Showing 297001 words to 300000 words out of 641791 words

Chapter 100 - HALYSAAH COMPLETE

rarrasheta kamar yarda ta saba ba. Duk da zuciyarta tana bu

gu haka ta mayar da idanunta kan T.V a zahirance kallon take amma a ba’dinance kukan Ayra ne yake tsaya mata a zuciya. Ta da’de tana kukan kafin Amman ta saki ajiyar zuciya ta ‘dago kanta. Idanunta cikin nata ta ce “Saurareni Ayra, idan kina son ganin walw

alata ya zama dole wannan karan ki yi ya’ki da zuciyarka ki amincewa auren nan, idan ba haka ba kin bar ganin walwala ta. A kullu yau min ina gaya miki ba duka maza ba ne halinsu ‘daya akwai wa’danda halinsu ya Sha banban da na mahaifinki yanzu yayyenki ba

duk sun yi auren ba, duk da ta ki k’addarar ta fi ta su girma, kada ki manta ni kaina idan na tuna lamarinki abin yana min ciwo wani lokacin kwana nake ban yi barci ba saboda tsananin b’acin rai kuma ma ba wannan ba, ki tuna wani abu ‘daya mana yau ace na

mutu na barki ina za ki kama? D’an uwana ‘daya tak da nake da shi kina ganin dai shekaru ashirin ba mu ji labarinsa ba, aurenki fa shine abinda ya fi cancanta..” Hawaye take idanunta ba k’akkautawa ita Kanta Amman danne zuciyarta take bata bayyana nata ku

kan ba, amma wanda take yi a zuciyarta ya fi na Ayran yawa ya fi shi kuma ciwo. Ayran da sauri ta mik’e ta shige wani k’aramin falo da yake k’asa. Kuka take sosai tana tunanin ina ma zata iya da ta amincewa aurennan tunda yanzu ta lura burin Amma gaba ‘day

a ya tattara ga son aurar da ita, sai dai ina har a lokaci zuciyarta bata karkata da neman rushewar wancan adawar da takewa aure ba, ba zata iya ba ba zata iya ha’da makwanci da namiji ba…. Ba zata iya bawa namiji lokacinta ba balle ta masa girki ko ta nun

a masa wata kulawa Menene Mafita? Shine kawai abinda take tunani ta runtse idanunta kawai tana hango wata mafita da take tunanin ita ce zata tserar da ita daga wannan auren ba tare da kowa ya zargeta ko ya k’alubalanceta ba…. Ta dinga sakin ajiyar zuciya t

ana jin cunkoson b’acin ran da zuciyarta ta yi tana warwarewa hankalinta ya kwanta ta mik’e tana ka’de jikinta….

________________

Magriba sakaliya ya shiga gidan nasa. Alh.Sulaiman turaki ya yi parking a bakin harabar gidansa. Kana ganinsa ka ga usul

in fulani kuma ingarman namiji mai tsayi da fa’di fari tas da shi, farin nasa har wani ratsawa yake yellow. Ba walwala a fuskarsa ko ka’dan don bai kasance daga cikin mutane masu walwala ba. Ya dinga amsawa masu gadinsa sannu da zuwan da suke masa fuska a

ha’de.

Ta k’ofar baya ya shiga gidan nasa, k’ofar da direct zata sada shi da stair case ‘din da zai hau zuwa part ‘dinsa.

Ta ga shigowar tasa ta ji kuma takunsa don haka ta mik’e tsam ta sake bulbulawa kanta turare sannan ta bi bayansa, ta cikin sashen d

a take da zai sadata itama da stair case ‘din nasa. Ta yi kyau sosai cikin shadda light brown da ta sha ‘dinkin y’an senegal, jelar gashinta sai reto take a gadon bayanta. Farin ciki fal fuskarta da zata yi arba da shi a yau bayan shafewar wasu watanni tun

