Showing 462001 words to 465000 words out of 641791 words

Chapter 155 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

211

yanda take yi duk sanda ya shigo, kallon saman gadon dakin yayi, ya mike ya karasa kan gadon ya zauna yana kallonta ya kai fuskarsa kusa da nata yayi kasa da murya yace "I know you are not sleeping

Jeeddah, plss ki bude idonki don Allah...." Ganin ba bude idon zata yi ba, a hankali yace "Shikenan since you don't want to see me, i am leaving for Abuja before dawn tomorrow in sha Allah, zan je wajen Ammi she lost her father this night" Yana kai wa nan

yayi pecking cheek dinta a hankali ya mike ya fara tafiya yana waigota, tana jin ya tashi daga kusa da ita ta bude idonta a hankali abinda yace na mata yawo a kai, sai da taji ya bude kofar dakin ta kasa daurewa kawai ta juya kanta a hankali suka yi ido hu

du da shi, tsaye yayi yana kallonta hannunsa rike da handle din kofar dakin, ta cire idonta daga nasa tana jin zuciyarta na bugawa, cire hannunsa yayi a handle din kofar walking slowly ya koma kusa da ita ya zauna yana kallonta yayi kasa da murya yace "Jee

ddah" Ta daga ido ta kallesa nan da nan taji hawaye sun kawo idon nata, dai dai nan Aunty ta shigo dakin tare da cousin sister dinta Hajiya Nafisah, hakan yasa ya mike without looking at them ya gaida Hajiya Nafisah sannan ya fita daga dakin, Aunty sai kal

lon Khaleesat take babu ko kiftawa abinda Hajiya Nafisah tace na mata yawo a kai, ko amsa gaisuwar Khaleesat din bata yi ba ta juya ta fita daga dakin, Hajiya Nafisah ta juya ta bi bayanta, sai da suka fita daga part din Hajja gaba daya Aunty na kallon Haj

iya Nafisah tayi kasa da murya tace "Ni duk kaina ya kulle fa Nafisah, anya baki yi kuskuren suna ba kuwa?" Nafisah tace "Haba sai kace wata shashasha, ba ita bace Hauwa Aliyu, ana kiranta Khaleesat" Aunty tace "Kwarai..." Aunty Nafisa tace "To ita zata ha

ifi Yarima karami na masarautar nan, kuma ko muna raye ko a mace sai

ɗ

an ta yayi mulki a masarautar nan" Aunty tace "To ni abinda ban gane ba, sake amshe title din Yariman za ayi wajen Jawwad a mayar ma Junaid kenan ko kuwa? Don maganar da nake maki yanxu

dai Jawwad ne magajin sarki a Emirate din nan, sarki bai canza haka ba" Nafisa tace "Abu ya zama wasan yara ma kenan in aka sake mayar ma Junaid title, kuma ni ba ace min za a mayar masa ba, ni nafi tunanin kilan wataran Jawwad din zai nada

ɗ

an Junaid din

matsayin Yarima a maimakon

ɗ

an sa, nan kawai tunanina ya tafi gaskiya, in kuma na kara yin wani tunani sai in ga ae su Maimuna baza su ta

ɓ

a barin haka ya faru ba...." A fusace Aunty tayi kasa da murya tace "To ba a gaya maki menene makomar Walid ba a gidan

nan? Shi bazai yi sarauta ba kenan ake nufi ko me? To wallahi sunan Jawwad matattce, ko da last kobo dina ne sai an kawar da shi, ae sai yana da ran zai yi sarauta dai ko?? Da yayi sarauta astagfirullah ba gwara Junaid yayi ba zan fi jin kamshin sarautar

a kusa" Nafisa tayi kasa da murya tace "Mu je dai sashinki fulani, don maganar ba ta tsayuwa bace, Junaid kam babu zancen sarauta a tare da shi sai dai Jawwad, har nuna min shi aka yi a throne din mulki" Rai bace Aunty ta dinga bin Nafisah za su koma part

