Showing 375001 words to 378000 words out of 641791 words

Chapter 126 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

110

da wayar gefenta, Safiyyah bata sake kulata ba ta fara cin abincinta, Khaleesat ta kwa

nta gefen gadon Safiyyah a hankali, Safiyyah dai sai kallonta take da gefen ido tana cin abincinta. Sai kusan karfe biyu da rabi Khaleesat ta tashi daga baccin da ya dauketa a kan gadon Safiyyah, bayan tayi sallan azahar tana zaune kan darduma Safiyyah tac

e "Me zan dafa mana, ko za ki ci Indomie? Or should I make us Couscous?" Khaleesat dai tayi shiru don gaba daya taji bata da appetite har sannan she was moody, Safiyyah ta mike ta fita daga dakin ganin ba tanka mata zata yi ba, a hankali Khaleesat ta jawo

wayarta wanda tun da ta ajiye daxu bata sake dauka ba sai yanzu, message din Ajay ta gani, ta wani hade rai ta bude message din taga yace "Start coming back home now" Few minutes ago ya tura mata text din, ta wani hade rai zata mayar da wayar ta ajiye sai

kuma ta bude data ta hau WhatsApp dinta, zaro ido tayi ganin miss call din Jay ya mata WhatsApp call, she couldn't believe her eyes ta dinga kallon call din babu ko kiftawa, duk da he is not online haka nan tayi returning masa call din, har sai da ya katse

sannan ta ajiye wayar, ko da Safiyyah ta dawo dakin bayan minti talatin tayi mamakin ganin Khaleesat ta sauko kamar ba ita ba daxu har da hiranta, Safiyyah ta ajiye masu Indomie din suka ci, duk tana kula da yanda Khaleesat ta sake kamar ba ita ba, Safiyy

ah tace "Kin ki bani labarin Convocation din da kika je ko" Khaleesat ta

ɗ

an bude ido tace "Da gaske fa ba wani labari, I met Jay's Cousin sisters a wajen kuma gaba dayansu basu yi welcoming dina ba, even his Aunties ni ban san me nayi masu ba" Safiyyah da

ke ta kallonta tace "Ohk ba cousin sisters din Ajay bane kenan sai dai Jay?" Khaleesat tace "Oho, duk daya ne ai" Safiyyah tace "To baki hadu da matar Jay ba" Shiru Khaleesat tayi taki ce mata komai tana cin Indomien gabanta, Safiyyah tace "Na zata ita ke

convocation din ai" Khaleesat tace "Ni ban sani ba kam" Daga haka Khaleesat ta canza labarin zuwa na Practical din da za su yi gobe a schl, bayan sun gama cin abincin Safiyyah ta kai plate din kitchen ta dawo, Khaleesat ta dauko laptop din Safiyyah tace "L

et's study a little about the practical before tomorrow" Duk da collective reading da suke yi lokaci lokaci Khaleesat ke jawo wayarta ta duba, Safiyyah duk tunaninta agogo take dubawa, can dai tace "Ya baki lokacin da zaki koma gida ne halan?" Sai a sannan

Khaleesat ta tuna text din da Ajay yayi mata daxu, ta turo baki tace "Toh ba karatu muke ba, ban gaya maki ba ina apartment dina fa" Safiyyah tace "Ban gane ba" Khaleesat tayi murmushi don har cikin ranta dadi take ji apartment dinta da ya maida ta, tace

"Jiya ya kai ni Apartment din, I think his stepmom and Aunty sun zo Maryland ne, kuma kinsan basa so na...." Safiyyah tace "Ashe gata yayi maki, to ke kadai ce a apartment din?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Eh, kawai ya bar motarsa a Garage ne, amma n

i kadai na kwana gidan" Safiyyah tace "Ikon Allah, duk abun sa kuma yana da kirki da hangen nesa fa, gashi baya son a tsangwame ki ya maida ke apartment dinki kilan har zuwa lokacin da za su tafi" Khaleesat bata ce komai ba ta ci gaba da karatun da take, d

aga karshe ta tashi zata shiga bandaki tayi alwala tayi sallah ta tafi gida kafin ya turo mata wani text din, Safiyyah ta bi ta da kallo har ta shiga bandakin sannan ta jawo wayarta da sauri ta bude don ta san password dinta, WhatsApp ta bude bayan ta kunn

a data, DM din Jay ta shiga ta fara cin karo da WhatsApp calls din da suka ma juna, can ta fara scrolling chat din nasu tun daga farko making sure she is fast kafin Khaleesat ta fito, ita dariya da mamaki ma abun ya bata ta dinga kallon ikon Allah tana kar

