Showing 30001 words to 33000 words out of 641791 words
sa da kallo har ya fita sannan ya kulle kofar ta waje, karasawa kusa da window tayi ta
Ι
an bude curtain kadan tana kallonsa har ya shiga motarsa a garage yayi reverse, sai da ta daina hangen motarsa sannan ta sake curtain din a hankali, tafi min
ti uku a tsaye wajen ta jingina da window, daga karshe tana tafiya a hankali ta wuce dakinta bayan ta kashe wutan parlon..... Washegari Khaleesat na sauka daga Lyft bayan ta dawo school taga motar Housemate dinta heading toward the garage, kafin ta karasa
apartment din nasu har ya shiga ciki, murda kofar tayi taji a bude ya bar mata alamar ya ganta shi ma, tana shiga parlon yana fitowa daga kitchen rike da Lemon gwangwani me sanyi, ya karaso cikin parlon yace "Are you just coming back from school?" Gaishesa
tayi, yace
"Good evening Halysaah" Bedroom dinta ta wuce ta bar sa a parlon, it's almost 6pm na yamma kuma Safiyyah ce ta bata masu lkci tana mata bayanin wani course dinsu da tace bata ganewa, wanka Khaleesat tayi ta sauya kayan jikinta zuwa kananun kaya
sannan ta saka hijab ta fito parlor, yana parlon har sannan yana operating laptop dinsa, ganin zata shiga kitchen yace "Ki bari ki hutu, zan fita sai na siyo abinci" Khaleesat ta kallesa tace "I am cooking noodles" Yace "Ohk then" Tana fadin haka ta wuce
kitchen, Ya mike ya wuce dakinsa da laptop dinsa, cikin mintunan da basu da yawa Khaleesat ta gama dafa noodles din da take, ba da yawa ta dafa ba don bata san ko zai ci ba, zata yi dishing din abincin a plate taji ana knocking kofar parlor, ta ajiye plate
din hannunta sannan ta fito daga kitchen din, Housemate dinta ta gani har ya fito shi ma to check on who is at the door, amma ganinta kawai ya juya ya koma dakinsa, karasawa tayi ta bude kofar, lkci daya taji komai ya tsaya mata cak ta dinga kallonsa babu
ko kiftawa kamar ranan ta fara ganinsa, Yana kallonta daga sama har kasa yace "Meye kike kallo na haka Malama?" Tayi wani yake zuciyarta na bugawa tana in-ina da kyar tace "Ya Abdul, I.. I.. was surprised, san..nnu da zuwa" Da sauri ta juya ta koma parlon
, ya bi bayanta yana duba wayarsa dake vibrate a hannunsa alamar ana kiransa, ita dai ta koma bayan kujera ta tsaya kamar munafuka tana kallonsa zuciyarta na bugawa sosai, kana ganinsa kasan ba a lkcn ya shigo America ba, probably tun daxu ya shigo ya sauk
a hotel, ya
Ι
aga kiran da ake masa ya kai kunne, tana ganin haka ta juya ta nufi corridor din dakunan apartment din tana waige waige, ganin attention dinsa na kan wayar da yake ta bude kofar dakin Housemate dinta ta shiga da sauri ta kulle kofar, Housemate
dinta ya juya yana kallonta da mamaki, gaba daya a rude take ta nufesa tana yarfe hannu ta duka kusa da shi, ya mike still looking at her with surprise yace "Are you alright Halysaah?"
07087865788β
π»
β¨β¨
HALYSAAH β¨β¨
By _Khaleesat Haiydar_β
π»
1
0.....