da ya dawo wajen amaryarsa bai sake waiwayarsu ba don haka ta shirya taran sa tana son kuma ta nuna masa tana nan a Hameedarta mai tsananin kishi wanda dama dalilin hakan ya sa ya barta a can k’asarsu ya kuma hanata zuwa Nigeria. Sai yanzu da ya tabbatar g

irma yazo mata hankali ya samu ya san da wuya ta zo ta aiwatar da haukan kishi zata ji kunyar hakan. Tsawon shekaru sha biyar da aurensa da amaryarsa tun a lokacin ta so dawowa mahaifarta cikin dangin babanta amma S.Turaki ya kafe sam bai amince da hakan b

a kuma ko hutu bai amince ta zo ta yi ba. Yanzun ma an kai ruwa rana kafin ya amince da zuwan nata, kuma zuciyarsa tana d’ar-d’ar sai dai ko a waya bai nuna mata ba, dalilin yayan Babanta ne ya sanar da shi ya kamata ta zo ta ga dangi yaranta kuma su san d

angin kakansu tunda Amin da y’ar uwarsa ne kawai suka tab’a zuwa. A can ya ha’du da ita wajen business ‘d’insa soyayya mai k’arfin gaske ta shiga tsakaninsu, duk da ra’ayinsu ya sha banban shi mai kafaffiyar zuciya ne yayin da ita kuma ta kasance mai sassa

uk’an hali. Ko a wajen tarbiyyar yara sai da suka sha artabu don sosai ya nuna mata ya fi son yaransa su tashi da harshen hausa a bakinsu ba harshen su na labanawa ba, don dole ta amince take musu magana da duka harsunan biyu shi yasa suka iya hausa kamar

me? Tunda itama bahaushiyar ce mahaifinta haifaffen cikin garin kano ne kuma asalin bahaushe, mahaifiyarta ce kawai ta kasance daga jinsin larabawan labanon. Tun lokaci da ta rigime da son zuwa Nigeria shi kuma ya tattara ya mata yaji tsawon wata bakwai sa

i da ya ga abin nata ba na k’are bane sannan ya ce su tattara su taho ya gama musu gini.

A hankali ta tura k’ofar idanunsu suka gamayya da juna. Fuskarsa ta ‘dan saki ka’dan yayin da tata ta washe da fara’a gaba ‘daya ta dinga jifansa da k’awataccen murm

ushi.

Hannu kawai ya mik’a ya janyota kusa da shi ba tare da ya yi magana ba. Ta shige jikinsa sosai tana k’ok’arin kawar da kishin da yake k’asan ranta. Sosai ta shiga nuna masa yarda ta yi kewarsa tana gaya masa yayinda shi kuma ya shiga sarrafata ba bak

in magana a tunaninsa hakan ne kawai Zai nuna mata ya yi kewarta ba ‘dan ka’dan ba…..

Zazzafan coffee ‘din ta shiga jujjuya masa tana k’ok’arin mik’a masa murya a sauk’ak’e ta ce “Na samarwa Turaki mata…” gaba ‘daya cup ‘din ya sub’uce a hannunsa yana d

ubanta ya ce “Ba dani ba, na gama yiwa Turaki aure yana zubar min da mutunci ta hanyar sakin yaran mutane..”

HALYSAAH

PAGE 9

2

Nenne ta jawo handbag din Khaleesat bayan ta ajiye maficin da take yi ma Khaleesat din fiffita da shi ta bude jakar ta ciro w

ayar sannan ta fara tashinta tana cewa "Ga wayarki na ta ruri ki duba ko kira ne, kila ma Ahamad din ne" Khaleesat ta juya ma Nenne baya taki bude idonta kuma taki cewa komai don wani azababben ciwo kanta ke mata, Aunty Murja ce ta shigo dakin tace "Nenne

ai da kin bar ta tayi baccin tunda bata jin dadi, kuma har da gajiyan hanya ma" Nenne tace "Ƙudajen nan naki ai ba bari za su yi tayi baccin cikin dadin rai ba, na tambayeki ko kiwon su kike kince A'a, banda ma ina korasu da mafici ai dakin bazai zaunu ba

