Showing 489001 words to 492000 words out of 641791 words

Chapter 164 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

137

sa da ita yaga ko zata sauraresa Ajay ya daga kai ya kallesa sai kuma ya mike ya tsaya gabansa yayi kasa da murya yace "No, I kno

w she won't give me a listening ear.... Safiyyah tayi dariya tace "To shine baza kayi biyayya ba kana raina 3 months seniority" Ajay ya shafa kansa bai ce komai ba, Safiyyah na murmushi tace "Yanxu abinda zai faru Ya Junaid kawai ka koma gida, idan Ya Jaww

ad ya gama yi mata magana sai su koma can gidan tare, nasan kafin nan ta huce, yanxu idan tana ganinka bazata yi saurin hucewa ba" Ajay ya sauke idonsa a hankali yace "Ohk" Jay yace "No he should stay, she will listen in sha Allah?" Ajay ya daga kai ya kal

lesa yace "A'a zan tafi, she is still angry" Safiyyah tace "Gaskiya kam, just leave Ya Junaid.... Everything will be fine in sha Allah" Ajay na kallon Jay a hankali yace "Thank you" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciy

a ta koma ta zauna tana kallon Jay da ya zauna shi ma staring at the book shelf in the parlor kamar me tunani, Safiyyah dai bata ce komai ba, after some minutes ya kalleta yace "Safiyyah kin tambayeta me ya ja yayi mata maganganun nan?" Safiyyah ta dan yi

murmushi tace "Wai ya ga u are depressed, shi kuma bazai iya ci gaba da ganinka a haka ba, so he felt he can sacrifice anything for you, a takaice ya nuna mata dai you first before her, in dai farin cikin ka zai dawo shi zai iya rabuwa da ita haka yace mat

a" Jay ya dam yi murmushi kamar bazai ce komai ba, can yace "I think he is on weed" Sosai ya ba Safiyyah dariya tace "Ban gane he is on weed ba" Jay yace "Eh mana, kilan can Zanzibar din ya samo abunsa ya fara sha, if not shi din ne zai iya rabuwa da ita,

karya yake" Safiyyah ta dinga kallonsa ganin he was serious, ta kwantar da murya tace "Koma dai bazai iya rabuwa da ita ba ai gashi ya furta out of Empathy for you Ya jawwad, why not appreciate that?kana fa ganin halin da ya sakata saboda furucinsa meaning

he was serious with his words to her, if he wasn't serious bazai gaya mata ba sai dai ya gaya ma wani, ya nuna mata zai iya yin komai in dai akan ka ne, idan ma ba haka bane a ransa Let pretend da gaske yake mana" Jay ya gyara zama yace "In gaya maki meye

damuwar Ajay a yanxu?" Safiyyah tace "Ina ji" Jay yace "He no longer have anywhere to Hijack what doesn't belong to him, babu wanda yake pestenng yanxu yake damun rayuwarsa yake takurasa, babu wanda zai tsokana kawai don yaji dadi, sannan kinga ita macece

bazai iya daukan kayanta ya sa ba. Safiyyah na dariya tace "Stop it pls Ya Jawwad Jay ya dan yi murmushi yace "That's the fact" Safiyyah tace "Yanxu dai bari in je ince mata ya tafi in lallabata ta fito" Yace "Alright Safiyyah" Mikewa tayi ta bar parlon y

a jinginar da kansa da kujera ya rufe idonsa, sai da Safiyyah ta dinga yi ma Khaleesat rantsuwa kan Ajay ya tafi sannan ta yarda ta sakko downstairs, kanta a kasa ta zauna parlon Jay na kallonta calmly yace "Halysaah" A hankali tace "Na'am" Yace "Kiyi haku

ri, do not take Ajay's words to heart, we all know he didn't mean it..." Ita dai bata ce komai ba wasu hawayen na taruwa idonta, yace "Ki yi hakuri Shiru tayi don ko kadan bata ji zata iya hakura ba, sosai taji zafın abinda yayi mata, amma saboda bata ma s

on maganar yayi tsayi cikin sanyin murya tace "Na hakura Ya Jawwad" Yace "Ko ke fa, kuma ki dena kukan nan, if there is anything always feel free to speak to me about it Halysaah, kin san dai no marriage is hundred percent perfect right?" Ta gyada masa kai

without looking at him, ya sauke idonsa a hankali yace "Allah ya baku zaman lafiya, be a good wife pls" Nan ma dai gyada masa kai kawai tayi, yace "Yanxu za mu koma can gidan tare inyi dropping din ki" Da sauri tace "Ai gidanmu zan je" Yace "Me za ki yi a

