Showing 450001 words to 453000 words out of 641791 words
Jay, kwance ta samesa kan 3 seater shi kadai a parlon, ya juya jin an bude kofa, ganin ita ce ya dauke kansa, ta karaso ciki tace "Nayi tunanin ma ka koma bacci, Sarkin 'yan bacci"
Ya sauke idonsa a hankali ya gaisheta, ta amsa tace "Hadiyar bata tashi ba" Bai ce komai ba, Calmly tace "Jawwad ka tafi ka duba
ɗ
an uwanka ba shi da lafiya sosai, daga can wajensa nake yanxu" Dai dai nan Hadiyah ta fito daga kitchen rike da cup din tea ta
na sanye da Kayan bacci, ganin Hajja cike da damuwa tace "Yauwa Hajja gwara kiyi masa magana kilan yaji naki a kira masa Doctor, bai fa yi bacci jiya ba bashi da lafiya kuma yaki barin in kira likita" Hajja tace "Subhanallahi, me ya samesa?" Hadiyah tace "
To nima dai ban sani ba, he was running temperature and throwing up all through the night, ko masallaci bai iya yaje ba da aka yi sallah yanxu, he is just lying down here" Hajja dai tayi shiru tana ta kallon Jay, can ta karasa har inda yake kwance ta kai h
annu goshinsa taji zafi kamar wuta, shi dai kallonta kawai yake, a hankali Hajja ta zauna kan kujera bata sake cewa komai ba. Da gayya Gimbiya Firdausi ta zo bangaren Mami tare da su Ummi, Hajiya A'isha har da Hajiya Sumayya wajen karfe bakwai da rabi na s
afe duk a sunan ta zo duba condition din Khaleesat bayan Mami ta kirata a waya don Mami ƙin zuwa sashin da take tayi, dama tun jiya su Hajiya A'isha ke cewa Gimbiya Firdausi taje kawai tace zata duba Khaleesat don ita kadai ce zata tona asirin Junaid har m
a da Khaleesat din don wannan abun bai yi kama da komai ba sai plan da aka shirya na rainin wayo a masarautar, don kaf dinsu babu wanda yaji wani ihu, ita tasan inda ta tafi ta tsaya tayi ihun har Mami da Hajja suka jiyota tunda su ne Main target dinta dam
a, sai da suka jira ranan da Hajja ta sauka masarautar sannan za su aiwatar da shirinsu, Su Hajiya A'isha duk suka zauna parlon Mami ko dakin basu karasa ba, Aunty dake zaune kan kujera a parlon ta amsa gaisuwansu cike da kasaita, ita din ma kiri kiri daxu
ta bi Mami har kitchen ta nuna mata wannan abun shiri ne kawai don babu bazawarar da ta ta
ɓ
a komawa budurwa in ba raina ma mutane hankali Junaid zai yi ba, Mami dai bata tanka ta ba ta ci gaba da abinda take a lokacin, Gimbiya Firdausi kadai ta karasa har
Bedroom din Mami ta shiga da sallama, Khaleesat na kwance don ko zama ta kasa yi, Mami dake zaune dakin tayi nisa tunanin da take, ga breakfast a gabanta ta kasa ci, ita ma duk ta dawo wani iri kamar tare suke jinyar da Khaleesat, Gimbiya Firdausi ta zaun
a kan kujera bayan sun gaisa da Mami tace "Sai fa an samo hand gloves, in kuma akwai to a bani...." Mami dai bata ce komai ba, don banda Hajja ce tace ayi ma Gimbiya Firdausin magana ita da kawai likitar dake dubata zata kira ta zo ta duba Khaleesat, can M
ami tace "Sai a siyo, don bani da Hand gloves tunda ba aikin lafiya nake ba" Gimbiya Firdausi tace "Da aka san babu ai tanadinsa ya kamata ayi kafin ma a kirani, tunda dubata aka ce za ayi, hakan kuma ba mai yiwuwa bane babu gloves" Mami bata sake tankata
