Showing 600001 words to 603000 words out of 641791 words

Chapter 201 - HALYSAAH COMPLETE

ya sauka daga kan gadon, zai dau Atm card Jay ya rigasa dauka ya nufi kofa ya fita Ajay na biye da shi a baya, tsaye Jay yayi a corridor din dakunan hotel din with the room key a hannunsa yana

jiran fitowar Ajay, bayan Ajay ya fito Jay yace "Let me get my phone...." Komawa cikin dakin yayi ya kulle kofar ya sa makulli yace "Good night, ai jiya ba dakin nan ka kwana ba" Ajay yayi murmushi ya jingina da bango yana shafa gashin kansa, a lokacin da

ace da Atm card a hannunsa wani dakin kawai zai biya ya shiga ya kwanta, ya fi minti biyar jingine da bango bai dai ce ma Jay komai ba, can ya gyada kai kawai ya nufi dakin da Khaleesat take, bude kofar yayi ya shiga ciki, tana kwance yanda ya bar ta, tana

jin shigowarsu ta dena kukan da take kuma bata juya ba, ya karasa yayi kwanciyarsa other side of the bed, tana ganin haka ta dau pillow ta sauka ƙasan tiles ta kwanta fuskarta a murtuke, shi dai kallonta kawai yake, kamar bazai ce komai ba, kawai dai yace

"Koma kan gadon ki ni zan kwanta a kasa" Kamar jira take ta mike a fusace tace "Kar ka sake min magana" Yace "Ohk...." Ta dake kar ta fashe da kukan da ya zo mata tace "Dama saboda ka walakanta ni ka taho da ni garin nan ashe...." kamar Ajay bazai tanka t

a ba, after some seconds yace "Idan baki gode ma mutanen nan ba baza ki je kina frowning masu fuska ba Jeeddah, why are you taking every little thing too personal? Mutanen nan sun yi deserving kiyi masu abinda kika yi?" A fusace tace "Na dauka personal din

, ok in gode masu rungumar ka da aka yi kake nufi ko? to ai ni ban ma yi zaton zaka bar garin yau ba, na zata can zaka kwana kana lallashin yarinyar tunda rayuwarta tsayawa yayi cak bayan ka bar garin" Calmly Ajay yace "Ai da na sani na kwana can din, tund

a shekara biyu nayi ina kwana gidan so ba sabon abu bane, kuma ko na kwana ina lallashin yarinyar she deserves it...." Mikewa Khaleesat tayi ta dau hijab dinta ta fice daga dakin, direct dakin da Jay yake ta nufa ta kwankwasa, duk zaton Jay Ajay ne ke kno

cking yaki tankawa, har sai da tace "Ya Jawwad" Jay ya mike ya nufi kofar dakin ya bude yana kallonta, kawai ta bi gefensa ta shige cikin dakin ta fashe da kuka, ya bi ta da kallon mamaki yace "Me ya faru?" Taki ce masa komai ta fada kan gadon tana rera ku

ka kamar an aikota, Jay ya fita daga dakin ya nufi other room din, bude kofar dakin yayi yana kallon Ajay yace "What did you say to her?" Ajay yaki tankasa, har sai da Jay yace "Junaid...." Ajay ya kallesa yace "Abinda ta ce maka shi nace mata, pls first t

hing tomorrow morning kawai ka dauketa ku yi tafiyar ku gida, idan na gama abinda nake zan biyo ku" Kallonsa Jay ya dinga yi yace "You must be joking, no matter her tantrums ai sai kayi enduring since you know her condition" Ajay yace "Enduring din ne yasa

har yau ban ta

ɓ

a complain ba ai, ba wani condition, after all she is not the first woman to get pregnant, she just derive joy in creating issues out of nothing" Yana fadin haka ya mike ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa alamar baya ma son maganar, Jay

ya kunna wutan yace "Ina ma magana zaka kashe wuta" Ajay ya lumshe idonsa bai sake tanka Jay ba, har sai da Jay ya gaji ya fita daga dakin, lallashin duniya sai da Jay yayi ma Khaleesat amma kamar kara tunzura ta yake, daga karshe ya koma can dakin ya tara

r Ajay har yayi bacci abun sa, kwanciya yayi shi ma a dakin ya bar mata can dakin. Tunda Khaleesat ta kyallara ido ta ga Atm card din Jay a daki take ta Allah Allah karfe biyar na asuba yayi, ko baccin kirki bata yi ba wannan daren, karfe biyar nayi ta shi

ga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, ta shirya ta dau Atm card din da cash din dubu biyar da ta gani ta fice daga dakin, tsaf tana rike da pin din Jay a kanta don duk abinda suka siya a hanya sanda za su taho Benue da Atm card din suke using, ta

tare

ɗ

an sahu tace ya kai ta tashan da zata hau mota zuwa Abuja, a motor park ta shimfida

