Showing 228001 words to 231000 words out of 641791 words
fi maki, you are not a kid Khaleesat, kinsan sonki Jawwad yake, so me tsanani kuwa" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba, sai ku
ma a hankali tace "Kinsan me Sophie?" Safiyyah na kallonta tana washe baki tace "Ina jin ki" After some seconds Khaleesat tace "Abdul came to my apartment yesterday night" Mikewa Safiyyah tayi ba tare da tasan ta yi hakan ba a tsorace, tana kallon Khaleesa
t with shock all over her face tace "Waye kuma Abdul? Did you have another frnd that is Abdul by name da ban sani ba?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta, cikin sanyin murya tace "Abdul dai guda da kika sani" Safiyyah tace "Na shiga uku na lalace, Abd
ul tsohon mijin ki wai kike nufi?" Khaleesat ta kasa ce mata komai, Safiyyah ta koma ta zauna tana kallonta da wani expression tace "Ta yaya yasan apartment din ki Khaleesat? Kuma me yaje yi maki a apartment? Don Allah ki min bayani yanda zan gane, i am lo
st...." Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Wallahi ban san ta yaya yasan apartment dina ba Sophie, ni kaina i am still shock up till now, ko breakfast na kasa yi saboda tsoro, yanda kika san an jefo sa" Safiyyah ta maida jakarta gefe tace "Innalil
lahi wa inna ilaihi raji'un, ji min shege
ɗ
an iska, to wai uban me yaje maki a apartment din, tell me what happen da yaje, ke kuma da yaje kofa kika bude masa ya shigo?" Khaleesat tace "Bayan Housemate dina yayi dropping dina a gida ya tafi ana ruwa, after
like 10 mins sai aka danna bell, to na mance jakana a motar Housemate i was thinking shi ne ya dawo ya kawo min jakar, da na sauka downstairs sai na bude kofa kawai, ashe Abdul ne" Safiyyah da tayi mitsi mitsi da ido tana sauraron Khaleesat tace "Go on, i
na jin ki, sai aka yi yaya?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "I was very shock and afraid bayan na bude kofan ya shigo, shi ne na shiga kitchen da gudu dama wayata na hannuna nayi dialing number Ya Junaid, sai gashi ya biyoni kitchen din ya karbe way
ar" Buda baki Safiyyah tayi tana kallonta da firgici a fuskarta, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaya mata duk abubuwan da Abdul yace mata a kitchen din bayan da ya sameta a ciki, da kuma yanda Ajay ya zo gidan duk bata boye mata komai ba.... Safiyyah na g
irgiza kai tace "Amma kin bani mamaki Khaleesat, yanxu shi Abdul har wani abun tausayi ne shi da zaki boyesa a apartment dinki? Abdul fa???" A hankali Khaleesat tace "Ce min fa yayi in tuna alkhairansa gare ni Sophie, kuma he look afraid also baya son Ajay
ya gansa, shi ne yace in rufa masa asiri" A fusace Safiyyah tace "Wani shegen alkhairin yayi maki da zaki tuna? Harrassing dinki da ya dinga yi ko kuma gorin da yake lafta maki da walakanta ki da yake yi? Nan nan ranan kika bani labarin zaman ukuban da ki
ka yi a gidansa kafin ya sake ki, da yanda ya bar ki da kwalin indomie ko albasa babu balle tarugu, marukan da ya dinga maki da zagin cin mutunci ne alkhairin da zaki tuna game da shi? Mutumin da ya ci mutuncinki ya sake ki bayan ya samu abinda yake so a w
ajenki har shi ne abun tausayi Khaleesat? Yanxu kina nufin kika boye Abdul har washegari a apartment din ki kika bar Ajay da gadin ku? Ikon Allah, Gaskiya baki ta
ɓ
a bani tsoro irin yau ba Khaleesat, i fear who no fear you, me yake damun ki ne haka?" Khalee
sat da duk jikinta yayi sanyi tana kallon Safiyyah tace "Safiyyah kar ki manta this is America, we are not in Nigeria, Ya Junaid na lura temper dinsa a kusa yake, yana da zuciya sosai, what if yaje ya masa wani illa wajen dukansa don nasan definitely bazai
kyalesa ba idan ya gansa a gidan, kina tunanin idan yayi masa wani abu za a kyalesa ne a kasar nan? dole doka zai yi aiki a kansa, kuma duk saboda ni sai haka ya faru Sophie??" Safiyyah ta wani kalleta tace "Sannu me hangen nesa, da duk baki san da hakan
