Showing 453001 words to 456000 words out of 641791 words

Chapter 152 - HALYSAAH COMPLETE

gyars

kwanciyarta har sannan mamaki kwance fuskarta tace "Ke da wa ku ka zo Noor?" Noor na murmushi ta zauna gefenta lace "Ni da Nenne da Aunty Murja" Khaleesat ta zaro ido tace "Yau ku ka zo ko yaushe?" Noor tace "A'a 3 days ago muka zo, muna gidan Aunty Murja

all this while" Khaleesat felt so happy seeing her sister, amma kuma deep down bata so zuwan su tana cikin halin da take ciki ba, gashi ko zama sai ta daure take iya yi, a hankali ta kamo hannun tace "Umman mu fa?" Noor tace "L tana gida Khaleesat tace "Ba

ba yace a gaisneni?" Noor na murmushi ta gyada máta kai, Khaleesat tace "Islam kuma taki ta biyo ku ko?" Noor tayi dariya tace "Tace ita bazata je ba" Khaleesat ta jawota jikinta tace "How about Aunty Farida?" Noor tace "She is at home too" Nenne ce ta shi

go dakin da Aunty Murja, Khaleesat tayi murmushi tana kallon Nenne tace "Shi ne baku ce min za ku zo ba Nenne" Nenne ta zauna kan Carpet tace "Meye hadin biri da gada Khaleesah, ni wajen Murja na zo duba mara lafiya, tana ta yawo gwanin sha'awa a keker gur

agu da Mijinki ya siya mata me tsada irin na kasar waje wallahi, kamar ma keken da kansa yake tafiya fa" Khaleesat ta sauke kai bata ce komai ba, nan da nan mood dinta ya canza bayan Nenne ta ambato mata Ajay, Nenne dai ta ci gaba da bada labarin keken yar

inyar Aunty Murja da kuma uwar kudin da Ajay ya bada a dinga kula da lafiyan yarinyar, gashi yarinyar ta dawo fes da ita kamar ba me lalura ba, To cut the conversation Khaleesat ta kalli Aunty Murja dake ta murmushi tace "Aunty ya Aunty Murja tace "Alhamdu

lillah Khale Ina ta son zuwa amma ban san ko kun dawo daga Amurkan ba, sai da Nenne ta zo take gaya min ai kun dawo tuntuni..." Khaleesat ta dan yi murmushi tana wasa da duvet din jikinta, Nenne tace "Ni banda ma Murja ta hadani da Allah mu taho mu duba k

i ai baza ki gan mu a gidan nan ba Khaleesat, mun ma yi ta kiran mijinki daxu bamu samesa a waya ba, ashe ma baki ji dadi ba yanxu Hajiya ke gaya mana ai baki da lafiya" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Nenne tayi kasa da murya tace "To me ya

ke damunki? Na ma ga kin yi kyau kin kara haske, idanuwanki ne dai suka fada" Sai kuma ta kalli Noor tace "Ke Noor tafi parlor tunda kun gaisa mu ma yanxu za mu fito" Mikewa Noor tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kulle kofar, Nenne ta kara yin kasa d

a murya tace "Ko ciki ne da ke?" Khaleesat ta hade rai taki bata amsa, Nenne tace "Ba hade rai ba ki bude baki ki min magana don duk nasan halin da kike ciki tunda ke munafuka ce algunguma warce bata san ciwon kanta ba, yanxu idan baki gaya ma İyayen da su

ka haife ki matsalarki ba uban wa gare ki a duniya da zaki gaya ma? To da yake wannan kawar taki er albarka c ta gaya min halin da kike ciki tun aurki na farko ashe dalilin mutuwan auren kenan ma, mu zaki tona ma asiri wancan kin yi shiru an sako ki duk da

