Showing 438001 words to 441000 words out of 641791 words

Chapter 147 - HALYSAAH COMPLETE

a baya, wannan shi ne best moment din da aikinsu zai yi tasiri kan Jay. Har kusan karfe biyar Khaleesat suna bangaren Mami

, Khaleesat ta amshi girkin da Mai aikinta ta zo zata yi mata a kitchen, sai da Mami ta fito ta ga tana girkin Mai aikinta kuma na tsaye kitchen din tana taimaka mata da miko abubuwa, Safiyyah kuma ta kama parlon da babu ko kwayar datti sai shara take tana

goge goge ga turaren wuta a burner ta kunna, Mami bata iya tace komai ba kawai ta juya ta koma dakinta, Khaleesat ta gama girkin da take ta fito parlor sai ga Ajay ya shigo parlon, suna hada ido sai da taji gabanta ya fadi, ta tura baki ta dauke kai, sai

kuma ta juya ta nufi kitchen, wato sai yanzu yasan zai dawo gidan in ma duka ne da an gama dukanta, shi dai ya bi ta da kallo ya karaso cikin parlon, Safiyyah ta gaishesa ya amsa ya zauna kan kujera, after some minutes ya mike ya nufi kitchen din Mami, tsa

ye ya ganta ta jingina da Island din kitchen din fuskarta a daure, yana kallonta calmly yace "Ke ina kika ga ma karfin dukanta, ko dai ke aka ma duka kika ce min kin mata duka?" Ta wani juya ta kallesa tace "To ai sai ka tambayi Sophie ka ji" Ya rungume ha

nnunsa bayan ya jingina da kofar kitchen din yana kallonta a hankali yace "To rike maki ita aka yi kika fara dukan nata?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ko ba rike min ita ba, wallahi i beat her blue black today, ask Safiyyah" Yace "Shi ne n

ake son sanin ta yanda aka fara dukan, halan ta baya kika yi taking it unaware?" Wani irin kallo tayi masa sai kuma ta karasa gabansa tace "Kaga muna parlor ni da Sophie sai gata ta shigo, ta fara zagin Sophie, shi ne Sophie tace zata mata duka, ni kuma sa

i na fara ba Sophie hakuri nace ta zo mu wuce daki, kawai shine fa ta wanka min mari, ina ganin haka na rama, sannan na fincikota haka na fara dukanta...." Ajay ya bude ido sosai ganin yanda ta finciko rigarsa wai tana gwada masa yanda tayi ma Hadiyah, ta

kyalkyale da dariya zata koma baya ya fixgota ta fado jikinsa, ta boye fuskarta a kirjinsa kamar zata yi kuka tace "Nuna maka yanda nayi fa nake yi...." Muryar Mami da yaji ya sa yayi saurin saketa ta koma baya da sauri ita ma, shi kuma ya juya ya fita dag

a kitchen din. Wajen karfe takwas da rabi na dare Khaleesat na biye da Mami da ta kai ta har parlon Mai martaba, sai dai Mami bata shiga parlon ba tayi juyawanta don kawai kawo Khaleesat tayi kamar yanda Mai martaba ya umarceta da tayi, ita dai Khaleesat k

anta na kasa har ta karasa cikin babban parlon ta zauna kan Carpet, Sarki ne kadai zaune parlon nasa sai Hadiyah dake zaune daga gefe idonta ya kumbura don kuka, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaishesa, Sarki ya amsa, bayan wani

