Showing 564001 words to 567000 words out of 641791 words

Chapter 189 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

174

lafiya, yasa ayi aikin a sa'a" Yace "Ameen Aunty" Kallon Khaleesat yayi yace "I will wait for you outside" Daga

haka ya mike ya kara yi ma Aunty Farida sallama ya fita daga parlon, mikewa Khaleesat tayi ta koma kusa da Aunty Faridah tana murmushi tana kallonta tace "Aunty kin ga kyan da kika yi kuwa?" Aunty Farida ta mata wani kallo, Khaleesat ta kyalkyale da dariy

a ta mike ta shiga dakin Aunty Faridah, girgiza kai Aunty Faridah tayi tana murmushi ta tashi ta bi bayanta zuwa cikin dakin. Gun Mai martaba ne waje na karshe da Ajay da Khaleesat suka tafi don yi masa sallama, Sarki kallonsu kawai yake a parlon bayan Aja

y ya sanar masa za su tafi, Khaleesat dai kanta na kasa tana wasa da veil dinta, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Surgery din da healing duk bazai wuce wata daya ba ai ko?" Ajay ya daga kai ya kallesa yace "Haka ne ranka shi dade" Mai mart

aba yace "Nan da wata dayan za ku dawo kenan?" Ajay ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds a hankali yace "Ina son za mu zauna a can na wani lokaci ranka shi dade" Kallonsa Mai martaba ya dinga yi babu ko kiftawa, bayan wani

ɗ

an lokaci calmly yace

"Har na wata nawa?" Ajay bai ce komai ba, Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma kasan ba mu je can Benue wajen mutanen can ba Ahmad, kar ka zama me mance alkhairi mana" Ajay ya girgiza kai yace "Wallahi ban manta ba ranka shi dade, ko jiya mun yi m

aganar da Mukhtar, nayi bincike na gane local govt din wajen har da sunan garin, nace zan tura masa kudi ya kai masu kafin mu dawo, i still can't bear journeying on water for now ur highness, I think I've got Aquaphobia for now, kuma dole sai an bi ta ruwa

za aje garin" Mai martaba ya gyada kai a hankali yace "I understand Junaid, ko baka nan za mu je garin da Mukhtar din in sha Allah, jiya ma DSP Bilyamin ya ajiye min message ta WhatsApp zai shigo Bauchi gobe, kasan 2 days ago na siya masa motar 25M, and h

e appreciate it so much..." Ajay na kallon Mai martaba yace "Allah ya kara budi ranka shi dade" Mai martaba yace "Ameen, amma ina son in an gama Surgery din ka samu lafiya ku dawo Nigeria, idan ma baza ka zauna a Emirate ba you can stay outside of the Emir

ate bazan hana hakan ba yanxu, ka zabi duk inda kake son ka zauna da matar ka...." Ajay ya gyada masa kai a hankali yace "To in sha Allah ranka shi dade, Allah ya kara girma" Mai martaba dai kallonsa kawai yake cause he can't bear Junaid being far away fro

m him again, America yayi nisa kuma baya son wani abu da zai sake sa

ɗ

an nasa yayi nisa da shi, Mai martaba ya kalli Khaleesat da kanta ke kasa har sannan, sai kuma ya kalli Ajay yana nuna masa ita yace "Ka ga Jiddah..." Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat

, Calmly Mai martaba yace "Ɓacin ranta

ɓ

acin rai na ne, a duk sanda kayi kuskuren bata mata rai, to ka sani wallahi ni ka

ɓ

ata ma Ahmad, don haka try all possible best to avoid hurting her by all means, kuma ka sani ko da ka ci amanarta wataran ko da raina

ko babu raina to wallahil Azeem amanata ka ci" Khaleesat ta ji hawaye sun kawo idonta, shi dai Ajay kallon Mai martaba kawai yake a sanyaye, Mai martaba ya girgiza kai yace "Ko da wataran ka ji kana son kara aure to Ahmad ka sani ba da son raina zaka yi a

uren nan ba, ba kuma da goyon bayana zaka yi auren ba, kawai dai babu yanda na iya ne saboda addininmu ya yarje maka da karin auren, amma baka da goyon bayana idan har hakan ta kasance, yanda nake jin 'ya yan da na haifa a cikina haka nake jin Jiddah, she

means a lot to me, don haka ka guji duk wani abu da zai bata mata rai, yin hakan tamkar ka guji

ɓ

acin raina ne, ita kuma na yarda da ita nasan bazata ta

ɓ

a sa

ɓ

a maka da gangan ba sai dai bisa kuskure, ina kuma fatan Allah Ubangiji yayi maku albarka, ya baku

zaman lafiya na har abada ya baku zuri'a masu albarka, but know that Jiddah is dear to me Ahmad..." Ajay ya sauke idonsa a hankali maganganun Mai martaba na sinking cikin kansa.

