Showing 51001 words to 54000 words out of 641791 words

Chapter 18 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

135

yana d

anna wayarsa daya hannunsa rike da jacket dinsa, yana ganinta yace "Are you ready? Where is ur jacket?" Karasawa yayi inda take tsaye yace "It's cold outside" Yana fadin haka ya ajiye mata Jacket dinsa kan kujeran dake kusa da ita yace "Use this, bari in d

auko wani" Dakinsa ya koma ita dai ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo parlon with another Jacket, ya saka a kan rigar jikinsa yace "Mu je" Ta sauke idonta ta dau Jacket din nasa, Kofar parlon ya nufa ta bi bayansa har suka fita daga pa

rlon, ya kulle kofar ya kalleta yace "Na lura kina son so much perfume ke dai" Ta girgiza kai tace "A'a ni ban sa ba yanzu" Yace "Ohk" A tare suke tafiya with nobody saying anything, tun ba su kai ko ina ba taji tana jin sanyi sosai, hakan yasa ta

ɗ

an saci

kallonsa sannan ta saka jacket din hannunta yace "Ai na zata baza ki sa ba kina forming big gal" Kawai dai tayi murmushi bata ce komai ba, tana jin kamshin turarensa da ya cikata na jikin Jacket din, dai dai yake tafiya da ita to keep same pace with her,

slowly suke tafiyar with absolute silence har suka yi nisa away from home, Jay yayi breaking silence din yace "Soon za a fara snow" Tace "In sha Allah kafin nan mun gama Exams dinmu" Zai yi magana wayarsa ya fara vibrate ya ciro a aljihunsa yana duba me ki

ransa, ta gefen ido ta kalli wayar tasa taga Ajay, yayi silencing wayar ya mayar aljihunsa, ta tabe baki tace "Shi dole sai ya dinga damunka da kira ne as if you are with his kidney?" Jay yayi dariya yace "Kidney ai me sauki ne, cewa za ki yi kamar life di

nsa na wajena dai, a rana sai ya kirani sau ashirin in banyi hankali ba" Khaleesat ta kyabe baki sai ga shi ya sake kiran wayar, Jay ya kara ciro wayar yayi picking ya sa Hands-free yana tafiya yace "What again?" Daga daya bangaren Ajay yace"I need ur lapt

op, zan duba references dinka, na mance zan shiga schl gobe, i

am outside with my frnd now" Jay yace "Da laptop din na fita ai, kuma i am not coming back home anytime soon" Ajay yace "Gidan wannan mara kunyan ka koma kenan? Wai are you even okay Bruh? Me k

ake yi da wannan yarinyar da ya sa kake zama gidanta? Ko iskanci ka fara ne? In ma iskancin zaka yi why with that little local brat pls?" Jay that was trying not to laugh yace "Kai kar ka bata min rai fa" Ajay yace "On a serious note idan baka daina zuwa g

idan nan ba i promise you am gonna report you back home kasan karamin aikina ne hakan ko?" Jay yace "In ka fasa, kai duk takurani da kake da yan iskan abokanka a can gida ban kai report ba sai ni da na bar maka gidan for peace to reign shi ne zaka kai kara

ta? To references din ma baza a nuna ba, go and sort ur self out" Yana kai wa nan ya katse wayar ya mayar cikin aljihu, ita dai Khaleesat bata kallesa ba kuma bata ce komai ba amma har cikin ranta take jin Ajay bai mata ba, she doesn't like him or anythin

g concerning him, ta tsani mutum that is too pompous and proud of himself, Jay yace "Baya karatu fa, in ma wani aiki ne sai dai kai kayi ya gani sannan yayi nasa, har ma nasan yafi naka at the end" Khaleesat tace "To me yasa har yanzu ba a koresa ba daga m

akarantar?" Dariya sosai Jay yayi yana kallonta yace "Baya karatu doesn't mean he is dull Halysaah, kinsan Genius? That is who Ajay is, he is naturally gifted, he graduated as one of the best medical student during our degree program in this state and mast

ers, kuma kar kice wani karatu yake, mu ne dai sai mun yi karatun za mu wuce" Yana murmushi ya kare maganar, Khaleesat ta wani kyabe baki kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "To ai gwara kai karatun kayi ka wuce, shi kuma banza kawai yake ci" Jay na da

riya yace "Ai shi sa na bar masa gidan cause idan na ci gaba da biyesa da abokansa wucewa zai yi ya bar ni, su kansa abokan nasa ina tausaya masu biyesa da suke" Khaleesat tace "Shi ne yasa kake Co-living?" Yace "Yeah, shekaranmu na karshe kenan idan Allah

