Showing 120001 words to 123000 words out of 641791 words

Chapter 41 - HALYSAAH COMPLETE

tace "Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi kenan za mu je gi

dansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen kar

fe biyar da rabi na yamma Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin Umma ba take cewa "Umm

a yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gid

a ga yan unguwa na ta tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a kulle, don ma akwai kanwarta

da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Is

lam suka marairaice wai za su bi ta, ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta dawo amma

sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wuj

iga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita, ai ko tana

isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata ta

Ι“

a saninta ba a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata c

e, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci amanarta tace ma yan sanda ita bata ta

Ι“

a ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da

kuka tace "Ban ta

Ι“

a tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata ta

Ι“

a gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma

kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda Gaje ke cewa.

_Thanks sooo much for the birthday wishes everyone, Allah ya saka da alkhairi_

*As usual yau akwai discount na littafin Halysaah daga yanxu har zuwa gobe karfe goma na safe, the bo

ok will be 300 naira, via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence through 07087865788*

Thank you sooo much everyone.

Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Deejah me sana'ar lamurje da ganja, tare da Aunty Amzaj Maman mara Jidda da Damsalele, Uwata Ze

enariya kema an gaisheki da babban murya tare da Hajiya Safiyyah Usman me kantin kayan yara

😁

Aneesah Zero zero da Ummi matar mijin uwar gida ku ma na gaisheku da siririn murya, Barrister Inna da 'ya ta Uwar Annur da Hajiya Sadiya Uwar Hanan kuma duk na ga

isheku da fatan alkhairi, Hajiya Sadiya Chamo au banda ke

πŸ™„

, Mom Asas, Maman Faruk me data, da Sis Aisha Dalhat ga kuma Maman Aisha da Hajiya Bilkisu duk Khaleesat na maku fatan alheri

πŸ’–

HALYSAAH 38

Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan B

aaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta ta

Ι“

a saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abi

nda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayani

yar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan ga

banta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke fa

ruwa ne a gidan?" Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsa

ya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga..." Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin s

ai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga

basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace "Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka

san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai"

Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace "Mu dai mun san ko ma wani ta

karda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arz

ikin da ba a ta

Ι“

a yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har 'ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu m

a mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu

Ι—

an uwanki" Sha'awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun nem

an agaji su da yaransu, Sha'awa tace "Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fu

shi ba wallahi" Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha'awa ta rama tace "Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari" Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha'awa dake kunduma

ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha'awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha'awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa "Shegu

en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba" A haka dai aka fitar da Sha'awa daga gidan

, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin

hasken, Noor na kallon Umma tace "Umma kinga babu kayan abincin a inda suke" Umma ta kalli inda Mam

an Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mey

e haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki? Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila'i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila'in ku ke ko menene haka? Doo Allah

duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata" Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Zahra'u me suka dauka a dakin Alin da

suka zo?" Umma da ta zauna gefen katifar ta tace "Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma" Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace "Har dakin naki suka shiga ne? To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka

shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?" Mama Shatu tace "To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga? Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu

ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke" Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace "Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina

ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan? Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alham

dulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me

tsaya mana" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace "Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka kark

ade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba" Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace "Ba ruw

ana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani sa

Ι“

on da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimak

o ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare" Islam tace "To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne" Nenne ta gwal

o ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace "Zahra'u ina kayan abincin? Ko kasuwa ki ka kai kika siyar? Fatarar taki ta kai haka Zahra'u?" Umma tace "Saboda me zan kai kayan abinci kasuwa in s

iyar Nenne, daga zuwa gidan Baaba Gaje in dawo nima na tarar an kwashe kayan abincin" Nenne ta ajiye jarkan hannunta a kidime ta saki salati tana tafe hannu tace "Baki kulle dakin bane Zahra'u?" Umma tace "In zan fita ai ina sa ma dakina kwado, to fasa kwa

don aka yi, ga makullin ma a jakata" Nenne ta juya ta fita daga dakin dai dai shigowar Usama wani almajirin Malam Ali dake tare da shi tun yana da arzikinsa, kuma har yanxu dai yana tare da shi, Nenne na haska sa da tocila tace "Yauwa Usama kace iya wani d

aki mutanen suka shiga a gidan nan?" Usama yace "Iya dakin Alhaji kawai suka shiga" Nenne bata sake cewa komai ba ta nufi dakin Mama Zubaida don yafi kusa da ita, tana dage labulen dakin ta fara haske hasken tocila, sai kuma ta duka karkashin gadon karfen

dake dakin ta hango carton din indomie biyu an tura su can ciki, ta kwalo ma Usama kira ya karaso da sauri tana haska masa karkashin gadon tace "shiga ka jawo min kwalayen taliyar yaran can" Ai ko ya shiga ya kwaso su ya fito da su, Nenne ta shiga cikin da

kin tana duba bayan kyaure nan ma taga Babban jarkan man gyada ta sa Usama ya fiddo waje, ta gama duba dubenta a dakin bata ga wani kayan abincin ba sannan ta nufi dakin Mama Shatu, a bayan kyaure taga buhun shinkafa daya da quarter an lullube da zani, ta

kwalo ma Usama kira shi ma ta saka ya kinkimo su ya fitar waje, a dakin Mama Shatu still taga kwalayen taliya da na maggi da jarkan manja duk ta sa Usama ya fiddo su waje, Nenne na kallonsa tace "Kwashe su ka mayar dakin Zahra'u Usama" Yace "To Nenne" Sai

a sannan Nenne ta juya tana kallon su Mama Shatu da suka yi wuki wuki da ido ko wacce na kokarin diban ruwan alwala a buta, Nenne tace "An dai yi asara duniya da lahira, barayin banza barayin wofi, tirrr da halin ku, wato ga sabon jarin kayan abinci kun sa

mu ko, tunda Zahra'un ta maida kanta er wahala warce bata san ciwon kanta ba, da ban ce a tsam min manja ba shiru zata yi maganar ta bi rariya ta bar ku da haram, ko zama da ku kadai ya isa ya dinga jefa Ali a masifa iri iri, ai ba kyau zama da jahilai shi

ne kawai bai gane ba" Daga haka ta juya ta koma dakin Umma. Khaleesat na bakin pampon dake compound din Aunty Farida tana wanke wanke, ita kadai ce a gidan gaba daya don duk sauran tenant dake gidan sun fita aiki, Aunty Farida kuma ta tafi kasuwa, juyawa K

haleesat tayi jin an bude gate, ta mike tsaye tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya rufe gate din ya karaso cikin compound din shi ma yana kallonta, ta sauke idonta a hankali tace "Sannu da zuwa" Yace "Good morning Halysaah" Ɗan murmushi tayi ta sunkuya

r da kai ta gaishesa sannan ta juya ta tafi ta bude masa kofar shiga parlon Aunty Farida tana kallonsa, yace "Aunty fa? ina ta kiran wayarta no response" Khaleesat tace "Eh ta bar wayar a gida ne ta tafi kasuwa" Ya kalli plastic chair dake veranda din Aunt

y Farida yace "Let me seat here ba sai na shiga ba, i just came to check on you" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "I really appreciate Housemate" Yace "To ki zauna mana" Ta kalli second

chair din dake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login