ba, after a while ta dau wayarta ta fara kiran Mukhtar yaje ya siyo Hand gloves din.... Bayan Gimbiya Firdausi ta gama duba Khaleesat a dakin Mami ta fita ta koma can sashinta dake cikin gidan, nan ta tarar da su Hajiya A'isha zazzaune a parlor suna jiran
dawowarta don tuntuni suka baro part din Mami bayan da Hajja ta shigo, tun da Gimbiya Firdausi ta shigo parlon su Ummi ke ta kallonta suna jiran jin Feedback, Kilishi ta kasa daurewa tace "Duk plan ne ko Aunty Gimbiyah? Naga duk ranki a bace da alama
ɓ
ata
maki lokaci kawai aka yi gashi ko Breakfast baki yi ba" Gimbiya Firdausi ta zauna kan kujera ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tace "To amma menene fa'idar cewa da aka yi yarinyar ta ta
ɓ
a aure? Kuma naji an ce daga bakin iyayenta hakan ya fito, to guduw
a tayi bayan an daura mata auren amma dai ko?" Duk su Ummi da Hajiya A'isha suka dinga kallon Gimbiya Firdausi babu wanda yace komai, Can Hajiya Habibah tace "Ikon Allah, a takaice dai yarinyar budurwar ce kenan dai Yaya Gimbiyah?" Gimbiya Firdausi tace "T
o sai ma an hada mata da dinki, yanda ku ka san mara hankali haka yaje mata...." Takaici yasa Kilishi ta kasa cewa komai ta wani rungume hannuwanta tana zaune ta cika one sitter sai sauke numfashi take da kyar tsabar kibarta, da wani expression Ummi tace "
Budurwa ce dai kenan?" Hajiya Habibah tace "Kin ji ki da wani zance Maimuna, abu kina ji ance sai an hada mata da stitches, duk yanda aka yi auren farko da aka yi mata shegiyar ƙin zama tayi ta gudu saboda ta kwallafa rai kan Jawwad, kilan ma shi zai ce ta
gudu kar ta zauna duba da yanda yayi ta jigila da ita, wannan dalilin ne yasa mijin ya saketa babu tantama kar taje ta kashesa, dama gashi mun samu labarin tun ma kan aurenta na farko suke tare da Jawwad din ai a Amurka a apartment daya ma suke rayuwa, ha
r gidan sarki na Baltimore an sha kamata, Fulani da kanta ta kamata a gidan" Mikewa Gimbiya Firdausi tayi ta wuce cikin daki, Kilishi ta bi ta da kallo zuciyarta na suya sosai, Ummi kuwa kara gode ma Allah ta dinga yi a zuciyarta da Mami tabi duk yanda ta
bi ta ruguje maganar auren Khaleesat da Jay duk da ita ma tana ta bi ta karkashin kasa bata zauna ta zura ido ba, ashe da auren ya tabbata ita ma dai budurwa ce ba Bazawara ba kamar yanda suke kiranta, da haka Jay zai ta rawan kafa da rawan kai a kanta sai
dai er ta Hadiyah tayi ta kwasan haushi da bakin ciki, kai dole ta kara gode ma Allah, Hajiya Sumayya dake zaune parlon taki cewa komai tun daxu ta tabe baki tace "As far as ta ta
ɓ
a aure ta fito kafin ta shigo gidan nan babu abinda zai goge wannan tag din
Bazawarar a rayuwarta, ko mijinta na farko ya sadu da ita ko akasin haka to bazawara ce dai tunda ya saketa ta fito ta sake wani auren...." a fusace Kilishi tace "Atohh dai Momy, kema dai kya fada, tunda har tayi aure ta fito mu dai har abada a Bazawara z
a mu dinga kallonta babu ruwan mu da cewar ta zo gidan nan da budurcinta, da bakin iyayenta suka furta cewar Bazawara ce er su tunda su ma sun san gaskiya, in dai kayi aure ka fito to babu zancen wani Budurci ko da mijin bai sanka ba ka fito gidan" Hajiya