ya yarda so i need much privacy to study very hard to earn my PhD, in kana tare da Ajay ba wani abun arziki da zaka yi in dai bangaren karatu ne, sannan baya barina inyi bacci sosai, nuisance ne shi fa, Ya Subhanallah" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa,

sai kuma ta sauke idonta, yace "Year nawa kike yanzu?" A hankali tace "Year 3" yace "Kince Pharmacy ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kin kusa gamawa kema ai in sha Allah" ita dai tayi shiru bata ce komai ba suna ci gaba da tafiya slowly, ita ce tayi breaking

silence din after almost 10 mins da ya biyo baya tace "You know him back home?" Jay ya kalleta yace "Wai Ajay? Yeah he is my favorite, yanzu ma dai kin ga budurwa nake nema masa bashi da mashinshiniya ko daya wallahi" Khaleesat tace "Ashe bazai taba samu b

a, ai he is way too rude and full of himself, wacece zata yarda ta auresa in dai ba auren dole aka mata da shi ba, ko makala mata shi aka yi?" Jay dai dariya kawai yake yana kallonta yace "Ya kai Saurayin ki?" Nan da nan mood dinta ya canza, taki ce masa k

omai tana ci gaba da tafiyarta, yana kallonta yace "Naga kin yi shiru ko compare and contrasting kike yi a zuciyarki? Tell me pls ya kai saurayinki?" Without looking at him tace "Kamar lokacin sallah yayi, and it's getting dark already" Yace "Ke ina ruwank

i da sallah tunda ba yi kike ba?" Khaleesat was dumbfounded jin abinda yace, ta kasa kallonsa kuma taki basa amsa still walking slowly, Roadside chair ta hango ta tafi ta zauna, ya karasa wajen yace "Ko har kin gaji ne?" Tace "To da bazan gaji ba, muna ta

tafiya for almost an hour now" Yace "Akwai wani Eatry a area din nan, mu je sai mu yi dinner before going back home, the eatry isn't far away from here" Khaleesat tayi shiru, ta san Eatry din da yake magana don sun ta

ɓ

a zuwa da Abdul kuma abincin wajen she

gen tsada ne da shi, yace "Let go" Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya, hakan ya sa ta mike ta bi bayansa, ya jira har ta iso inda yake sannan suka ci gaba da tafiya a tare har suka isa Eatry din, suna shiga ta kalli Jay that was grinning kamar yaga wan

da ya sani a cikin Eatry din, lkci daya ta hango Ajay that was sitted da wata baturiya a cikin eatry din yana mata magana, ga abinci kala kala a gabanta, shi kuma ruwan gora ne kawai a gabansa, Khaleesat ta dauke idonta speaking calmly tace "I think zan ta

fi gida kawai, dama ba wani yunwa nake ji ba, i will order a Lyft in koma gida" Jay ya riko gyalenta don har ta juya zata fita yace "C'mon Halysaah, so kike ya kara raina ki, kina fita zai yi zaton tsoronsa ne yasa kika kasa shigowa kika fita and he will b

e very happy, kawai kiyi fuska ki tafi ki zauna" Khaleesat ta tsaya bayan ta

ɗ

an yi nazarin abinda Jay yace, kuma fa haka ne zai yi zaton tsoronsa take, hakan yasa ta karasa Jay na biye da ita a baya ya jawo mata kujeran dake facing inda su Ajay ke zaune t

a zauna, Jay ma ya zauna sannan ya kalli direction din Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, Jay ya daga masa hannu with smile all over his face alamar Hi, Ajay ya dauke kai kamar bai ta

ɓ

a saninsa ba a rayuwa, Jay ya daga kafadarsa yana murmushi sanna

n ya dau menu dake saman table ya mika ma Khaleesat yace "Duba abinda zaki ci" Ta amshi Menu din tana kallo, cikin few minutes Jay ya saka masu order aka kawo masu abincin, duk da Khaleesat tana facing din Ajay ko da wasa bata yarda ta kallesa ba, tayi kam

ar bata san da shi a Eatry din ba, Jay kuwa cin abincinsa kawai yake with full concentration not minding her in his front, lkci lkci Khaleesat ke kallonsa, ta lura he doesn't joke with food and sleep for anything, dariya ma ita yake bata, ita kam a hankali

take cin abincin gabanta, ya daga kai ganin bata wani ci Crab patatoe Chips din gabanta ba yace "Should i fetch some of urs?" Ta wani kallesa tace "Do you have an extra stomach?" Bai san sanda yayi dariya ba yace "I don't understand an extra stomach?" Ta

