Showing 519001 words to 522000 words out of 641791 words
yi tafiyar, me yasa ka dawo babu s
hi? Where did you leave him pls?" Jay ya kasa ci gaba da tsayuwa cause his legs couldn't carry him any longer, a hankali ya duka kan knees dinsa feeling so emotional, at this point he couldn't hold it anymore, ya dafe kansa da ya dinga juya masa with tears
running down his eyes, Khaleesat ta tsaya tana kallonsa babu ko kiftawa with fear written all over her face, bata san sanda ta kurma wani uban ihu ba da sai da gidan ya amsa, action din Jay ne ya fara dawowa da ita reality din da taki amsa tuntuni, his ac
tions explains everything to her, ta zube gabansa cikin wani irin shock jikinta na rawa tace "Na shiga uku, don Allah ka gaya min me ya samesa?" Jin yaki cewa komai ta Cakumosa da karfi cikin birkicewa tana zare ido tace "Ka gaya min me ya sami mijina don
Allah, tell me what happened to him, da gaske ne an kashe min shi? Dama da gaske ne?" Jay couldn't raise his head yana jin ihunta har tsakiyar kansa, ta sake kurma wani uban ihun ta dora hannu a ka, su Hajiya Shafa'atu da Hajiya A'isha da Kilishi duk suna
parlor sun yi tagumi babu wanda ya iya shiga cikin dakin, Aunty Farida dake jingine da bango a parlor ita kanta bata iya ta shiga dakin ba hawaye kawai ke sauka idonta tana nanata Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un a zuciyarta, Khaleesat bata fasa jijjiga
Jay ba ko ina na jikinta na rawa tace "Don Allah ka rufa min asiri ka dawo min da mijina Housemate, kar ka ce min ya mutu, wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba, me yasa zai tafi ya bar ni bayan kwana biyu kawai yace min zai yi ya dawo, na shiga uku, don Al
lah ku taimake ni" Hadiyah tayi karfin halin sauka daga kan gado ta nufeta zata dagota, Khaleesat ta riko hannunta cikin kuka tace "Don Allah ki tayani tambayarsa me ya samu mijina, don Allah ki tambayesa" Shi dai Jay yaki daga kansa, hakan yasa kawai Khal
eesat ta mike ta warce hannunta daga rikon da Hadiyah tayi mata da nufin zata fita daga dakin ba tare da ta ma san ina zata je ba, sai a sannan Jay ya daga kai a hankali yana kallonta, lokaci daya tayi saurin dafa stool dake kusa saboda wani sharp pain da
taji a maranta ta durkusa kasa da kyar, Jay bai san sanda ya mike da sauri ba ganin jini na diga daga kafarta yayi saurin dagota, Hadiyah tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Sosai hankalinsa yayi mugun tashi, kan kace me sai ga jini kamar an bude pam
po har shi da Hadiyah dake kusa da ita sai da jinin ya
ɓ
ata masu kafa, tuni likitan dake tsaye dakin all this while cike da tausayin Khaleesat tayi hanzarin karasawa kusa da su tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Hasbunallah...." Wannan ne yasa
su Hajiya Shafa'atu suka yi saurin shigowa dakin gaba dayansu, su ma duk suka saki salati cikin rikicewa, Hajiya Shafa'atu ta fashe da kuka tana girgiza kai, shikenan
ɗ
an cikin ma da suke lallabawa gashi tayi
ɓ
arinsa..... Kukan bakin ciki sosai Hajja tayi
bayan an kai mata mummunan labarin miscarriage din da Khaleesat tayi na cikin yan biyun dake jikinta, gashi bata da lafiya ko fita bata iya yi balle taje ganin halin da Khaleesat din ke ciki, ta dai ce kar su gaya ma Mai martaba a bar sa yaji da abinda yak
e ji tukun, Nenne ma taci kuka ta gode Allah, haka ma Umma dake tausayin halin da er ta take ciki, gashi tunda dangin mijinta na kanta su sai dai su zauna a dakin da aka saukesu ita da Nenne da Aunty Murja sai Mama Zubaida, Aunty Farida ce kawai ke shiga w
ajen Khaleesat frequently.... Damuwa da tashin hankalin da Jay ke ciki ya ninku a kan wanda yake ciki, gaba daya ya dawo kamar wanda ya fara samun issues da brain dinsa, miscarriage din da Khaleesat tayi ya kara destabilizing dinsa yana ganin shi ne ya ja
hakan, just like that the twins are gone too, yayi da ya sanin amincewa da yayi har yaje wajenta tunda zuwansa ne ya ja har cikin ya zube, all this while taki yarda da cewar abu ya samu mijinta amma ganin hawayensa yasa ta gaskata abinda taki yarda for day