gidanku?" Tana wasa da veil dinta tace "Ai yasan zan je yau" Jay yace "Ohk i will drop you home, sai ya kai ki can gidan naku" Ji tayi wani hawaye ya kawo idonta don da gaske bata son ma ta ga Ajay, muryarta na rawa tace "Don Allah ka kai ni gidanmu, ai y

asan zan je, ka kirasa ma ka tambayesa" Jay yayi shiru yana kallonta, can yace "Then mu fara zuwa can gidan mu yi picking dinsa sai mu tafi gidan naku gaba daya, nima zan gaida su Kaka......" Khaleesat tayi shiru, ya mike yace "Idan kin shirya sai ki samen

i kofar gida" Ta gyada masa kai, ya nufi kofa ya fita sannan ta mike tana goge idonta ta bar parlon ta wuce sama. Jay na fita kofar gida ya jingina da motarsa staring at the flowers outside babu ko kiftawa, har su Khaleesat suka fito kofar gidan bai sani b

a sai da yaji an kullo gate, ya daga kai yana kallon Khaleesat with full attention as if figuring out something, har ta karaso kusa da motar ganin zata zaga zuwa front seat ya bude mata door din baya yace "Naga kamar baki da lafiya ko, ki shiga nan kawai"

Khaleesat ta sauke idonta ta dawo ta shiga bayan motar ya kulle, ya kalli Safiyyah yace "Thanks Safiyyah, i will take my leave now" Safiyyah tace "To shikenan Ya Jawwad Allah ya tsare" Yace "Ameen" Bude driver seat yayi ya shiga ya tada motar, Safiyyah na

murmushi ta daga ma Khaleesat hannu, ita dai Khaleesat ta jingina da kujeran motar don wani sabon jiri take ji tun da suka fito daga cikin gida, gaba daya ta ma rasa me ke mata dadi, she is restless, Jay ya ja motar suka bar layin, sai bayan da suka bar un

guwan ya kara kallon fuskarta ta madubin gaban mota, after some seconds yace "Ko zaki kwanta?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, kamar yasan kuwa she is not comfortable don gaba daya kamshin motar ya dameta, ta kirkiri murmushi tace "I am fine" Yace "Sannu

" Tayi shiru bata ce komai ba, tunani ta fara yi what is making her feel this way da bata son kamshi just like that yau, bata san sanda tayi saurin gyara zamanta ba ta zaro ido tana lissafin the last time she saw her period, ji tayi ta kasa kwakkwaran mots

i, can ta daga kai a hankali ta kalli gaban motar suka hada ido da Jay, tayi saurin sunkuyar da kanta....

HALYSAAH

PAGE 165

..,..

Har suka isa gida Khaleesat bata sake kallon gaban motar ba, Jay ma bai kara ce mata komai ba, ta dai yi convincing din zuciy

arta period dinta was only being late and nothing more, hakan kuma yasa hankalinta ya kwanta don wani lokacin cycle dinta yana canzawa, tana saka ma ranta haka kuwa kamshin motar ma ya dena damunta kwata kwata, Jay yayi parking a compound ya bude motar ya

sauka sannan ya bude mata back seat ganin bata da niyyar budewa, Bata yarda su hada ido ba, a hankali tace "To ai kace can gidanmu za mu tafi daga nan, i will wait inside the car" Jay yace "A'a, sakko mu shiga ciki dai" Tace "Don Allah kayi hakuri in jira

a nan, i don't want to go inside pls" Yayi shiru, sai kuma yace "Alright" Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo yace "But you know what?" Ta girgiza masa kai, yace "Do not say anything to anyone back home, komai ya wuce, promise me that" Ta sauke idonta tace

"In sha Allah" Cikin gidan ya nufa, ta rungume hannunta ta daure fuska don ita tayi niyyar ko Aunty Farida ta gaya ma, banda kar yaga tayi disobeying dinsa ma kawai ji take ina ma kafin su fito daga cikin gidan tayi tafiyarta ta nemi a daidaita sahu da za

i kai ta gida, after almost 15 minutes sai ga Jay ya fito gidan, daga bisanni Ajay ma ya fito daga cikin gidan, kauda kai tayi ta kara murtuke fuska tayi using veil din jikinta ta rufe half of her face tana kallon direction daban, har suka iso kusa da mota

r Jay ya bude kujera me zaman banza ya shiga ya zauna, hakan yasa Ajay ya zaga ya bude driver seat ya shiga yana kallonta ta madubi, ko da wasa Khaleesat bata yarda ta juyo kanta ba balle ya samu daman kallonta da kyau, Mai gadi ya bude gate din gidan baya

n ya fahimci fita za su yi, Ajay ya ja motar suka bar gidan, Jay ya gyara zama ya rufe ido kamar me bacci a cikin motar, lokaci lokaci Ajay yake daga kai ya kalli madubi duk da ta rufe rabin fuskarta kuma outside of the road take kallo taki yarda ta bari y

a kalleta, the 40 minutes ride was silent, Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu a tudun Yola, ta bude motar ta sauka without looking at anybody tayi wucewarta ciki ya bi bayanta da kallo sannan ya kalli Jay dake danna wayarsa, kashe motar yayi ya jingin

a da kujeran driver a hankali.... Khaleesat na shiga parlonsu step siblings dinta suka taso yi mata Oyoyo, su Noor da Islam ma duk suka rungumeta, har lkcn hutu ake ba ayi resuming school ba, ta dai samu suka saketa ta nufi dakin Nenne da sauri,

