Showing 174001 words to 177000 words out of 641791 words
dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin. Nenne na gyara daurin dankw
alinta tayi kasa da murya tace "To ke banda abun ki ai Zahra'u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi
suka yi da ita sun mayar da ita Bora? Ai bari ki ji Parida, Zahra'u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci
tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra'u na yi ma Ali addu'an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tuna
ninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin baƙin talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni'imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki
dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata? Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan y
i maganinsu daga Alin har Zahra'un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin? Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko? To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Kha
leesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wan
i
ɗ
an iska ma kar ya amince" Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga g
idan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace "Wai fita zaki yi ne Nenne?" Ba tare da Nenne ta juyo ba tace "To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lok
aci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata" Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sanna
n ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta.
_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da ka
yan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trus
ted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
👈🏻
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwa
nciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Read my book "HALYSAAH" on ArewaBooks, Platform available: "app only" :: https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH 54
Wajen karfe shidda
na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kac
e gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen 'ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana
kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la'asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu
ke yi mata ta nufi gun Umma tace "Zahra'u Alin ya dawo ko be dawo ba?" Umma ta gaida Nenne sannan tace "A'a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa" Nenne tace "Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi Ɗan Agundi, ni ce har Na'ibawa yau, tun safe na
bar gida sai yanxu nake dawowa 'yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai...." Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace "Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya
dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra'u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu
, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya" Umma na girgiz
a kai tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Nenne tace "Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi " Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke
ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace "Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska? Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kam
ar baka ta
ɓ
a haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle baƙi a kasuwar ka hakura da zuwa mana" Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace "To wajen kai da matar ka Zahra'
u na xo" Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace "To lafiya dai ko?" Nenne tace "A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin 'yan Adam sun zo gidan nan sun ce za s
u ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra'u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi? Da maya
r da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata? In ita Zahra'u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali? Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu? To wallahi ko karshen bangon
duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin" Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace "A ina kika ji wannan zancen Nenne?" Nenne tace "Labarin duniya na buya ne dama?
Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau...." Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace "Amma Nenne na farkon ma ba a wanye la
fiya ba shi ne za a sake na biyu? Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa
in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa 'ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fata
r ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta? Haba sam batun na
n babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi...." Nenne ta kundumo wani zagi tace "Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de karatu ne kamar tayi ta gama sai dai bakin ciki ya ka
she duk wani shege wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min baƙar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince
koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja m
ata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza K
haleesah take ba farin jininta ya shahara" Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace "Ke kuma Zahra'u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun? To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tu
nda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba" Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace "Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake ba
rin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama'an gari su ce a kaina? Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami'ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure
mata" Nenne ta kallesa da sauri tace "A gidan uban wa zaka samu kudin? Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra'ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra'ayinka
ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a garek
a to Bismillah" Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya
ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na 'yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina
bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba" Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace "Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji k
ina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra'u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta? Ita ta tsugunna ta haifar maki er? Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba? Saboda an san
baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin ƙwaƙwalwa zaki yarda ta yanke hukunci akan 'er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai
san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?" Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace "Lafiya Nenne? Ai magana t
a wuce yanda kika ce haka za ayi" Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace "Ali y
au sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin ƙwaƙwalwa wato mahaukaciya er macukule? Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya? Tunda nake me na ta
ɓ
a zuwa gun almajirin ubanta dake bara a
bakin danja nace ya bani? Me na ta
ɓ
a rokon uwarta me shanyayyen kafa? Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra'u ni na haifar mata er da zan yanke mata hu
kunci akan ta? Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na? Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe d
a ni Shatu tace min me son abun duniya?" Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace "Shatu ki tafi gida, sai na neme ki" Mama Shatu ta gwalo ido tace "Ban gane in tafi gida ba Malam, w
ani gidan zan tafi?" Malam Ali yace "Gidan iyayenki, ki je na sake ki" Mama Shatu ta zabura tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace" Labibah ta mike tana huci tace "Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu m
a" Nenne tace "Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai" Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace "Kar in dawo in sameki a gidan nan" Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a san
nan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace "Ke kam kinyi asara wallahi Zahra'u, ko wani bala'i ta dalilin ke
da tsinannun 'ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri'ar ki Zahra'u" Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama S
hatu na kuka sosai tace "Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra'u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min
ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na