s shi ne har ta shiga shock din da ya ja mata miscarriage, Hajiya Shafa'atu da Mami duk sai da suka yi da sun sanin tilasta Jay yaje wajenta, kuma duk tunaninsu idan ta gansa zata sa ma kanta salama ta nutsu ashe ba haka bane, Har kusan asuba Mami na zaune
gefen Khaleesat don ciwon mara mai tsanani take yi tun bayan fitar pregnancy tissues din, sai wajen karfe hudun asuba ta samu bacci ya dauketa, sannan Mami ma ta samu tayi shimfida nan kasan carpet ta kwanta, ita kanta Mamin karfin hali kawai take don zaz
za
ɓ
i take ji sosai a jikinta, ko minti talatin Khaleesat bata yi ba da fara baccin ta farka a firgice, Mami na jin motsinta ta mike zaune, Khaleesat ta sauko kusa da ita tana kallonta cikin wani yanayi tace "Mami da gaske fa bai mutu ba, wallahi nayi mafar
kinsa yanxu yace min zai dawo" Mami dai ta sauke ido tayi shiru bata ce komai ba, Cikin rawan murya Khaleesat tace "Mami ki ce wani abu don Allah, wallahi yace min zai dawo" Mami ta kasa kallonta, cike da karfin hali ta gyada mata kai kawai tace "Na sani H
alysaah, amma mu yi ta addu'a kin Ji?" Khaleesat tace "Ina son in ga Ummata" Mami tace "To bari in kira maki ita yanxu" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin, ko da tayi sallama dakin da su Umma suke daga Umma har Nenne idonsu biyu suna zaune kan dar
duma kusan yanda suke ganin rana haka suka ganin dare tun zuwan su, Nenne na ta sallah kan darduma, Mami ta karasa ciki tana kallon Umma dake rike da carbi tace "Maman Halysaah ki zo" Sosai gaban Umma ya fadi tana kallon Mami, ita kanta Nenne daburcewa tay
i a sallahn da take, Mami taga tashin hankalin dake kwance fuskar Umma tace "Ki kwantar da hankalinki babu komai, Halysaah ce take tambayarki yanxu ta farka bacci" Umma tace "Toh" Daga haka ta mike ta bi bayan Mami suka fita daga dakin zuwa wajen Khaleesat
..... Washegari Khaleesat na zaune ta jinginar da kanta da gado hannunta rike da carbin da Mami ta bata, ba komai yasa Mami ta bata carbin ba tace ta dinga ja sai don yayi distracting dinta ta dena maganganun da take kamar warce ke neman zaucewa, yanxun ma
dai tana rike da carbin ne amma tayi nisa tunanin da take, Hadiyah da su Iklima da Shahuda suna can zaune far end of the room, sai Khadeejan Aunty dake zaune bakin kofa, Ummi kuma na daga gefen Khaleesat tana jan nata carbin a hannu, Hajiya Shafa'atu da K
ilishi ma duk suna dakin zaune kan Carpet babu me cewa komai, aka murda kofar dakin, sai a sannan Khaleesat tayi firgit ta dawo duniyar tunanin da ta tafi ta sauke ƙafafuwanta daga kan gadon da sauri tana kallon kofar dakin jin exactly irin yanda Ajay yake
bude kofa ne, don sau da yawa idan ya murda kofa sai yayi jim before gently pushing the door open, Ummi ta daga kai ta kalleta ganin wajen kofar take son tafiya da sauri, tuni Kilishi ta mike ta tareta zata maidata inda take zaune, Ummi ma ta tashi duk su
ka yi preventing dinta from going further, Khaleesat ta fashe da kuka tace "Wallahi nasan shi ne, don Allah ku bar ni in je...." Bata rufe baki ba Sophie ta karasa tura kofar dakin amma ta kasa shigowa ciki, Khaleesat ta dinga kallonta, kawai Safiyyah ta j
uya zata fita saboda hawayen da suka fara sauka idonta, da gudu Khaleesat ta bita ta rikota ta fashe da kuka sosai cikin rawan murya tace "Don Allah Sophie ki gaya min ko kun yi waya da shi, he is still not yet back" Safiyyah ta kasa cewa komai hawaye na z
uba idonta, instead kawai ta rungumeta jikinta trying hard to control her self, Khaleesat ta dinga kuka kamar ranta zai fita tana cewa "Sophie nasan he is not dead, nasan zai dawo, and i will wait for him"
H
ALYSAAH
Har yammacin ranan nan Khaleesat bat
a dena kukan da take ba, gashi tun da gari ya waye taki shan ko ruwan zafin da ake bata saboda miscarriage din da tayi balle kuma ta ci abinci, wankan ma sai da Mami ta sakata gaba tayi mata, duk ta fita hayyacinta, Safiyyah na dakin amma baza kace tana na