HALYSAAH...,

Bayan Ajay sun fito bangaren Mai martaba ya kalli wayar hannu

nsa dake vibrate ya ga Jay ne ke kiransa, tun daxu Jay ke waje yana jiran fitowar su, Ajay ya kalli Khaleesat ganin hanyar part din Hajja ta nufa yace "Ina kuma za ki wife?" Ta juya ta kallesa tace "I want to meet Hadiyah, ba mu yi sallama da ita ba" Bai c

e mata komai ba ya bi ta da kallo har tayi corner sannan yana tafiya slowly ya nufi hanyar fita waje, har sannan maganganun Sarki basu dena yi masa yawo a kai ba, tun Khaleesat bata karasa part din Hajja ba ta hadu da Hadiyah a hanya, Hadiyah tace "Na je s

ide din Mami naga baku nan" Khaleesat tace "Eh tun daxu muka bar part din, dama ce maki zan yi we are leaving now...." Hadiyah ta sauke ajiyar zuciya su ka ci gaba da tafiya a tare tace "Yanxu wata nawa za ku yi a can idan kun je?" Khaleesat na kallonta ta

ce "I don't really know... Na gan ki wani iri hope all is well?" Hadiyah ta daga ido ta kalleta,

ɗ

an murmushi tayi irin na karfin hali tace "Nothing, har naji na fara missing din ku wallahi...." Khaleesat tace "To ko za ki bi mu?" Hadiyah tayi er dariya ta

ce "A'a ai it's too late kuma, after the surgery zan zo in duba yaya in sha Allah" Khaleesat tace "Da gaske?" Hadiyah tace "Yeah, amma idan zan samu Visa within the period in sha Allah zan gaya ma Mai martaba sai in je" Khaleesat tace "To Allah ya sa ki zo

din" A haka suka fita har haraban gidan, Ajay da Jay suna jingine jikin mota suna jiran fitowar Khaleesat, Jay dai kallon Hadiyah yake har suka karaso wajen motar, Hadiyah na kallon Ajay da murmushi fuskarta tace "Yaya Allah ya kai ku lafiya, Allah kuma y

a baka lafiya" Ajay yace "Ameen" Ta juya ta kalli Khaleesat tace "We will speak on phone in sha Allah Halysaah, wishing you all safe trip and journey mercies" Khaleesat ta

ɗ

an yi murmushi tace "Thanks dear" Hadiyah bata yarda ta kalli Jay ba, ta juya ta ba

r wajen, Jay ya bude front seat ya shiga, dogarin dake tsaye wajen ya bude back seat da sauri, Khaleesat ce ta fara shiga motar sannan Ajay ma ya shiga dogarin ya kulle motar yana jera masu kirari tare da masu fatan Allah ya kiyaye hanya. Washegari da yamm

a sosai suka sauka kasar America, Lyft da Jay yayi order ya daukesu daga airport zuwa gida, Jay ya sauka daga Lyft din tare da drivern suka zaga bayan trunk din motar don fiddo da akwatunan su, Ajay dai kallon Khaleesat kawai yake ganin tayi nisa cikin tun

anin da take, ya kai hannu lap dinta yana shafawa a hankali in a romantic way, lokaci daya ta dawo reality ta juya da sauri ta kallesa, ya jingina jikinta murya can kasa yace "Tunanin me kike Slushie?" Tayi murmushi a hankali tace "Ina tunanin ranan farko

da na fara ganin ka ne" Ya

ɗ

an bude ido yace "Really, a ina kika fara gani na?" Ta saka hannunta cikin nasa slowly tace "A kofar gidan nan, dai dai inda Lyft din nan yayi parking is the exact spot da Ya jawwad yayi parking ranan da asuba, ka fito gida tare

da karen nan naku" Yace "Sai me ya faru?" Still smiling tace "A ranan na fara ganin ka, kawai naji gabana ya fadi sosai" Tana fadin haka ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, tana murmushi tace "Sosai fa gabana ya fadi da na gan ka th

at very night, shi ne na fara boye fuskata da mayafina da sauri, sai abun yake min kamar na ta

