Showing 528001 words to 531000 words out of 641791 words

Chapter 177 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

213

why not kawai a bari Jay da Halysaah su auri juna, to amma me yasa har yanzu babu wanda yayi tunanin hadasu aure a gidan, hadasu

aure ne kawai zai basu daman consoling junansu su hakura su yi facing rayuwa kuma haka, ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta shiga bangaren Ajay ta tarar Khaleesat ta shiga bandaki tana alwala, ta zauna parlor tana jiran fitowarta sai ga Mami ta shigo Parlon

, da ladabi likitan ta gaisheta Mami ta amsa tace "Kin hada kayan nata kuwa?" Likitan tayi murmushi tace "Ranki shi dade ita bata yarda Abuja za ku ba har yanxu tana ganin kamar Kano za ki kai ta, na hada kayan da safe kan in shiga kitchen in fito har ta m

ayar cikin wardrobe dinta" Murmushi kawai Mami tayi tace "To zan hadata da Ammin su yi waya kilan zata yarda ta haka, amma ta ci abinci daxu?" Likitan:,: tace "Ta ci ranki shi dade" mami tace "Idan tayi sallah ki taho da ita bangarena" Likitan tace "To ran

ki shi dade" Juyawa Mami tayi ta fita daga parlon

HALYSAAH

.

Da sallama Khaleesat ta shigo parlon Mami tare da likitan ta bayan ta idar da sallahn Magrib, tayi ma Jay dake zaune parlon kallo daya sannan ta tafi ta zauna kasan carpet, likitan tayi masa

barka da zama ya gyada mata kai kawai, ta nemi waje ita ma ta zauna, Daga kitchen Mami ta fito da fruits, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Ina yini Mami" Mami ta karaso parlon ta ajiye ma Jay fruits din sannan ta zauna tana kallon Khaleesat tace

"Lafiya lau Halysaah, ashe baki zauna gidan Hajja ba daxu da ku ka je?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba tana wasa da hijab din jikinta, Dr tace "Barka da yamma ranki shi dade" Mami tace "Yauwa Dr...." Sannan ta maida dubanta kan Khaleesat t

ace "Halysaah kin hada kayan naki kuwa?" Khaleesat ta kalli likitan ta, Dr din tayi murmushi tace "Ranki shi dade ai tuni ta maida su cikin wardrobe tace she doesn't feel like going...." Mami ta

ɗ

an yi murmushi ita ma tace "To bari in kira Ammi sai ki gaya

mata haka ko? Auren Inteesar guda ki ce baza ki ba Halysaah, Ammi ai bazata ji dadi ba, ita ma Inteesar din won't be happy, nan ta zo tayi kusan wata daya gidan nan saboda ke kwanaki...." Khaleesat tayi shiru kuma bata dago kanta ba, Mami ta dau wayarta t

ayi dialing din number Ammi, tana dagawa tace "To Hajiya Ammi ga er taki kuyi magana...." daga haka ta mika ma Khaleesat wayar ta amsa ta kai kunne cikin sanyin murya ta gaida Ammi, Hadiyah ce ta shigo parlon da sallama ta nufi hanyar kitchen din Mami, Jay

ya bi ta da kallon gefen ido ganin dressing din da tayi sai baza kamshi take, kitchen din ta shiga ya kalli Mami dake kallon Khaleesat da suke waya da Ammi, not long after Hadiyah ta fito daga kitchen din ta ajiye tray din hannunta me dauke da drinks da b

ottle water biyu sai bowl din fresh fruits, tana kallon Mami tace "Mami ina snacks din fa, naga basa kitchen din" Mami tace "Ki duba wancan dakin, daxu su Kilishi suka shigo naga za su cinye maki na kai dakin na ajiye" Hadiyah ta juya ta nufi dakin, bayan

ta shiga cikin dakin Jay na kallon Mami yace "What are the snacks and fruits for?" Mami ta amshi wayar da Khaleesat ke mika mata tace "Ka tambayeta mana, ba ga ka gata ba" Jay bai sake cewa komai ba, Hadiyah ta fito daga dakin da foil plate babba dauke da

different snacks da aka rufe da cling film, Hadiyah ta ajiye foil plate din kan table tana kallon Khaleesat tace "To ki rakani mu je Halysaah" Mami tace "Tashi ki rakata Halysaah" Mikewa Khaleesat tayi duk da mood dinta wasn't good saboda wayar da suka yi

da Ammi, har cikin ranta ta kasa yarda Abuja kawai za su tafi bikin Inteesar, gani take gida za a maidata daga Abujan, Khaleesat ta dau plate foil din, Mami na kallon Hadiyah tace "Ina za ku zauna?" Hadiyah tace "Parlon Hajja" Mami tace "Ohk" Daga haka ta

dau tray din ta nufi kofa Jay ya bi ta da kallo har ta fita, Khaleesat na tafiya a hankali ta bi bayanta ita ma ta fita daga parlon, Jay ya kalli Mami yace "Me za ayi a parlon Hajjan?" Mami tace "Kai nima ban sani ba, ba a gabanka suka fita ba me ya hanaka

tambaya" Shiru yayi bai sake cewa komai ba, after some minutes ya mike ko fruits din bai sha ba ya nufi kofa, Mami ta bi sa da wani kallo har ya fita daga parlon. Kan kujera Khaleesat ta zauna a parlon Hajja tana gaida Ibrahim Khalil which was also from a