Habibah ta wani ta
ɓ
e baki tace "Ga dai Hajja sai nanata cewa take jinin budurci ne kan gadon da yake dama babu wanda take so a gidan nan irin Junaid in ma ba gaskiya bane ita tuni ta nemi rufa ma shi da matar tasa asiri tun a daren jiya, sai wani farin cik
i take uwa an mata albishir da aljanna, tayi sintiri bangaren Aseeyah yafi a kirga da safen nan, me yasa bata ma Hadiyah haka ba tunda dai ita ma a matsayin budurwa aka aurar da ita, anya kuwa??? ko da yake mu ma mun fi sati a gidan nan bayan tarewar Hadiy
an amma bamu ga alamar komai ba wallahi, ko canjin taku..." Hajiya A'isha ta dinga ma Hajiya Habibah alamar tayi shiru ga Ummi zaune a wajen, tuni Hajiya Habibah ta ankare tayi maza ta canza zancen don shafff ta mance Ummi na parlon, Ummi na mata wani kall
o tace "Anya me Yaya Habibah? Me kike nufi?" Hajiya Habibah ta buda hannuwa biyu uwa almajira ta langwabe kai tace "Anya kuwa ta dau Hadiyah da Jawwad yanda ta dau Junaid? Jawwad din da ta rasa mahaifinsa tun yana karami wallahi bata nuna masa soyayya yand
a take ma Junaid dake da gatansa ba tunda ga Mai martaba a raye, ko zuwan nan da tayi ma na samu labari daga tushe me karfi ta zo ne don ta umarci Sarki da ya mayar ma Junaid Title dinsa na Yarima kar rai ya
ɓ
aci" Ummi dake ta kallon Hajiya Habibah babu ko
kiftawa tace "A ina kika ji wannan magana Yaya Habibah?" Hajiya Habibah ta gyara zama tace "Kema dai Maimuna, kin fa san maganar cikin gidan nan bai boyuwa gaba daya barin ni da na jiyo hakan daga majiya me tushe, muna nan dake ba dai anjima ne zaman Meet
ing ba zaki ce Habibah ta fada, Hajja bata duba cewar idan aka bar ma Jawwad title din nan ba sarauta bazai ta
ɓ
a barin lineage dinmu ba tunda Hadiyah dai dole ita zata haifi future king din Emirate din nan, kuma ita din jikar sarki ce uwarta er sarki, amma
take so ta karfi da yaji ta mayar ma Junaid ta yanda buzaye za su amshe mana sarauta wataran muna ji muna gani, kan kace me gaba daya masarautar sai dai a ga jajayen buzaye na yawo maimakon Hausa Fulani" Mikewa Kilishi tayi fuuu ta wuce dakin Gimbiyah Fir
dausi, ta zauna kan kujera tana kallonta don shayi take hadawa zata sha, Gimbiya Firdausi tace "Amma nayi mamaki ainun kasantuwar yarinyar nan budurwa Kilishi" Cikin
ɓ
acin rai Kilishi tace "Yanxu Aunty Gimbiyah ya kike ganin za ayi wannan abu, sannan ga wa
ni labarin daga bakin Habibah kin santa da munafurci wani lokacin kafin labari ma ya zo garemu yaje mata ita da ba ma garin take ba, to wallahi wai ta samu labarin Hajja ta zo ne ta tilasta Sarki ya mayar ma Junaid Yarima a yau yau din nan, shi ne ma meeti
ng din da za ayi anjima, in haka ya faru fa
ɗ
an da shegiyar buzuwar can zata haifa ne zai yi mulkin Emirate din nan wataran ko da ranmu ko babu ran mu, a da muna tunanin juya hankalin Jawwad kan Humaira tunda Shahuda dai tace Junaid take so, sai gashi ma z