gantalallen aure ne kuma sakin shi ne mafi alheri, wannan kuma auren da kowa ke alfahari da shi shima so kike ki kashesa? Ina batun aure babu kwanciya? Aure tsawon wata shidda amma haka Yariman ke kallonki shi bai gaya mana matsalar ki ba don shi din yaro

ne me kunya da nutsuwa, ke kuma mahaukaciya kin ki magana mu san na yi? to bamu haifi er da zata tona mana asiri a duniya ba, don haka ga nan magunguna a jakana babu inda ban shiga ba da taimakon uban kishiyar Murja mun nemo maki taimako, an kuma tabbatar

mana asiri ne a jikin ki shi yasa hakan ke faruwa, duk ma wanda yayi maki wannan asiri kina fara maganin zai koma kansa, tun da na shigo garin nan ban zauna ba sai fafutukan nema maki mafita nake duk ranan garin ya babbake min fuska, yanxu dakin naki ne n

an? Sai ki samu akwati ki saka magungunan a ciki kar ayi tunanin wani mugun abu na kawo maki masarauta?" Khaleesat da har sannan fuskarta ke daure tace "Ni ba dakina bane nan" Hajja tace "Dakin waye nan din?" Khaleesat ta kai tace "Bangaren Hajja ne gaba d

aya Nenne ta ja bakinta ta tsuke tana rarraba Ido jin abinda Khaleesat tace, can dai kuma ta kara cewa "To babu wannan kamaran da masu kudi ke sakawa ya nannade maganar mutane?" Khaleesat ta girgiza mata kal, Nenne tace "Ba kuma abun in ce ki tashi mu je b

angarenki ba ayi tunanin wani abu na kawo maki, ae da sai mu koma sashin ki tunda mun gaisheta" Khaleesat tace "Bani da lafiya ai shi yasa nake nan" Nenne tayi kasa da murya sosai tace "To ni dai ban san yanda zanyi da itatuwan nan ba, ban san yanda zan da

mka maki a hannu ba ki fara amfani da su cikin gaggawa, ba aburi in bude jakar ba ma yanxu aji kamshinsu a zata wani asiri ne" a hankali Khaleesat tace "Duk ranan da za ku koma Kano ai sai inje gidan Aunty Murja in maku sallama sai ki bani a can" Nenne ta

hade girar sama da ta kasa tace "Ni da nake son in ga aikin maganin kafin in tafi? Ai sai naga kamun ludayin lamarin zan bar garin nan, Sai dai in kin zo da sunan yi mana sallama sai in baki sannan in zauna har sai naji yaya ake ciki idan kika yi amfani da

su, don gaskiya wannan babban magana ce ba karam wallahi ko bacci ban yi ba ranan da Safiym ta gaya min, ana idar da sallah na sa Malarn Ali ya goyani a machine sai tasha, kin san ya siya machine sabuwa dal Khaleesat ta dan yi murmashi tace "Da gaske Nenn

e?" Nenne tace "Al Malam Ali Alhamdulillahi yanxu, kasuwancinsa na ta bunkasa a sannu sannu" Khaleesat tayi shiru, nan ta fara tunanin ba ma Abban nata miliyan goma daga cikin account dinta ya kara jari, don kudaden ciki yanxu sun yi 16M, a hankali tace "N

ima in sha Allah zan zo Kano, ko kuma in bi ki mu koma tare" Nenne ta hade rai tace "Ki zo ki mana uban me, in ba jinyan laulayin ciki zai kawo ki ba babu shegen dake bukatar ki a Kano a yanxu dai" Khaleesat ta dinga kallon Nenne, Nenne tace "To shikenan t

unda mun gaisa kuma kince zaki je can gidan bari mu tashi kawai mu tafi, kar a ga mun dade cikin dakin" Daga haka ta mike tana gyara yafin gyalenta tace "To tashi ki mana rakiya ko?" Khaleesat tayi shiru, Aunty Murja tace "Nenne a kwance fa muka sameta ba