ɗ

an tafiya

r da tayi daga bakin gate zuwa cikin gidan ji take kamar zata fadi, tana shiga dakin, Nenne da Mama Shatu suka bi ta da kallo don saman gado ta nufa ta kwanta tana sauke numfashi, Nenne tace "Allah me iko, ko minti goma fa ba ayi ba yanxu nake cewa ko dai

kun tafi Bauchin ne, ashe kuna hanya" Mama Shatu tace "Ai ko dai yanxu kika gama magana Nenne" Khaleesat ta juyo ta gaishesu, duk suka amsa Nenne tace "Sai kace warce ta zo unguwan da kafa naga sai faman nishi kike" Khaleesat ta yatsine fuska tace "Na gaji

ne...." Sai kuma ta mike zata dauko ruwa a fridge, taji wani jiri ya debeta tayi saurin dafa gado tana rike kanta, Nenne ta mike da sauri tace "Subhanallahi, lafiyar ki kuwa?" Komawa Khaleesat tayi ta zauna kan gadon har lokacin tana dafe da kanta a hanka

li tace "Kai na ke min ciwo" Nenne ta karasa kusa da ita tace "Sannu, ke kadai kika zo ko da mijin naki?" Khaleesat tace "Ya Jawwad ma yana waje wai za ku gaisa" Nenne tace "Kai haba Ahmad dai nawa, Allah sarki yana Kanon shi ma ashe" Da sauri ta mike ta b

ude wardrobe din dakin ta jawo babban mayafinta gogagge tace "Sun shigo parlor ne?" Khaleesat tace "Ki ce su Noor su je suce masa ya shigo yana waje" Nenne tace "Yanxun nan kuwa" Daga haka Nenne ta fice daga dakin, sai kuma tayi saurin dawowa tana kallon M

ama Shatu tace "To ke Shatu tunda mun gaisa ai sai kije ki duba yanayin da yara suka yi da dakin ki, don naji jiya ma ance an fasa maki kwalban man gyada a dakin" Mikewa Mama Shatu tayi don dawowarta kenan daga biki taje kauyensu shi ne ta shigo gaida Nenn

e, daga nan ne ta zauna suke ta hira, tana fita daga dakin Nenne ta kalli Khaleesat tayi kasa da murya tace "Wallahi sace sace suke min, ba daman in bar daki a bude sai a sure min abu kamar beraye ita da Zubaida" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba Nenne ta

juya ta fita tana cewa "Ohh Allah ga Ahmad ya zo kuma Zahra'u da kanwarta basa nan sun tafi gidan Gaje, kai amma dai ban ji dadi ba wallahi, ai ya dade rabonsa da gidan nan yaron...." Khaleesat ta fara bacci Nenne ta shigo dakin, tashinta Nenne ta fara yi

tana cewa "Ke za su tafi fa, ban san ko tare za ku koma ba, tashi...." A hankali Khaleesat ta bude idonta, Nenne ta zauna kusa da ita tana kallonta da mamaki jin jikinta ya dau zafi tace "Ke wai baki da lafiya ne? Jikin ki fa ya dau zafi" Khaleesat dai ba

ta ce komai ba sai gyara kwanciyarta da tayi, Shiru Nenne tayi tana ta kallonta, can tace "Ko dai ciki gare ki Khaleesat?" Khaleesat ta wani kalleta ta mike zaune da sauri, kamar zata yi kuka tace "Kamar yaya ciki? Kawai daga jin jikina da zafi sai ki ce c

iki" Nenne ta kai hannu kirjinta, komawa baya tayi tana tura baki tace "Ni al'ada ma fa nake yi" Nenne da har zata fara murna sai kuma murna ya koma ciki, a hankali tace "Da gaske al'ada kike?" Khaleesat tace "Ehh, shi sa ma duk bana jin dadi yau, cikina k

e ciwo" Nenne ta sauke wani ajiyar zuciya, ta marairaice tace "To Allah gamu gareka, naga kirjinki ne sun cicciko gashi sai walkiya fuskar ki yake har na fara tunanin ciki ne wallahi" Khaleesat tace "A'a ba wani ciki, al'ada nake yi ni dai" Daga haka ta ko

ma ta kwanta, Nenne tace "To Allah ya kawo me albarka, ga can mijinki da

ɗ

an uwansa za su tafi, bin su za ki yi ko yaya?" Khaleesat tace "A'a zan kwana ne a nan" Nenne tace "To tafi ki masu sallama ki dawo, ai haka ake yi, na ji gobe wai za su koma Bauchi

inji Ahmad din...." Khaleesat tayi shiru, Nenne tace "Ji jaraba, ki tashi kije ki masu sallama mana, har sun fita gidan nan fa" Girgiza kai Khaleesat tayi tace "Ba sai naje ba, mun yi waya da shi yace sun tafi kawai, ai shikenan" Nenne ta riƙe ha