ɗ

an lokaci yace "Jiddah me

nene ya hadaku da Hadiyah?" Khaleesat bata dago kanta ba a hankali tace "Bangarena ta zo...." Sarki ya dakatar da ita yace "Bangaren ki?" Khaleesat tace "Eh" Ya kalli Hadiyah yace "Kika ce a hanya ku ka hadu?" Hadiyah tace "Wallahi wallahi karya take ur hi

ghness, a hanya muka hadu da ita zan je gaida Mami, ni ban je bangarenta ba, me zai kai ni bangarenta that is very far?? wallahi karya take min Abbanmu" Sarki yayi shiru duk yana kallonsu, Khaleesat tsabar yanda ta girgiza da rantsuwar da Hadiyah take kant

a tsaye ta dinga kallonta babu ko kiftawar kirki, Sarki ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Hadiyah yace "Yanxu waye shaidan ki?" Hadiyah tace "Iklima, tare da ita muke tafiya a lokacin" Ya kalli Khaleesat, calmly yace "Jiddah wa zai shede ki akan cewar bangar

enki taje ta same ki?" Khaleesat ta sauke idonta ta ma rasa abinda zata ce gashi bata son involving Sophie, don ko ta sakota nan ma ƙaryatata kawai Hadiyah zata yi, can ta girgiza kai a hankali tace "Bani da shaida ranka shi dade, amma wallahi ita ce ta zo

har inda nake ta sameni...." Sarki yayi shiru, bayan kusan minti daya yace "Zan sa a duba min Cctv din parlon, ta nan ne za a gane me gaskiya da kuma me karyan a cikinku" Hadiyah ta daga kai da sauri tana kallon sarki gabanta na faduwa don ita ma mance da

wani abu wai shi Cctv Camera, Sarki yasan babu Cctv Camera a

ɓ

angaren Ajay tunda ba kowa ke zuwa

ɓ

angarensa da ya wuce shi ba, but yasan ta haka kadai ne zai gano me gaskiyar cikinsu cikin ruwan sanyi, Khaleesat became confused too, to amma ranan har Wali

d ke ce mata babu Cctv Camera a parlon, ko dai daga baya ne Ajay ya saka, duk Sarki na kula da reaction dinsu, ita Hadiyah sai mutsu mutsu take ta ma kasa zama waje daya tunda Sarki ya ambaci Cctv, ita kuma Khaleesat ha confusion karara kwance a fuskarta,

duk sai ya ma rasa gane me gaskiyan cikinsu, Cikin nutsuwa yace "Bayan na sa an dubo min Cctv din duk wanda na kama da min karya will face the music, don ba a min karya, ku tashi ku je...." Hadiyah ta fashe da kuka taki tashi, kamar yanda Khaleesat ma ta k

asa tashi a inda take zaune, cikin kuka Hadiyah tace "Ur highness wallahi da naje parlonta ni ba da niyyar fada naje ba kawai sharrin shaidan ne, shi ne ita kuma ta min duka ta zazzageni, a gafarceni ranka shi dade" Sarki dake ta kallon Hadiyah yace "Ohk a

she ke kika je kika sameta, kin ga kenan bata da laifi ke da kika je kika sameta har parlonta kece me laifi and that serves you right, sannan saboda ke baki tsoron Allah kike rantsuwar baki je bangarenta ba, lamarin naki ya kai haka Hadiyah? To daga yau na

sake ganin kafarki a hanyar sashinta sai nayi mugun sa

ɓ

a maki, mutuniyar banza kawai, maza bude baki ki bata hakuri yanxun nan" Hadiyah dake kuka ta kalli Khaleesat zuciyarta na tafarfasa tace "Kiyi hakuri" Khaleesat ta sauke idonta tace "Kema kiyi hakuri

" Sarki na kallon Hadiyah yace "Tashi ki ban waje" Mikewa tayi tana kuka ta fita daga parlon.