ba kika doka masa kira? Why did you call him at the first place idan ba don ya zo ya fitar maki da Abdul ba?" Hawaye ya cika idon Khaleesat tace "Ai a sannan ban san da wani Intention ya zo min gida ba, kinga if he just came to harm me wannan daban ne, amm
a he meant no harm he was even afraid, banda haka ai bazai rokeni kar in gaya masu ya zo gidan ba" Safiyyah tayi wani murmushi tace "Maa sha Allah, kinga shawara daya kawai Abdul ya koma Nigeria ya bada sabon sadaki a kara daura maku aure kije can ku karat
a, tunda yanxu kam ya tuba kuma har kin yarda da tubansa kina mugun tausayinsa a rai, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu yawa" Khaleesat ta hade rai tace "Come off it Safiyyah, ni nace maki i am ready to accept his repentance? Ko sake daura min aure
aka yi da shi ba sai dai a kai gawata gidan ba, how will I forget what i went through so soon Safiyyah, wallahi kawai kalman alkhairi da ya furta ne da kuma irin sigar da naga ya zo min yasa na rufa masa asiri, ni ba butulu bace bazan ce Abdul bai min abu
buwan Alkhairi ba a rayuwata, in ba don shi ba yaushe har ma zan zo kasar nan in hadu da su Housemate dina? I lacked nothing tun da Abdul ya kawo ni kasar nan karatu, don har nafi wasu da iyayen nasu ke daukar nauyinsu, kinga bazan ce Abdul bai min wani ab
un alkhairi ba, kuma bazan ta
ɓ
a iya biyansa abinda yayi min ba, ki fahimce ni plss Sophie, ba wai nace ya kamata in sake kulasa bane, don wallahi ko ganinsa bana son yi don hakan na fama min ciwon dake zuciyata..." Safiyyah ta tabe baki tace "Tun da kin ru
fa masa asiri kin ga yau ma nasan yana can bakin apartment din naki yana jiran ki, hauka ake zan rufa ma Abdul asiri idan ni ne a shoe din ki? Abdul fa? Ai ko duk alkhairan duniya yayi min wallahi bazan rufa masa asiri ba sai dai Allah ya yafe min kawai, M
onster in form of human ne fa Abdul, gaskiya kin ci amanar Junaid, kin cuce sa, kuma da ya kuskura yasan abinda kike boyewa a gidan nasan ko ciki daya ku ka fito da shi bazai sake barin wata alaƙa ta hada ku ba har abada, kuma bazai ta
ɓ
a yafe maki ba, in k
ina tsoron kar Ajay ya masa illa me ya hanaki kiran 911?" Khaleesat dai tayi shiru tana bin inda suke zaune da ido, Kawai ganinsa suka yi a gabansu, ta rike numfashi tsabar yanda tayi shock tana kallonsa babu ko kiftawa, Safiyyah da ita ma ta gwalo ido tan
a kallonsa da mugun mamaki ta mike tana huci tace "Kai bawan Allah lafiya muna zaune zaka tsaya mana a kai, ko dai batan hanya kayi ne?" Sau daya ya kalli Safiyyah sannan ya mika ma Khaleesat wayoyin dake hannunsa guda biyu yana kallonta, daya na Jay daya
na Ajay, Khaleesat ta wani hade rai tace "Abdul kaga bana son muyi creating scene a nan, kindly stay away from me, are you even okay? Meye zaka dinga bibiyata?" Safiyyah ta figi jakarta tana kokarin ciro wayarta tace "Idan ban kira maka 911 ba Allah ya tsi
ne min albarka...." Tana ciro wayar ya fixge daga hannunta yana kallonta da kyau yace "Wajen ki na zo da zaki kira min 911 Malama?" Safiyyah ta kundumo wani zagi tana kallon Khaleesat tace "Kin dai ga crook din da kika ji tausayi har kika boye a apartment
din ki kar Ajay ya gansa ya jibgesa ko, kin ta
ɓ
a ganin inda shedan ya tuba dama? Shey u can see the useless monster you are pitying har da boyesa kar a dokesa?" Abdul na mata wani kallo yace "Hey watch your tongue, idan ba haka ba i will teach you a bitter
lesson Billah, Ajay kika kirasa ko? To ya zo ya dokeni tunda ni statue ne, ina ga shi ko gidan dambe bai ta
ɓ
a zuwa ba, ki je ki tambayi wanene ni a Lagos..." Khaleesat ta maida box din zobenta cikin jaka sannan ta mike ta amshe wayar Safiyyah dake hannuns
a, ta dau jakar Safiyyah da nata ta fara janta su bar wajen, banda zagi babu abinda Safiyyah ke kunduma ma Abdul idonta rufe tana cewa "Munafuki kawai algungumi, wato saboda ka san tana da tausayi shi ne ka dawo sumui sumui da kai kamar na Allah zaka kara
