Showing 165001 words to 168000 words out of 641791 words

Chapter 56 - HALYSAAH COMPLETE

ta bi Khaleesat da kallo ita ma duk da Khaleesat bata ganta ba, Khaleesat na shiga dakin Ummanta ta fada jikinta ta fashe da kuka a hankali, Kasa cewa komai Umma tayi tana kallonta d

a mamaki, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin ita ma, sosai gabanta ya fadi ta tsaya nan bakin kofa tana kallon Khaleesat, da kyar Umma ta dago kanta cike da karfin hali tace "Me ya faru?" Khaleesat ta kasa cewa komai tana kuka sosai, Umma da nan da nan ita

ma hawaye ya cika idonta ta rungumeta bata sake ce mata komai ba ta bar ta tayi kukan me isarta, cikin sanyin jiki Aunty Farida ta karasa cikin dakin ta zauna gefen katifa tayi shiru, Umma ta goge idonta tana patting Khaleesat a baya a hankali trying to c

alm her amma bata hanata kukan da take ba, sun fi minti biyar a haka sai ga Mama Zubaida ta dage labulen dakin tace "To

ɗ

an sahu dai na ta jira a mika masa kudinsa a kofar gida" Magana take amma idonta na kan Khaleesat da Umma, tsabar gulma yaron makota me

adaidaita sahun ya aiko cikin gidan amma tayi karaf ta mike bayan yaron ya sanar masu ta nufo dakin Umma taki barin yaron ya karasa, don tun shigowar Khaleesat suka baza kunnuwa ko za su ji wata magana amma shiruu basu ji ko tari ba a dakin Umma, Aunty Fa

rida ta dau handbag dinta ta fita daga dakin ta sake labulen daga hannun Mama Zubaida dake rike da shi, sannan ta fita zuwa gun mai adaidaita sahun, sai a sannan Umma ta iya daga kan Khaleesat, suna hada ido Khaleesat ta sauke jajayen idanuwanta, Umma tayi

karfin halin cewa "Me ya faru Jiddah?" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na zuba idonta tace "Yace ya sakeni" Hawayen dake makale idon Umma ya zubo tana kallon Khaleesat babu ko kiftawa, Khaleesat ta rufe fuskarta jikin Umma ta fara wani sabon kukan,

Umma ta rungumeta sosai, cikin rawan murya tace "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, kiyi hakuri kin ji?" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata tana shesshekan kuka, a haka Aunty Farida ta dawo dakin ta same su, Aunty Farida ta zauna gefen Umma

tana kallonsu, Da kyar Umma ta kalleta tace "Wai sakin ta yayi" Ƙasa cewa komai Aunty Farida tayi tsabar yanda ta girgiza, ta dinga kallon Umma babu ko kiftawa, nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, after a while ta goge hawayen dake zuba idonta ta fita

ta dau buta tayi alwalanta ta dawo ta tada sallah, Umma ta dago Khaleesat da tayi shiru a jikinta, sai taga bacci take, Khaleesat ta bude ido a hankali, Umma tace "Kin yi sallah ne?" Girgiza mata kai Khaleesat tayi, Umma tace "Ki je kiyi alwala kiyi salla

h" Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin. Khaleesat na idar da sallah Aunty Farida na kallonta tace "A zubo maki abinci?" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Na koshi" Daga haka ta mike ta hau saman gadon Ummanta ta

kwanta, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya iya cewa komai a dakin, suna ta zaune har kusan karfe shidda, ita dai Aunty Farida tana rike da Al-qur'ani tana karatu silently a ranta, su Islam suka dawo hadda wanda s

uke zuwa har ranan friday, Umma ta sa su je su hura gawayi su dora girki, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana cewa "To Zubaida sai ki dau na annabawa don kin tafka asara lafiyayye yau, almajirai na mugun wasa suka ham