ɗ

ankwalinta tayi sallah, ta ciri kudi ta biya kudin mota me zuwa Abuja, bayan

ɗ

an lokaci suka dau hanya. Karfe bakwai na safe Jay ya ga debit din kudin da Khaleesat t

a cire a wayarsa, mamaki ne ya cikasa, ya juya ya kalli Ajay da ya koma bacci bayan sallan asuba, ya mike da sauri ya fita daga dakin, knocking yayi dakin da take amma ya ji shiru, hakan yasa ya bude kofar dakin yaga babu ita babu Atm card dinsa da cash di

n da ke hade da katin kudin, ya fi minti uku tsaye a dakin Khaleesat ta gama cikasa da mamaki, it was funny and at the same time not funny don ta tafi da Atm card ta bar su stranded a garin Benue, wato su karata, numberta yayi dialing yaji switch off, ya j

uya ya fita daga dakin, yana shiga daya dakin ya kai ma Ajay duka yace "Malam tashi zaka yi, baka ga ta bacci ba" Ajay ya bude ido yana kallonsa, Jay yace "Matar ka tayi tafiyarta da Atm card" Ajay ya dinga kallon Jay, can ya mike zaune yace "Sai kaje bank

i kayi using cheque ka cire kudi" Jay yayi masa wani kallo yace "Ranan Saturday din ne zan je bank? Kuma ta kama hanya ita ba isasshen lafiya ba amma kai maganar aje bank a cire kudi kake" Ajay yace "Ai daga jiya ta samu sauki, da za mu dawo da yamma kaga

ta kara langwabewa?" Jay yace "On a serious note this is way too early in ur marriage, kai baka san yanda zaka bi da matar ka ba? What if cikin jikinta ya samu matsala, public transport fa ta bi" Ajay yace "Wait Jay.... Tell me what my fault is in here? So

tayi nima in daure fuska yanda tayi masu a garin? Did she know how dear those souls are to me?" Jay dai kallonsa kawai yake.... Duk da yanda Khaleesat ta wahala a 6 hours journey din da suka yi from Benue to Abuja haka nan ta kara hawa wata mota zuwa Kano

daga Abujan, ai ko ta ji jiki ba kadan ba, har ta mance rabon ta jigata haka, ta dinga amai a hanya gashi babu komai cikinta, wannan yasa duk ta fita hayyacinta zazza

ɓ

i ya rufeta, mutanen cikin motar na ta tausayinta suna bata attention, a haka suka isa K

ano bayan isha'i mutane biyu daga cikin motar suka samar mata adaidaita sahu har zuwa tudun Yola, tun daga park aka biya mai adaidaita sahun kudinsa, wannan yasa yana parking a inda Khaleesat ta nuna masa a kofar gidansu tayi using strength dinta na karshe

ta shiga cikin gida ko gaida Mai gadin gidan dake zaune bakin gate da shi da Ɗan mijin Hajiya Zaliha bata yi ba, Mama Zubaida na zaune barandan Chalet dinta tana waya da er uwarta tayi saurin mikewa ganin mutum ya fadi a tsakar gida rigijib, da sauri ta s

auka kasa tace "Subhanallahi, Khaleesat, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya same ki?" Dagota tayi ganin kamar suma tayi yasa ta fara kwala ma mutanen gidan kira su fito su kawo agaji, wannan yasa Mai gadi da Haiydar suka shigo compound din da sauri,

Nenne ce ta fara fitowa a kidime ta saki salati ganin Khaleesat a hannun Mama Zubaida bata motsi, jiki na rawa ta isa kusa da su tace "Mun shiga uku mun lalace, me ya sami Junaidun kuma, wani iftila'in ya kara samun sa, ku kira min Parida jama'a, wayyo Al

lah na" Umma da Mama Shatu duk suka fito tsakar gidan da sauri, Umma was shock ganin Khaleesat a haka, ta ma kasa karasawa kusa da ita, Haiydar ya sa Mai gadi ya bude masa gate ya shigo da motarsa dake kofar gida don a sa ta a motar su tafi asibiti, su Mam

a Shatu ne suka dagata suka sakata a bayan motar, tuni Nenne ta shige motar babu ko takalmi balle gyale, Haiydar ya sa Mama Shatu ta shiga gaban motar sannan suka dau hanyar asibiti.... Sai wajen karfe sha daya da rabi na dare Khaleesat ta bude idonta da s