yaudaranta ka cuceta, har kana cewa ta rufa maka asiri, to kuwa sai na tona asirin nan naka wallahi, shegen duka za ayi maka da zai sumar da kai, in ka farfado ka siya ticket ko koma gida kayi jinya, tsabar baka samu daman ci gaba da musguna ma kawata ba h
ar da rama sai da kayi kamar me ciwon Aids, to wallahi in baka fita harkar Khaleesat ba sai nayi maka abinda har ka koma ga Allah bazaka manta ba, mugu azzalumi kawai" Gaba daya attention din mutane ya dawo kansu a wajen, Abdul yayi wani murmushi yace "Sai
kinyi regretting duk kalaman nan naki wallahi, sai na sa an lalata maki rayuwa i promise you this...." Khaleesat dai ta samu ta ja Safiyyah suka bar wajen gaba daya, banda rawa babu abinda jikinta yake yi don tsoro, Safiyyah ta warce hannunta tana kallont
a a fusace tace "Kin dai ga
ɗ
an iskan da kike tausayi ko? ashe da sabon salo kawai ya dawo don ya samu attention din ki, ke kuma ga sarkin masu tausayi, to kuwa rabon a karyasa yasa ya dawo Amurka don wallahi Ajay karyasa kawai zai yi" Khaleesat ta zauna t
a rufe fuskarta da hannunta tana kuka a hankali, gaba daya ta gama tsorata, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, zaman apartment din nata ita kadai ya fara bata tsoro kuma, can ta kalli Safiyyah dake ta bambami cikin rawan murya tace "Sophie ko dai in ma Y
a Musty magana da kaina ki dawo apartment dina da zama tunda exams za mu fara? Wallahi bazan iya zama ni kadai ba kuma a gidan nan Sophie, i am afraid..." A fusace Safiyya tace "Ai baki zama afraid ba tunda har kika iya boye kasungumin
ɗ
an daba a gidanki y
a kwana, Abdul har abun yarda ne bayan duk mun san
ɗ
an iska ne shi? Wani dadin baki zai maki har ki yarda da shi? Kin dai ga abinda yayi min ai yanxu, dama kuma me hali baya ta
ɓ
a fasa halinsa" A hankali Khaleesat tace "To ko dai in yi ma Ajay bayanin abind
a ya faru jiya kar ya zo ya gano yaji haushina? Wallahi i am so confuse Sophie" Safiyyah tace "To nima naji haushin ki balle Ajay da yayi gadin ke da Abdul ku ka sharbi baccin ku? ai wallahi kin cuce Ajay kuma sai Allah yayi masa sakayya" Khaleesat ta goge
hawayen gefen idonta tace "To amma sai dai inje can gidan nasu in masa magana ko? Don kar yaje yayi misinterpreting dina ta waya idan na kirasa, i want to explain to him ta yanda zai gane" Safiyyah tace "Dama ai gwara ki samesa face to face kiyi masa baya
ni, sannan kar ki kuskura ki ce masa a gidan Abdul ya kwana don daga nan zai fatattake ki ya kora ki, ko ya hadaki da karensa ya kora ki, inda Ajay ke burgeni kenan wallahi, no nonsense Man kike ji, sam baya daukan wargi, tsayayyen namiji kenan, kawai ce m
asa zaki yi kin shiga kitchen zaki zuba abinci sai kika ga kamar Abdul a jikin window din kitchen dinki yana kallonki, shi ne duk kika rude kika kirasa jiya da daddare, daga baya kuma kika ga wajen wayam ba kowa, amma da ya zo sai baki gaya masa hakan ba t
unda baki tabbatar ba kin zata hallucination kawai ki ke yi don dama kanki na ciwo jiyan, sai ki ce masa yau kina department muna zaune ni da ke kawai sai ga katon a gabanmu, ashe jiya shi din dai kika gani a jikin window, kinga ai maganata tayi making sen
se akan ki ce masa ai boyesa kika yi a daki jiya...." A hankali Khaleesat tace "To bari inyi order din Uber zuwa gidan" Safiyyah tace "Sannan idan kin je gidan ki fara masa godiyan gadin ki da yayi jiya ya hana kansa bacci, don nasan ba hankali gare ki ba
kina iya zuwa ki fara maganar da ya kai ki kanki tsaye...." Khaleesat ta ciro wayarta za tayi order din Uber da zai kai ta gidansu Ajay, kafin tayi order din ta kalli Safiyyah tace "Ko zaki rakani mu je mu biyu?" Safiyyah ta rike ha
ɓ
a tace "Wa?? Ni? Salon
inje ya koro ni mutumin da ba kirki ne da shi ba, a'a wallahi bazan je ba, ko kadan bai ta
ɓ