ɓ

a sanin ka a wani waje, bayan ni dai nasan ban san ka ba, ban kuma ta

ɓ

a ganin ka ba sai a wannan ranan, but you know what?? I just realized probably a mafarki na

nasan ka, i might have dreamt of you, shi yasa nake jin kamar na san ka da na ganka...." A hankali yace "You felt our connection right from day one Jeeddah, sign ne aka maki a ranan cewar i am the Man for you, ni kuma ranan ban ga fuskar ki ba, i only kne

w that a lady was sitting at the front seat" Ta jinginar da kanta a jikinsa a sanyaye tace "Har muka isa apartment dina gabana bai dena faduwa ba ranan, sai kuma muka hadu a eatry few weeks later, nan ma sai da naji gabana ya fadi da na gan ka, but before

then duk sanda ka kira Housemate dina zan tsaya in ta kallon number ka, tun ma ban gan ka ba, infact ban ma saba da Housemate dina ba a lokacin sosai, kawai dai on several occasions in na fito zan je kitchen sai in ga kana kiran wayarsa, cause he sometimes

use to neglect his phone on the sofa, I don't know ko yanda yayi saving sunanka ne yayi catching attention dina, ko kuma kawai don Allah ya rubuta kai ne future Husband dina, but I always stare at ur phone number anytime you call Ya Jawwad" Lumshe ido tay

i saboda yanda memory din komai ya fara dawo mata tiryan tiryan kai, a hankali yace "I have always felt connected to you tun daga ranan da na fara ganin fuskar ki Jeeddah, the birthday gift you gave to me was one of the best thing I appreciate till date, i

was so happy with the gift" Ta daga idanuwanta ta kallesa, muryar Jay suka ji dai dai side glass din back seat din yace "Ko dai ya maida ku airport din ne kawai?" Khaleesat ta

ɗ

an yi murmushi ta bude other side din motar ta sauka, Ajay ma ya sauka daga mo

tar, zata dau akwati daya Jay ya langwabar da kai yace "A'a ku tafi ku ci gaba da labarin ku, zan taho da su ai tun a Nigeria ni ke jigila da su" Er dariya tayi tace "A'a bari in dau karamin Yaya Housemate" Bata jira me zai ce ba ta dau karamin box din ta

nufi cikin gidan, Ajay dai yaki daukar komai yayi gaba ya bar Jay da boxes din. Har wajen karfe tara Khaleesat bata gama gyaran gidan da take ba cause the House was so dusty tunda babu kowa a ciki, a haka don ma Jay yayi assisting dinta wajen gyaran parlon

daga karshe ya

ɓ

ige da bacci kan kujera, bayan ta gama komai ta wuce sama zuwa side din Ajay feeling so exhausted, tun shigowarsu gidan ta fara gyara masa

ɓ

angarensa ya shiga kafin ta sauka downstairs ta fara gyare gyaren parlor, bata samu Ajay a parlonsa

ba ta kalli abincin da ya ci ya bari, ta karasa bedroom dinsa ta bude kofar a hankali ta shiga, ta gansa yayi rub da ciki cikin lallausan white bedsheet din kan gadon yana bacci, kana ganin yanda ya kwanta zaka san yayi missing gadon nasa, ta karasa ta ru

fa masa white duvet ta dau sauran fruits din da ya bari a bedside drawer ta fita da shi..... The next day da safe suka fita zuwa asibiti don ranan suke da appointment a John Hopkins Hospital dake nan Maryland, memories iri iri suka dinga dawo ma Khaleesat

during their ride to the hospital, tana ta kallon streets din Baltimore da yanda tayi rayuwa har na shekara hudu a garin, ta tuna farkon zuwan ta Maryland tare da Abdul, how her first 3 years went with Abdul sponsoring her education and Welfare, sannan had

uwar ta da Jay a apartment dinta tana dab da shiga final year a makaranta, few weeks da haduwanta da Jay kuma ta hadu da Ajay, how things suddenly took a quick U-turn and everything changed, but all this happened because of Abdul, shi ne sanadin komai da y

a faru a rayuwarta, wani ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tasan tayi hakan ba, Ajay dake gefenta ya juya ya kalleta, sauke idonta tayi, she felt like crying ta rasa dalili, amma ta dake bata yi kukan ba, but remembering her past got her so emotional, Ajay

ya kamo hannunta cikin nasa kamar yasan tunanin da take, ta daga kai ta kalli Jay dake zaune gaban mota, tasan she will forever be grateful to him and Abdul, ko ba komai ita bazata manta alkhairin Abdul a gareta ba, don alkhairinsa ya fi sharrin sa yawa,

he gave her a sound education, and she live a perfect life all through her first 3 years in Maryland bata ta

ɓ

a rasa komai ba duk da abubuwan da yake mata, he made sure she lacks nothing duk da halinsa, a haka suka isa John Hopkins Hospital aka yi admitting

Ajay don a ranan da yamma za ayi masa Surgery dinsa.... Smoothly aka yi ma Ajay surgery dinsa na raguwan fragments na bullet dake jikinsa, and they were in hospital for close to 3 weeks for the healing process, sosai Jay ke basa kulawa yanda ya kamata, do

n Khaleesat yawanci sai dai taje gida tayi bacci ta dawo da yamma, ranan da suka cika sati uku a asibitin ne aka yi discharging dinsu zuwa gida.