Khaleesat ta gyada masa kai tana rufe bakinta da hannunta murya can kasa tace "Plss i have a visitor, i want u to plss pretend you are not staying here, just pretend u came to drop some books for ur Female friend living here plssss" Kamar zata yi k
uka ta kare maganar tana kallonsa, yayi shiru shima yana kallonta at first, sai kuma yace "As in how Halysaah?" Ta marairaice masa tace "Kawai dai kayi kamar ba a gidan nan kake ba don girman Allah ka rufa min asiri, u know my former housemate mace ce, act
as though u are her friend, kayi kamar wajenta ka zo pls, don Allah ka taimake ni" Bata jira cewarsa ba ta mike ta juya da sauri ta fice daga dakin kafin Abdul ya biyo ta, ya bi ta da kallon mamaki baya ko kiftawa, can kawai yayi murmushi ya zauna ya ci g
aba da abinda yake yi a Laptop dinsa, parlor Khaleesat ta dawo suka kusa cin karo da Abdul da ya nufo corridor yace "Me kika je yi a ciki? You didn't even get me something to drink" Ta
Ι
an yi murmushi a hankali tace "Why didn't you let me know u are coming
? Me yasa baka gaya min zaka zo ba?" Yace "Sai na gaya maki in zan zo? Ko ke zaki biya min ticket din jirgin?" Ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Aa ba haka nake nufi ba, ya hanya?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "What is wrong with you, why we
re you sick?" Ta sauke manyan idanuwanta kasa a hankali tace "I don't know too, but i am much better now, naji sauki Alhamdulillah" Yace "Rashin lafiyar ne yasa kika dena daga kirana all this while?" Ta marairaice masa tace "Don baka san yanda nake ji bane
a sannan, let me get you water to drink" Daga haka ta wucesa da sauri, ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen, Khaleesat ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta dafe kirjinta that was heaving so fast, after few seconds ta sauke numfashi sannan ta dau
tray ta bude fridge ta dauko ruwa da lemo da glass cup sannan ta fito daga kitchen, zaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, ta karasa ta duka gabansa ta ajiye masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai tunda ta fito kitchen din yake bin ta da ido
, ta zauna kan carpet ta tankwashe kafarta ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "Ya su Mumy da Daddy?" Jin yayi shiru ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta kawai yake, a hankali ta sauke idonta kasa, yace "Duk kwana biyun nan kin canza Baby, you d
on't look critically ill da har zaki kasa daga kirana, menene yasa kika dena kirana kuma
idan na kira ki ki dagawa? Common WhatsApp kin dena min magana yanzu" Ta kasa kallonsa, tana wasa da gefen hijab dinta a hankali tace "To kwanan nan sai kayi ta min fa
da ta waya baka considering dina, ga kuma course dinmu da wahala ka sani" Ita kanta ta rasa dalilin da yasa hawaye ya cika idonta, He let out a sigh har a sannan yana kallonta, sai kuma ya dagota sitting her down by his side, gabanta ne ya fara faduwa, in
da akwai abinda ta tsana kuma take fargaba a rayuwarta bai wuce Abdul ya zo America wajenta ba, duk da yawanci zuwan da yake it's either tare da Mom dinsa or his Dad, amma duk da haka a dar dar take da shi saboda wasu abubuwan da ya tsira wanda a baya baya
mata haka, duk zuwansa kasar sai ta kirko wani abu da zai maidata unhealthy wani lkcn har sai an kai ta hospital, ita da tasan zai kamo hanya ya taho da bata fara ce ma Safiyyah tace masa bata da lafiya ba, yana caressing fingers dinta yayi kasa da murya
yace "But you know i love you Khaleesah, ke ce kike jawowa nake maki fada a ko da yaushe" Ita dai bata ce komai ba hawayen dake makale idonta ya gangaro bisa kuncinta, ya kai hannu yana goge hawayen a hankali yace "Ohk, but you know i love you so much righ
t?" ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Housemate dinki fa? Is she around?" Sosai taji gabanta ya fadi, taki barin su hada ido tace "No ban sani ba, i saw she had a visitor daxu ya zo nemanta, probably her friend...." Yana kallonta yace "Friend? Namij
i kenan?" Khaleesat ta gyada masa kai, lkci daya ya hade girar sama da ta kasa yace "Yaushe ta fara kawo namiji gidan? When did that start?" Khaleesat tayi karfin halin cewa "Dama tana kawowa time to time ai but not frequently, sai in kilan sun kawo mata r