dinta, saukan Nafisah gidan kenan ta dawo daga kasar Nijar duk akan aikin Aunty. Ajay na zaune parlon Mai martaba wajen karfe tara da rabi na dare, Aunty ma na zaune parlon, Mai martaba na kallonsa yace "Allah ya kai mu goben, karfe nawa zaka tafi?" Ajay y

ace "Before subhi in sha Allah, driving zan yi zuwa Kano sai in bi jirgin karfe takwas zuwa Abuja" Mai martaba yace "Me yasa baza ka tafi Abujan direct daga nan ba?" Ajay yace "Babu jirgi time din, kuma ina son in samu sallan jana'iza ne" Mai martaba yayi

shiru, sai kuma yace "Tare za ku tafi da Jawwad?" Ajay ya girgiza kai yace "Ban gaya masa ba tukunna, seems ya fita baya nan" Aunty tace "Ya kamata kam ku je tare da shi, tafiyar mutum biyu ma tafi dadi ai" Ajay dai ko kallonta bai yi ba, Sarki yace "To ya

maganar tafiyarku zuwa Tanzania da matar ka? Fulani Aseeyah tace can zaka fara zuwa, in kun dawo sai ku tafi Ethiopia da Jawwad haka ne?" Ajay ya gyada kai yace "In sha Allah, jibi ne tafiyar dama, amma zan yi rescheduling ticket din zuwa nan da 4 days, d

on zan yi kwana biyu a Abuja" Mai martaba yace "Alright, amma kayi ma Jawwad magana ku tafi gaisuwan tare" Aunty tace "Gaskiya kam, hakan yafi ku je tare" Ajay Yace "In sha Allah ranka shi dade" Ajay na barin parlon Sarki ya hadu da Jay ya dawo zai tafi pa

rt dinsa, kallo daya Jay yayi masa yace "Evening" Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa bai tsaya ba, Ajay ya juya ya bi sa da kallo, yace "Za mu je Abuja gaisuwa gobe, Ammi lost her Dad" Jay ya tsaya ya juyo yace "Allah ya gafarta masa, but i am occupied gobe

, sae dai jibi" Ajay yayi shiru at first don ba haka ya so ba, tamkar Grand dad dinsa yake kallon mahaifin Ammi saboda love din da ya nuna masa tun yana karami, sai kuma yace "Ohk... Allah ya kai mu" Jay yace "Ameen" Daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa par

t dinsa. Aunty na zaune dakin Walid wajen karfe sha biyun dare tana magana kasa kasa tace "Kuma tunda sarki yayi magana nasan dole tare za su je gaisuwan nan" Walid ya zauna da kyar saboda har lkcn kugunsa bai dawo dai dai ba, yace "To a motar wa za ayi ta

fiyar?" Aunty tayi shiru, sai kuma tace "Bazai wuce motar Junaid ba mana tunda tafiyar tasa ce, kafin sallan asuba dae za su dau hanya, wallahi ko yau sai da Nafisah ta sake maimaita cewar Malamin yace in dai ba kawar da Jawwad aka yi ba to babu kai babu m

ulki, yau Jawwad na barin duniya kai za a nada Yarima tunda babu zancen wani Junaid" Walid yace "Shikenan, kawai ki tafi ku kwanta nasan me zan yi Momy" Aunty tayi murmushi tace "I trust you my son, but be extremely careful" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fit

a har lkcn tana murmushi, Walid ya dau wayarsa ya fara dialing number wani dogari dake masa aiki idan bukatar hakan ta taso a gidan, su biyu ne trusted people dinsa a masarautar, duk wani evil plan dinsa da su yake shiryawa ko ma wani iri ne, be it na ciki

n masarauta ko outside of the emirate.., Yana fara ringing dogarin ya

ɗ

aga ya fara jero masa kirari.

HALYSAAH

Halysaah....