, ke dai kina da tsaftarki da sai ince kazanta ce ta kawo maki su, ina Parida ta zo ta duba ko kiran waya ne, tun daxu wayar ke ruri" Aunty Farida ce ta shigo dakin Nenne tayi maza ta mika mata wayar tace "Gashi yana ruri duba ko kira ne" Aunty Farida ta a

mshi wayar taga Jay ke kira, Aunty Farida tace "Jawwad ke kiranta" Nenne tace "Waye Jawwal, ko Ahamad din?" Aunty Farida tace "Eh shi ne" Da sauri Nenne tace "To

ɗ

aga mana Parida, tun daxu fa yake ta kira, ki daga ki ce masa bata jin dadi tun da muka sauka

Bauchi, yanxu haka a kwance take, kar ya ga an masa walakanci, maza ki

ɗ

aga don Allah" Aunty Farida tayi murmushi ganin seriousness din Nenne, fita tayi daga dakin ta daga kiran, bayan kusan minti biyu ta dawo dakin tana kallon Aunty Murja tace "Wai gashi

ki masa kwatancen nan din Aunty Murja" Aunty Murja ta amshi wayar, Nenne dai sai murmushi take har Aunty Murja ta gama yi masa kwatancen ta mika ma Aunty Farida wayar, bayan Aunty Farida ta katse wayar Nenne tace "To kun ga ai gwara haka, ai shi ma

ɗ

an Ba

uchi ne, yaro me kirki ga hankali da nutsuwa" Aunty Murja ta mike tace "Allah sarki, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi, to yanxu Nenne a dora tuwo ko kuma shinkafar za a sake maku naga yamma ya gabato" Nenne ta kalli Aunty Farida tace "Gwara ki hura

iccen Parida tayi mana girkin ke kuma ki ji da yaranki kawai..." Nenne bata rufe baki ba sai ga yarinyar Aunty Murja me Cerebral palsy tana rarrafowa zata shigo dakin, Nenne tayi wani ihu tana yarfa mata mafici da sauri tana cewa "Tafi, tafi ki je can kofa

r gida, fitaa...." Aunty Farida ta

ɓ

ata rai tana kallon Nenne tace "Haba Nenne meye haka?" Nenne ta wani kalleta tace "Ha

ɓ

a Nenne? Aljanu fa suka maida mata halittar ta haka tana dalalar da yawu, in bance ta fita ba me zance? Me zata shigo tayi cikinmu ida

n ba neman magana ba, ai laifin Murjan ne da take barin ta a sake, nace ta dinga daureta ko jikin bishiyar tsakar gidan nan nasu ne taki ji, ai ba a bari su shigo cikin mutane babu kyau haka, sa'ar su Islam ne fa amma ku dubeta kamar er shekara shidda in b

a aljanu ba wa za su yi haka, su suka shafeta a ranan da aka haifeta" Ita dai Aunty Murja tayi shiru bata ce komai ba tana

ɗ

an murmushi, Aunty Farida ta mike ta

ɗ

aga yarinyar suka bar wajen, duk da ciwon kai da ya saka Khaleesat a gaba ga wani tashi da zuc

iyarta yake tun bayan da Nenne ta tilastata ta sha fura da Nonon da aka kawo masu daxu amma haka nan ta daure ta mike zaune tana ma Nenne wani kallo tace "To wai Nenne ita ba mutum bace kamar kowa? Wa ye yace maki aljanu ne suka shafeta? Tunda ba karatu ki

ka yi ba ai baza ki san meye matsalar ta ba, ita da gidansu kuma ki dinga korarta bayan wajen Mamarta take son zuwa" Nenne tace "Ni bazan biye ki ba kiji da ciwon kan da ya saka ki gaba, mu zamaninmu yaushe za a bar irin wannan yarinya ta shigo cikin mutan