uka yi mata nauyi, Nenne dake zaune sai zuba uban gyangyadi take a gefenta ta bude ido da sauri jin motsin ta, da sauri Nenne ta mike ta fita ta kira likita don dama sun ce tana farkawa ayi masu magana, Khaleesat ta cire drip din hannunta cause she was pre

ssed, da kyar ta sauka daga saman gadon ta shiga bandakin dake ward din, ko da ta fito ta tarar da likitan da Nenne a ward din, Likitan na kallonta yace "Sannu Hajiya, how are you feeling now?" Khaleesat ta sauke idonta tana dafa bango ta isa har kusa da g

adon don jiri take gani, likitan dake kallonta yace "Tell me how you are feeling, ya jikin?" Khaleesat ta dafe gadon ward din ta duka a hankali tace "I saw spotting when i went to ease my self" Likitan ya

ɗ

an bude ido yace "Really? Light or heavy spotting?

" Cikin sanyin murya tace "Light" Likitan yace "Do you know the gestational age of the pregnancy?" Ta girgiza masa kai, yace "Baki yi scanning ba har yanxu kenan?" Ta gyada kai, yace "When last did you see ur period?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Almost

6 to 7 weeks now" Nenne dake gwale ido tana bin ko wannen su da kallo tace "Wai me ke faruwa ne? Sikanin din me za ayi? Ba na ce maka tana da juna biyu ba ku san irin alluran da za ku mata? Na fa gaya maka tun kan ku ta

ɓ

a min jikata" Likitan yace "Baaba t

unda kika ce tana da juna biyu ai mu mun san aikin mu...." Ya kalli Khaleesat yace "Ki kwanta Hajiya, ina zuwa" Juyawa yayi ya fita daga ward din, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Menene yake faruwa ake maganar gwaji" Khaleesat ta hau saman gadon a hankali t

ace "Jini na gani da naje fitsari" Nenne ta dafe kirji tace "Mun shiga uku mun lalace, jinin uban me, jinin al'ada ko me?" Khaleesat taki tanka Nenne ta kwanta kan gadon, Nenne ta kara zaro ido tace "Kaddai cikin ne ya zube Khaleesat?" Hawaye ya cika idon

Khaleesat taki cewa komai kawai ta fashe da kuka sosai, Sai ga likitan ya shigo da Nurses biyu, likitan yace "Kin ta

ɓ

a

ɓ

ari ne?" Nenne da duk ta rude tace "Tayi

ɓ

ari shekara biyu da suka wuce, likita ka gaya min lalacewa cikin yayi ne?" Bata jira me likita

n zai ce ba ta figi wayarta dake ruri ta daga ta kai kunne hankali tashe, Jay yayi mata sallama daga daya bangaren yace "Kaka ya sunan asibitin, mun shigo Kano yanxu" Nenne ta rushe da matsanancin kuka tace "Wallahi yanxun nan likitan ke gaya mana wai tayi



ɓ

ari Jawwal, cikin dai ya zube" Daga Nurses din har likitan sai da suka juya da sauri suna kallon Nenne baki sake, Sai da Jay yaji wani dum a kansa jin abinda Nenne tace, tana fadin haka kuma ta katse wayar tana rusa kuka, Ajay dake kallon Jay ganin yanda

yayi stiff a gaban motar ko motsi bai yi, lokaci daya yaji gabansa ya wani fadi, bai san sanda ya fixgosa ba zuciyarsa na bugawa yace "Me ya faru Jawwad?"

HALYSAAH PAGE 210

all this?" Ajay da hankalinsa yayi mugun tashi yace "Pls tell me what's hap

pening Jay? Did anything go wrong with her? Pls tell me" Jay na kallonsa yace "Sai da na ce maka ka bi ta a hankali saboda condition dinta, l told u this severally, to yanxu da ta yi miscarrying cikin hankalin ka ya kwanta ai ko?" Sai da Ajay yaji kansa ya

wani sara masa jin abinda Jay yace, everywhere became blurr to him at first, abinda Jay yace ya dinga yi masa yawo a kai, a hankali ya jinginar da kansa da kujeran motar ya runtse ido yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Bai ma san hakan da ya fada y

a fito fili ba, Jay yayi masa wani kallo, after a while ya ja tsaki don har cikin ransa bai ji dadin wannan abu ba kuma duk laifin Ajay ya gani ba nata ba, ya dau wayarsa yana tunanin wanda zai kira a gaya masu wani hospital ne don yasan in dai ya sake kir

an Nenne bayani zata tsaya yi masa tana koke koke, banda dare yayi da sai su tafi can Tudun Yola yasan a gidan baza a rasa wanda zai masu rakiya zuwa asibitin ba, but it's very late now, number Aunty Farida ya kira don ita ce ta fara kiransu bayan da Nenne