Royal home, ya amsa mata da fara'a yace "Ya kwana biyu Halysaah?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Yace "To ya jiki?" Ta

ɗ

an yi murmushi tana wasa da fingers dinta tace "Lafiyata qlau yanxu" Yace "Alhamdulillah, haka muke so ai" Ta juya ta kalli Hadiyah tac

e "Zan tafi...." Hadiyah tace "Baza ki zauna ayi hira ba" Ta girgiza kai tace "Wajen Mai martaba zan je" Hadiyah tace "To a gaishesa" Mikewa Khaleesat tayi tana kallon Khalil tace "Tohm sai anjima" Yana murmushi yace "Nagode da gaisuwa Halysaah" Kofa ta nu

fa walking slowly ta fita daga parlon, Khalil ya kalli Hadiyah yace "Amma dai jikin nata da sauki yanxu?" Hadiyah ta

ɗ

an yi murmushi tace "To Alhamdulillah za a ace, nasan bai wuce labarin mafarki zata je yi ma Mai martaba ba yanxu haka" Khalil ya sauke aj

iyar zuciya yace "Allah sarki, this shall pass in sha Allah, she will surely overcome it" Hadiyah tace "Hopefully" Yace "Amma kuma sai naga kamar therapy din isn't working for her, kusan shekara biyu fa yanxu, i think it's best a samu me irin predicament d

inta a hadasu su dinga communicating sosai suna hira, let them be friends and discuss their situation together, i mean warce mijinta ita ma ya rasu, i assure you she will gradually start coming back to reality...." Hadiyah tayi shiru tana kallonsa, can tac

e "To zan gaya ma Mami haka" Yace "Allah Ubangiji ya yaye mata" Hadiyah tace "Ameen" Yace "To meye labari gimbiyata" Tana murmushi tace "Yana wajen ka kai da ka tafi business trip na kusan wata biyu ban gan ka ba, nayi missing dinka sosai...." Khaleesat na

fita ta nufi part din Mai martaba, duk sanda take son zuwa part dinsa take zuwa kanta tsaye tunda Aunty bata kasar, he is always alone zaka samesa yanxu a part dinsa, sallama tayi ya amsa mata sannan ta shiga, yana zaune Main parlonsa ta samesa da fruits

a gabansa amma ba sha yake ba don yayi nisa tunanin da yake yi, ya

ɗ

an yi murmushi calmly yace "Jiddah, yau baki shigo da safe ba" Ta zauna inda ta saba zama ita ma tana murmushi tace "Mun je gidan Hajja ne" Yace "Ai Hajja tace kin ki zama da kuka je" Sunk

uyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, sai kuma ta gaishesa ya amsa yace "Ya jikin naki?" Ta daga kai ta kallesa tace "Ai naji sauki ranka shi dade, daxu ne dai yace in gaida masa kai" Sarki na gyada kai cikin sanyin murya yace "Ina amsawa Jiddah"

Ta gyara zama tace "Kuma ya gaya min abinda za ayi masa idan zai dawo, kasan ya kusa dawowa....." Mai martaba ya sauke idonsa a hankali yace "Ohk...." Cikin sanyin murya tace "To ranka shi dade baka tambayeni me yace za ayi masa ba?" Sallaman Jay yasa Sark

i ya daga kai yana kallon bakin kofar sannan ya amsa masa, Jay ya shigo parlon walking slowly ya karasa ciki ya zauna sannan ya gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace "Ya aiki Jawwad?" Jay ya sauke Idonsa yace "Alhamdulillah" Khaleesat tana

kallon Sarki tace "Zan tafi ranka shi dade" Yace "To ki dawo anjima sai mu ci gaba da maganan ko?" Ɗan murmushi tayi alamar taji dadi tace "To zan dawo ranka shi dade" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon zata tafi side din su Kilishi, Mai ma

rtaba ya kalli Jay ganin kamar da magana a bakinsa yace "Ya aka yi Jawwad?" Jay ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds yayi kasa da murya yace "Dama ranka shi dade na zo ne akan maganar Hadiyah" Sarki dai kallonsa kawai yake, Can yace "Ohk ina jin

