Showing 39001 words to 42000 words out of 641791 words

Chapter 14 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

202

sa da kallo har ya isa parlor, jingina taga yayi ta

bayan kujera ya rungume hannunsa ya rufe ido, Khaleesat ta sauke idonta sannan ta fito daga dakinta tana tafiya a hankali ta tafi parlon, bude ido yayi da sauri jin tafiya, sai kawai ya nufi kofar fita daga parlon, tace "Since u can't control ur self a ko

ina ka samu bacci kake, be it standing, sitting, driving and even walking, then why not sleep over?" Ya dan kalleta jin abinda tace, nan da nan kuwa yaji baccin ya bar idonsa gaba daya, yana mata kallon mamaki at the same time yana sosa kai yace "Yaushe ki

ka ga nake yin duk wannan da kika lissafa Housemate?" Ita

dai ta rungume hannu tana kallonsa bata ce komai ba, ya dauke kai yace "I was only meditating ba wai bacci nake ba, in dai kika ga na rufe ido to i am meditating" Yana fadin haka ya nufi kofa ya bud

e yace "Good night, kar ki manta ki kulle kofar" Daga haka ya fita ya tura mata door din,

ɗ

an murmushi tayi tana tafiya a hankali ta isa kusa da window ta dan bude curtain din tana lekansa, parking space taga ya nufa ya bude motarsa ya shiga, she is just h

oping yana shiga bazai fara wani baccin ba a cikin motar, after few seconds taga ya fara reverse, ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa har ya bar Garage din ya dau hanya, sake curtain din tayi slowly, ta dan tsaya for few minutes sai kuma ta tafi daki ta d

auko key dinta ta kulle kofar ta wuce dakinta, sake kiran Ummanta tayi ta WhatsApp, bayan Umma ta daga Khaleesat tace "Ko kin fara bacci ne Umma?" Umma tace "Aa idona biyu ina jiran ki, Abdul ya maki wata magana ne?" Khaleesat tayi shiru jin abinda Umma ta

ce, ta girgiza kai tace "A'a bai ce min komai ba, me ya faru Umma?" Umma tace "Daxu Hasiya Matar Malam Saleh ta zo gidan nan" Sosai Khaleesat taji gabanta ya fadi, Malam Saleh aminin mahaifinta ne, yawanci abubuwa da yawa a bakin matarsa Ummanta ke ji tund

a ba gaya mata baban nasu ke yi ba, abu da yawa ma sai dai taji a duniya ba dai a bakinsa ba, Khaleesat tayi karfin halin cewa "Me tace Umma?" Umma tace "Wai ko an tsaida maganarku da Abdul, haka dai tace min" Khaleesat was short of words, lokaci daya jiki

nta yayi sanyi, sosai maganar ta zo mata a bazata, she could feel her self tearing up, hankalinta yayi mugun tashi cikin lkci kadan, Umma tace "To ina jira dai in ga ko Malam din zai yi min magana, in ba ayi hankali ba kuma in ji a bakin matansa tun da su

zai gaya masu ai, kuma kin ce Abdul din bai ce maki komai ba har yanzu ko?" Khaleesat ta goge hawayen da ya gangaro idonta, tana gyada kai da kyar kamar Umma na ganinta amma ta kasa cewa komai, Umma tace "Khaleesah?" Da kyar Khaleesat ta bude baki ta amsa

don bata son Ummanta tasan kuka take, Umma tace "Naji kinyi shiru ne" Khaleesat ta dake tace "Ba komai Umma, ina duba wani karatu ne a takarda" Umma tace "To shikenan, kiyi karatun ki ma yi magana washegari ko?" A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayar h

annunta ta kwantar da kanta saman pillow hawaye na sauka idonta, bata san menene ya sa all of a sudden taji she can't marry Abdul ba unlike before da har cikin ranta tasan bata da option dole ne aurenta da shi, tana kuma masa fatan ya canza wataran, yanzu

kam bata jin haka a ranta, instead ji take bazata iya aurensa ba ma, Khaleesat bata yi wani baccin kirki ba daren ranan nan fargabanta daya kar ma yace a daura auren nan take, tasan in har suka ce ma iyayenta haka babu abinda zai hana a daura auren nan sai

wani ikon Allah. Da safe Khaleesat ta tashi da ciwon kai sosai, kana ganinta kasan tana cikin damuwa ba kadan ba, haka dai ta shirya ta fita zuwa makaranta, warce take son tayi ma magana ta dan ji saukin abinda ke damunta sai bata shigo school ranan ba, w

ayarta ta ciro kawai tayi dialing number Abdul cause she can't hold it anymore, kiran na shiga ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne a hankali ta gaishesa, amsawa yayi yace "Ya aka yi?" At first tayi shiru, sai kuma tace "Ba komai i only called to greet