ta kirata ta daga mata hankali ita kanta tayi tunanin ko wani abu ne ya samu Ajay, tunda kowa yasan akan Ajay ne kadai za a ga Khaleesat a halin da ta shigo gida yau, har kiran ya katse Aunty Fa bata daga ba, Jay bai sake kiranta ba, can ya tuna yana da n

umber Umma, duba number yayi ya kira, ba a dau lokaci ba Umma ta daga, gaisawa suka yi sannan yace "Umma kiyi hakuri na kira ki a wannan lokaci" Umma tace "Ayya ba komai Ahmad, ya mai dakin taka?" Jay yace "Tana lafiya, dama Umma asibitin da aka kwantar da

Halysaah nake tambaya, yanxu muka iso Kanon za mu je asibitin" Umma tace "Ae kam ban san asibitin ba, amma bari a tambayo yanxu" Yace "To Umma" Katse wayar tayi tana kallon Islam dake dakin ita ma bata yi bacci ba, tace "Islam je ki duba ko Mama Shatu bat

a yi bacci ba ki tambayo ta wani asibiti ne" Islam ta mike ta fita daga dakin, babu bata lokaci sai gata ta dawo ta gaya ma Umma asibitin da Mama Shatu ta ce, Umma ta mika mata wayar tace "To kirasa ki gaya masa" Islam tayi dialing number Jay, bayan ya dag

a ta gaya masa sunan asıbitin.... Har Jay ya isa hospital din babu abinda Ajay yace a gaban motar, kamar ma baya cikin motar, gaba daya a sanyaye yake ba kadan ba, he looks so despondent at this point, Jay ya bude motar ya sauka, da kyar ya dake shi ma ya

sauka daga cikin motar, a haka suka shiga cikin asibitin with Ajay feeling so weak, gun Nurses dake reception suka nufa, bayan sun gaisa Jay yace anyi admitting patient dinsu ne daxu shi ne suka zo dubata, wata nurse tace "Wata warce kawo tare da kakarta?"

Jay yace "Yeah" Nurse tace "Sai da safe ne za ku iya ganinta, yanxu ta samu bacci" Nenne dake zaune a can wani gefe a reception din bayan likitoci sun koro ta daga ward din Khaleesat, ta mike da sauri ganin su Jay ta nufe su tace "Ashe asibitin yan iska k

awai Haiydar ya kawo mu Ahamad, tun daxu suka koroni waje ban san halin da jikata take ciki ba yanxu haka, kowa ya ki kulani balle in san me ke faruwa, na kira Parida tace gobe da safe zata taho don Sarki ma yace ta taho gobe" Jay ya sauke ajiyar zuciya do

n duk ta cika asibitin da magana, he wish bata ma hango su ba, A hankali yace "Amma kaka ai da baki kira Aunty ba tunda nace maki muna hanya" Nenne tace "Ai zubewan cikin ne ya gigita ni Jawwal, na fito ina ihu shine mutanen nan suka kulle kofar dakin suka

ki barin in kara shiga har yanxu da nake maka magana, kuma sun ki gaya min halin da take ciki" Ajay ya nemi waje ya zauna a reception din don ji yake tsayuwar na neman gagaran sa, Jay na kallon Nenne yace "Bari mu shiga Office din likitan mu yi magana da

shi kaka" Nurse din tace "Sorry, but Dr is not on seat now, sai da safe" Nenne ta kankance ido tace "Sai da sate za ayi me? Ban gane sai da safe ba bamu san halin da yarinya ke ciki ba, gaskiya Haiydar ya ja mana babban matsala wannan asibitin gantalallu d

a ya kawo mu, haba sai kace ba dan boko ba kawai ya kinkimo mu ya kawo mu asibiti babu bincike akan wani irin asibiti ne" Jay wish zai disappearing daga reception din, har yaji kansı fara ciwo a wajen, yaki ce ma Nenne komai, Dai dai nan wani likita ya shi

go reception din, Nurse din na kallon sa tace "Sir, wajen patient din ka suka zo...." Nenne ta dinga hararan likitan don shi ya koreta kuma yaki mata bayanin komai har yanxu, Likitan na kallon Jay suka gaisa sannan yace "Are you related to the patient?" Ja

y yace "Certainly..." Likitan yace "To mu je office" Jay ya juya ya kalli Ajay da ya mike jin abinda likitan yace, likitan na fara tafiya suka bi bayan sa, sai da likitan yayi nisa ya juya ya ga Nenne ma na biye da su, tsayawa yayi yace "A'a Mama, ban da k

e, ki koma reception kiyi zaman ki kawai" Nenne tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ko dai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login