anta chat, jin alamar Khaleesat zata fito ta maza ta fita daga WhatsApp din ta kashe data tayi saurin mayar mata da wayar ta ajiye ta ci gaba da danne danne a laptop dinta, bayan Khaleesat ta fito ta tada sallah Safiyyah ta mike ta shiga bandakin tayi alwa

la ita ma. Karfe hudu da rabi Khaleesat ta gama shirinta zata tafi, Safiyyah tace "Bari in shirya in raka ki apartment din naki tunda ke kadai ce" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Da gaske?" Safiyyah tace "Eh mana, in na raka ki ba sai in dawo gida b

a" Khaleesat ta ji dadi har cikin ranta, tace "To kiyi sauri ki shirya, tun karfe biyu da wani abu fa ya turo min text in koma gida" Safiyyah ta bude baki tace "Tun karfe biyu shi ne kika yi ignoring text din??" Khaleesat ta hade rai tace "To ba karatu muk

e yi ba? Ai ba wasa muke ba" Safiyyah tayi er dariya bata ce mata komai ba ta mike ta fara shiri, bayan ta gama tace "Ina zuwa" Fita tayi daga dakin, Khaleesat na ta zaune bayan tayi order din masu Lyft da zai kai su gida, har minti goma ya shude Safiyyah

bata dawo dakin ba, zuwa yanxu kam hankalinta yayi gida don karfe biyar ya gota, ganin Lyft din ya iso ta mike ta dau handbag dinta bayan ta saka wayarta a ciki ta nufi kofa ta fita daga dakin, Safiyyah ta fito kitchen rike da leda ganin Khaleesat ta fito

tace "Yauwa fito mu tafi" Za su fita daga parlon Safiyyah tayi kasa da murya tace "Tana kitchen leka kiyi mata godiya ki ce kin tafi, har da tsaraba ta baki" Khaleesat ta

ɗ

an bude ido da mamaki, can ta leka kitchen din tayi ma Surayyah sallama, Surayyah ta

ce "Yauwa sai anjima ki gaida gida" Da haka suka fita daga parlon, sai kusan karfe shidda suka isa gida, bayan sun sauka Lyft Safiyyah ta kalli Garage tace "Ke ya dawo" Khaleesat tace "Ai bai tafi da motar jiya ba dama" Safiyyah tace "Au to, don da na juya

na yi komawata bana son jaraba" Suka karasa bakin apartment din Khaleesat ta bude kofa ta shiga Safiyyah na biye da ita a baya, kamshin turarensa taji a parlon, can ta juya da sauri ta kalli bakin kofa bata ga takalminsa ba, tayi ma Safiyyah alamar da tay

i shiru ta tsaya, tana tafiya a hankali ta haura sama ta bude duk dakunan bata gansa ba, ta sake dawowa kasa ta shiga kitchen nan ma baya nan, turo baki tayi tace "Kilan ya zo ne yaga ban dawo ba shi ne ya tafi" Whereas bata san yana nan neighborhood din b

a kuma yaga sanda suka shiga apartment din, Safiyyah ta rike ha

ɓ

a tace "Naga wani sabon raini kike ma Ajay din nan, ko da yake shi ne bai yi maganin ki ba har yanxu" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ni dai mu je sama" Sama suka tafi zuwa dakinta, Safiyyah t

ace "Ni ba ma dadewa zan yi ba kinga yamma yayi" Zaunawa gefen gadon tayi ta fara bude ledan dake hannunta, Khaleesat dai sai kallonta take, Safiyyah ta tsuke fuska ta ciro magungunan mata dake cikin ledan tace "Ga su nan saboda Allah ta baki kuma wai kin

yi aure bata baki komai ba, wallahi ba kowa ma take ba ma ba wannan kayan ba, baki ga jikinta luwai luwai ba da kika zo, duk kayan gyaran jiki ne, ance in mutum na da kyau ya kara da wanka, fatar ki zai kara fresh fiye da yanda kike yanxu, kinga wannan da

madara ake sha ko zuma, nasan ba lallai ki samu zuman ba so kiyi using madara, wannan kuma saboda raman nan da naga kinyi ne zai sa ki murmure nima shi nake sha nake cikowa idan naga na rame, shi ma da madara zaki sha, wannan kuma riga-kafin infection ne k

insan mu mata, to shi ne ta baki ki dinga using nima kwanaki ta tsam min....." Khaleesat ta dinga kallon Safiyyah da ta dinga zayyano mata amfanin magunguna kusan shidda dake cikin ledan da kuma yanda zata sha su, har sai da ta gama tace "Kin gane ko in da

wo farko? Naji kinyi shiru" Khaleesat ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace "Sai dai ki raina ma kanki hankali, ke kije ki gyara jikin ki da su mana, zaki wani kawo min maganin mata ki ce min na gyaran jiki, nace maki I have anything to do with