a burgeni ba dama ni, tun farko tamu bai zo daya da shi ba don na tsani mutum fitinanne, da dai Housemate ne sai in bi ki mu je, kuma banda ma yafi Housemate zafi me
zai sa ma a sako sa cikin wannan case din, to tsorona muna iya sako Housemate yaje ya fara ba Abdul din hakuri kinga ai lamari ya lalace kenan, babu dai yanda muka iya Ajayn zaki je ki sama duk da mugun halinsa, ayi mutum ace bai son mutane kullum yayi ta
daure fuska yana fushi shi kadai" Khaleesat na kallon Safiyyah cikin sanyin murya tace "Ko dai kawai in gaya ma Housemate in kyale Ya Junaid din?" Safiyyah ta wani hade rai tace "Wani Housemate, hakuri kike son ya tafi ya ba Abdul din kenan yanda zai ji d
adin ci gaba da iskancinsa, ai karki kuskura ki gaya ma Housemate he won't help matters at all, gwara Ajay no nonsense, tsaf zai mana maganin Abdul, amma Housemate ai har durkusawa sai ya iya yi ya ba Abdul din hakuri yanda suka yi ma Aymaan shi da Ya Must
y, Ajay ai shi ne namiji" Khaleesat dai bata ce mata komai ba tayi order din ride din, Safiyyah ta zaro ido tana kallon hannun Khaleesat tace "Ina zoben naki? Mun shiga uku ko dai Abdul din ya kwace?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ga fa shi
nan a jaka" Safiyya tace "Atoh, don ni yanda na gansa wujiga wujiga anya karayar arziki bai fada masu ba kuwa, kamar wanda yake yunwa duk ya rame sai idanuwa da hanci, da kyar idan ba talauci a tattare da shi" Khaleesat dai bata tanka Safiyyah ba, Safiyya
h tace "To ki saka zoben mana, ko jere zaki yi da shi a gaban madubi?" Khaleesat ta bude ido sosai tace "Ina zan je da zan saka zobe Sophie?" Safiyyah tace "Ke dai kin ki wayewa a rayuwarki Khaleesat, ba don gayu ya siya maki ba dama?" Warce jakar tayi ta
ciro box din zoben tace "Dalla ki saka" Khaleesat tayi murmushi ta amshi zoben ta saka tana kallonsa admiringly, cif ya zauna mata ta kalli Safiyyah dake ta murmushi ita ma kamar bakinta zai yage tace "It's sooo cute, gaskiya Housemate is so romantic, har
na hango kun yi aure, wallahi kashe ki zai yi kawai da soyayya, in soyayya ne a bar ma Housemate kawai, in kuma kwato hakki ne a bar ma Ajay" Dariya sosai ta ba Khaleesat, kawai ta mike bayan ta maida wayarta da empty box din zoben cikin jaka, Safiyyah ta
rakata har zuwa inda Lyft dinta ke jira, ta bude motar ta shiga, hannu ta daga ma Safiyyah dake ta murmushi tana kallon zoben yatsanta dake ta kyalli, a haka Lyft din ya bar wajen, tun da suka kama hanya Khaleesat ke ta waige waige to be sure babu motar da
ke bin su a baya, don ita kam yanxu duk a tsorace take, tunda har Abdul ya iya gano apartment dinta to babu kuma abinda bazai iya yi ba, har dai suka isa bata ga alamar ko wani mota dake biye da su a baya ba, ta sauka daga lyft din tana tafiya a hankali ta
shiga compound din, it's almost 4pm na yamma, motar Ajay ta fara gani a parking space din gidan, sannan ta ga motar Jay ma alamar duk suna gidan, walking slowly ta karasa har entrance din parlon dai dai sanda aka bude kofar parlon, ta
ɗ
an koma baya tana k
allon Housemate dinta dake kallonta da mamaki, cikin dubara ta boye zoben finger dinta da veil dinta kar ya gani, tana kirkiran murmushi a hankali tace "Good evening" Yace "Evening Housemate, come in" Ta sauke kanta kasa ta bi bayansa har zuwa cikin parlon
, ta zauna kan kujera shi ma ya zauna yana kallonta hoping all is well don sai yaji gaba daya hankalinsa ya tashi ganinta a gidansu, jin tayi shiru yana kallonta yace "Hope all is well Housemate?" Tana murmushi tace "Alhamdulillah, babu komai, Ya Junaid ya
na nan? I came to greet him" Jay yayi shiru yana kallonta, after some seconds yace "Yeah, he is upstairs" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ohk, i want to meet him" Jay ya gyada mata kai yace "He is at the parlor upstairs, ki samesa a can" A hankali tac
e "Sai na je sama?" Jay ya mike yace "He