na kallonsa calmly tace "Naga duk kai ka kusa cinye abincin kan table din nan" Jay ya bude ido sosai yace "Har da sharri? Me da me na ci a table din?" Ta tallabi chin dinta tana murmushi tana kallonsa wanda har sai da dimples dinta ya lotsa, Mistakenly ta

daga ido suka hada ido da Ajay dake kallonsu babu yabo babu fallasa, nan da nan murmushin dake fuskarta ya bace ta sha kunu, Jay bai ma san tana yi ba don tuni ya ci gaba da cin abincinsa har ma ya diba na gabanta, Khaleesat ta kalli wayarta dake vibrate k

an table, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, Jay ya daga kai ya kalleta yace "Ba kiran ki ake ba?" A hankali tace "Na sani" Yace "Why are you not picking?" Tayi shiru, sai a sannan ta tuna fa ashe ya kirata severally

bata daga kiransa ba, Jay

yace "Ko de saurayinki ne?" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, yace "Ki daga mana kar kiyi laifi" Sauke idonta tayi ta daga kiran a hankali ta kai kunne tare da sallama cikin sanyin murya.....

07087865788✍

🏻

Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::h

ttps://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6

✨✨

HALYSAAH✨✨

By _Khaleesat Haiydar_✍

🏻

17....

Daga daya bangaren Abdul yace "What is wrong with you these days Khaleesat? Me yake damun ki?" Tunanin abinda zata ce masa ta fara yi, t

ayi shiru gabanta na faduwa, ita ta ma rasa me yasa take ƙin daga kiransa kwanan nan, kawai a zuciyarta take jin bata son waya da shi, Jay ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru ga waya ƙare a kunnenta, amsar wayar yayi ta zaro ido tana kallonsa da mamaki w

ith fear, ya sa wayar handsfree ya rage volume sannan ya ajiye saman table ya ci gaba da cin abincinsa, a fusace Abdul yace "Wai baki ji na ne, or is something wrong with you?" A hankali Khaleesat tace "Ina jin ka mana, na mance wayar ne a gidansu Safiyyah

, i just got it now" Sounding so provoked yace "Ni zaki raina ma hankali? Ke ce zaki bar wayarki tun jiya gidansu Safiyyah?" Khaleesat ta wani kyabe baki ta kauda kai tace "Haka dai kawai bazan ki daga kiranka ba, me yasa baza ka min uxuri ba?" Abdul yace

"Wait Khaleesat, where are you getting ur liver from these days? Who is ur vendor? Yaushe kika fara samun courage din mayar min da magana?" Khaleesat tace "Toh ni yanzu me nayi? Nace maka wayar baya wajena and u are trying to create an issue out of nothing

, Nan da few weeks fa za mu fara jarabawa, you are only adding more pressure to the one i am already in, ka dinga considering dina mana pls" Jay ya

ɗ

an daga kai ya kalleta, sai kuma yayi murmushi ya dau ruwan gora ya bude yana sha, Abdul yace "A kanki aka

fara jarabawa? What is the big deal ah jarabawan da zaki yi? Ko dai Safiyyah ce ke dora ki akan abinda bazai fisshe ki ba? Safiyyah ce take zuga ki har kika fara samun courage din mayar min da magana ko? Switch to video call now" Khaleesat taji gabanta ya

fadi sosai, Jay dai murmushi kawai yake, a hankali Khaleesat tace "Ohk i will, amma kayi hakuri let me dress up first..." A mugun fusace yace "Ki bar shi" Yana fadin haka ya katse wayar, Khaleesat dai tayi shiru tana kallon wayar nata, Jay yace "Ki gama ci

n abinda zaki ci mu tafi Halysaah, it's pass magrib now zan je inyi sallah" Khaleesat ta daga idanuwanta tana kallonsa, yace "Ko ayi maki takeaway din abincin?" Ta sauke idonta bayan sun hada ido da Ajay da ya mike daga inda yake zaune, Jay ya juya ya

ɗ

an

kalli Ajay yace "Hey man, ka hada har nawa bills din" Ajay yaki kallon direction dinsa kai kace bai san sa ba ma, Jay ya kira daya daga ma'aikatan wajen ta karaso, ya sa tayi masu packaging abincin da Khaleesat bata ci ba, ita dai Khaleesat har sannan taki

cewa komai kana ganinta kasan she is a bit disturb, Jay ya bi Ajay da kallo har ya fita daga Eatry din da baturiyar da suke tare, shi bai ma ta

