Showing 636001 words to 639000 words out of 641791 words
tuba tun da dadewa kafin ma ciwon ya kwantar da ita har zuwa yanxu da yayi ajalinta. Daren ranan Ajay na tare da Khaleesat a daki yayi dialing number Abdul, ita dai Khaleesat na rike da Eeman da ya shigo tare da ita, Little Jay kuma na can wajen Mami, sa
i da kiran ya kusa katsewa Abdul ya daga yayi sallama, Ajay ya amsa masa sannan suka gaisa, duk da Abdul ba shi da number Ajay amma ya gane muryarsa, bayan Ajay yayi masa ta'aziyyah Abdul yayi masa barkan karuwan da ya samu, Ajay yayi masa godiya sannan ya
kalli Khaleesat yace "Ga ta nan, zata yi maka gaisuwa" Abdul yace "Alright" Ajay ya mika ma Khaleesat wayar, ta amsa sannan ta saka handsfree, gaisawa suka yi sannan tayi masa ta'aziyyar Momynsa, yayi mata godiya yace "Ya baby?" Tace
"Alhamdulillah" Yace
"To Allah ya raya sa, yayi masa albarka" Tace
"Ameen, nagode" Yace "Ki dan ba Mai gidan naki wayar let me speak to him" Tace "Ohk" Ta mika ma Ajay wayar, Abdul yace "Idan ba damuwa i will want to convey my mum's message to her ranka shi dade" Ajay yace "Ok
, it's fine..." Mayar mata da wayar yayi, ita dai Khaleesat kallon Ajay kawai take, can ta amshi wayar tace "Ina ji" Calmly Abdul yace "Maman Baby, tun da dadewa Momy ke ta son neman gafaran ki, even before she passed away sai da tayi maganar ki, ta so a k
awota wajen ki but na nuna mata kina gidan
ki,
beside ba a Kano kike aure ba, so i want to use this medium to
for
forgiveness on behalf of my late Mum, kiyi hakuri ki yafe mata
duk
abinda tayi maki, this is the only thing I can do for her, na so ta nemi ab
inda tayi maki, this is the only thing I can do for her, na so ta nemi gafaran ki da kanta but that wasn't possible tunda kina gidan mijin ki, duk abinda tayi maki ki dubi Allah ki yafe mata pls" Khaleesat tayi kokarin ganin hawaye bai zuba idonta ba, ta g
irgiza kai tace "I hold no grudges against her, idan ma ta min wani abu wallahi na yafe mata tun da dadewa, kuma ina yi mata fatan samun rahaman Allah, Allah ya sa mutuwa ya zamto hutu a gareta, Allah ya kyautata namu karshen" Abdul yace "Ameen, thank you
so much Maman Baby, Allah ya saka da alkhairi, ya kara maki zaman lafiya a gidan auren ki" Ta gyada masa kai tace "Ameen, Nagode, sai anjima" Yace "Ki basa wayar in masa sallama...." Ta mika ma Ajay wayar, Abdul yayi masa godiya tare da sallama sannan Ajay
ya ajiye wayar, babu abinda Momy ta boye ma Abdul a kan abinda tayi ma Khaleesat kafin ta rasuwa, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta komai na dawo mata a kai tiryan tiryan amma har cikin zuciyarta ta yafe ma Momy kuma tana fatan Allah ya rahama mata, Ajay
yace "Can i ask a question Jeeddah?" Ta daga idanuwanta ta kallesa, Calmly yace "Can I?" Duk da a ranta taji bata son ko ma wani tambaya zai mata in dai wanda ya shafi Abdul ne, after some seconds tace "Ina jin ka" Ajay yace "Me mahaifiyarsa tayi maki da
take neman gafaran ki, and from the look of things ba karamin abu tayi maki ba tunda har tace a kai ta wajen ki" Khaleesat tayi murmushin karfin hali, duk da shi yayi requesting sanin dalilin da yasa ake neman gafaranta she don't think she can tell him thi
s, don shi ma bazai so ji ba, barin yanda ta san sa da azababben kishi, he is only being curious shi yasa ma har yayi tambayar, ta langwabe kai tace
"Ka san sha'anin zaman tare, but i really can't say ga abinda tayi min fa, Allah dai ya ji kanta" Ajay na k
allonta yace "Ameen" But he sensed bata son gaya masa koma menene, tayi saurin kawar da zancen tace
"Kaga yanda Eeeman ke kallon ka kuwa, kamar ta fara gane ka fa" Ya wani kalleta yace "Jaririyar ce ta fara gane ni" Dariya Khaleesat tayi, yana murmushi ya
kai hannu ya amshi Eeeman dake ta kallonsa yayi kissing cheeks dinta yace "Are you trying to tell me something daughter?" Ya kai kunnensa kusa da face dinta yace "Tell me, ina jin ki my love" Ita dai Khaleesat murmushi kawai take tana kallonsu, after some
