Showing 585001 words to 588000 words out of 641791 words
"Ko dai kitso zan fara yi maka?" Kissing dinta ya fara yi yana cuddling kirjinta, Sun dade a parlon yana sarrafata, TV na ta aiki shi kadai, da Khaleesat taga abinda yake kokarin yi t
uni ta maido da hankalinta jikinta tana kallonsa da idanuwanta kamar me jin bacci tayi kasa da murya tana girgiza masa kai tace "Noo plss, don Allah mu tafi sama, ba mu kadai ne a gidan ba fa...." Da kyar ya iya bude baki yace "No one is coming downstairs
Slushie" Tace "Nooo, ni dai plss let go upstairs, Wallahi kunya nake ji" Kawai gani tayi ya dauketa sai Laundry room alamar upstairs is too far for him at this point, sosai Khaleesat ta saki jiki suka mori juna, ko
ɗ
an zafin ma da take ji a farko yau sam b
ata ji sa ba, ta bar sa yayi yanda yaga dama da ita a wajen. Da safe wajen karfe bakwai da rabi Khaleesat na sanye da hijab har kasa ta sauko downstairs zata tafi kitchen ta hada ma Ajay coffee, tsaye tayi bata karasa kusa da kofar kitchen din ba bayan taj
i alamar akwai mutum a ciki, after some seconds ta
ɗ
an leka kitchen din taga Hadiyah ce, bude ido tayi da mamaki ta karasa ciki taga lafiyayyen girki take yi, haka kawai Khaleesat taji dariya ya taho mata, ta dafa gwiwa ta dinga babbaka dariya, Hadiyah ta
juya ta kalleta tace "Ke wai komai sai kin yi dariya, to meye abun dariya yanxu" Da kyar Khaleesat tace "To ke wa yace maki amarya na shiga kitchen da sassafe, what are you even cooking?" Hadiyah ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta juya mata ido ta
ce "My husband's favorite" Buda baki Khaleesat tayi tana kallonta with shock, wani sabon dariyan ta fara yi tace "Kawai ki ce min yesterday night was splendid" Hadiyah ta harareta tace "Idan na gama zan dafa maku ruwan shayi in gasa maku bread a toaster da
ke da Yaya in case za ku yi breakfast anjima" Khaleesat tace "Ai koma meye favourite din mijinki shi ne favourite dinsa shi ma, duk abinda Ya Jawwad ya ci shima sai ya ci...." Murmushi kawai Hadiyah tayi tace "Gaskiya bazai samu da yawa ba, dai dai mijina
nayi"
Some weeks later
Ajay ya bude kofar bedroom dinsa ya karasa ciki yana kallon Khaleesat dake kwance kan gado tana bacci, ya duka kusa da ita ya sauke bargon jikinta, yayi kasa da murya yace "Jeeddah" Da kyar ta bude ido tana kallonsa with sleepy ey
es, yace "Kin zama sleeping beauty yanxu ko, haka za mu tafi Airport anjima kina bacci wife...." Miƙa tayi a hankali ta kai hannunta cikin lallausan gashinsa tana birkitawa gently, sai kuma ta rungumosa zuwa kirjinta cike da shagwaba tace "Me yasa zaka tas
heni bayan ina baccina me dadi" ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada, maƙe masa kafada tayi ta turo baki bayan taji abinda yace, ya dinga kallonta da lumsassun idonsa, sake rungumosa tayi murya can kasa tace "Bacci fa nake ji dear, kayi hakuri pls" Yace
"To yi baccin ki my love" A hankali tace "Ka gama hada min kayan ne?" Yace "Na gama ranki shi dade" Ta turo baki tace "Ni dai wallahi idan ka mance min komai sai ka dawo kasar nan ka daukar min da gaske" Yana murmushi ya ja hancinta yace "Ban mance komai b
a Slushie, idan ma na mance zan dawo in dauka wallahi" Tace "Akwai fa shoes dina a laundry room ka dauko?" Ya
ɗ
an bude ido yace "To bari aje a dauko yanxu, me kike so a siyo maki for breakfast?" Slowly tace "Nasan Hadiyah zata yi girki ai" Ko rufe baki bat
a yi ba aka yi knocking kofar dakin, Ajay na kallonta ya shafa tummy dinta yayi kissing flat tummy din yana kallon cikin, ita dai sai kallonsa take ganin yanda yake kallon cikinta, sai kuma ya mike ya nufi kofa ya bude, Hadiyah ce tsaye bakin kofar ta koma
gefe tace "Yaya ina kwana, Halysaah ta tashi ne?" Without looking at her yace "Morning" Fita yayi daga dakin, ta
ɗ