n ba don far end of the room take zaune ba um ba um um, kana kallonta kasan ta shiga damuwa sosai ita ma, ko kadan bata da courage din ce ma Khaleesat komai at this Stage, Gimbiya Firdausi ta shigo dakin tana kallon Mami dake zaune kusa da Khaleesat tace "
Aseeyah an zo za ayi mata ta'aziyyah ne i think his friends, kawarta ta rakota sai su fito parlorn ko?" Mami ta kalli Khaleesat dake rike da carbin da ta sake bata, Kuka Khaleesat ta fara yi tace "Dama ana yin ta'aziyyar wanda bai mutu ba?" Gimbiya Firdaus
i ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta fita daga dakin, haka nan Mami ta lallaba Khaleesat tace ita suka zo gaidawa da jiki ba ta'aziyya suka zo ba, a haka aka samu ta sauka daga kan gadon Safiyyah na rike da hannunta suka fita zuwa Main parlor, babu wanda Kh
aleesat ta amsa ma a cikinsu hawaye masu zafi na zuba idonta jin ana ce mata Allah ya ji kansa, she believe her husband is not dead shi yasa taki amsa ma kowa a cikinsu, suka gama addu'o'in su sannan Mukhtar yayi leading dinsu su kusan takwas suka fita dag
a parlon ko wannensu jiki a sanyaye cause Ajay is the most nicest guy to be with, Khaleesat ta daga kai ta kalli Safiyyah da ta sunkuyar da kai ita ma hawayen ke zuba idonta sosai, dai dai nan Jay ya shigo parlon, Safiyyah ta
ɗ
aga kai tana kallonsa, sosai
zuciyarta ya kara karyewa ganin yanda ya koma saboda grieve, he isn't even looking normal, tare ya shigo parlon da Abdul dake biye da shi a baya, Khaleesat dai kallonsu take babu ko kiftawa, kallo daya Abdul yayi mata ya sauke idonsa a hankali, ya karasa c
ikin parlon ya zauna, Jay ya juya kawai ya fita daga parlon ya tafi jikin wani kofa ya jingina yana kallon sama, Abdul na kallon Sophie yace "Safiyyah, ya karin hakuri?" Kai kawai Sophie ta gyada masa ta kasa cewa komai tana goge hawayen dake sauka idonta,
ya maida dubansa kan Khaleesat but seeing the way she is crying ya kasa ce mata komai ya sauke idonsa, lokaci daya zuciyarsa ya karaya, da kyar dai daga karshe yace "Kiyi hakuri Khaleesat, Allah Ubangiji ya gafarta masa, Allah ya sanyaya maki zuciyarki ya
baki hakurin wannan rashi" Ta kara fashewa da matsanancin kuka tace "Ni wallahi mijina bai mutu ba fa...." Abdul ya sauke idonsa, can ya kwantar da murya yace "If you have that feeling Khaleesat keep on praying, duk inda yake Allah ya bayyanasa cikin kosh
in lafiya da aminci, mu ma za mu yi ta addu'a in sha Allah" Sai yau wani ya gaya ma Khaleesat abinda yasa taji wani salama ya sauka zuciyarta, ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauka idonta da sauri, ita dai Safiyyah bata daga kanta ba, Abdul yace "
Amma kuma idan baki kwantar da hankalinki ba ta yaya za ki nutsu har kiyi addu'a Khaleesat, so try to be strong and confident ki ci gaba da addu'a kin ji...." Wasu hawayen na sauka idonta ta kara gyada masa kai tace "Nagode Ya Abdul" a haka Abdul ya fita y
a bar su a parlon duk jikinsa a sanyaye, ya tarar da Jay tsaye yayi nisa tunanin da yake. Tun faruwan lamarin nan sai yau da aka yi kwanaki uku Mai martaba ya fito, shi ma ta dalilin relatives din late wife dinsa da suka taho daga Ethiopia har su goma, mat
a bakwai sai maza uku, Mai martaba bai iya ya kalli idon ko mutum daya a cikinsu ba, kana ganinsa kasan yana cikin matsanancin damuwa, dukkaninsu da yaren turanci suka yi masa ta'aziyyar don basa jin Hausa, sosai zaka ga alhinin dake kwance fuskokinsu gaba
daya, daga karshe Mukhtar ya kai baƙin mazan masauki a nan gidan sarki, matan kuma Hajiya Shafa'atu tayi masu iso har zuwa bangaren da aka gyara masu me dauke da dakuna uku manya da babban parlor har da kitchen a bangaren, cimar kasar su aka yi masu iri i
ri tun basu karaso ba aka kai masu bangaren, Da turanci Hajiya Shafa'atu ke sanar masu matar Junaid din tana bacci idan ta tashi sai su shigo bangarenta su yi mata ta'aziyyah, daga haka ta fita daga part din. Ita ma dai Aunty sai yau ta samu ganin Mai mart