seconds ta sauke idonta tace "Ina ta son zan maka tambaya...." Ajay ya daga kai ya kalleta yace "Me ya hanaki wife?" Tana murmushi ta sauke idonta tace "I just want to ask about the people in Benue" Ajay na ta kallonta yace "Ke da kika yanka alakata da su
wife, cewa fa kika yi babu ni babu su" Khaleesat ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, cikin sanyin murya tace "Ni ba haka nake nufi ba wallahi, i am so sorry if i made you think that way, I don't know what came or mia at
that time" Ya kashe mata ido daya yac
e "Little Jay" Ita da tana kallonsa, he could see how remorseful she was, ya kivantar da
murya yana murmushi yace "Do not feel bad Jeeddah, Jay took careof that, ya kawo su masarauta sun hadu da sarki, Mai martaba ya siya masu gida a nan Benue which I know
they will never leave the riverine area to live in Benue, Jay yayi sponsoring education din yarinyar har Higher institution a nan Benue, ni kuma na ba babanta da Baabarta jari, sanin baza su iya rayuwa outside of Abinsi ba saboda fishing na yi masu gyara
sosai a nan cikin gidan nasu, i made their compound one of the best a garin, two months back da muka je Abuja da Jay sai da muka je har Benue wajen su, and they were so happy to see us" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya tace "l am so hap
py to hear this, nima watarana ina son ka kai ni mu je garin" Ajay ya bude ido yace "Salon ki ga an rungume ni aurena ya mutu? Idan aurena ya mutu nima ai na mutu kenan" Dariya Khaleesat tayi ta boye fuskarta a shoulder dinsa tace "A'a ko ma me za ayi maka
ni ba ruwana kawai kallo zan yi inyi dariya" Yace "Humm sai kace gaske" A hankali tace "Wallahi da gaske nake, ai na yarda da kai mijina" Shi dai murmushi yayi yace "Ko ma baki yarda da ni ba bazan maki kishiya ba Jeeddah, bani da ra'ayin mata biyu a rayu
wata, ko iya ke da ceeman da little Jay kun isheni rayuwa" Washegari kuma masarauta sư Pasni da mummunan labarin mutuwan Walid a kasar Nijar.....
Halysaah
*Plss do say a prayer for my late dad
😓
Feb 19 made it 2 years since he left this world, Allah
Ubangiji ya sabunta masa rahama da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu kurakuransu, Allah ya bamu guzurin tarar da su*
🥹
*My Arewabook/Arewapen readers, Allah ya maku albarka ya kara maku b
udi ta yanda baku tsammani, ina yin ku dari bisa dari*
Ajay na zaune parlon Mai martaba bayan sun gama shirin tafiya Nijar da shi da Jay da Mukhtar sai wasu daga cikin hadiman Sarki da Hajiya Shafa'atu da Kilishi da Gimbiya Firdausi, Hajja ta so bin su a
mma Sarki yace ta zauna Emirate kawai tunda za ayi ta zuwa gaisuwa, irin kukan da Hajja tayi zai nuna maka duk yanda jikanta yake fa ita dai a haka take mugun son abun ta, sosai mutuwar Walid ya ta
ɓ
ata don kwana tayi tana kuka tana nema masa gafara wajen U
bangiji, shi ma dai Ajay tun da ya ji rasuwan Walid jikinsa yake a sanyaye yana kuma ji a ransa ya yafe masa duk abinda yayi masa, Mai martaba yayi breaking silence din parlon yana kallon Ajay dake zaune a hankali yace "Walid is no more now Junaid, and I a
m hoping ka yafe masa duk wani abu da ya hada ku during his lifetime...." Ajay ya kasa
ɗ
aga kansa, Mai martaba ya ci gaba kamar bai son maganar don no matter who Walid is shi ya haifesa dole zai ji mutuwarsa komin halayyansa, calmly sarki yace "Abu daya ne
ya faru tsakanin ka da shi da har yau bana jin dadin abun idan na tuna saboda image din ka da kayi tarnishing a gidan nan har ma da waje without considering ur then title, and the news was everywhere, this gave me sleepless night, I felt baka daukeni da m
uhimmanci ba a matsayina na mahaifinka which warrant Decrowning you because of that Ahmad, idan na tuna ina jin zafin abun har yanxu..." Ajay ya kasa
ɗ