Da yamma wajen karfe shidda Khaleesat na zaune ita kadai daki bayan Ajay ya je dropping din Noor a gidan Aunty Murja, tasan kila

n ya ma dawo ya tafi part dinsa don tun la'asar ya fita da Noor, she is so bored and tired of staying in Hajja's part, dan parlon da take fita ta zauna wani lokacin ma ta dena fita yanxu saboda bata son issue da Hadiyah, Allah ma ya sani ta gaji da bangare

n nan amma bata san yanda zata yi ba, bata san wa zata gaya ma haka ba, mai aikin Hajja ce tayi sallama bakin kofar dakin, ta amsa mata sallaman, matar ta shigo cikin ladabi tace "Ranki shi dade kin yi bakuwa tana nan parlor tana jiran ki" Khaleesat tayi s

hiru tana tunanin wace bakuwa tayi ita kuwa, wa ta sani a Bauchi da har za a zo wajenta, a hankali ta sauka daga kan gadon ta dau veil dinta ta fita daga dakin Mai aikin ta kullo kofar sannan ta bi bayanta, tana shigowa parlon Hajja ta dinga kallon Safiyya

h da mamaki don ko daxu sun yi chatting kuma bata ce mata tana hanya ba, Hajja na zaune parlon sai Hadiyah dake kwance kan 3 sitter ta wani murtuke fuska tunda Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta karaso tana murmushi ta zauna a kan Carpet tace "Sophie" Safiyya

h dai sai murmushi kawal take tana sinne kai saboda Hajja dake parion, ta kalli Khaleesat tace "Tashi ki zauna an kujera Jiddah" Khaleesat ta sauke idonta ta mike a hankali ta koma saman kujera ta zauna, Hadivah ta wani kalli Haiia iin tace KhaleesatHadiya

h ta wani kalli Hajja jin tace Khaleesat ta koma kan kujera, Hajja tace "Kawarki ce wannan kenan Khaleesat ta gyada kai tace "Eh kawata ce Hajja ta kalli Safiyyah sai kuma ta kalli Khaleesat ta sake kallon Safiyyah tace "Maa sha Allah, er baka da ita kuwa

kyakkyawa...." Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tana kallon Sophie, Safiyyah dal sinne kai kawai take tana murmushi, Hajja tace "To bara Yakumbo ta shigo sai ta raka ki can bangaren mijin naki tun da kin ji sauki yanxu" Khaleesat taji dadin hakan so

sai a ranta amma bata dago kanta ba, nan ta fara addu'an Allah ya sa Yakumbo ta shigo da wuri su yi su bar bangaren ita da Sophie, Masu aikin part din Hajja suka kawo ma Safiyyah fruits, Hajja ta mike ta koma second parlor dinta ta bar masu wannan parion,

sai a sannan Hadiyah ta ja wani dogon tsaki tace "Aikin banza kiyi ta mana kwashen kwashen mutanen da bai kamata su shigo gidan nan ba, ko da yake kema by mistake kika shigo gidan ai" Ko kallonta Khaleesat bata yi ba, haka Safiyyah da ta maida dubanta kan

Khaleesat tace "Kawata Yarima ne fa ya aika mota aka dauko ni tun daga Gombe" Khaleesat tace "Haba? Ai kam bai gaya min ba" Safiyyah na murmushi toce "Wallahi kuwa, da uncle dina ne zai yi drop dina sai ga mota an aiko daga gidan nan, bayan mun iso can ban

garenki fa na tafi ban san kina nan ba, da naga ba kowa a can zansan kina nan ba, da naga ba kowa a can zan tafi part din Mami muka hadu da Jay a hanya shi ne ya rakoni har nan muna hira wallahi...." Khaleesat tace "Ayya ai Mami tana Gombe Safiyyah tace "H