an leka ciki sannan ta shiga, Khaleesat ta mike zaune tana kara wani miƙan don duk jikinta is weak, ta jawo hularta ta saka a gashinta, Hadiy
ah na murmushi ta zauna kusa da ita tace "Kwana biyu kin yi scarce a gidan nan daga bacci sai command din Yaya kawai kike...." Khaleesat ta zaro ido tace "Ban gane command dinsa ba, kuma jiya ba tare muka yi kallo da daddare downstairs ba?" Hadiyah tace "J
i mata, ko minti biyar bamu yi da fara kallon ba kika yi bacci kika bar ni da TV" Khaleesat tace "To ni ban ma san how manage na dawo part din nan ba, kawai tashi nayi cikin dare na gan ni kan gado fa" Hadiyah tayi er dariya tace "Mijinki kika hada da aiki
, nima fitowa nayi daga kitchen ban gan ki ba a parlon daga zuwa in hado tea, yanxu dai me za ki ci tunda jiya kin ce baki son breakfast din da nayi, har sai da kika aiki yaya uwa duniya cikin sanyin nan ya siyo maki abinci, shi da baya son fita cikin sany
i, ai ko sai da yayi zazza
ɓ
i da ya dawo kina nan kina ta bacci" Khaleesat ta dinga kallonta tace "Da gaske?" Hararanta Hadiyah tayi, a hankali Khaleesat tace "Yau da na tashi kawai naji ina sha'awar cin tuwo dama mu yi tuwon yau" Hadiyah ta wani kalleta ta
ce "Dama inyi dai, ke yaushe rabon ki da girki a gidan nan, ko hanyar kitchen bakya bi matar nan" Khaleesat ta saki baki tace "Kin fiye sharri Hadiyah" Hadiyah tace "A takaice dai yau
ɗ
an baba tuwo yake so ko?" Khaleesat tayi shiru tana kallon Hadiyah jin
abinda tace, Hadiyah tayi er dariya tace "Ya kike kallona haka" Khaleesat tace "Waye kuma
ɗ
an baba?" Hadiyah tace "Gashi makale cikin ki ya maida ki sleeping beauty a gidan nan" Mikewa tayi ta fita daga dakin tana murmushi, Khaleesat dai ta bi ta da kallo,
daxu da Ajay ya shigo shi ma sleeping beauty yace mata, ta
ɗ
an turo baki, ita dai tasan bata da komai don bata dade da gama period ba. Tun da Ajay ya shiga laundry room Jay dake zaune parlor ya bi sa da kallo, sai gashi ya fito da shoes din Khaleesat guda
uku da gogaggun hijabs dinta biyu kuma da alama shi ya goge, Ajay na kallon Jay ganin kallon da yake masa yace "Ko kayi rescheduling flight ticket din ne kake kallona haka?" Jay yace "Kai kuma a haka fatherhood din ya zo maka, ana tsaka da controlling din
ka sai kuma ga fatherhood ya shigo, kaga sai abinda kawai muka gani game da kai...." Ajay yace "Kai matsala ta da kai sa ido, daga safe har yamma sai dai ka wani hakikance a gida kana muzurai, idan dare yayi ka shige daki da yarinya kana er murya, yanxu t
akaicin ka bana taya ka zama during the day muna ma yaran mutane muzurai ko" Bai jira cewar Jay ba ya wuce sama, Jay dai ya bi sa da kallo, can ya girgiza kai yayi murmushi don har cikin ransa tausayi Ajay yake basa yanda Khaleesat ta maidasa a gidan sai y
anda tayi da shi kamar ma tsoronta yake, yanxu kuma ga karamin ciki don yasan wannan baccin da take yi a duk inda ta samu ba na lafiya bane, wani lokacin takaici yake sa Jay baya zama duk inda suke zaune, idan suka fita titi sai Ajay ya dau miskilancinsa y
a dora a kai kamar ba wanda mace take juyawa ba, suna dawowa gida a bakin gate yake cirewa ya ajiye kafin ya shiga ciki, Jay ya ga abubuwa iri iri zamansu a gidan nan wanda yana jin in shi ne bazai iya tolerating ba a dai yanda halinsa yake, bai ta
ɓ
a zaton
akwai ranan da zai zo Ajay ya sauke duk wani ji da kansa ya zama sai yanda mace tayi da shi ba, sam bai son
ɓ
acin ran matarsa, lallabata yake kamar something that is so fragile, yanda yake bi da ita ko kwai albarka, don dai shi Hadiyah tasan halinsa ne ba
nda haka da sai ta dinga jin haushin baya treating dinta yanda Ajay ke treating din Khaleesat a gidan, shi dai yasan duk son da yake ma mace bazai ta
ɓ
a maida kansa zuwa level dinta ba yanda Ajay yayi, he will show her love saisa saisa but not stooping so l
ow, har ya fara tunanin yanda zai ceto
ɗ