eading materials ko bata da lafiya sun zo dubata" Yace "Kuma mazan na kwana a nan?" Khaleesat ta hadiye wani abu da kyar tace "Ni ban sani ba gaskiya, tunda ina dakina always a kulle ai" Kallonsa tayi to cut short the conversation tace "Na dafa noodles yan
zu bari in kawo maka kar ya huce" Tana fadin haka ta mike da sauri zuciyarta na bugawa, dai dai nan Housemate dinta ya fito daga dakinsa, Khaleesat taji zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tsabar kidimewa, tayi saurin dauke kai tayi hanyar kitchen, Abdul ya
juya jin an bude kofar daki, hada ido suka yi da Housemate din nata da ya shigo parlon yana tafiya slowly waya kare a kunnensa duk da ba magana yake a wayar ba hannunsa daya rike da wani Textbook, idonsa kuma na kan Abdul, hannu ya daga masa calmly yace "H
ello" Abdul ya bi sa da kallo babu ko kiftawa without replying to his Hello, shi dai Housemate din nata yana tafiya calmly ya nufi kofa ya fita daga parlon, tuni Khaleesat har ta shige kitchen hankalinta a tashe ta dafe kirjinta tace "Na shiga uku....." A
haka dai ta fara zubo noodles din a plate, cike da karfin hali ta dawo parlon, Abdul dake ta kallonta yace "Who is he Baby?" Khaleesat ta
Ι
an yi fari da ido tace "Ni ban ma ta
Ι
a ganinsa ba sai yanxu, Nancy ya kawo ma littafi ina ga" Abdul ya mike yace "Ta
yaya zaki dinga rayuwa under same roof da wani gardi Baby? Yaushe Nancy din ta fara shigo da samari gidan nan? All this while dama yana cikin gidan nan?" A hankali Khaleesat tace "Na fa ce maka ban ta
Ι
a ganinsa ba, i have never seen him before sai yanzu" A
jiye abincin hannunta tayi cike da karfin hali tace "In dafo maka black tea?" Komawa yayi ya zauna yaki cewa komai, kana ganinsa kasan he is boiling inside, ita dai ta juya tana tafiya kamar munafuka ta koma kitchen, mikewa yayi ya bi bayanta har zuwa kitc
hen din yace "Ta yaya wani banza can zai dinga shigowa yana kalle min ke anyhow Khaleesah?" A hankali Khaleesat tace "Ya Abdul kar ka manta communal living muke a gidan nan, this is America.... this isn't my apartment alone, bazan iya cewa ga wa enda za su
shigo gidan ba tunda ba gidana ni kadai bace" Tsawa ya mata yace "And so what??? An gaya maki bazan iya kama maki hayar gidan ke kadai bane? Banda kince kina tsoron zama ke daya a gida do you think u will be sharing an Apartment with anyone in America? Do
u think I can't afford a full apartment for you??" Har jikin Khaleesat ya fara rawa ganin how fiercely he was speaking to her yana huci, ga idanuwansa sun fara sauya launi, sosai take jin tsoron Abdul ita kam, hawaye ya fara gangarowa idonta muryarta na r
awa tace "Ka fara kuma ko?" Kamo hannunta yayi fuskarsa a murtuke suka fito daga kitchen din, ta fashe masa da kuka a hankali har suka dawo cikin parlon, cike da fada yace "Ya bazan fara ba naga wani katon banza under same roof with you? Me yasa tun tuni b
aki gaya min Housemate dinki na shigowa da gardawa cikin gidan nan ba in samar maki other alternative? Me yasa baki da hankali baki da tunani ne ke a rayuwarki?" Zaunawa tayi ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da kujera, ya zauna yana huci, ita dai kuka
kawai take tana shessheka, after few minutes ya koma kusa da ita ya dagota drawing her closer to him kamshin turarensa ya cika mata hanci, nan da nan ta hadiye kukan da take tana zare ido, Gently yake caressing dinta murya can kasa yace "I am sorry Baby, a
mma da kin gaya min da na samar maki wani apartment din ai...." Ta fara kokarin komawa baya tana son kwace kanta daga hannunsa, kin saketa yayi a fusace yace "Why do u always act like a Bush gal Khaleesah? Har yanzu rayuwar Ghetto bazai fita a kanki ba? Wh
at is the meaning of this nonsense?" Ta ki barin su hada ido, da kyar tace "To ai... This is a promise you made, amma kuma sai ka dinga..." Cikin tsawa yace "So f what if i break the promise? Ko ance maki tsoronki nake ne? Ko kuma wani ne zai aure min ke d
ama?" Ta marairaice masa kamar zata yi kuka tace "Ni dae bari in kawo maka black tea" zata mike ya fixgota har sae da fado kansa, ya fige hijab din jikinta yace "Naga alamar kin ma maida ni wani gara don kinga ina biye ki" Ta takure waje daya wasu hawayen
na taruwa idonta taki yarda su hada ido tana kokarin kwatar kanta daga grip dinsa, skirt karami ne sosai jikinta sai half vest shi sa ma take ta yawo da hijab tun daxu da ta dawo schl, ya sake fixgota sosai jikinsa, kuka ta fara yi muryarta na rawa tace "D