lafiya, mu yi tafiyarmu kawai in ta samu sauki sai taje can gidan namu" Nenne ta tabe baki ta nufi kofa, Aunty Murja tayi ma Khaleesat sallama sa murmushi ta bi bayan Nenne, Khai ta sauke idonta jin hawaye ya fara taruwa idon, a nake su zsunty murje suka l

ite uaja dakin, Hajja na parlor har sannan da Noor a gefenta tana cin Apple din da Hajja ta sa ta dauka, tana ganin sun fito ta mike ta koma wajen yayarta a daki, Hajja na kallonsu Wenne tace "Madallah har kun fito" Nenne tace "Mun fito ranki shi dade, ung

uwanmu da nisa shi ne nace gwara mu kama hanya da wuri kar yamma yayi mana a hanya" Hajja tace "A'a ba kwana biyu ku ka zo yi mana ba dama" Nenne na murmushi tace "Daga mu sai kayan jikinmu fa ranki shi dade, dama ziyara ce kawai ba wani abu ba" Hajja tace

"Ikon Allah, duk tunanina za ku mana kwana biyu, amma ya kamata gaskiya ku dawo da shirin kwana" Nenne tace "Gaskiya ne Ranki shi dade" Daga part din Hajja masu aiki suka yi ma Nenne da Aunty Murja rakiya zuwa bangaren Mami don can aka kai masu abinci, na

n din ma Nenne tace a koshe suke iya fruits kawai suka sha sai su alkaki da dublan da suka ci, ba yanda Mami bata yi dasu su ci abinci ba suka ki. Bayan sun yi sallan la'asar Mami tace "Ai Yariman ma ba shi da lafiya Hajiya, shi yasa ma zo gaishe ku ba yan

a can kwance sh Nenne tace "Subhanallahi, ai kuwa daxu nasa Murja ta kirasa ta sanar masa za mu shigo Gidan Sarki don hatta ita Khaleesat din bata san da zuwan mu ba wallahi, to Murja bata samesa a waya ba ashe bai da Isfiya bawan Allah" Mami tace "Wallahi

kam bal ji dadi ba" Nenne tace "To Allah (Ubangiji ya basa lafiya, Allah ya sa kaffara ne" Marni tace "Ameen, bari in raka ku can bangaren nasa sai kuyi masa sannu" Nenne tace "Eh gaskiya kam ya kamata" Mami ta rakasu har part din Ajay suka zauna babban p

arlor, ita kuma ta karasa cikin Parlonsa, zaune ta samesa yana shan fruit ga darduma a shimfide parlon alamar sallah ya idar, he looks much better akan few hours ago, tace "Ka tashi baccin Junaid?" Ya sauke idonsa yace "Na tashi" Tace "Ya jikin fa?" Yace "

Da sauki" Mami tace "Kakar Halysaah ce suka zo, ka fito ku gaisa za su koma ne yanxu" Ajay ya daga kai da sauri ya kalli Mami, ko me ya tuna sai kuma yayi maza ya sauke kai bayan sun hada ido, Mami na kula da tun safe yaki yarda ya hada ido da ita yanxun m

a by mistake hakan ya faru, yayi kasa da murya yace "Mami ko dai ka kice ina bacci" Mami ta kallesa daga har kasa tace "Ko ba bacci ba, dalia tashi mu fita Malam, gida za su koma, Drivern da zai maida su ma na jira a waje" Ajay bai ce komai ba kuma bai dag

o kansa ba, Mami ta juya ta fita ta koma can wajensu Nenne, da kyar Ajay ya mike ya fita daga Parlonsa, yana shiga Main parlor ya zauna kan Carpet yana gaida Nenne da Aunty Murja kansa a kasa, Nenne ta amsa cike da damuwa tace "Sannu Ahmad, ashe baka ji da

di ba, Allah Ubangiji ya baka lafiya ya sa kaffara ne" Bai dago kansa ba yace "Ameen Kaka" Aunty Murja ma tayi masa fatan samun sauki, yace "Ameen, ya Jeeddah fa" Aunty Murja na murmushi tace "Tana nan lafiya wallahi Yarima" Basu fi minti biyar a part din