HALYSAAH

Cikin sanyin murya Khaleesat ta fara ba ma sarki hakuri yace "It's okay, tashi ki tafi Jiddah ae baki da laifi, Fulani Aseeya ta gaya min ita ta same

ki parlon ki ta mare ki" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, after few seconds tana wasa da yatsunta a hankali tace "Kuma dama ina son zan maka magana ranka shi dade" Sarki na kallonta yace "Ohk, ina sauraronki Jiddah?" A hankali tace "Dama It's about Ya J

unaid, don Allah ranka shi dade kayi hakuri ka yafe masa...." Mai martaba ya katse ta yace "It's okay, it's fine... ki tashi ki je kawai, Allah ya maki albarka" Khaleesat bata sake cewa komai ba, can kuma tayi masa sallama ta mike a sanyaye ta fita daga pa

rlon nasa. Kuka Hadiyah ta dinga yi a parlon kamar ranta zai fita, ita ba ma dukan da Khaleesat tayi mata bane ya tsaya mata, maganganun da ta gaggaya mata ne suka makale mata a kirji, tsabar bakin ciki har yanxu ko abinci ta kasa ci, Jay din ma taki saura

ronsa taki barin part din Hajiya A'isha, all this pain not being enough shi ne sarki zai sa ta bata hakuri, ga duka ga zagi da gori sannan ga bada hakuri duk ita kadai, ji tayi gaba daya duniyar yayi mata zafi bata san me za ayi ma Khaleesat ta samu saukin

ƙunar da zuciyarta yake mata ba, Hajiya A'isha da Ummi da Kilishi sai Hajiya Habibah dake parlon duk takaici ya hanasu magana dama tun da Sarki yace daga Hadiyah sai Khaleesat yake bukata a parlornsa suka san an kulla wani babban makircin kuma ba kowa zai

kulla wannan makircin ba da ya wuce Mami, cikin

ɓ

acin rai Kilishi tace "Ba dai Hajja ta shigo garin nan ba kuma gobe zata shigo masarautar nan in sha Allah, to za kuwa a zabi ko er gidan sarauta ko kuma bare da ba a san cikakken asalinta ba" Hajiya Habiba

h tace "Shikenan kuwa, sai a zabi ko Hadiyah ko matar Junaid, kuma bai kamata mu zuba ma Aseeyah ido haka a gidan nan ba, ban ta

ɓ

a ganin makira me fuska biyu mara tsoron Allah irin ta ba, idan ba makirci ba kin ce baki son yarinya ta auri

ɗ

an ki kika yi ru

wa kika yi tsaki kika ruguza maganar auren, rana daya aka mayar da auren kan Junaid, Amma saboda munafurci da fuska biyu yau kuma ki ce baki da warce zaki dinga goya ma baya a gidan nan da ya wuce ita wannan yarinya saboda kina kishi da kulawar da

ɗ

an ki k

e ba Hadiyah da Soyayyar da yake mata?? Anya matar nan zata gama da duniya lafiya kuwa? To za kuwa ta ga ikon Allah don baza mu zuba mata ido tana yanda taga dama a gidan nan ba, a yanda na kula da take takenta sai ta iya sa Junaid ko kuma ta bi duk hanyar

da zata bi na ganin ya saki matar ta mayar ma

ɗ

an ta tunda er son zuciya ce duk mun sani, ga yarinyar yanxu bata da aiki sai shige mata sun zama kamar tib da taya" Takaici gaba daya ya hana Ummi magana tana ta tunanin irin tuggun da zata shirya ma Mami wa

jen Hajja gobe, Hajiya A'isha na kallon Hadiyah dake rusa kuka tace "Amma ace Mai martaba bai yi la'akari da yanda ta kumbura maki baki ba, ta kwantar maki da jini a ido ga ciwon jikin da ta bar ki da shi zai ce ki bata hakuri?" A fusace Ummi tace "Ai ba d

au hanyar da za ayi shari'ar adalci ba Aunty A'isha, dama tun daga sanda yace baya bukatar mu a parlonsa nasan akwai wani abu da Aseeya ta kulla, amma babu komai zan jira har Hajja ta zo gobe ta tunatar masu matsayin Hadiyah a cikin gidan nan in sun mata,

ita kuma matsiyaciyar Bazawarar can bata daki banza ba wallahi tana kasa tana dabo, zata san ta ta