them ne??" Safiyyah tayi dariya don ita mance cewar Khaleesat ta ta

ɓ

a aure ma take, ashe fa tasan duk magungunan nan, can dai Safiyyah ta mayar da magungunan gefe ta hade rai on a serious note tace "Bari ki ji Malama idan zaki kama mijinki ki rike hannu b

ibbiyu ki dena hauka kan Housemate din ki to ina baki shawaran kiyi hakan tun wuri, don Housemate dai na can yana shagalinsa da matarsa sai abinda suka manta, da koro koro eyes dina naga zafafan hotunan da yayi updating a status dinsa na shi da matarsa kam

ar zasu hade su zama daya ga wani kallon soyayya da yake mata, ke kina ganinsu kinsan ba karamin amarci aka ci ba, see the way they were looking at each other a pics din ai duk nayi screenshot, tsabar shock sai da na farka cikin dare na sake kallon hotunan

na koma na kwanta, sabili da haka yasa na sa Surayyah ta debar maki kayan gyaran nan kema ki ji da mijinki ki samu lada, ke idan ma kina da isasshen hankali har sai wani ya baki shawaran abinda ya kamata bayan dawowarku daga England? Na zata you will be m

otivated ai ki dawo senses din ki, wai ko ba gabanki suka dinga hotunan bane?" A takaice Khaleesat tace "Ban san maki ba, ba cewa kika yi ba dadewa zaki yi ba idan mun zo, beside it's almost dusk ya kamata ki zo ki tafi" Safiyyah tayi shiru tana kallonta,

can tayi kasa da murya tace "Naji amma kina da kayan shayi a gidan nan ki dibar min, Surayya dai ta boye nasu" Har sannan fuskar Khaleesat a daure yake ta nufi kofa zata je ta dibar mata kayan shayin da Ajay ya kawo mata jiya, tana fitowa daga dakin ta gan

sa tsaye a corridor ya rungume hannu, she was very shock taji kamar ta juya ta koma cikin dakin tace ma Safiyyah ya zo, can kuma ta turo baki ta ki yarda ta kara kallonsa, kamar munafuka ta fara sauka downstairs, ya bi ta da wani kallo, Safiyyah na ganin K

haleesat ta fita ta mike da sauri ta dauko handbag dinta ta bude ta ciro wayarta tayi unlocking sannan ta shiga WhatsApp, blocking number Jay tayi bayan tayi deleting duk chat dinsu, ta tafi call logs dinta na WhatsApp da phone call ma duk ta goge numbersa

, ta shiga text message shi ma kafin tayi deleting sai da tayi blocking number ta yanda phone call ma bazai shigo ba sannan ta mayar mata wayar cikin jaka ta ajiye da sauri, waige waige ta fara yi jin kamar kamshin turare alamar dai wani ya shigo, ta mike

kamar munafuka tana rike da handbag dinta ta nufi kofar dakin da Khaleesat ta bari slightly open, ido hudu suka yi da Ajay that is looking at the room, Safiyyah ta

ɗ

an yi yake tana sosa keya tace "Good evening" Bata jira sai ya amsa ba ta sauka downstairs

da sauri, Kitchen ta samu Khaleesat ta tula mata Milo da Madara a ziplock bag, Safiyyah ta zaro ido tace "Ke kika siya?? Ji min mata" Khaleesat tayi kasa da murya tace "Ya dawo fa" Safiyyah ta rike ha

ɓ

a tace "Baki ga na lallaba na sauko downstairs ba babu

shiri" Khaleesat tace "Is he still upstairs?" Safiyyah tace "Eh mana, kawai kamshin turare naji na leko na gansa, ai ko sum sum na sakko kar ya koreni" Khaleesat tace "To me yake a wajen har yanzu?" Safiyyah tace "Oho" Ni dai nayi ordering Uber, sai mun ha

du school gobe, tare suka fito daga kitchen din bayan ta ba Safiyyah ledan kayan shayin da ta dibar mata, a nan kan kujera a parlor Safiyyah ta ajiye mata ledan cikin dubara don ita ba abinda zata yi da kayan shayi, ko damunta bai yi ba ma kawai tana son u

sing privilege din ne tayi abinda zata yi a wayar Khaleesat, Khaleesat ta rakata har wajen apartment din sannan ta koma ciki, amma fa duk ta tsargu kar ace Ajay yaji conversation dinsu da Safiyyah.