aka yace min shi ma, har na amshi numberta ma a wajensa nace zan kirata in gaisheta, da nasan tana Gombe al da na je har inda take" Mikewa Hadiyah tayi tana huci tace "Wallahi Jawwad ya fi karfin ya tsaya hira da ke har ya baki number Mami, makaryaciyar ba

nza kawai, ke a wa har zai tsaya dogon magana dake Sai a sannan Safiyyah ta kalli Hadiyah, sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Wai wacece wannan ne kawata? Ni fa duka nake idan mutum yace zai kawo min iskanci kema kin sani, kar in doki yarinya ace min don me

a gidan nan Hadiyah ta mike tsaye a fusaçe tace "Kan bala'i, ni zaki duka?? To idan baki dokeni ba baki haifu ba, ki taso ki dokeni in kin isa, a cikin masarautar mu zaki dokeni saboda kinyi hauka? Ai ko da sai kin yi life imprisonment kuma babu uban da y

a isa ya fito dake wallahi" Safiyyah ta bude baki tana kallonta, can tace "To naga kawata ma da ta doke ki ba ayi komal ba a gidan, ko dai ba ita kika ma duka wancan ranan ba Khaleesat?" Hadiyah tayi wani kukan kura ta finciko Safiyyah tana cewa "In baki d

okeni ba baki haifu cikin uwarki da u ba, don Allah ki dokeni ki ga abinda zai laru yau a gidan nan, daga ke har kawar taki sai kun yi life imprisonment wallahi" Murmushi kawal Khaleesat tavi iin abinda Hadivah ke

take ba tana kallonta, Safiyyah ta wani y

atsine fuska tace "Kwana biyu fa kawai zan yi a nan, kai baka san abinda zaka ce ma Daddy ba...." Katse wayar tayi ta mayar cikin jaka tana cewa *Since he covered up for me all through my stay in Gombe wannan ma ai zai iya, don dai karin kwana biyu" Yakumb

o ta fito parlon bayan ta gama gyara ma Safiyyah Bedroom, tana kallon Khaleesat tace "To Gimbiya bari inje a taho da abinci kafin a kira Magariba" Khaleesat ta gyada mata kai, tana son tambayarta ko Ajay na part din amma ta kasa har Yakumbo ta fita daga pa

rlon, Safiyyah ta mike tace "Ni dai bara in shiga ciki inyi wanka in canza kaya, wani dakin aka gyara min a dakunan?" Mikewa Khaleesat tayi Safiyyah ta bi bayanta zuwa dakin da aka gyara mata, Khaleesat taga ba dakin da boxes dinta ke ciki ba Yakumbo ta gy

ara ma Safiyyah, instead daya dakin dake kusa da shi ta gyara mata, Safiyyah na shiga dakin ta cire kaya ta shiga bandaki har sannan tana bakin cikin abinda Khaleesat tace mata akan Ya Musty, Khaleesat ta fita daga dakin ta nufi parlon Ajay, bude kofar par

lon tayi gently ta shiga ciki tana kallon bakin kofar parlon ko zata ga indoor slippers dinsa, nan ta gansu a bakin kofa alamar baya nan, tana taeva a hankali ta karasa bedroom dinsa ta kofar a hankali tana leka ciki, it was extremely neat as usual ga wani

daddaden kamshi dake tashi, littafin da ta gani kan gado ta karasa ta tashi, littafin da ta gani kan gado ta karasa ta dauka tana kallon title din kamar haka "The 5 love languages" tana ta kallon book din sai kuma ta juya ta koma parlonsa ta zauna still h

olding the book.... Bayan magrib Yakumbo tayi sallama bakin kofar parlon, Khaleesat ta mike daga kan darduman da take zaune ta tafi ta bude kofar Yakumbo tace "Ranki shi dade ga abinci an ajiye a parlor...." Khaleesat tace "Ohk, dama bai dawo ba?" Yakumbo

tace "Eh bal dawo ba ranki shi dade" Khaleesat tace "Ohk" Yakumbo tace "A hada maki ruwan dumi a bandaki yanxu ko Gimbiya?" Khaleesat tace "To Mama" Daga haka ta juya ta koma parlon Yakumbo ta bi bayanta sannan ta nufi hanyar bandakin dake parlon ta bude t

a shiga, da farko Mami ce ta dinga hada mata ruwan dumin da take seat bath, tayi mata haka for 3 days sannan Yakumbo ta ci gaba da yin hakan, kullum sai Yakumbo ta hada mata ruwan dumi sau biyu a rana, bayan wani lokaci Yakumbo ta fito tace Zaki iya shiga