ɓ

a jinin sarauta sannan jikar gidan nan" Tun bayan da Khaleesat ta fito daga Parlon sarki ta nufi part din Ajay take a tsorace kar ace wani ya biyota sai waig

e waige take kamar mara gaskiya, a haka dai ta isa bangaren Ajay ta shiga parlor ta tarar da shi zaune a parlon, ya

ɗ

aga kai yana kallonta studying her mood at the same time, ta zauna kan kujera tayi shiru, shi dai kallonta kawai yake, can ta mike ta bar p

arlon ta bude kofar dakin Safiyyah ta sameta kwance tana waya, da sauri Safiyyah ta katse wayar ta mike zaune tana kallonta tace "How did it went? Ina nan gabana na ta faduwa kar sarki yace a zo a kirani, har na gaya ma Ajay Gobe da sassafe zan tafi Gombe

wajen Cousin sis dita bata da lafiya...." Khaleesat ta karasa cikin dakin ta zauna gefen gado, nan ta fara fada ma Safiyyah duk yanda aka yi a parlon Mai martaba, Safiyyah ta buda hannuwanta tace "Alhamdulillahi kinga kin doketa kin doki banza wallahi, ku

ma ina me tabbatar maki daga yau zata fara shakkar ki a gidan nan kun goge raini ai kuma, kai amma gaskiya wannan sarki adalin sarki ne, gashi dai kin jibgeta ta baki hakuri" Khaleesat tace "Ni rantsuwar da ta dinga yi ne ma ya tsorata ni fa, ban ta

ɓ

a gani

n wanda ya dage yana rantsuwar karya kamar ta ba" Safiyyah tayi tagumi tace "Allah sarki Yaya Housemate jarabawa ya fada masa, Allah ya hadasa da er iska a matsayin mata, duk ta shanyesa, tun da ya shigo yana querying dinmu akan me aka dokar masa mata jiki

na yayi sanyi na gane lamari ya lalace, uwarsa ce ma abun tausayi, nasan zuwa yanzu tana nan tana da ta sanin kin yarda da aurenki da Jawwad da tayi" Mikewa Khaleesat tayi, tayi ficewarta daga dakin ta shiga parlon Ajay sannan ta karasa bedroom dinsa, baya

n ta fiddo kayan baccinta ta cire hijab din jikinta ta linke sannan ta shiga bandaki, tana fitowa wanka tayi saurin shiryawa don kar ma ya shigo dakin ya sameta a haka, har yanxu bata mance abinda ta ji daren jiya ba, ta saka hijab dinta zata fita sai gash

i ya bude kofar dakin, taki kallonsa zata fita ya rikota yana mata wani kallo yace "So you are waiting to for me to ask you what happened ko?" Ta marairaice tace "To ai baka tambayeni ba" Washegari da safe Khaleesat na kwance dakin dake kusa da wanda Safiy

yah ke ciki tayi nisa cikin tunanin da take, tun karfe sha biyun dare ta gudo dakin ta saka makulli, jin sallaman Yakumbo ta mike ta jawo Hijab dinta a hankali ta saka sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi kofa ta bude kofar dakin, gaisawa suka yi da Yaku

mbo da ta sanar mata an shigo da Breakfast bangaren, Khaleesat tace "Toh Mama mun gode" Yakumbo tayi kasa da kai tace "Kuma don Allah kiyi ta hakuri ranki shi dade watarana sai labari, ki kuma dage da addu'a da neman Allah ya dora ki kan duk makiyanki da m

ahassadan ki na fili da boye" Khaleesat ta gyada kai cikin sanyin murya tace "In sha Allah" Ajay ne ya fito daga parlonsa, ko kallon inda suke bai yi ba ya nufi Main parlor Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Yakumbo ma da ta duka har kasa tana ga

ishesa bai tsaya ba yayi tafiyarsa, juyawa Khaleesat tayi ta koma cikin dakin cikin sanyin jiki ta tafi gefen gado ta zauna, zuwa yanxu ta fara tunanin wanda zata ma magana akan issue dinta, kunyar yi ma Aunty Farida magana take balle kuma Umma, Nenne kam