ka" Bai yarda ya dago kansa ba yace "I think i am now ready, zan maidata ko gobe" Mai martaba was just looking at him, don a kwanaki da aka yi masa maganar Khaleesat har ya gigice yace gwara kawai ya maida auren Hadiyah don shi babu aure tsakaninsa da mata

r

ɗ

an uwansa, bayan few weeks Mai martaba yayi masa maganar Hadiyah don yana ganin idan da mace kusa da shi zai daina shan abubuwan da ya tsiri sha all of a sudden, amma Jay ya nuna bai ma san ya fada cewar zai maida wata Hadiyah ba, shi bai san sanda ya f

ada haka ba, ko kadan Mai martaba bai son tilastasa a lkcn shi yasa ya bar zancen bai kara tado sa ba, Hajja ma bata sake masa magana ba don ita ma duk wani abu da zai zama an turasasa Jay yanxu bata so, barin yanxu da ta rasa Ajay bata son komai ya samar

mata Jay riritasa kawai take tana lallabasa kamar kwai, da kanta ma tace kar wanda ya kara yi masa maganar Hadiyah tunda baya so, Allah Ubangiji yayi ma Hadiyah zabi na alkhairi, Mami ma tayi masa magana kusan sau biyu duk yaki bata listening ears, and thi

s was almost 5 months ago, Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "To yanxu kun yi magana da Hadiyar ne Jawwad?" Jay ya girgiza kai yace "A'a, ba sai nayi magana da ita ba ranka shi dade" Mai martaba yace "Kana nufin kawai a maida auren without her knowle

dge?" Ya gyada kai, Mai martaba ya

ɗ

an yi murmushi yace "It's not done that way Jawwad, dole sai ka sameta kun yi magana kun kara fahimtar juna da ita before the next step" Jay yayi shiru don baya jin zai iya, Mai martaba yace "Idan ku ka yi magana da ita

sai ka dawo ka sanar min yanda ku ka yi, sannan sai in tuntubeta ita ma" Jay bai iya yace komai ba, after a while da kyar yayi ma Sarki sai da safe sannan ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon. That same day wajen karfe goma da rabi na dare Mami na zaun

e parlon Mai martaba bayan yayi kiranta, ta sauke ajiyar zuciya after listening to him attentively, cikin nutsuwa tace "Wallahi nayi farin ciki da wannan batu ranka shi dade, bazan ce i am not in support ba, kuma gaskiya bazan ce i am in support ba saboda

Fulani, don kasan mu mata dole dai baza a rabamu da taya namu kishi ba, muna tare da Fulani Hafsat for more than 30 years a gidan nan da dadi babu dadi, kaga dai bazan ce lallai ayi mata haka ba, kuma bazan ce kar ayi ba....." Tana murmushi ta kare maganar

, sai kuma tace "Amma fa abu ne me matukar kyau da ace zai yiwu" Sarki dai kallonta kawai yake, can ya nisa yace "Fulani ai duk kame kame kike min a nan, you are not being straightforward, bazan ce maki na fahimci inda zancen ki ya dosa ba, da zuciyata kaw

ai nayi wannan shawaran, sai ke yanxu da na zauna ina neman taki shawarar, ko Hajja bata san komai ba, kin ga kuwa ya kamata ace kin zama very straight, tunda ke na zaba inyi magana da before anyone" Mami dai bata fasa murmushin da take ba, ta gyara zama t

ace "Ranka shi dade, kamar yanda nace maka wannan batu ne me kyau wallahi, kuma nayi farin ciki da jin sa, sannan kaga zaman Khaleesat a gidan nan won't look somehow again, don nasan ba kowa zai fahimci halin da yarinyar ke ciki idan ba zaunawa yayi da ita

ba, gani kawai ake tana ta zama gidan nan tun bayan rasuwan mijinta shekara biyu kenan bata koma gaban iyayenta ba, sannan mu ma bamu ce ta koma ba alhalin ba 'ya ya gareta tare da marigayi ba balle ace zaman da take kenan, gani za ayi abun babu tsari, an

d the question will be what is she still doing in the Emirate for 2 years now, don ni akwai warce ta min wannan maganar kawai dai nayi murmushi ban bata amsa ba, nan kuwa basu san taki zaman gidan nasu bane, mu kadai muka san halin da take ciki sai iyayen

nata, shi yasa kwanaki nayi mata sha'awar auren Jawwad kaga da hakan ta kasance babu wanda zai yi querying zamanta a masarauta kuma, amma yanxu kaga idan akwai uwarta a gidan nan babu me cewa komai wallahi" Mai martaba ya gyada kai cikin gamsuwa yace "That