an uwansa daga tarkon Khaleesat da ya fada, nan kuma bai san reverse is the case ba don yanda Ajay baya son bacin ranta ita ma haka, har tafi gudun
ɓ
acin ransa ma da lallabasa, gashi bata rage sa da komai a wajen kwa
nciya ba yana samun yanda yake so dari bisa dari, wannan ne yasa ake ganin kamar tana controlling dinsa, kuma a ko ina bata iya boye son mijinta ga shagwaban da take masa da kukan ba gaira ba dalili a gaban ko waye, Ajay ya zama kamar rayuwarta, tana jin b
azata iya rayuwa babu shi ba, ko fita suka yi da Jay ta dinga kiran sa kenan ya dawo gida, a gaban Jay ma nuna son mijinta take yanxu, ga uban kishi idan taga ya bar ta for long yana wajen Jay. Karfe shidda da rabi na yammacin ranan suka tafi Airport don F
light din su zuwa Nigeria na karfe takwas ne, tafiyarsu Nigeria ma Khaleesat ce tace ma Ajay su tafi don gobe Friday ake daura auren Safiyyah da Ya Mustapha, ko musu Ajay bai mata ba duk da baya son komawa Nigeria, ita din ma tafi son zamansu a Maryland ga
shi tana jin dadin zama da Hadiyah, amma she just have to show up in Nigeria for her Besty, Ajay bai gaya ma Jay Khaleesat ce tace su tafi Nigeria ba, kawai ce masa yayi su je su gaida Mai martaba it's been long.
HALYSAAH,...
Washegari karfe biyar na y
amma Khaleesat suka sauka garin Abuja, their Flight to Kano was is in less than an hour, wannan ne yasa basu bar airport din ba suna jiran lokacin, Khaleesat na zaune kusa da Hadiyah cikin airport din, lokaci lokaci take
ɗ
aga kai ta kalli Ajay da hankalins
a ke kan wayarsa da yake dannawa, haushin hakan taji har cikin ranta ganin duk attention dinsa na kan wayarsa ko kallon inda take baya yi, ta
ɗ
an kalli Jay dake zaune not too far away from Ajay shi ma dai wayarsa yake dannawa, mikewan da tayi tsaye yasa Aj
ay ya daga kai ya kalleta, Jay ma ya daga kai ya kalleta, Ajay na ganin mood dinta ya ajiye wayarsa, ta tafi inda yake ta zauna gefensa amma taki kallonsa, shi dai kallonta kawai yake, sai kuma yayi kasa da murya yace "You need something dear?" Shiru tayi
taki cewa komai, ya matsa kusa da ita a hankali yace "Jeeddah" Nan ma taki cewa komai sai ma kauda kai da tayi, Jay duk yana kallon ikon Allah, haka ma Hadiyah dake ta kallonsu, Ajay ya kai hannu jikinta yaji her temperature is normal, ya tashi ya koma day
a side din da ta mayar da kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "To yi hakuri wife" Shi dai kawai ya bata hakuri ne ba don yasan fushin me take ba, tana cika tana batsewa da kyar ta bude baki tace "Ni na gaji, ina son in kwanta" Ya kwantar da murya y
ace "Ai mun kusa boarding flight din mu to Kano, nan da 30 mins za mu tashi in sha Allah" Kamar zata yi kuka tace "Ni bazan iya tafiyar ba na gaji, i just want to lie down, bacci nake ji" A hankali yace "Duk baccin da kika yi a jirgi wife" Ta wani hade rai
tace "Yaushe nayi bacci a jirgi?" Yace "Ohk na tuna baki yi ba" Ta tura baki ta jingina da kujeran da suke zaune, Ajay dai kallonta kawai yake, can ya juya ya kalli Jay, after some seconds ya mike ya tafi inda yake zaune, Jay ya daga kai yana kallonsa, Ca
lmly Ajay yace "Can we reschedule our ticket to tomorrow?" Jay yace "Why?" Ajay ya
ɗ
an sosa kai yace "Erm, naga kawai yamma tayi ne" Jay yace "Idan muka fasa tafiyar sai me zai faru?" Ajay yace "Zan mana booking hotel ne mana" Jay dai kallonsa kawai yake d
aga sama har kasa don yasan duk tsarin matarsa ce, but considering her condition sai bai ce komai ba, Ajay ya mike ya koma kusa da Khaleesat yana danna wayarsa zai masu booking hotel, in 40 mins time suka isa hotel din da yayi masu booking, tun a hanya Kha
leesat ta fara bacci har suka iso hotel din, da kyar Ajay ya lallabata tayi wanka a hotel room dinsu sannan tayi sallah ta ci abinci a nan inda take zaune ta fara bacci, ya fito daga wanka ya sameta a haka, dukawa yayi ya dauketa ya kwantar da ita saman ga