you" Yace "Which side of the bed did you wake up from today da kika kirani ki gaisheni?" Tayi masa shiru, yace "ke dai fadi abinda kike so Malama, foodstuffs din ki ne ya kare ko me?" Ta hade rai tace "Yaushe ka siya da har zai kare?" Yace "Bazai kare ba

dama mana tunda baki wani cin abinci sai cookies da kayan kwadayi" Ta wani turo baki bata ce masa komai ba, after few seconds tace "Kawai naji a jikina ne kamar da wani abu dake shirin faruwa shi sa na kira ka" Yace "Wani abu kamar me fa?" She was mute bat

a basa amsar tambayarsa ba, yace "Anyway, ko ma me kika ji a jikin ki haka ne, zan shiga meeting yanzu sai anjima" Katse wayar yayi a nan take, ta dinga kallon screen din wayarta wani tsanarsa na yawo a zuciyarta, a baya duk abubuwan da yake mata bata taba

jin tsanarsa ba sai dai haushinsa yanzu kuwa kawai ji tayi ta tsanesa, ta ja tsaki ta mayar da wayarta jaka tana jin wasu hawaye na cika idonta, rashin zuwan Safiyyah makaranta ya sa bata tsaya su gama karatun ranan ba ta kama hanyar gida kawai cike da da

muwa, tana jiran Lyft din da tayi ordering sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tun daxu ta kirata bata daga ba sai yanzu ta biyo ta, Khaleesat ta daga ta kai kunne tana jin muryar Safiyyah tace "Baki da lafiya ne?" Da kyar Safiyyah tace "Tun jiya da da

ddare, na ma zata rasuwa zan yi kawata" Khaleesat ta

ɗ

an bude ido tace "Me ya sameki?" Safiyyah tace "To ina ma na sani Khaleesat, Allah sa ba poison dina matar nan tayi ba don tun jiya sai yanzu nasan mutanen dake kaina" Khaleesat tace "Subhanallah, kina

gida ne yanzu?" Safiyyah tace "Har da karin ruwa kuwa" Khaleesat tace "To bari in taho gidan yanzu" Khaleesat na maida wayarta jaka ta nufi gidansu Safiyyah, bayan tayi knocking kofar Surayya ta bude mata, Khaleesat ta sauke ido ta gaisheta, in ba kasa kun

ne sosai ba ma baza kasan Surayya ta amsa ba, Khaleesat taji muryar Mustapha na tambayar matar tasa wanene, ji tayi kamar ta juya ta fasa shiga cikin gidan, amma kasancewar a bude Surayya ta bar kofar yasa ta karasa ciki walking slowly, without looking at

Mustapha dake parlor ta gaishesa, ya amsa yace "Ya karatun Khaleesat?" Khaleesat tace "Alhamdulillah, ya jikin Safiyyah?" Yace "Alhamdulillah, she is inside her room" Khaleesat ta juya ta nufi dakin Safiyyah, da gasken ruwa ta tarar ake kara mata don ta za

ta kawai tace mata haka ne don ta zo, Khaleesat ta zauna gefenta da damuwa tace "Sannu Sophie, ya jikin?" Safiyyah tace "Ba sauki Khaleesat, wallahi kilan abu matar nan ta saka min a abinci" Khaleesat tace "Don Allah ki dena cewa hka, kin ga yayanki ai baz

ai ji dadi ba in kina wnn magana" Safiyyah tace "Wallahi ita ce don lafiya na dawo gida jiya, ni na zata ma na rasu, sai da na farfado naga ba haka ba" Khaleesat tace "Allah dai ya baki lafiya, kin ci abinci?" Safiyyah tace "Ni bazan ci abincinta ba gaskiy

a tun daxu sai fruit kawai nake ta sha da lemon kwali" Khaleesat tace "Ko in je gida in maki girki? Me kike son ci?" Safiyyah tace "Ko tuwo da miyar kuka ne ki min in kina da ingredient, kawai shi naji nake so wallahi" Khaleesat tace "To ba damuwa, bari in

yi sallah sai in tafi in maki girkin" A haka Khaleesat tayi sallahn azahar ta bar gidan bayan tayi ma Surayya da mijinta sallama, Mustapha ne ma ya tambayeta har zata tafi, Shine tace masa zata dawo

anjima, Khaleesat na isa gida taga motar Housemate dinta

a Garage, tana bude kofar ta shiga parlor ta gansa kwance kan 3 seater yana bacci, har ta kulle kofar bata ga ya bude ido ba, ta nufi dakinta ta shiga ciki ta canza kaya sannan ta fito ta shiga kitchen, tuwon ta dora har zata fara hada ingredient na miyar

kukan sai kuma ta fasa taji gwara tayi vegetable soup kawai, ita kanta bata san menene yasa take son yin vegetable soup din ba duk da bata wani son cin miyar ganye she prefer slimy soup, sai da ta gama tuwon sannan tayi ordering lyft da zai kai ta nearest

African store da zata iya siyan ingredients din miyan Vegetable.