is my thought too Fulani, nayi wannan tunanin few months ago, kawai dai zuciyata ce bata bani go ahead din furta batun nan ba sai a yanxu" Mami tace "Sannan bayan haka kai kanka kana bukatar kulawa yanxu ranka shi dade, bazai yiwu kana zaune for more than

a year a haka kai kadai babu kowa kusa da kai even though an san lalura ne ya jawo hakan, i know you are still yet to recover fully from the death of Junaid, sannan ga zama kai kadai which is giving you enough space to think and ponder, shi yasa health di

nka ke deteriorating now and then don ma kana da karfin hali, don haka nake ganin kayi abinda ya kamata kawai amma sai in Hajja ta yarje maka da yin hakan ranka shi dade" Mai martaba na jinjina kai yace "Shikenan Fulani, duk yanda ake ciki i will let you k

now first before anyone...." Tace "To Allah ya kara maka martaba ranka shi dade...." Sallama tayi masa daga haka ta mike ta fita daga parlon, Mai martaba ya jingina da kujeran da yake zaune yana kara nazarin maganar.... Wajen karfe tara na safe Malam Ali y

a shigo dakin Nenne da sallama, Nenne tace "Yanxu nake shirin zuwa in same ka a parlon ka don yau na tashi cikin matsanancin damuwa Ali" Zaunawa yayi kan Carpet din dakin yace "To Allah ya sa lafiya dai Nenne" Nenne tace "Ina fa lafiya Ali, yanxu haka za m

u zuba ido kamar marasu makabuli mu bar yarinya a gidan sarauta ba gaira ba dalili shekaru sun doshi biyu kenan? Ko dai mun sallama masu Khaleesat din ne Ali? Su kansu kallon shashashan iyaye za su dinga yi mana wallahi a yanxu dai, to tare da su zata zaun

a har abada kenan ko kuma dama wanda ya mutu yana dawowa ne balle mu ce zaman jiran marigayi take? A ina aka ta

ɓ

a haka ita ba 'ya ya gareta ba balle jikoki a gidan? Gaskiya abun ya fara damuna babu inda ake haka a duniya, kar mu zama yan iskan iyaye gwara

ayi abinda ya kamata mu sa Bala yaje ya kamo mana ita ya dawo da ita gidan nan, in ma daureta za mu yi mu daureta, gashi talakawan unguwan nan da na ja zuwa jikina nake da na sanin haka yanxu sai tsegumin mu suke wai mun sallama ma masarauta er mu, kilan j

ira muke sai an raba gadon marigayi ta amso kasonta sannan ta dawo, ni tsorona ma kar masarautar ma su yi zaton dalilin da yasa muka bar masu ita kenan a gidan muka yi shiru, ka duba wannan lamari Ali babu inda ake haka wallahi, ga dai Zahra'u kullum cikin

kuka tana son er ta a kusa da ita" Tun da Nenne ta fara magana Malam Ali yayi shiru yana sauraronta har ta kai karshe, jin shirun nasa yayi yawa tace "Ba shiru zaka yi ba Ali ya kamata ka zama uba jajirtattce kasan yanda zaka dawo da er ka gabanka, kar a

mana kallon marasa lissafi mana" Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanxun nan muka gama waya da Sarki shi ne ma dalilin da ya sa na shigo nan" Nenne ta zaro ido tace "Sarki da kansa? Ahaf kaga su ma sun gaji da rashin lissafin mu, wato ya kira yace a

zo a dauketa ko? Yanxu ina amfanin haka, baka ji yanda naji kunya ba tsamo tsamo, akan Khaleesat aka fara mutuwar miji da zata haukata kanta haka ta maida mu iyayen banza? Allahn da ya fi ta sonsa ne ya dau kayansa, wannan ai kafirci ne rashin danganar da

taki yi, duk musulmin kwarai an san sa da tawakalli da

ɗ

aukan ƙaddara mummuna ko kyakkyawa, yanxu ba sai su ga bamu bata ilimin addini bane tunda gashi bata san dangana ba, mu dai ta cuce mu wallahi, sai ka kira Bala yaje ya daureta ya taho mana da ita kaw

ai tunda mahaukaciya ta maida kanta, sau nawa ana dawowa da ita gidan nan ta faki ido ta gudu, to su ma sun gaji shi yasa ya kira ka" Malam Ali yace "Ni ba maganar Jiddah yayi min ba Nenne" Nenne tace "Maganar me yayi maka to?" Malam Ali ya sauke ajiyar zu

ciya yace "Wai gobe juma'a zai aiko wakilai a daura masa aure da Farida, in kuma can Nijar za aje daurin auren to sai aje, kiran da yayi min kenan yanxun nan" Sai da Nenne ta mike tsaye tsabar gigicewa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login