Showing 111001 words to 114000 words out of 641791 words

Chapter 38 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

171

daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga kamar jira take, yayi kasa da murya yace "C

an you hear me Safiyyah?" Tace "Ina jin ka, plss ba a san inda Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano" Yace "Where are you at now?" Da sauri tace "Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi n

e na zo gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da" Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay yace "I mean are you at home or where?" Cik

in kuka tace "A'a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don't know where she will be now, i am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me" Calmly yac

e "Look, this should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this...." Da sauri Safiyyah tace "Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless marriage" Jay yace "Ohk, he

re is ur frnd speak to her....." Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya

hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Sophie" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Khaleesat, i am so happy you are safe and sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tac

e "Bana kano Sophie" Da mamaki Safiyya tace "To kina ina?" Khaleesat ta daga kai ta kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace "Ina Lagos" Safiyyah tace "Lagos wajen wa? Ko wajen Aunty Farida?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Am

ma Umma bata san kina nan ba" a hankali Khaleesat tace "Bata sani ba" Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Pls kar ki tada hankalinki kinji kawata, i know ur Housemate won't allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da Abdul don b

ai yi deserving din ki ba, i can't imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa" Khalees

at dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya zauna yace "Safiyyah" A sanyaye Safiyyah tace "Na'am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya mata ak

an issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi, har abusing dinta yana yi" Jay dake sauraronta yace "In sha Allah we will try our very best ki taya mu da addu'a" Safiyyah tace "In sha Allah, but how can i be

reaching her?" Yace "Don't you have her aunt's number" Safiyyah tace "Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida" Jay yace "Keep this confidential pls Safiyyah" Safiyyah tace "Trust me Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is

safe" Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci, iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta zauna, sai da ta jira suka gama waya da Saf

iyyah sannan ta kallesa tace "Ina Junaid din ga abincin na zuba maku" Jay yace "Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske" Aunty Farida tace "Ai ko in baku ci ba bazan ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake

nema kuma breakfast kace kawai ku ka yi" Jay dai murmushi kawai yake, can yace "Toh zan ci Aunty" Tace "To ko kai fa, ina Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci" Jay na shafa kansa yace "Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci abincin ba na sani, bai fiye

cin abinci da rana ba" Aunty Farida tace "Ikon Allah to saboda me?" Jay yace "Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi" Aunty Farida tace "Iko sai Allah" Jay na kallon abincin da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace "Zan ci wannan kar mu bata a

bincin Aunty" Aunty Farida tace "Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad" Yace "Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa zan yi ba ma" Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace "Ai shikenan"

Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa

akan titi yace "To ya ku ka yi da Lauyan?" Ajay yace "He said we should meet in kano" Jay ya

ɗ

an kallesa yace "Zuwa gobe kenan?" Ajay yace "Sure, tomorrow in the morning za m

u tafi kano" Jay bai sake cewa komai ba har suka isa gida, yau dai traffic din da

ɗ

an sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace "Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma" Ajay yace "Ai matar ne ta fiye taku

ra da sa ido" Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaish

esa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna parlon ya gaida Ummi ta amsa tace "Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?" Jay ya

ɗ

an buda ido yace "Mun fasa" Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata gansa ba, U

mmi ta kalleta tace "Ke baki ga yayanki bane" Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace "Oh, ok, Good evening" Jay yace "Ya hanya?" Tace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Mami tana sama" Jay ya mike yace "Ohk" Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon ge

fen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace "Fadan ku ka sake yi kenan?" Hadeeyah ta

ɗ

an yatsine fuska taki cewa komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace "Kun fi kusa dai" Jay na bude kofar dakin da yasan Maminsa na

ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace "Mami" Mami tayi ma warce suke wayar sallama ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace "Ina ka je tun saf

e Son? I was thinking zaka zo airport kayi picking din mu" Jay ya

ɗ

an kalleta yace "Karfe nawa ku ka iso Mami?" Tace "Karfe sha daya da rabi na safe" Jay yace "Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba" Mami tace "Kaga da ubansa ne zai sauka Lagos duk ab

inda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun tafi gantali" Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace "Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you okay?" Jay yace "Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria n

e" Mami tace "Nasan shi zai zugaka ku dawo Nigeria kar ka biyo min ta UK" Jay ya

ɗ

an hade rai yace "Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria" Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi ko

fa yace "Zan je inyi wanka" Mami tace "Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi

kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu" Jay ya juya ya kalleta yace "Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku" Bai jira me zata ce ba ya fice daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa

don Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sa

nnan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara'a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace "Wanne ne son din naki a ciki Hajiya?" Mami tayi pointing Jay tace "That is my son" Matar na kallon Ja

y tace "Maa sha Allah, ai kuwa ga kama na gani" Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya mike yace "Mami za mu je Gym ne" Mami ta kallesa tace "Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne zaka je Gym?" Jay yace "Ai ba nisa Gym din" Ha

jiya Batula tace "Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je da nisa ba" Jay ya kalli Ajay yace "Mu je" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga dakin, Hajiya Batula tace "Amma