*Make ur payment before the end of free pages*

_Halysaah is just 500 naira_

07087865788 ✍

🏻

Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd9004

51c8e6

✨✨

HALYSAAH✨✨

By _Khaleesat Haiydar_✍

🏻

13....

Har Khaleesat ta fita daga gidan zuwa Supermarket Housemate dinta bai tashi ba, bayan ta dawo sai bata gansa a parlor ba alamar ya shiga dakinsa, kafin karfe hudu da rabi na yamma Khalees

at ta gama miyan da take, tayi dishing ma Safiyyah abincin a warmer din da zata kai mata, kan kace me aroma din girkin ya cika gidan, ko tuwon bata ci ba ta tafi dakinta tayi wanka tayi alwala tayi sallan la'asar sannan ta shirya, fitowa parlor tayi ta nuf

i kitchen, tsaye ta ga Housemate dinta ya jingina da cabinet din kitchen din idonsa a lumshe, ya dora lipton a gas, tace "Bacci kake a kitchen din?" Bude ido yayi ya juya ya kalleta yace "Not at all" Tace "To me kake yi?" Ya dan shafa kansa yace "I am havi

ng a terrible headache" Tayi kasa da murya tana kallonsa tace "Ka sha magani?" Ya kashe gas din yace "Zan sha" Tace "To in sa maka abinci?" Yace "What did you cook?" Tace "Tuwo...." Bai jira ta karasa ba da sauri yace "A'a, Alhamdulillah, am full" Murmushi

tayi tace "To ai ba miyar kuka bane, vegetable soup ne" Tana fadin haka ta bude masa tukunyar miyar tana kallonsa, bayan ya ga miyar a hankali yace "Ohk, but let me dish the food my self" Ita dai bata ce masa komai ba ya dau plate ta nuna masa inda tuwon

yake, kallon dan tuwon da ya zuba ta dinga yi, sai kuma tace "Wannan dan kadan din?" Without looking at her yace "Zai isheni" bata sake cewa komai ba ya zuba miyar a gefe with just one protein ya saka spoon a gefe, sannan ya dau mug ya debi lipton da ya da

fa ya dau plate din tuwon yace "Thank you" Bin sa tayi da kallo har ya fita daga kitchen din. Ko da ta fito parlor da abincin Safiyyah ta samesa zaune kan kujera bai fara cin abincin ba, ya daga kai ya kalleta, ta dau handbag dinta dake saman kujera, yace

"Are you going out with food?" Tace "Yea, kawata zan kai ma abinci she is sick" Yace "Ohk Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har kusan Magrib Khaleesat na tare da Safiyya, sosai jikin Safiyyah yayi sauki sai labari take ma Kha

leesat da tayi shiru hankalinta baya kan hirar, da ta tuna maganar da Ummanta tayi mata jiya da kuma abinda Abdul yace mata da ta kirasa daxu sai taji duk duniyar tayi mata zafi babu abinda ke mata dadi a rai, Safiyyah da ta kula da yanayin Khaleesat tace

"Wai me ke damun ki ne kawata?" Khaleesat ta kalleta, sai kuma ta dan yi murmushi tace "Bakomai Sophie, kawai na gaji ne sosai har na fara jin bacci" Ba don khaleesat bata son gaya mata damuwarta bane yasa tace mata haka sai don bata son fadin damuwar tata

a wnn lkcn, but tasan dole zata gaya ma Safiyyah abinda ke faruwa, Safiyyah tace "To ki kwana a nan mana

tunda bamu da lectures gobe, it's already pass 7 yanzu" Khaleesat ta dan bude ido tace "In kwana a ina? A'a ni dai kin ga tafiyata" duk yanda Safiyyah

ta so convincing Khaleesat ta kwana gidan, khaleesat ta ki sauraronta tayi sllhn magariba ta kama hanyar gida, dama tun da ta kawo tuwon da tayi ma Safiyyah daxu Mustapha ya shigo har dakin ya diba ta zama uncomfortable zama a gidan, matarsa kuwa ta kasa

ta tsare a parlon gidan, ko da ta fito parlorn ita kadai ta samu zaune fuska a murtuke, Khaleesat tayi mata sallama ita dai har ta fita daga gidan bata ji ta amsa mata ba. Khaleesat na isa gida ta kulle kofar parlon ta karasa ciki tana kallon plate din dak

e saman kujera da yayi covering with another plate, mug din shayin ma na ajiye bai sha ba, ta tafi ta bude plate din tuwon taga bai ci ba, abinda ya fada mata a kitchen ne daxu ya fado mata that he is having headache, ta juya tana kallon kofar dakinsa, tan

a tafiya a hankali ta nufi dakin tayi knocking gently, sai da ta sake knocking jin bai amsa ba ta