aba, a duk kwanakin nan tana cikin damuwa sosai ganin har ita Mai martaba yayi restricting dinta daga shiga inda yake, to ko dai ya gano wani abu ne, banda haka ai ita ya kamata ace tana kusa da shi tana karfafa masa gwuiwa tare da kwantar masa da hankalin
sa, ga kuma Walid can a asibiti scan ya fito ana tunanin ya samu matsala a spinal cord dinsa idan ba wani ikon Allah ba ba lallai ya tashi ba, yanxu haka wani asibiti a India za a kai sa, duk har da wannan ya kara birkita mata lissafi, ko abinci bata iya c
i, da daddare ma bata iya bacci, a daren ranan nan Mai martaba ya tafi wajen Khaleesat for the first time tun faruwan abun.... Days went by slowly then months, amma a haka Khaleesat ke zuba ido kullum tana jiran ranan da Ajay zai dawo, abunta ya dinga taba
rbarewa ta dawo kamar ta fara loosing mind dinta ne, she is always saying things that are not making sense, ko gaisuwa aka yi mata sai ta sakar maka kuka ta fara rantse rantse tace ita mijinta bai mutu ba yana nan kuma zai dawo ya gaya mata haka a mafarki,
gaba daya taki tsayawa ta nutsu tayi takaba wai a haka su Mami da Aunty Faridah suna saka mata ido, ga kuma Dr dake gidan takanas saboda ita, the Dr is always by her side, kusan kullum yanda take ganin rana haka take ganin dare baccinta baya wuce minti as
hirin zata farka a firgice, sai dai idan likitanta tayi mata alluran bacci shi ne zata dade tana bacci, kuma babu ranan da zata rufe ido bata yi mafarkin Ajay ba, duk ta rame ta fita hayyacinta ta dawo kamar me matsalar ƙwaƙwalwa whereas brain dinta Lafiya
lau don sai da Mai martaba yasa aka kai ta asibitin ƙwaƙwalwa, abinci sai by the grace of God ake tilasta ta ko cokali daya ne ta ci, sai kuma ruwan lipton, sosai likitan dake kula da ita ke jin tausayinta da halin da take ciki abu almost 5 months amma ku
llum kamar sabo yake a wajenta, banbancin ta da Jay ƙalilan ne don shi baya cewa Ajay bai mutu ba tunda a gabansa aka harbesa kuma har sannan last words dinsa da yace masa he should take care of Jeeddah sun ki fita daga kunnensa kamar a lokacin yake gaya m
asa haka, babu ranan da bazai zubda hawaye ba a gidan nan, kullum missing din Ajay kara yawa yake a ransa, yaji ina ma ana maida hannun agogo baya ko duk abinda ya mallaka Ajay yace yake so he will sacrifice it for him wholeheartedly, he regrets everything
that happened years ago, yayi da ya sanin duk abubuwan da yayi akan Halysaah... kullum Hajja kara jan Jay take a jiki tana basa baki bayan ta fahimci su fa ya kamata su fara daukan dangana kafin su daura Jay da matar Ajay a hanyar yin hakan su ma.... 7 mo
nths later Mai martaba ya biya aka kai Khaleesat Turkey For therapy sannan a binciki lafiyarta don abun nata is getting too much day by day, suka je ita da Aunty Farida, likitan ta, da Mukhtar da yayi masu rakiya, a watannin da suka yi a Turkey Aunty Farid
a babu wani improvement din da ta gani sai kara rikicewa ma da lamarin Khaleesat ya kara yi, ga wani kakkaryewa da gashinta yake yi, kana jan gashin zai biyo ka kuma me yawa, hankalin Aunty Farida ya tashi sosai, nan ta fahimci kawai rokan Allah za a dukuf
a da yi mata babu wani zancen asibiti, haka nan suka tattaro suka dawo Nigeria kawai. Bayan sun dawo Nigeria Aunty Farida tayi shawara da Mami a bari ta tafi da Khaleesat kano tunda ta fita takaba, duk da bata san yanda ake yi a gidan sarauta ba amma tana
son ta tafi gida da ita, a hankali Mami tace "Haka ne Farida, in tayi nisa da Emirate din nan damuwarta zai ragu ta fara accepting reality, zan yi magana da Mai martaba da Hajja sai a kai ku Kanon in sha Allah, ni kaina nayi wannan tunanin" A ranan kwana K
haleesat tayi tana kuka kamar ranta zai fita wai ita bazata je Kano ba she want to be in her husband's part, sai da Mami ta dinga lallabata kan cewa kwana uku kawai zata yi a kanon sannan a dawo da ita duk don ta yarda ta bi Aunty Farida, a haka tabi Aunty