on Allah ka bari plss, this wasn't our deal, you are not keeping to ur promise" Kallonta ya dinga yi saboda yanda tayi provoking dinsa, duk da shi bai yi niyyar mata komai ba da ya wuce ya lallasheta amma tsabar yanda ta hasala shi sai ya fara kokarin kiss
ing dinta, Ζin yarda tayi tana kiciniyar kwace kanta tana kuka, House mate dinta ne ya shigo parlon a lkcn, ya kalli yanayin da suke da kuma yanda take struggling din kwatar kanta daga jikinsa, direct ya nufi cikin
parlorn har inda suke without a second th
ought ya cakumo Abdul yana kallonsa da kyau "Hey, this is America guy, what sort of molestation is this??" Mikewa Abdul yayi yana kallonsa da wani irin Expression na mamaki, bai yi wata wata ba kawai ya sauke masa fist dinsa a kirji har sau biyu, ya wani c
akumosa yace "Are you insane? How dare you??" Khaleesat ta zaro ido ta mike cikin tashin hankali ta riko Abdul tana zaro ido with shock, lkci daya ta kalli Housemate dinta da ya tsaya yana kallon Abdul baya ko kiftawa kuma bai yi attempting rama abinda yay
i masa ba, da kyar tace "He is my boyfriend, I don't think u have any problem with this, who are you? And where do you know us from? You have no right to intrude!" Housemate dinta dake kallonta ya sauke idonsa kamar bazai ce komai ba, sai kuma calmly yace
"My bad! And i am sorry, i thought u were in danger, i am only here to drop some books, sorry about that plss" Khaleesat ta wani kallesa tace "Do i know u from anywhere that warrant u intruding?" Ya girgiza kai yace "Not at all... I am sorry" Kallon Abdul
yayi, bowing his head gently at the same time yace "I am sorry, dude" Daga haka ya ajiye book din hannunsa ya juya ya nufi kofar parlon ya fita waje, that was when Khaleesat realized she was half dressed all this while, dukawa tayi ta fara kuka a hankali t
a hade kanta da kujera tana jin kanta na wani irin sara mata, wani kallo Abdul yayi mata yana huci, kawai ya dau wayarsa ya nufi kofa ya fice daga parlon kamar zae tashi sama, ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa tayi da sauri ta nufi window ta
na duba waje taga babu motar Housemate dinta har ya tafi, sae Abdul da ta hango yana tafiya down the street, dawowa parlon tayi tana goge hawayen dake sauka idonta ta dau Hijab dinta ta wuce daki da sauri, har wajen karfe tara na dare Khaleesat ta kasa tas
hi daga saman darduman da take zaune ga wani ciwo da kanta yake mata, jawo wayarta tayi a hankali, tun daxu take son kiran Abdul amma ta kasa kiransa saboda tsoro, daga karshe tayi gathering courage tayi dialing numbersa har ya katse bai daga ba, ta sake k
ira nan ma bai
Ι
aga ba, tasan ba lallai ya
Ι
aga ba dama, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado wasu sabbin hawayen na zuba idonta. Da safe duk da yanda Khaleesat ke jin ta wani iri kamar zata yi rashin lafiya haka nan tayi shirin makaranta ta saka Facemask
dinta sannan ta bar gidan, ta kusa awa daya a makarantar kafin Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta zauna gefenta tana kallonta tace "Why are you sitted here Khalee? Is the lecturer not around?" Khaleesat ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Safiyyah ta sauk
e Facemask dinta ganin swollen eyes dinta cike da damuwa tace "Subhanallahi, what is wrong Khaleesat? Kukan me kika yi? Ko jikin Mama ne?" Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye na taruwa idonta, hankalin Safiyyah ya tashi tace "Innalillahi, don Allah me ya
faru? Is everything ok?" Khaleesat ta girgiza mata kai tana goge idonta a hankali tace "Abdul ne ya zo" Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul kuma?? Yaushe? Kuma me ya maki kike kuka?" Khaleesat tace "He came yesterday evening" Safiyyah tace "Ji jaraba, to me
ya zo yi? Kuma me ya faru da ya zo din?" Safiyyah na jefa mata wannan tambayar taji hankalinta ya tashi lkci daya, let it not be what just crossed her mind now, tunda tasan ko wanene Abdul, ta kamo hannun Khaleesat da sauri cikin tashin hankali tace "Ko ya
maki wani abu ne? A gidanki ya kwana???" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a" Safiyyah bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba, can tace "Toh meye kuma na kuka don ya zo, ko rashin mutuncin da ya saba ya shuka maki?" Khaleesat na shess
heka a hankali tace