HALYSAAH

Wajen karfe biyar da rabi na yamma Ajay na zaune parlor tare da Jay a gefensa ya dora masa kafa y

ana shan fruit sai ga Khaleesat ta fito kitchen, ya bi ta da kallo for the countless time har ta tafi dinning area ta zauna tana danna wayarta da ta ajiye kan dinning table, girki take yi a kitchen shi yasa bata son tayi nisa da area din amma duk ta fito d

aga kitchen sai ya bi ta da kallo, in zata koma ma haka zai bi ta da ido, yanxun ma da ta fito lokaci lokaci yake kallon hanyar dinning din, tana lura da kallon da yake mata shi yasa taki kallon direction dinsu, gaba daya yaki concentrating kan football di

n da ake yi a TV, Jay ya dau remote ya canza tashar don shi ya dage sai an saka kwallo amma gaba daya hankalinsa baya gun kallon, Ajay ya juya ya wani kallesa, fixge remote din yayi yace "An gama ne zaka canza min" Yana fadin haka ya maida channel din zuwa

na kwallo ya ajiye remote din a gefensa yanda Jay bazai dauka cikin sauki ba, Jay ya wani kallesa bai dai ce komai ba ya bar sa da remote din, Khaleesat ta mike zata koma kitchen Ajay ya sake bin ta da ido, Jay yace "To ka shiga ka taya ta girkin mana" Aj

ay ya gyara zama ya sauke ƙafarsa daga jikin Jay yace "Ai bani da lafiya ne, i still don't have strength" Jay yace "Baka da lafiya amma inda hankalin ka yake daban ai" Ajay ya

ɗ

an kallesa yace "Ina hankalin nawa yake?" Jay ya buda hannu yace "Oho..." Yana

fadin haka ya jawo fruits din dake gabansu ya ci gaba da sha, Ajay ya maida kafarsa kan Jay yace "To ai ta gama girkin ina ga, ba sai an taya ta ba" Jay ya tura kafarsa yace "A'a je dai ka duba, tun daxu ma ya kamata kaje ka taya ta ai" Ajay ya mike kamar

jiran jin hakan yake ya nufi kitchen, Jay ya girgiza kai kawai yana murmushi yana shan grape din hannunsa, Ajay na shiga kitchen din ya tarar tana goge gogen kitchen din, duk da girkin ya dahu bata kai ga saukewa ba, ta juya tana kallonsa ya rufe kofar kit

chen din gently, sannan ya karasa ciki ya dau Glass din wine da ta ajiye kan kitchen island bata gama sha ba, yayi sipping wine din kadan sannan ya ajiye ya nufeta, ita dai kallonsa kawai take, yana isa inda take ya rungumota ta baya ya dora lips dinsa a w

uyanta murya can kasa yace "Taya ki aiki na zo yi wife" Murmushi tayi tace "Ko ba taya ni ba, sai da na gama zaka zo taya ni, ni dai ka fita don Allah, kaga Yaya Jawwad yana parlor" Yace "To ai shi yace in zo in taya ki" Dariya ya bata ganin inda yake kai

hannunsa a jikinta, ta fara nokewa tace "Don Allah ka bari, a haka zaka taya ni? Ni dai bari in zuba maka abincin ka je ka ci nasan yunwa kake ji" Yayi kasa da murya yace "I am eating the chef not the food...." Kunya sosai ya bata, ta marairaice tace "Don

Allah ka fita pls, Ya Jawwad fa yana parlor, kai baka jin kunya ne wai, bari in zuba maku abincin ka tafi maku da shi parlor" Bata rufe baki ba ya juyota ya jinginar da ita jikin Island din kitchen din ya hade bakinsu, ta kasa dakatar da shi nan da nan jik

inta yayi la'asar, ya fara kissing dinta gently, kasa daurewa tayi ta fara mayar masa da martani cause she misses his kiss so much, sosai suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login