a a amshe title din a hannun Jawwad din yau, kowa fa yana son mulkin nan ace ya dawo gidansa ko ta yaya, ita ma A'isha ina lura da take takenta so take ta cuso Iklima, ita kanta shegiya Maimuna ji murnan da take da aka kwace ma Junaid Yarima aka ba mijin e
r ta, don haka gaskiya gwara mu canza tsari Aunty Gimbiya, in har Hajja ta birkice ma Sarki fa to dole zai maida ma Junaid Title dinsa" Gimbiyah Firdausi tayi kasa da murya tace "Ke yanxu ya kike ganin za ayi Kilishi?" Kilishi ta dawo kusa da ita cikin rad
a tace "Ba kince tana can ya farketa ba har dole sai anyi dinki?" Gimbiya tace "Dole kuwa sai anyi dinki" Kilishi tace "To yanxu an tafi siyo maki kayan aikin da zaki dinka ta din ne? Abinda zai faru kawai cusa scissors zaki yi a mahaifar ki katse sa in za
i yiwu, wato dai kiyi damage din mahaifarta kawai Aunty Gimbiya yanda
ɗ
a bazai iya zama ciki ba, ko bazai yiwu ayi hakan ba?" Gimbiyah Firdausi ta zaro ido tace "In ma zai yiwu Kilishi a dakin Mamin zan yi wannan aika aikan matar da saboda bata yarda da ka
nta ba ko ina na bangarenta Cctv ne" Kilishi ta wani kalleta tace "Kai kin ji ki, wallahi ba wani Cctv a dakinta, Parlon ma saboda satan da Walid yayi mata kwanaki na gwala-gwalanta yasa ta saka Cctv din, amma ba komai dakinta, wallahi in wannan damar ta w
uce mu shikenan mun shiga uku mun lalace, kinga in aka ga bata haihuwa ai karin aure ya kama Junaid, to a nan za mu cusa Shahuda ko Humaira" Gimbiyah Firdausi tace "To har Aseeyan ta kira likitan da za tayi aikin, yanxu haka can na barosu tare da likitan,
balle ni ba mahaukaciya bace da zanyi wannan aika aikan a bangaren Aseeyah" Kilishi ta ciji yatsa tace "Kashhhh" shigowar Hajiya A'isha ne ya sa duk suka yi shiru, Kilishi tayi maza ta canza zancen. Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na bangaren Hajja a da
kin da Hajjan ta sa aka gyara mata aka shimfida mata lallausan zanin gado tun bayan da likitan Mami ta gama abinda zata yi mata ta tafi da safe, she felt a lot better akan yanda take ji daga daren jiya zuwa safiyan yau, duk da she is still in pain amma tan
a jin dama dama yanxu, kula na musamman Hajja ke bata making sure she is alright and needs nothing, haka ma Mami da every now and then take zuwa bangaren dubata, sai a yanxu Khaleesat ta fara jin kunyan da bata ji ba daren jiya, don ta kasa dinga hada ido
da Mami ko Hajja, sai tayi ta sunkuyar da kai, kaf gidan babu wanda ya shigo side din Hajja da sunan ya zo dubata sai dai in tasa ta shigo da shi sai Hajja tace ya shiga yayi mata sannu a daki, Hajja na parlor Jay ya shigo kansa a kasa, Hajja dai sai kallo
nsa take ganin har ya fada zazzabin da yayi, ya zauna kusa da ita tayi kasa da murya tace "Ya jikin Jawwad?" Yace "Naji sauki" Tace "Amma ka kara shan magungunan da likitan ya baka kuwa?" Yace "Na sha" Hajja tace "To ka ci abincin da na aika maka?" Yace "N
a ci" Hajja bata sake cewa komai ba tayi shiru tana kallonsa, tun daxu take son zuwa dubasa a side din nasa amma saboda bata son barin Khaleesat ita kadai gashi Mami ta fita yasa bata je bangaren nasa ba, hatta side din Junaid tana son zuwa don rabonta da