HALYSAAH

PA

G

E

117

Khaleesat na shiga apartment din ta s

amesa tsaye parlor, ta saci kallonsa zata wuce sama cikin tsawa yace

"Come back here" Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kallesa ta bata fuska, using a serious tone yace "From henceforth Kika sake ce min zaki je wani waje zaki sha mamakin abinda zan maki i p

romise you, ba dai baki da kunya ba? Zan yi maganin ki" Kamar zata yi kuka tana turo baki tace "To ko ba karatu muka tsaya yi ba muna da Quiz da za mu yi" Da gudu Khaleesat ta wuce sama ganin ya nufota fuskarsa daure, ta shige dakinta ta kulle, sai da ta z

auna gefen gado na kusan minti goma don seriousness dinsa ya tsorata ta, can ta e baki ta

mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta karasa bakin kofar a hankali ta bude tana leka downstairs amma bata ganin komai, corridor t

a fito ta leka taga baya parlorn, a hankali ta fara sauka stairs har ta shigo parlon taga alamar ya tafi, dakinta ta koma ta dau duk kayan matan da Safiyyah ta kawo mata ta sake sauka kasa ta shiga kitchen tayi disposing dinsu a dust bin sannan ta koma sam

a, wanka tayi ta canza kaya zuwa na bacci, sannan ta dau wayarta ta bude ta kunna data ta kwanta, ko yunwa bata ji don hankalinta duk na kan abinda zata yi a wayar, hancinta ta kai wayar jin kamar kamshin turarensa a jiki, she was very surprise, ta sake sh

inshina wavar to be sure of it, taji kamshin turarensa dai wayar yake, can dai ta bude WhatsApp dinta, after waiting for some second for her messages ta fara scrolling tana neman num

Jay, duk

iya dubawanta bata gani ba, ta shiga WhatsApp call logs dinta na

n ma babu numbersa, mikewa zaune tayi with shock tana kallon wayar babu ko kiftawa, nan tayi searching Housemate da sauri taga bai fito ba, ta koma contact dinta nan ma taga babu number, kasa ko kwakkwaran motsi tayi a inda take zaune, cikin mutuwar jiki t

a fara kokarin dialing number nasa thinking she still have it off hands kamar kwanakin baya amma duk yanda ta yi kokarin rubuto number sai taga ba haka yake ba, wasu hawaye ne suka cika idonta ta fada kan gado tana shesshekan kuka, ta yaya yasan password d

inta har ya dau wayarta, is this even possible, ita bata taba bude wayarta a gabansa ba ai balle yaga password dinta, kuka sosai take ta ma rasa abinda take ji a ranta, me yasa zai dau mata waya bata nan... Washegari Khaleesat taki tafiya school tsabar bac

in rai, tana ta kwance har karfe uku na yamma ko wank ta yi ba

balle breakfast, idonta duk sun kumbura don kuka, tun safe Safiyyah ke kiranta taki daga wayar daga karshe ma ta kashe wayar, sai kusan Magrib ta sauka kasa ta nemi abinda zata ci saboda yunwan

da take ji, ga mamakinta sai taga foodstuffs bakin kofar kitchen din, da Household items for cleaning, ta hade rai ta tsallake kayan tayi wucewarta cikin kitchen din, bayan ta hada shayi ta debi cookies ta wuce sama abun ta....

Washegari ma Khaleesat taki

zuwa school tayi ta kwanciya a daki, wajen karfe sha daya ta kunna wayarta kamar Safiyyah jira take sai ga call dinta ya shigo, Khaleesat ta dinga kallon kiran kafin tayi picking tayi shiru, Safiyyah tace "Me yasa kika kashe waya tun jiya Khaleesat? Hope

you are okay?" A hankali Khaleesat tace "Lafiya lau" Safiyyah tace "To me yasa kika kashe wayar? Kuma me yasa baki zo school jiy

yau ba

bayan kin san Friday ne Quiz din mu? Are you sure you are okay?" A hankali Khaleesat tace "Can you come over after schoo

l please?" Safiyyah tace "Sure, amma dai inji mijin ki baya nan?" Khaleesat ta hade rai tace

"Bana son haka Safiyyah, it's not funny" Safiyyah ta tabe baki tace "Toh naji, bayan azahar zan taho" Khaleesat tace "Apartment dina za ki zo" Safiyyah tace

"Apart

ment din ki? Har yanzu kina apartment din kenan?" Khaleesat tace "Eh" Safiyyah tace "Ohk to i will come in sha Allah after today's class" Daga haka ta katse wayar, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta looking so gloomy, mikewa tayi ta sauka downstai

rs har sannan foodstuffs din suna nan bakin kofar kitchen kuma bata ga alamar an shigo gidan ba duk yau, ta kwashi kayan abincin ta kai kitchen bayan ta ajiyes inda ya kamata ta hada breakfast ta fita daga kitchen din, sama ta tafi don kar ma ya zo gidan y

a ganta a parlorn, bayan ta gama breakfast din tayi wanka ta shirya sannan ta zauna gefen gado har sannan tana jin ranta babu dadi, ko bude WhatsApp

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login