do ta ci gaba da baccinta. Ba su suka bar Abuja ba sai ranan Lahadi all because of Khaleesat don ranan asabar ce ma Ajay tayi she don't feel like traveling, mamaki ya kusa kashe Jay ranan lahadi da Ajay yace masa ai mota za su bi kawai, da Jay ya tambayi d
alili sai ce masa yayi ai tafiyar mota yafi dadi, Jay yasan ba kowa ne yasa su bi mota ba sai Khaleesat, still dai yayi considering condition dinta suka kama hanyar Kano a mota, ai ko ta ji jiki a hanya kafin su karasa Kano, tun da ta fara laulayi bata yi
amai ba sai ranan, all through the journey tana kwance jikin Hadiyah duk ta jigata, gashi duk maganar da Ajay zai mata sai tayi masa jaraba sai kace shi yace su bi mota, daga karshe taki kulasa ma gaba daya a motar, duk abinda take so sai dai tayi ma Jay m
agana, a haka suka iso Kano da yamma sosai don tafiyar tasu bai yi sauri ba duk saboda ita don sai da ta sa suka tsaya a kaduna wai tana son ta huta kamar dai ita ke driving din, Jay was so patient a wannan tafiyar tasu don ma dai ita ce, da wata ce daban
da tuni yayi tafiyarsa ya kyalesu. Wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da take, mikewa zaune tayi ganin Ajay baya dakin, ta kalli flask din ruwan zafi da Hadiyah ta ajiye mata da kayan shayi tun zuwan su gidan, sauka tayi daga saman gado
ta dau hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita zuwa downstairs, kwance ta samesa kan 3 seater, duk da ba bacci yake ba yana ganin ita ce ta sauko kasa ya rufe ido kamar me bacci, tana tafiya a hankali ta karasa kusa da shi tana kallonsa, sai
kuma ta durkusa kasa ta kamo hannunsa a hankali tace "Me yasa zaka kwanta a nan" Bai yi niyyar bude idonsa ba amma jin jikinta da zafi yasa ya bude ido ya mike zaune ya dagota ta zauna kusa da shi yace "Are you okay?" Ta kwantar da kanta a jikinsa ta gyad
a masa kai a hankali tace "Na tashi ban gan ka ba a daki, i want to take tea" Tashi yayi zai tafi kitchen tace "Hadiyah ta kai min kayan shayin daki" Ya dawo ya dagota suka wuce sama. Khaleesat na shafa mai bayan tayi wanka wajen karfe sha daya na safe Ha
diyah ta shigo dakin rike da breakfast, Khaleesat ta kalleta tace "Are you going out?" Hadiyah tace "Ehh za mu fita ne da Ya Jawwad, za mu je gaida yayar Abbana she is kano, naga baki jin dadi ne shi yasa ban ce ki shirya mu je ba, beside kin ma ce gidan k
awarki zaki je yau" Khaleesat tace "Ni fa lafiyata qlau ba abinda yake damuna" Hadiyah tayi murmushi tace "Dama ai lafiyarki qlau kawai stress din hanya ne ya sa kike ta bacci, wani unguwa aka kai kawar taki ne?" Khaleesat tace "Wallahi ban ma sani ba, bat
a replying chat dinta, but I will call her zuwa anjima" Hadiyah tace "To shikenan, in dai kika ji shiru ban dawo ba ta zan kwana ne gidan Gwaggo na, duk yanda ake ciki dai i will call you, ga breakfast nan na kawo maki" A hankali Khaleesat tace "To nagode,
but i will miss you so much" Hadiyah tayi er dariya tace "Sai kace warce zata je wani gari, idan ma zan kwana bai wuce inyi kwana daya ba kar ki damu" Khaleesat ta langwabe kai tace "To shikenan, ki gaida min ita don Allah" Hadiyah tace "In sha Allah, kum
a don Allah ki dena ma yayana wannan masifar da kike masa duk kwanan nan" Khaleesat ta zaro ido tace "Yaushe nayi masa masifa?" Hadiyah tace "Oho dai, duk da mun san ba laifin ki bane" Hadiyah bata jira cewar Khaleesat ba ta fita daga dakin tana murmushi..
.. Ko da Khaleesat ta kira layin Safiyyah cousin sis dinta ce ta daga tace wayar na gida sai dai ta kira Ya Mustapha, Khaleesat ta duba ko tana da numbersa amma taga bata da shi yanxu, sake kiran cousin din Safiyyah tayi ta turo mata number Ya Mustapha, ka
rfe sha biyu Ajay yayi dropping khaleesat a dai dai address din gidan da Mustapha ya turo, Khaleesat na kallonsa a hankali tace "Karfe nawa zaka dawo?" Yace "Duk sanda kika ce ranki shi dade"