ɓ

a ganin y

anda ta daure fuska take maganar, can Nenne tace "Ikon Allah, ashe da sauran aiki a gabanmu, har ina ta murna hankali ya samu zuwan da ku ka yi jiya da daddare, ashe kya ce kanki ake ji er banza ina nan yanda nake, dama duk munafurtar mu kika yi ashe, ni d

a Farida muna ta murna har Hajiya Zaliha na taya mu daxu da safe" Khaleesat ta koma can daya side din gadon ta kwanta tace "Ni dai yunwa nake ji, idan akwai abinci a bani" Nenne ta ta

ɓ

e baki ta mike cikin sanyin jiki ta fita daga dakin. Shinkafa da miya da

nama Nenne ta bada a kai ma Khaleesat daki, ta mike zaune tana kallon abincin ta amsa, sai kuma ta maida stew din gefe ta fara cin shinkafan a hankali, bai fi cokali hudu ta ci ba ta rufe ta ajiye ta sha ruwa kadan ta koma ta kwanta, she is trying to pret

end kamar bata san zuciyarta na tashi ba don wannan ne ma yasa ta ajiye abincin, after a while taji ta dawo dai dai ta dena jin aman, lumshe ido tayi a haka bacci ya dauketa... Wajen karfe shidda saura Nenne ta shigo dakinta tana tashinta tace "Ke wani bac

ci ne wannan kike min a daki tun daxu ga magariba ta gabato, har an gama gyaran gida kin sa an tsallake min daki kamar er banza, don bakya sallah kuma sai kiyi ta bacci ba kwantrol uwa rubabbiyar tsohuwa, to ga can uwarki ma sun dawo ki tashi ki je dakinta

gaskiya a gyara min daki, don bazan kwana cikin kazanta ba" Khaleesat ta daure fuska ta mike zaune ta dau mayafinta da handbag ta sauka daga kan gadon ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Nenne tace "Haba, bacci sai kace kasa, tun azahar ake abu daya, in a

n gyara dakin sai ki dawo ki karata da gadon ba shikenan ba" Ko kallonta Khaleesat bata yi ba ta fice daga dakin ta nufi dakin Ummanta, Umma na zaune dakin ta bude tuwon da Baaba Gaje ta dage sai sun taho da shi tana tambayar Islam ko za su ci, Islam ta gi

rgiza mata kai tace "Sai dai Noor, bari in kira ta" Dai dai nan Khaleesat ta shigo dakin, tana jin kamshin miyan kukan Baaba Gaje ta toshe hancinta da sauri, sai kuma ta jefar da jakar hannunta da mayafi ta nufi bandaki da sauri, Umma dake rike da murfin k

wanon tuwon ta bi ta da kallo, Islam ta mike ta bi bayanta zuwa bandakin, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin, tana jin yunkurin aman da Khaleesat take yi tace "Subhanallahi, me ya sameta?" Umma dai ta rufe tuwon gabanta bata ce komai ba, Aunty Farida ta sh

iga bandakin, ta tarar da Islam ta dafa yayartata dake ta yunkurin amai tana mata sannu, Aunty Farida ta debi ruwa ta wanke mata fuska ita ma tana mata sannu, sosai jikin Khaleesat yayi zafi, Aunty Farida ta dagota suka fita daga bandakin, Islam ta fara wa

nke inda tayi aman, basu tarar da Umma a dakin ba don ta fita da tuwon zuwa kitchen, Aunty Farida ta kwantar da ita kan gadon Umma tana mata sannu, da kyar tace "Sanyi nake ji Aunty" Bargo Aunty Farida ta dauko ta rufa mata, sai ga Nenne ta leko dakin tace

"To ga can sun gama gyaran dakin, sai ki koma kiyi ta kwanciyar naki kamar ruwa" Aunty Farida ta kalli Nenne tace "Bata jin dadi ma Nenne" Nenne ta shigo dakin tace "To ko dai mijinta za a kira, tun daxu nima na lura bata da lafiya, tace min ai ciwon ciki

ne, maza kira mijinta Parida, in ma tafiya zai zo yayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login