can tun karfe biyu saura da taje ta samesa yana bacci bayan Likita ya dubasa, bata tashesa ba ta fito don taga Yakumbo ta kai masa abinci part din, kuma tana ta shiga wajensa now and then, Hajja dai sai kallon Jay take don taga alamar da maganar da ya zo z
ai mata ne, shi dai idonsa na kan TV dake aiki a parlon yayi shiru, Mami ce ta shigo cikin parlon da sallama ta dinga kallon Jay dake zaune kusa da Hajja, can ta sauke idonta, Hajja tace "Kin dubosa Aseeyah?" Mami tace "Eh bai tashi ba, baƙi muka yi Hajja"
Hajja tace "Baƙi daga ina ni da nake da mara lafiya da nake dubawa, ai ba a sanar min kowa zai zo ba" Mami tace "Kakar Halysaah ce...." Dai dai nan Nenne ta shigo parlon da sallama tana rataye da jakarta ta sha tsadadden lace da mayafi shi ma me tsada, ka
i baza kace ita ta haifi Malam Ali ba, bayanta kuma Aunty Murja ce ita ma ta yafa gyalen da Nenne ta ara mata me tsada akan sabuwar atamfar jikinta, Sai Noor da Aunty Murja ke rike da hannunta, da fara'a Hajja ta dinga masu sannu da zuwa tana kallonsu, Nen
ne ta tafi har gabanta ta zauna sannan ta mika mata hannu biyu cikin ladabi suka gaisa da Fara'a, Aunty Murja da ta zauna kasan carpet ta gaida Hajja cikin ladabi ita ma, Hajja na mata sannu da zuwa, Mami na kallon Noor da ta rakube jikin kujera tana wasa
da kujeran bata zauna ba tayi mata murmushi tace "To zauna kan kujeran mana yan mata" Noor ta sunkuyar da kanta ta zauna kasan carpet, Hajja ta mika mata hannu tace "Taho nan ki zauna yarinya, ya sunanki?" Noor ta mike ta tafi kusa da Hajja tace "Ina yini"
Hajja ta rungumota tana Kallonta da fara'a tace "Lafiya lau Baby girl, amma ke kanwar Jiddah ce ko, ga kama nan Maa sha Allah, ya sunanki?" Noor na wasa da fingers dinta tace "Sunana Noor" Nenne na murmushi tace "Fatima ce Ranki shi dade, shi ne ake kiran
ta Noor, tagwaye ne, dayar me suna Islam tana can ita bata iya nisa da uwar, duk kannen Khaleesat ne uwarsu daya ubansu daya" Hajja ta bude ido sosai tana kara kallon Noor da kamar an tsaga kara ita da Khaleesat tace "Maa sha Allah, takwarata ce ma ashe, s
annu da zuwa Noor, Allah Ubangiji ya maki albarka" Sai a sannan Jay ya gaida su Nenne, Nenne ta rike baki tace "Au, ai ban lura kai bane Ahamad, dama kai ne zaune?" Ya
ɗ
an yi murmushi a hankali yace "Ya hanya Kaka?" Nenne tace "Ai kwananmu uku kenan a Bauc
hi amma sai yau Allah ya bani ikon zuwa, na zo duba mara lafiya shi ne nace bara dai in zo mu gaggaisa a gurguje in koma, ashe da rabon zan hadu da Hajiya ne tana gari" Tuni masu aikin dake part din Hajja suka taho :da ruwa da lemo sai fresh fruits masu Ya
wa aka ajiye ma su Nenne.,
HALYSAAH
Khaleesat na kishingide tama repiving message din da Safiyyah tayi mata tun safe, nwa take i sosal amma duk abinda ta kal bakinta sai taji sa kamar magani, ga dal abinci iri ini da aka cika mata amma duk basu da dadi
a bakinta sai watermelon kawai take ta sha, ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, ajiye wayar hannunta tayi da mamaki tana kallon Noor babu ko kiftawa, Noor ta tafi da sauri ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Aunty" Khaleesat na