ɓ

are Suwaiba tallan da kika dora ma

ta ya kife a kasa, su kuma suka tsere, sanin azaban da zaki mata ta taho ta sameni tana kuka kamar ranta zai fita, yanzu haka tana can gidana nace tayi zamanta, ga robobin tallan da faranti nasa an kwaso maki kayanki, ko roba daya bata siyar ba suka hambar

e farantin" Mama Shatu ta saki salati tana kallon Mama Zubaida da ta nemi waje ta zauna jin abinda Nenne ke cewa, Nenne ta kwashe da dariya har da kyakyatawa tace "Yaran layi kuwa duk suka wawushe abincin da ya zube a kasa suka loda ma cikin su" Daga haka

ta nufi dakin Umma ta dage labulen tace "Zahra'u kina da er kuka ko kubewa ki tsam inje in ƙada miya" Umma bata yarda sun hada ido da Nenne ba tace "To bari in duba maki, Ina wuni" Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace "Wacece wancan kuma a kwance kan katifar

ki?" Umma dai bata ce komai ba ta tashi zata dauko ma Nenne kubewa busasshe, Aunty Farida ta gaida Nenne ba tare da ta kalleta ba, Nenne na kallon Khaleesat tace "Wai wa nake gani kamar Khaleesah a kwance?" Aunty Farida ta ajiye Qur'anin hannunta still bat

a kalli Nenne ba tace "Ita ce" Nenne ta shigo dakin tace "Wato ni dai shikenan kun nuna mata banda matsayi da har zata shigo unguwan nan ta karasa gidana ta gaisheni ko? In ma bata je ta gaisheni don Allah ba ai sai tayi don ubanta Ali tunda ni na haifesa

har ya haifeta" Daga Umma har Aunty Farida babu wanda yace ma Nenne komai, Nenne tace "Mijin ne ya kawota? Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya gani

n mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi

ɗ

an Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?" A takaice Aunty Farida tace "To sakin ta yayi..." Nenne ta ju

ya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace "Ban ji me kika ce ba Parida?" Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace "Sakinta Abdul din yayi" Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace "Sakin aure ko sakin me?" Aunty Farida dai bata t

anka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace "Wato dai

ɗ

an nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune" F

ita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace "Allah ya isa tsakanina da Zahra'u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdu

l ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta? Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari'arsu da Ali ya dawo sabo?" Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, ciki

n kuka Nenne tace "Ban ta

ɓ

a ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba, kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da 'ya

yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??" Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta

rushe da sabon kuka tace "Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali" Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace "Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da

muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra'un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin

ɗ

a na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi" Malam

Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace "Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida? Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki? Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?" A fusace Nenne tace "Ta zauna ta

yi ma uban wa zawarci a gida? Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri'armu babu wanda ya ta

ɓ

a zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mumm

unan bakar maganar da ya zo bakinta take ya

ɓ

a ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sha

rri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta..." Mama Shatu tace "Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai b

azai fara sakin ta ba" Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace "Innalillahi wa inna ilai

hi raji'una, Zahra'u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi" Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kal

lonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace "Mai gidan na ciki kuwa?" Mama Zubaida tace "To Allah ya sa dai lafiya Malam" Mutumin yace "Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan" Mama Zubaida tace "To ni mai

dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne" Mutumin yace "To ba damuwa" Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya taka

rdan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? w

ani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?" Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, "Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku" content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi t

akardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace "Ji tsinanne la'ananne matsiyaci? saki har uku kam

ar warce ta kashe ubansa ko uwarsa? To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da

ɗ

an barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma

ɗ

an daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba

na'am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kaw

ai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul? Khaleesah sai dai kawai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai

furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sa

ko mana ita, dama auren sha'awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi" Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace "To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah y

a maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake" Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace "Baki shanye kunun bane?" Khaleesat ta

dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kan

wa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta,

a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace "Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tamb

ayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace "Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra'u?" Umma

dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace "Farida" Aunty Farida ta

ɗ

an yi murmushi tace "Ina yini Maman Salame" Maman Salame tace "Wai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi ra

ji'un" Aunty Farida tace "A ina kika ji Maman Salame?" Maman Salame tace "Ga labari nan ya baza Mariri? Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida

na yo nan" Aunty Farida tace "To Allah ya sa mu dace" Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace "Garin yaya haka Khaleesah?" Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace "To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkh

airi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai saki uku ne Maman Salame" Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikin

ta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace "Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah" Umma tayi mata sallama, Maman

Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi it

a ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty kina da number Safiyyah?" Aunty Farida tace "Ina da shi" Khaleesat tace "Ina son zan kirata ne" Aunty Farida tace "Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai

kiyi magana da ita" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace "Wai Babanmu yace Khaleesat ta je" Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke

, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji haw

aye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a

hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because...." Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login