Ajay ba Mami ta mayar da su bangaren Hajja za su mata sallama, tsadaddun atamfofi biyar Hajja ta sa aka debo ma su, sai turarurruka kusan kala goma, sannan ta hada da dubu dari a kan kayan, ta kuma dage in dai za su bar Bauchi su zo ayi sallama, Nenne dai

sai godiya take mata haka ma Aunty Murja, Mami na kallon Nenne tace "Tunda za ku kara kwanaki a Bauchi ai da kun bar takwaran Hajja wajen yayarta tayi mata kwana biyu" Hajja tace "Gaskiya kam, ma naga ai duk anyi hutun makaranta Baby ma yau aka je daukota

daga makarantar su, kilan ma sun kusa yanzu haka" Nenne tace "To shikenan ranki shi dade sai ta zauna din har zuwa sanda za mu koma in sha Allahu" A haka Mami tayi ma su Nenne rakiya zuwa gun mota..... Maganganu ne fal cikin Nenne amma ba daman yi, har sai

da suka bar gidan a motar da zai maida su gidan Aunty Murja sannan ta kalli Aunty Murja tayi kasa da murya tace "Ke Murja wannan matar da ta mana rakiya fa kamar Uwar Jawwad ce in dal ba idona ke yaudarata ba, har gida fa tayi gayya suka je suka ci mana m

utunci babu abinda suka mance basu gaya mana ba daga karshe tace dan ta bazai auri Bazawara ba, muka ci kukan mu muka gode Allah, to sai kuma gashi naga mun zo....." Da sauri Aunty Murja tayi ma Nenne alamar tayi shiru ga dreba, Nenne tayi maza ta rufe bak

inta tana zare ido, bata sake cewa komai ba a motar, amma fa kanta ya gama kullewa ganin irin tarban da Mami tayi masu, duk da a farko ta ma kasa hada ido da su, to ko dai kawai kamanni ne. Bayan tafiyarsu Nenne Dr din dake duba Khaleesat ta zo ta d tayi m

ata injections dinta sannan ta wajen karfe biyar Hajja ta mike tana kallon Noor dake zaune parlon don Khaleesat tayi bacci tun da aka mata allura, Hajja ta sa daya daga masu aikin dake Part din nata su kai Noor wajen Mami don ita part din Jay take son tafi

ya don yanayin da ta gansa daxu taga alamar magana ya shigo yi mata sai kuma ga kakar Khaleesat, Yana zaune Parionsa ta samesa yana kallo, ta zauna kan kujera tace "Ina Hadiyah?" Ya jinginar da kansa da kujera bayan ya rage volume din TV din without lookin

g at her yace "I don't know, kilan tana can cikin gida" Hajja tace "Maimakon ta zauna ta kula da kai baka da lafiya sai ta tafi gantali cikin gida?" Shi dai bai ce komai ba don shi rabonsa ma da ganinta tun wajen 12 na rana da ta shirya ta ci kwalliya ta t

afi can wajen uwarta da yan gidan, Hajja tace "Amma jikin da sauki?" Yace "Na ji sauki" Tace "To an kawo maka abinci kuwa tunda ita gantalalliyar bata nan?" Duk da bai ci ba yace "Na ci" Hajja ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma tace "Daxu ka shigo kamar zaka

min magana sai ga baki sun shigo" Ya girgiza kal yace "A'a, naje daukan abinci ne" Hajja tayi shiru kallonsa, ya gyara zama yace "Na ji za ayi meeting bayan Magrib, don Allah Hajja ina son ki nema min alfarma gun Mai martaba Ina son zan koma UK in nemi ai