e, ai boye irinsu ake, ko a kai su wajen mai magani a bar su can, nono uwar zata bata da zata wani rarrafo ta biyo ta" Aunty Murja dake ta murmushi har sannan ta mike tace "Bari in hura abun girkin Nenne" Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat tace "Walla

hi ki dena haka Nenne babu kyau, ita ma mutum ce kamar kowa kawai lalura Allah ya jarabceta da shi tun daga wajen haihuwa, yanxu duk an dena kalan wannan tunanin naku na mutanen da, kai ya waye, yara masu lalura haka jan su ake a jiki suna bukatar kulawa d

a soyayya ba tsangwama ba, Aunty Murjan ma ai bazata ji dadi yanda kike ma yarinyar ba" A fusace Nenne tace "Zamaninmu daban naku daban, mu dai mun san 'yan ruwa ake haifowa haka ko kuma wa enda aljanu suka shafa tun a cikin uwarsu" Komawa Khaleesat tayi t

a kwanta don bata da strength din ci gaba da magana ga tashi da zuciyarta ke yi.... Karfe biyar da minti arba'in Khaleesat ta mike zaune da kyar ta dalilin tashinta da Nenne ke yi babu kakkautawa gashi ta samu bacci ya dauketa, Nenne na mika mata wayar da

sauri tace "Maza daga kiran, kilan shi ne ya iso" Khaleesat ta amshi wayar taga Housemate dinta ke kiranta, komawa tayi ta kwanta tayi picking call din yace "Halysaah" Da kyar tace "Uhm" Yace "Are you still sleeping?" A hankali tace "Na tashi" Yace "How ar

e you feeling now?" Tace "Uhm" Yace "Ina Aunt dinki da tayi mana kwatance daxu?" Khaleesat ta mika ma Nenne wayar tace "Aunty Murja zai yi magana da" Da sauri Nenne ta mike ta fita daga dakin da wayar tana cewa "To bara a kai mata, suna can sun daura mana

sanwa da Parida" Bayan minti goma yaron Kishiyar Aunty Murja ya dawo tare da su Jay bayan yaje ya taro su, daurewa Khaleesat tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka don Nenne takura ta tayi wai gasu can kofar gida ta tashi taje, tana fita waje taga Ride me

suna ride da suka zo da shi, tana tafiya a hankali ta karasa har kusa da motar, Jay ya sauke glass din motar yana zaune front seat yana kallonta, ta kallesa shi da Ajay sannan ta jingina jikin motar don har ta gaji

ɗ

an tafiyar nan da tayi, ya bude motar y

a sauka yana kallonta yace "Halysaah" Ta

ɗ

aga idanuwanta ta kallesa, yace "Me yasa kike damun kanki haka?" Ɗan murmushi tayi tace "Nace maka kaina ke min ciwo, kuma na gaji" Yace "Amma ai da wuri ku ka iso Bauchi" Ita dai ta sauke idonta tayi shiru bata ce

komai ba, yace "Kin ci abinci?" Gyada masa kai tayi duk da bata iya ta ci komai ba sai fura kadan daxu, yace "Ohk bari mu duba pharmacy so I can get you some drugs, ki koma ciki, idan mun dawo zan kira ki...." Ta gyada masa kai ta fara tafiya a hankali ta

shiga gidansu Aunty Murja, Jay ya koma cikin motar yana kallon Ajay yace "She is not feeling fine, mu

ɗ

an duba ko za mu samu pharmacy a nan in siya mata magani" Ajay dai bai ce masa komai ba ya tada motar ya fara reverse. Bayan minti arba'in suka dawo Jay

ya sake kiranta ta fito, Shopping yayi mata na abubuwan da zata bukata irin pack din bottle water, drinks, costly cookies,, Sae gwangwanin powdered milk da Milo with sugar, da carton din Indomie, bread ma manya uku ya siya da Butter, a gefe kuma ga kwai,

