Shi dai ko k
allon inda suke bai yi ba har ya fita, Mami ta ci gaba tana huci tace "Sai dai in bayan raina ne za a aura ma Jawwad bazawara wallahi, ai in an san wata ba a san wata ba" Tana kai wa nan ita da Aunty suka fice daga fadan, kuma duk wannan abun da Mami tayi
bata yarda ko da wasa ta hada ido da Jay ba ko kuma ta kalli inda yake, yi ma tayi kamar bata san yana padan ba.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
0708786578
8
HALYSAAH 95
Ajay ya bude kofar dakin Jay a hankali yana kallonsa, za
une ya samesa kan kujera yana danna wayarsa, karasawa cikin dakin yayi ya zauna still looking at him, shi dai Jay bai kallesa ba he was just pressing his phone, wani lokacin har mamakin karfin hali irin nasa Ajay yake yi ga dakiya da basar da duk wani situ
ation that is a threat to him in anyway, bayan kusan minti daya Ajay yace "I think this shouldn't be something to be worried about Bruh, I guess you weren't expecting less duba da cewar baka sanar masu wacece yarinyar da kake son aure ba, sannan baka gaya
masu matsayinta ba so their reaction is nothing to be surprised or worry about, even our dad was a bit disappointed at first after finding out truth, so sauran ma duk za su yi give up su hakura daga karshe, just that you have to turn deaf ear since the kin
g is fully in support of you" Shi dai Jay bai ce komai ba kuma bai
ɗ
ago kansa ba, mikewa Ajay yayi yace "Abba yace kaje yana jiran ka..." Daga haka ya juya zai fita daga dakin sai kuma ya karasa gaban mirror dake dakin ya dau turarensa biyu da Jay ya ajiye
wajen, ta madubi yaga Jay na kallonsa, Ajay ya bude turarurrukan yana perceiving kamshinsu yace "Why will you hijack my birthday gift..." Shi dai Jay bai ce masa komai ba, Ajay ya dau wanda kamshinsa yayi masa ya bar masa dayan sannan ya fita daga dakin.
Jay na zaune gaban Mai martaba idonsa a kasa yana sauraronsa, Mai martaba yace "Don haka ka kwantar da hankalin ka Ahmad, babu me hanaka auren yarinyar nan as far as I am concern don baza a maida ni karamin mutum ba, Fulani kuma ka kyaleni da ita ni nasan
yanda zan yi da ita, kaje ka ci gaba da shirye shiryen ka tunda kaga ba lokaci me tsawo aka tsayar ba don nasan ire iren issue din nan dole zai yi arising daga
ɓ
angaren iyayenka mata dama, daxu mun yi magana da Shafa'atu akan kayan da ake hadawa na aure, s
o ita zata hada na ita wancan yarinyar, su kuma nan su hada na Hadiyah ina ga zai fi" A hankali Jay yace "Nagode Abba, Allah ya kara girma" Mai martaba yace "Za ka iya tafiya Ahmad" Mikewa yayi Mai martaba ya bi sa da kallo har ya fita. Jay na fita parlon
Mai martaba babu dadewa sai ga Aunty ta shigo parlon, ta ajiye masa fruit din da ta kawo masa ta zauna tayi masa sannu da hutawa sai kuma tayi shiru, bayan wani
ɗ
an lokaci cikin kwantar da murya tace "Ranka shi dade dama wata er shawara ko ince suggestion
nake son badawa idan ka bani dama" Sarki na kallonta calmly yace "Ina jin ki Fulani" Ta gyara zama cikin nutsuwa ta fara magana tace "Ranka shi dade akan zaman Meeting din daxu ne da aka karesa babu dadi a zukatan mu gaba daya, sam ban ji dadin irin magang
anun da Fulani Asiya tayi maka akan
ɗ
an ta ba a gaban kowa da kowa, kuma ba yau ta saba maka irin wannan ba, amma na yau yayi min ciwo matuka, tun safe har yanzu bani da sukuni, ni kuma bana son biyeta mu yi batattciya a gidan nan, shi ne ni a nawa tunanin
nake ganin for peace to reign da an hakura da batun auren ita bazawaran nan tunda har Asiya ta nuna bata so, yanxu zancen da nake maka maganar nan duk ya zagaye masarautar nan kan kace me kuma har cikin gari sai maganar nan ta fita, kaga nan jama'a za su
dinga ganin don ba
ɗ
an cikin ka bane shi yasa ka amince da bukatarsa na auren Bazawara, don guje ma wannan zargi ina ga zai fi kyau a ajiye batun auren yarinyar kawai mu yi facing na Hadiyah ranka shi dade, ba wannan karon bane na farko da mutane ke ganin
kamar kana nuna bambanci tsakanin Jawwad da Junaid, ita dama Asiya kullum tunaninta a haka yake tana ganin baka yi ma
ɗ
an ta adalci don kawai ƙasa ya rufe ma ubansa ido, to ina amfanin wannan ranka shi dade ana
ɓ
ata maka suna a gari? Tun asali bai kamata k
a biye Jawwad da maganar nan ba duba da irin zaman da uwarsa ke yi da mu da wasu abubuwa marasa amfani da ta dauka ta saka a ranta taki a zauna lafiya, don haka ni a nawa karamin tunanin ya kamata kayi watsi da maganar bazawaran nan don a samu zaman lafiya
a gidan nan ka kuma guje ma kanka zargin da jama'a za su fara yi maka, tunda ga
ɗ
an cikin ka Junaid har yanxu ko buduwar auren ma bai da ita kuma baka ce lallai sai yayi ba, yanxu fa kamar ace Walid ya kawo maka bazawara mara asali yace zai aura ne, zaka
fara sauraronsa? Amma fa ni a karamin tunanina nake magana ranka shi dade tunda ban fi ka hangen nesa ba, kuma ina fatan ban
ɓ
ata maka rai ba Ur Highness" Mai Martaba dake ta sauraronta ya
ɗ
an yi murmushi yace "Kina zaune da ni shekara da shekaru kin ta
ɓ
a
ganin maganganun mutane ya girgiza ni ko ya hanani abinda nayi niyya Fulani?" Aunty tayi shiru, yace "Don haka in this case i don't think there is anything that will move me, as far as Ahmad is okay with marrying the lady, I am also okay with that, kawai d
ai Hadiyah ce zata zama matarsa ta farko kafin ita yarinyar wanda na riga na sanar da hakan tun farko, Walid kuma da kika ce in yau ya kawo min bazawa yace yana so zan basa shawara ya hada da budurwa duk a aura masa, hakan ma gata ne ai" Aunty ta sauke wan
i ajiyar zuciya ganin babu nasara a plan din nan ma, shiru tayi bata sake cewa komai ba. Har washegari Jay bai yarda ya hadu da Maminsa ba cause deep down he was really disappointed, tun jiya har yau bai dawo dai dai daga shock din da ya shiga ba, it was s
omething he never saw coming, ko da ya dawo masallaci ko zuwa gaisheta kamar yanda ya saba bai yi ba ya koma bangarensa ya kulle, bai san ita ma ana idar da asuba ta bar masarautan ba da traveling luggage dinta.... Wajen karfe shidda na yamma Malam Ali na
tsakar gida bakin pampo yana alwala, Nenne na zaune kan farin kujeran roba tana kara jaddada masa abubuwan da za ayi ma Khaleesat na fita kunya tunda ba karamin gida za a kai ta ba, Tace "Wallahi Ali sai kaga setin kayan gadon aka ce mana miliyan uku bab
u ragin ko biyar, setin kujeru kuma Miliyan biyu cif cif, in ba 'ya yan sarakunan