tasan tana mata magana zata gaya ma su Aunty Farida, hawaye taji ya gangaro fuskarta, she is really getting disturbed with the whole thing now, ta rasa yanda zata yi, can dai ta mike da kyar ta bude kofar dakin ta fita, ta tafi Main parlor bata gansa a par

lon ba, ta juya walking slowly ta tafi parlornsa nan ma baya ciki, ta karasa bedroom dinsa ta bude kofar a hankali ta shiga taga baya nan, to ko dai aiki ya fita, inda makullin motarsa yake ta duba taga babu nan ta gane ya fita kenan. Wajen karfe goma suna

zaune parlor da Safiyyah bayan an shigo an kwashe sauran breakfast din da suka rage, Safiyyah tace "Na ganki duk wani iri yau, ko an sake maki wani maganar ne akan abinda ya faru jiya?" A takaice Khaleesat tace "I am having Headache" Knocking kofar parlon

aka yi duk suka juya da sauri, Khaleesat tace "Waye?" Muryar Yakumbo ta ji, hakan yasa ta mike ta karasa ta bude mata kofar parlon, Yakumbo ta shigo, cikin ladabi tace "Allah ya taimake ki dama Yarima ne yayi kira cewar za ki shirya ke da Kawarki Dreba na

jiran ku, idan kun gama sai in raka ku har haraban gidan zuwa gun motar" Khaleesat tayi shiru da mamaki, can tace "Toh" Yakumbo na fita parlorn Safiyyah tace "To ina kuma za mu je, ni dai jiya kafin ki dawo daga kiran Sarki na ce masa zan je Gombe, ko tas

har mota za a kai ni?" Khaleesat dai bata ce komai ba, ta mike ta nufi Parlon Ajay, wayarta ta dauka tayi dialing numbersa taji ina za a kai su, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa bai daga ba, ajiye wayar kawai tayi ganin har minti goma yayi bai biy

o ta ba, ta fice daga Parlon. Bayan minti talatin sai ga Yakumbo ta dawo bangaren zata yi masu rakiya zuwa gun motar da zai fita da su, Khaleesat na rike da handbag dinta bayan ta shirya cikin daya daga cikin Abayan dake lefenta, Safiyyah sai kallonta take

ganin yanda tayi wani irin kyau na musamman duk da babu kwalliyan da tayi but she look gorgeous kuma Black Abaya din ya wani haskata kamar balarabiya, a haka suka fita daga parlon Yakumbo ta kullo kofar ta saka makulli, ta shiga gaba da sauri tana leading

dinsu, Khaleesat na kallonta tace "Zan fara zuwa bangaren Mami ince mata zamu fita" Yakumbo tace "To ranki shi dade...." Tun da suka shiga parlon Mami ke kallon Khaleesat, bayan ta amsa gaisuwarsu tace "Ina za ku?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Zan raka

Safiyyah zata je Gombe" Mami tace "Amma zata dawo ta nan dai?" Khaleesat ta gyada kai tace "Eh zata dawo" Mami tace "To Allah ya tsare, Allah ya dawo da ita lafiya" A haka suka fita daga

ɓ

angaren Mami da ta bi Khaleesat da kallo, ita dai Safiyyah da biyu

take son guduwa Gombe, na farko tsoron kada ace daga zuwa Masarauta anyi dambe saboda ita, haka kawai sarki yasa Dogarai su zaneta ta shiga uku, na biyu kuma bata san yanda zata yi da Nenne da ta shigo Bauchi tana ta fafutukan nema ma Khaleesat magani ba n

an kuma gashi taga alamar komai ya wakana tsakaninta da Ajay, shi yasa kafin Nenne ta zo palace din take son tayi ta kanta ta gudu zuwa Gombe, suna isa gun motar, Dreba ya bude back seat da sauri yana gaida Khaleesat cikin ladabi, Khaleesat ta amsa gaisuwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login