duk dai wani abu da zai sa ta zama comfortable a gidan duk da bai san kwanaki nawa zasu yi ba, sannan ya siya ne not for only her to use, ya kuma siya masu abinci a restaurant pack biyar da gasassun kaji, Ita dai Khaleesat na jingine jikin motar ta ma rasa

abinda zata ce har yara suka gama shiga gidan da kayayyakin, ya mika mata ledan drugs din yace "You check the prescription idan kin ci abinci sai ki sha" Cikin sanyin murya tace "Thank you so much, Allah ya saka da alkhairi" Ya wani kalleta, ita ma dai ka

llonsa kawai take

ɗ

an tsayuwar nan da tayi har ta gaji, yayi kasa da murya yace "Pls Halysaah in sha Allah komai zai wuce ki dena saka ma kanki damuwa, i am assuring you babu abinda ya isa ya maki don ya gama samun nasara kuma a kanki, ki kwantar da hankal

in ki and trust my words" Ɗan murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Go get some rest, ki ce da Kaka in sha Allah za mu dawo gobe yanxu Magrib ya gabato shi yasa baza mu shiga mu gaisheta ba, from our place to here is almost 45 minutes ride" Khaleesat

ta

ɗ

an bude ido cikin sanyin murya tace "Da nisa ashe" Ya

ɗ

an yi murmushi yace "May be mu zo around 11 in the morning gobe" Tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen, in kin ji zaki Iya magana anjima ki kirani, bana son in kira kina bacci kaka ta tashe ki" Ta

na murmushi ta gyada masa kai sannan ta

ɗ

aga masa hannu alamar Bye bye ta juya ta wuce cikin gidan, Jay ya shiga mota yana kallon Ajay yace "Common ya jiki baza ka iya yi mata ba alhalin idan ita ce sai ta maka ya jiki ko baza ka amsa ba" Ajay ya kallesa y

ace "Dama bata da lafiya ne?" Banza Jay yayi masa don shi ne ma ya hado mata maganin a Pharmacy shi kuma ya shiga yayi shopping wanda duk da Atm card din Ajay din suka yi duk siyayyar don shi ya mance nasa a gida amma yake masa tambayar rainin wayo yanxu..

... Washegari karfe takwas da rabi Jay ya kira wayar Khaleesat, Nenne dake ta tambayar wanene bayan Aunty Farida ta sanar mata Jay ne tace "Ɗaga ki bani shi" Aunty Farida tace "Ki ce masa me, bari dai in daga tunda bacci take" A fusace Nenne tace "Ki bani

nace, ke komai sai kin nuna iyawa" Aunty Farida ta kyabe baki tayi picking call din ta mika mata, Nenne ta doka sallama tace "Ina kwana Ahamad" Jay na jin muryarta ya gaisheta cikin ladabi, ta amsa tace "Wallahi in gaya maka jiya dai ba mu yi baccin kirki

ba, jikin nata ba dadi, dama tana dadewa ita bata yi ciwo ba amma in ta tashi yi ba kyau, da ta sha magungunan kamar zazzabin ya sauka sai kuma ya dawo da karfinsa, dama jiya muna mota zuwa garin nan sau biyu tayi amai, to daren jiya ma tayi sau biyu, gash

i taki cin komai har shayi an ƙada mata ta kasa sha" Jay dake ta sauraronta duk sai yaji a hankalinsa ya tashi, a hankali yace "Toh ina ga za a hada mata da allurai Kaka..." Nenne tace "Atoh, ni na rasa kan ciwon nata..." Yace "Yanxu za mu taho in sha Alla

h" Nenne tace "Toh Allah ya kawo ka lafiya Ahamad" Bayan Nenne taji shiru alamar ya katse wayar ta ajiye tana kallon Aunty Murja tace "Lafiyan Allah take da, daga sanda iyayen tsinannen yaron can Awdul suka turo barayin gwamnati da daddare wajen Ali shiken

an ta birkice, ba komai ne ya ja mata wannan ciwo ba sai damuwa, ta saka ma ranta damuwar abun sosai ba kadan ba, ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login