ɓ

a ganinta ba sai ranan duk kwashe kwashen Ajay ne, bayan ma'aikaciyar wajen ta gama packaging abincin, yana kal

lonta ya tambayeta bill dinsa, nan ta sanar masa Ajay ya hada har nasu ya biya, Khaleesat ta daga kai ta kalli waitress din jin abinda tace, Jay yace "Ok then" Mikewa yayi ya dau ledan abincin Halysaah yana kallonta, ta tashi ta dau wayarta, yana gaba tana

biye da shi suka fita daga wajen cin abincin, Lyft din da Jay yayi masu order har ya iso, ya bude mata back seat yana jiran ta shiga, Khaleesat felt somehow hakan da yayi, don duk fitar da suke yi da Abdul bai ta

ɓ

a mata haka ba, yawanci ma shi yake fara s

higa sannan ta shiga, bayan ta shiga motar Housemate dinta ma ya shiga, sai da suka kusa gida wayarta ya fara vibrate, ta kasa duba me kiranta sanin kila bazai wuce Abdul ba, Jay dake danna wayarsa ya kalleta yace "Kiran ki ake ai" Bata ce masa komai ba ta

kalli screen din wayar sai taga

Safiyyah ce ke kiranta, ta daga da sauri ta kai kunne tace "Hello Sophie" Safiyyah tace "Am at the door, nayi knocking shiru" Khaleesat ta

ɗ

an saci kallon Jay, sai kuma a hankali tace "Ohk na

ɗ

an fita ne amma ina hanya yanz

u" Da mamaki Safiyyah tace "Kin fita? Ban gane kin fita ba, Ina kika je?" Khaleesat tayi shiru, Safiyyah tace "Ko da Housemate din ki?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Hmmm i see, to in dai baku kusa dawowa ba bari inyi tafiyata kawai" Da sauri Khaleesa

t tace "Aa ki jirani am on my way" Tana fadin haka ta katse wayar, ajiyar zuciya ta sauke don tayi tunanin Abdul ne ya kira Safiyyah shine ta kirata, after some minutes suka isa gida, ta bude side dinta ta sauka daga Uber din, Jay ma ya sauka, Apartment di

nsu ta nufa, ta

ɗ

an rage pace dinta ganin kamar motar Mustapha a vicinity din, shi dai Housemate dinta na biye da ita a baya, sai ga Safiyyah ta fito daga motar Mustapha, da murmushi fuskarta ta nufesu ta gaida Jay, ya tsaya ya amsa mata sannan ya wuce cik

in gida, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Toh ki gaida ya Mustapha, dama girki na tsaya maki na zata har yanzu bakya iya tashi" Khaleesat ta kirkiro murmushi tace "Ohk bari in gaishesa" Zagawa tayi zuwa side din Mustapha taga yanda ya bi Jay da kallo har

Jay ya shiga cikin gida, gaishesa tayi kanta a kasa, ya kalleta yace "Who is he Khaleesat?" A hankali Khaleesat tace "Housemate dina ne" Mustapha ya kalli Safiyyah yace "There was a time da kika ce min mace ce Housemate dinta?" Safiyyah tace "Eh wallahi th

e lady packed out shine shi ya shigo, ai bai wani dade sosai da dawowa apartment din ba" Mustapha ya kalli Khaleesat yace "Me yasa zaki dinga zama gida daya da namiji da sunan Co-living Khaleesat, why not come stay together with ur frnd Safiyyah in my hous

e?" Safiyyah ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki, sai kace ya gama kwatar mata 'yan ci gun shegiyar matarsa balle ya kwatar ma ita da kawarta, ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana wasa da veil dinta, Mustapha yace "Wani yare ne Housemate

din naki?" Caraf Safiyyah tayi tace "He is from Tanzania, yaren can kasar yake yi, beside shi baya ma wani zama a gidan once a while yake zuwa yayi karatu kawai" Mustapha ya wani kalleta yace "Ke na tambaya?" Gefe ta koma bata sake cewa komai ba, Mustapha

yace "Daga ina ku ke da daddaren nan Khaleesat?" Khaleesat tace "I was sick tun da safe shine muka je ya siya min abinci yanzu" Mustapha dai sai kallonta yake, after some seconds yace "I will talk to my wife, sai ki dawo nan gidana kiyi zamanki tare da Saf

iyyah har ku gama Exams, i think the exam is by the corner...." Khaleesat tayi murmushi kawai bata basa amsa ba, Safiyyah tace "Mu je in kai maki abincin da na kawo maki ciki" Bude bayan motar tayi ta ciro abincin, Khaleesat tayi ma Mustapha sai da safe sa

nnan suka wuce apartment dinta tare da Safiyyah, nan parlor Safiyyah ta ajiye abincin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login