ago kansa har sannan, kamar zai yi magana kamar bazai yi ba, daga karshe da kyar yace "Abba Jeeddah ya bi
daki da asuba na tafi masallaci" iya abinda ya fada kenan yayi shiru, Mai martaba ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, duk da sanyin Ac na parlon sai da ya dinga jin zafi sosai, shi dai Ajay bai yarda ya daga kai ba, don tuno hakan kadai da yayi sai da yaji
sa wani iri yaji zuciyarsa ya cunkushe, da ranan ya tsaya karatu a masallaci babu abinda zai hana Walid far ma matarsa, it took the king almost a minute before he could utter anything, da kyar yace "Why did you hide this from me Ahmad?" Ajay ya girgiza ma
sa kai kawai, ya kasa cewa komai cause he is becoming emotional da ya tuna abinda aka yi masa akan haka, Mai martaba ya jinginar da kansa da kujeran da yake zaune ya lumshe idonsa don sosai yaji hankalinsa ya tashi, he became so guilty of what he did to hi
s son, sam bai masa adalci ba, bai basa listening ears ba ya yanke masa hukunci babu bincike, a hankali Mai martaba ya bude idonsa ya dafa Ajay yace "It's well son, it's well, da kai da Jawwad dama duk daya ku ke a wajena, but I am sorry for not giving you
a listening ear Junaid...." Ajay ya dora kansa a kafar Sarki, ko sau daya bai ta
ɓ
a jin baƙin cikin amshe title dinsa da aka yi aka ba Jay ba, what hurt him at that time was yanda kowa ya juya masa baya sai Khaleesat kadai that gave him a shoulder to cry o
n, daga wannan lokacin kuma ta ja sa a jiki ta amshesa a matsayin mijinta da bata yi ba a baya wanda hakan ya sa duniyar sa ta dawo sabuwa, and what happened seems like a blessing to him in disguise, some memories are just too hurtful to remember, har Ajay
ya bar parlorn jikin Mai martaba a sanyaye yake sosai, a karo na farko a rayuwarsa yayi da ya sanin yanke hukunci da yayi, not because Jawwad didn't deserve the title of a prince but because bai yi ma Junaid adalci ba as his father. Tawagar Emirate suka i
sa kasar Nijar inda Walid ya rasu, suka tarar da Aunty ta fita hayyacinta sosai, alamar mutuwar
ɗ
an nata ya daketa ba kadan ba, ta dawo kamar warce ta samu mental problem, dangin nata da ta guje ma duk sai da suka je Nijar din wajenta, irin kukan da Kilish
i take kai kace sun yi zama na mutunci da Walid kamar dai
ɗ
an ta ne ya rasu, Gimbiya Firdausi dama ita bata iya pretending ba ta samu gefe tayi zamanta tana alhinin rasuwan, Hajiya Shafa'atu ce kawai ke kusa da Aunty tana aikin lallashinta, duk yaran Aunty
mata uku suna tare da ita ashe a garin, kwana uku su Hajiya Shafa'atu suka yi a garin suka fara shirye shiryen komawa Nigeria, bayan sun gama shirin tafiya, Ajay ya kalli Baby dake gefensa, sai kuma ya kalli Aunty yace "Za mu tafi tare da Baby...." Aunty
ta daga idanuwanta da suka kumbura tana kallonsa, Hajiya Shafa'atu ta sauke ajiyar zuciya tace "Kamar ma bata da lafiya Babyn, ya kamata kam mu koma gida da ita, ba kuma hakan na nufin raba ki za ayi da ita ba, dama kuma duk in da uwa take dole 'ya yanta s
u neme ta, balle da ran Hajja kin sa yaran nan baza su ta
ɓ
a walakanta ba Hafsah, duk jikokinta daya suke a wajenta, don haka kiyi hakuri ki bar mana ita mu koma masarauta da ita, su ma yayyinta idan ku ka komo Nigeria da zaki kai zuciyarki nesa duk kiyi ha
kuri ki bari su koma where they belong don za a fi ganinsu da martabansu suna 'ya yan Sarki, don sun koma masarauta ba hakan ke nufin za su guje ki bane Hafsat" Aunty na kuka wiwi haka ta sadaukar suka bar garin tare da autar ta Baby me sunan Mahaifiyar Aj
ay, dama ko bata yarda ba Ajay bai yi niyyar barin baby a garin ba don bai ji dadin yanda ya ga yarinyar ba, ta rike sauran yaran nata but he is definitely leaving with baby, sosai Hajja tayi farin cikin dawowan da suka yi da Baby Emirate, Hajiya Shafa'atu