ɗ

an bude kofar slightly, bacci ta gansa yake yi saman gado, ta sauke idonta kasa, lkci daya ya bude ido yana kallonta, ta

ɗ

an koma baya kamar mara gaskiya tan

a kame kame tace "Are you okay?" Kansa kawai ya nuna mata ta karasa cikin dakin ta duka ta side dinsa da damuwa tace "Baka sha maganin bane?" Bai yi responding ba hakan yasa ta kai hannu kusa da forehead dinsa sai dai bata ta

ɓ

a sa ba, amma she could feel h

e is running temperature, a hankali tace "Should i order an Uber ride sae kaje asibiti?" Ya girgiza mata kai idonsa a lumshe, rasa abinda zata yi tayi, lkci daya taji hankalinta ya tashi, mikewa tayi ta fita zuwa dakinta ta dau karamin towel tayi soaking d

insa da ruwa bayan tayi squeezing ta dawo dakin, ta nufi inda yake kwance ta duka kusa da shi ta dora karamin towel din da ta linke saman forehead dinsa, ya bude idonsa, cikin sanyin murya tana kallonsa tace "In yi ordering ride din?" Ya dafe towel din da

ta dora masa a forehead yace "Don't worry Halysaah" ita dai kallonsa kawai take, can ta tuna tana da pain reliever a daki, mikewa tayi dai dai nan taji kamar ana kwankwasa kofa a parlor, ta juya ta nufi kofar ta fita zuwa parlorn, tsaye tayi bakin kofar pa

rlon tana tambayar waye at the same time tana bude kofar, ta

ɗ

an koma baya tana kallonsa with surprise, shi ma daga sama har kasa yake kallonta hannunsa rike da wayarsa, su biyu ne tsaye bakin kofar, lkci daya ta hade rai tace "How may i help you?" Kai tsa

ye shi wanda yake mata kallon sama da kasa ya shigo parlon har sai da ta matsa gefe da sauri kar ya bangajeta, shi dayan mutumin dake tsaye bakin kofar calmly yace "Hello, plss is Jay in here? Ahmad Jay...." Mutumin da ya shiga parlon ya juya yana masa wan

i kallo yace "Kaii wajenta ka zo halan?" Shi wanda ke waje ya

ɗ

an yi murmushi ya shiga parlon ya sauke kai kasa, amma sai ya tsaya daga bakin kofar bai karasa can cikin parlon ba, shi ko wanda ya fara shigowa har ya nufi hanyar dakunan dake apartment din,

da sauri Khaleesat ta nufesa a fusace tace "How will you just barge into someone's apartment without excuse or an explanation?" Juyawa yayi ya kalleta from head to toes, ita kanta bata san me yasa ta tsaya

ɗ

an nesa da shi ba taki ci gaba da bin sa ba amma

bata fasa masa kallon da take masa ba fuska a daure, ya gyada kai ya ci gaba da tafiyarsa kamar yasan dakin, kawai taga ya bude ya shiga ciki, ta juya ta kalli mutumin dake tsaye har sannan a parlor tace "Ku haka ake yi daga inda ku ka fito?" Cikin nutsuwa

mutumin yace "We are sorry Madam, location shi Jay din ya tura masa wai bashi da lafiya and here is the location sannan mun ga motarsa a garage din apartment din nan, hope we are in the right place?" Khaleesat tace "Sai bayan kun shigo za ka tambayeni ko

kuna right place din?? Where Is it done this way?" Mutumin ya hade hannunsa biyu alamar bada hakuri yace "Kiyi hakuri dai" Yana fadin haka ya bi bayansa ya shiga har cikin dakin shi ma, bin su tayi amma ta tsaya a corridor, ji tayi wanda ya fara shiga daki

n da farko na cewa "Jay me kake yi a gidan nan da wannan karamar yarinyar da bata da manners? Is this the reason why ka dena zama 24/7 a gida yanzu? When did u start this useless life? First of all who is the little brat i want to know?" Da wani expression

yake kallon Jay dake fama da kansa a kwance yaki basa amsa, shi dai mutumin da ya shigo a karshe na tsaye daga daya gefen Jay yana masa sannu, sai kuma ya kalli Ajay calmy yace "Kaga dai bashi da lafiya yanzu Ajay, all this question isn't necessary now" D

a kyar Jay yace "Ka kyale

ɗ

an iska mana, laifina ne da na tura masa location" Ajay dai sai bin dakin da kallon mamaki yake yi ganin property din Jay

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login