ki a can" a hankali Hajja tace "UK kuma Jawwad?" Mace "In sha Allah" Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kasan bazai amince da haka ba Jawwad" Jay yace "In ke kika yi masa maganan nasan zai amince" Hajja bata sake cewa komai ba a Parlon, after a wh

ile ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ka je can bangarena ka sameni nan da minti sha biyar" Daga haka ta mike ta fita daga parlonsa, bangaren Ajay ta nufa zata dubasa, ya fito daga kitchen kenan rike da cup din Coffee Hajja ta iso corridor din, ta bude

kofar Parlonsa ta shiga ya bi bayanta, ta zauna kan kujera tace "Kajl dama dama kenan" Bai ce komai ba ya zauna sannan ya gaisheta ba tare da ya kalleta ba, tana kallonsa tace "How are you feeling now?" Shi dai bai dago kansa ba a hankali yace "Alhamdulil

lah" Hajja tace "Tunda jikin ka da sauki kaje ka duba matar ka" Sai da gaban Ajay ya fadi jin abinda Hajja tace, yayi yana juya Coffee din hannunsa da s a hankall, Hajja tace "Ko kuma ka tashi mu tafi, tana can bangarena..." Da sauri Ajay yace 'A'a sal anj

ima Karfe shidda saura Jay ya shigo parion Mami ta dalilin kiransa da tayi a waya, zaunawa yayi kan kujera donsa a kan TV yace "Gani Mami" Mami dai ta ci gaba da dama fura da take, Noor na zaune kasan carpet tana kallon Tv, tun daxu take son komawa part di

n Hajja taje gun Khaleesat amma ta kasa gaya ma Mami, Noor ta gaishesa, jin bai amsa ba Mami tace "Ana gaishe ka" Bai cire idonsa akan TV ba Without interest ya amsa a takaice, Mami dai ta ci gaba da abinda take, ya kara kallon Mami don barin parlon yake s

on yi yace "Mami kin yi kirana" Mami tace "Fura da nono ne gashi nan ban gama damawa ba" Yace "A'a bazan sha ba, na koshi" Yana fadin haka zai tashi Mami tace "Ka jira in gama ka tafi da shi, duk sanda ka so sha sai ka sha" Shiru yayi bai ce komai ba amma

ransa bal so ya tsaya din ba, after some minutes Mami ta kalli Noor tace "Je kitchen ki dauko cup in zuba maki Noor" Noor ta dan yi murmushi tana girgiza kal tace "Na koshi" hatta muryarta Mami jin sa kamar ne Khaleesat, Jay ya mike à Laka yace "Mami idan

anyi sallah zan dawo Dai dai nan aka bude kofar parlon sai ga Hadiyah ta shigo, kallo daya tayi ma Mani sai kuma ta kalli Jay ta hade rai tace "Sni ne tun daxu nake neman ka ashe nan ka zo ka zauna.... Mami ta daga kai ta kalli Jay tace "Je ka, zan bada fu

ran ma...." Hadiyan ta wani kalleta, sal kuma ta tabe baki ts juya ta fice daga parlon without noticing Noor, Jay ya nufi kofa ya fice daga parlon. Bayan Magrib Ajay ya dake ya fita daga part dinsa zai je bangaren Hajja, kansa a kasa yake tafiya slowly yan

a sanye da thick Jacket dinsa ya saka har hulan Jacket din da ya rufe har kusan goshinsa kamar wani Villain, hannunsa duk biyu na cikin aljihun jacket din, har lokacin jikinsa a sanyaye yake sannan ba wal wani karfi yaji ba sai karfin hali, duk baccin da y

a dinga yi yau Khaleesat kawai yake gani a baccin nasa, condition din da take ciki ya tsaya masa sosai a rai duk da halin da shi ma yake ciki but gaba daya hankalinsa na kanta, he couldn't sleep all through yesterday a haka ya isa part din Hajja

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login