na zaune parlon Mai martaba da daddare, duk ta labarta masa halin da suka tarar da Aunty wanda duk sai da suka ji tausayinta a garin, ta kare maganarta da cewa "Allah Ubangiji ya sa mu fi karfin zuciyarmu yasa mu gama da duniya lafiya, sannan abu na karsh
e Mai martaba yaran nan Khadijah da Maryam in ma da fushinsu a ranka domin Allah kayi hakuri ka yafe masu, nasan basu kyauta ba biye ma mahaifiyarsu da suka yi, sannan ita Maryam tunda har ta idar da karatun ta tun shekarun baya kuma naga suna good time da
Mukhtar, why not ka hadasu aure kawai, bikin Iklima da Shahuda da za ayi nan da watanni shidda ina ga da sai a hada har na Maryam din da Mukhtar" Mai martaba dake ta sauraron Hajiya Shafa'atu ya sauke ajiyar zuciya, duk cikin 'yan uwansa a masarautar nan
da ita kawai yake jin dadin magana har ma su yi shawara, ya sha kiranta su yi solving issue a tare don ita kadai zata yi maka magana ta hankali babu son zuciya, sai kuma Mami da yake yawan magana da ita yanxu a masarautar, after some seconds yace "Shawaran
da kika kawo shawara ce me kyau Shafa'atu, amma sai na tuntubi Mukhtar din in sha Allah" Hajiya Shafa'atu tace "To Allah Ubangiji yayi mana abinda yafi alkhairi ranka shi dade, shi kuma Walid Allah ya ji ƙansa ya gafarta masa kurakuransa" Mai martaba yace
"Ameen" Khaleesat na duke gaban Mami a parlonta kanta a sunkuye, Mami na kallonta tace "Kuma kar kiyi wasa da cin abinci, you have to take care of ur self very well kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai a hankali tace "In sha Allah Mami, Nagode Allah ya sa
ka da alkhairi, Allah ya kara girma" Mami na murmushi tace "Ameen daughter" Babu yanda Mami ta iya but she know she is definitely going to miss Khaleesat and little Jay, duk da dare ne amma har compound kusan duk yan gidan suka rako Khaleesat, Kilishi na d
auke da Little Jay, Ajay na tsaye jikin motarsa da Jay dake kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Ajay, calmly yace "So nothing is making u change ur mind Junaid" Ajay yayi murmushi yace "Kai ma tun asali kasan bana son zaman gidan nan ai, beside I will be com
ing frequently to check on my daughter" Jay bai tanka sa ba don yayi kokarin convincing Ajay ya zauna a Emirate amma Ajay yaki, Hadiyah na gefen Khaleesat har suka iso parking space din tare, kana kallon Hadiyah kasan gaba daya a sanyaye take, Khaleesat ta
juya ta kalleta amma ta ma rasa abinda zata ce mata, don tasan tana magana yanxu sai ta iya fara mata hawaye, kawai tayi mata side hug sannan ta shiga back seat da aka bude mata, Kilishi ta mika mata little Jay, jakadiyar da Mami ta zabo mata ta shiga mot
ar dake bayansu, Jay ya karbi Eeeman dake hannun Ajay, Ajay ya
ɗ
an bude ido yace "Da ita ai za mu tafi malam" Sai a sannan Hadiyah tayi murmushi tana kallon Ajay, Ajay ya shiga back seat shi ma yana murmushin yana
ɗ
aga ma Eeeman hannu ai ko ta fara babbaka
masa dariya, a haka suka bar gidan Khaleesat na daga ma Hadiyah da su Kilishi hannu, it's been 4 months and some weeks since she gave birth to little Jay, bayan tayi arba'in da kwana biyu ta tafi Kano tayi ma Umma sati uku ita da little Jay Umma ta ci gab
a da kula da su, duk safiya kafin Malam Ali ya fita kasuwa sai ya sa an kawo masa little Jay don har cikin ransa yake jin yaron, dama Khaleesat have always been his favorite a duk cikin yaransa, a sati ukun nan sau biyu Ajay ke zuwa Kano duk sati ganin wif
e da son dinsa, Khaleesat ta murmure duk jikinta suka cicciko ta dawo kamar ba ita ba ga wani bala'in glowing da take, sosai jego yayi mata kyau, little Jay ma look very healthy, har sannan taki yarda ta basa madara breastfeeding dinsa take fully, tana shi
rye shiryen dawowa Bauchi kuma Aunty Farida ta haihu a Dubai, ta samu twins dinta duk mata, Khaleesat da Nenne da Umma where among the people da Sarki yayi ma Visa na zuwa Dubai tun kafin haihuwan, wannan yasa kawai daga nan Kano suka fara shirye shiryen z
uwa Dubai wajen Aunty Farida,