Gimbiya" Mikewa Khaleesat tayi ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye sannan ta dau littafin da ta dauko al dakinsa ta shiga bandakin da shi, ta fi minti sha biyar zaune cikin bath tub din da Yakumbo ta tara mata ruwan dumi a ciki, duk hankalin kan li

ttafin hannunta tana duba content c bude kofar bandakin aka yi ta daga kai don yakumbo sai ta fara knocking ko da zata shigo balle tunda ta samu lafiya Yakumbo ta dena

balle tunda ta samu lafiya Yakumbo ta dena tsare ta a bandaki, ta zaro ido tana kallonsa

with shock har sai da book din hannunta ya fada cikin ruwan ta cire da sauri ta ajiye tace "Meye haka? don girman Allah kayi hakuri ka fita sosai ta tsorata ganinsa a bandakin, Nannade long sleeve din shirt dinsa ya fara yi yana kallonta, tayi saurin jawo

Shower gel da Yakumbo ta ajiye mata ta tsiyaya kusan rabi a tub din tana kadasa a ruwan don yayi kumfa ta yanda bazai ga jikinta ba, babu abinda ya dawo memory dinta sai daren da yayi disvirgin dinta and the pain and everything came back fresh in her brai

n taji hawaye sun kawo idonta zuciyarta na wani irin bugawa, ya karasa har gaban Bath tub din ya durkusa yana kallonta a hankali kamar me rada yace "Jeeddah" ta fashe masa da kuka har sannan bata fasa motsa ruwan tub din da hannunta ba duk da yayi kumfa so

sai, hannu taga ya kai yana laluban Bath plug din ya cire, ta fara kokarin mayarwa muryarta na rawa tace "Nooo, don Allah ka bari piss kayi hakuri tuni ruwan ya fara raguwa don sai da ya cire plug din, ya rage sai Sud din bathtub din dake covering din nake

d skin dinta, taga ya zame shower cap dinta sannan ya bude shower ruwan dumi ya fara sauka jikinta, ka take masa sosai tace "Don Allah kayi haku fita pls ina rokon ka, wallahi bana so" Kallon naked skin dinta kawai yake yi bayan ruwan shower din ya wanke d

uk Sud din jikin nata,

HALYSAAH

shower din ya wanke duk Sud din jikin nata, bal taba ganinta cikin haske a haka ba, sai dai cikin duhu ko dim light, and he couldn't stop staring at her beautiful body, every part of her body is breathtaking, ganin da gas

ke ta tsorata ga kukan da take yi sosai, ya kwantar da murya yana gyara mata dogon gashinta yace "Ba abinda zan maki Jeeddah, I just want to help...." Cikin kuka tace "Bana so, kawai ka fita pisss" a hankali yace "Ohk" Mikewa yayi ya nufi kofa yana jan kaf

a ya fita daga bandakin, da sauri ta karasa dauraye jikinta ta fito daga bath tub din jikinta na rawa ta dau towel ta daura ko bin ta kan littafin nasa bata yi ba ta fice daga bandakin, hijab dinta ta saka a parlor ta maza ta fita zuwa Bedroom dinta zuciya

rta na bugawa har lokacin. Bayan Khaleesat tayi sallan asuba tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba sannan ta koma bacci, wajen karfe bakwai saura taji ana shafa gashinta a hankali

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login