ɗ

an uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai" Mami

tace "Eh Cousin dinsa ne" Hajiya Batula tayi kasa da murya tace "Ko dai shi ne

ɗ

an sarkin dai?" Mami ta tabe baki tace "Shi ne" Hajiya Batula tace "Ya sunansa?" Mami tace "Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake kiransa" Hajiya Batula tace "Ikon Allah, shi kam

Jawwad babu ruwansa..." Cike da takaici Mami tace "Ni babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid din ne ke juyasa" Hajiya B

atula tace "A'a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai martaba ya nuna son kansa a fili karara nada

ɗ

an sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina ce Jawwad din ya girmi

ɗ

an sa?" Mami tace "Ya basa wat

anni har uku" Hajiya Batula ta rike ha

ɓ

a tace "Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?" Mami tayi shiru, can tace "Ci

kin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiran

ta da Ummi...." Hajiya Batula tace "Ikon Allah, to amma...." Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic din tace "Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?" Mami tace "In sha Allah" Ummi ta ajiye plate din hannunta tace "Sannun ku,

gashi nan kaza na tsaya gasa maku" Hajiya Batula na murmushi tace "Allah sarki, sannu da aiki" Ummi tace "Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye" Daga haka ta fita daga dakin, Mami tace "Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai ba

ta so Junaid din da aka nada Yarima me jiran gado ba" Hajiya Batula tace "To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada

ɗ

an yayansa da ya mutu ya bar

masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada

ɗ

an cikin sa?" Mami tayi wani murmushi tace "Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa, as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa

duk daya..." Hajiya Batula tace "To halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?" Mami tace "Wani Junaid? Amaryarsa da

suke kira da Aunty na da

ɗ

a me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada

ɗ

an ta Yariman ai" Hajiya Batula ta rike ha

ɓ

a tana kallon Mami. Ajay y

ayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few second

s of listening to what the frnd was saying ya zaro ido yace "What???" Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa, Nan da nan J

ay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya fixge wayar hannun Ajay yace "What's happening plss?" Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza, Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu

ne ya kira nan yaji hankalinsa ya

ɗ

an kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a daga ba, a hankali Ajay yace "Salim aka harba" Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace "What? Harbi kuma? Is

he dead?" Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately.....

_Barka da sallah everyone, Allah Ubangiji ya maimaita mana Ameen, ina nan ina baza ido ina jiran go

ron sallah na

🙄

_

*Next update sai bayan an gama suyan nama*

😁

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788

👈🏻

, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankal

i don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

HALYSAAH 36

Washegari sai da rana Ajay da Jay suka samu ganin Salem a hospital din da aka yi admitting dinsa, iya kafadarsa ne kadai aka nannada ma bandage alamar a nan aka harbesa

amma duk kamanninsa ya canza alamar ya ci duka ba na wasa ba, Jay ya zauna kujeran dake kusa da gadon yana kallon Salem that was in pain yace "Hasbunallah, How did this happen Salem?" Shi dai Ajay na tsaye ya rungume hannu shi ma yana kallon Salem ganin y

anda aka canza masa kama, ya ma kasa cewa komai, Salem dake kishingide jikin pillow da kyar don ko iya motsa kafadarsa daya baya yi ga duk jikinsa yayi tsami yayi karfin halin cewa "Ban san su ba suka yi attacking dina" Jay yace "Har gida suka same ka?" Sa

lem ya girgiza kai yace "I stayed out late yesterday in wudil naje gurin wani abokina, he insisted i stay till the next day amma saboda ina da abun da zanyi washegari da safe a kano sai naki kwana a garin muka yi sallama da shi, bayan na kusa unguwan da na

ke da zama sai na lura da wata mota na biye dani a baya amma ban yi tunanin komai ba na zata ya shigo layin ne bai san hanya ba shine yake bi na ko nima fita zanyi daga unguwan mun fita tare, bayan na shigo layin mu babu kowa saboda dare yayi tun kan ma in

sauko daga motata in shiga gida in bude gate sai nake ma motar alama da hannu ya tafi gaba zai samu hanya, sai kawai matukin motar ya fito ya nufo ni, duk da haka ban wani damu ba na zata direction zai tambayeni, na tsaya har ya iso dai dai gabana ban ank

ara ba kawai sai jin saukan naushi nayi ta ko ina a fuskata ina kokarin defending kai na sai sauran mutane ukun dake cikin motar suka fito su ma suka hau dukana ta ko ina at the same time they were asking me about a girl i know nothing about, wai inyi prov

iding dinta ko su kashe ni" Da wani expression Jay ke kallonsa, sai kuma ya mike da sauri ya dafa gadon da Salem yake kai yace "A girl?" Salem ya gyada kai da kyar yace "Wai Khaleesat, ni ban ma taba jin sunan ba wallahi, suka yi ta dukana wai sai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login