Showing 162001 words to 165000 words out of 641791 words
you doing this to me Khaleesat? Why are you frustrating me?" Kasa ce masa komai tayi jikinta na rawa hawaye na zuba idonta, ta gaji da ce masa ita bata san abinda ke faruwa ba, cikin daga murya jikinsa na rawa yace
"Ki bani amsa? Me na maki kike wahal dani kike cutata haka?" Khaleesat dai ta kasa ce masa komai jikinta na rawa don tsoron magana ma take ya gaggaura mata mari, yana wani irin huci ya turata yace "Ki jika abun ki ki sha" Yana fadin haka ya sauka daga sam
an gadon ya saka Pajamas dinsa ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Khaleesat dai ta jawo duvet ta rufe jikinta har sannan zuciyarta na bugawa ta fashe da matsanancin kuka, bayan kusan minti goma taji fitar motarsa a gidan gaba daya. Da yammacin ranan
Momy na parlonta da Godiya sai ga Abdul ya shigo kamar an hankado sa, Momy na kallonsa tace "A'a Babana, sannu da zuwa" Juyawa yayi ya fice daga parlon ganin Godiya, Momy ta
ɗ
an zaro ido tana kallon Godiya sai kuma ta mike da sauri ta tafi kusa da kofar ta
bude tana leka corridor taga bangaren Abbansa ya tafi, ita ta dade bata gansa cikin irin wannan yanayin ba ma, ta kulle kofar ta dawo tana kallon godiya tace "Anya Godiya Malamin nan ba maye bane kuwa, kin ga dama yace Abdul zai zo yau gashi kuma ya zo di
n kamar an jefosa" Godiya tayi wani dariya tace "Ke ma dai wallahi sai kace yau Danger ya ta
ɓ
a maki aiki da zaki yi mamaki? Yanxu dai sai ki tashi kije ki dora masa girkin da ya fi so da maganin" Momy tace "Ikon Allah, in dai kana da kudin ka zaka ga aiki
da cikawa kawai, yanxu ki dubi yanda ya shigo mana a firgice kamar mara lafiya" Godiya tace "Ina kuwa lafiya dama an hanasa angwancewa da amarya, sai kace baki san maza in suka kwallafa rai kan wannan lamari ba" Suka kwashe da dariya gaba daya har da kyaky
atawa, Momy tace "Toh yanxu zan tura cikon aikin nan na karshe, yaushe zaki koma wajensa mu je tare in masa godiya" Godiya tace "Nan da kwana uku in sha Allah, kin ga bari in tashi in tafi mai gidana na hanyar dawowa yau" Momy tace "Haka fa kika ce, toh sh
ikenan sai mun yi waya dai kawai" A haka Momy ta raka Godiya har gun motar ta sannan ta dawo cikin gidan ranta fari ƙal, bangaren Alhaji ta nufa ta tarar da Abdul kwance a parlor idonsa a lumshe, zaunawa tayi gefensa tana kallonsa cikin kwantar da murya ta
ce "Babana baka da lafiya ne?" A takaice yace "Hutawa nake yi Momy, i need privacy pls" Momy tace "Toh shikenan, bari in sa a daura maka favorite din ka, ina Mamata fa?" Shiru yayi yaki ba Momy amsa, Momy ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo ko
far, sai a sannan tayi wani murmushi ta koma bangarenta zata dau maganin da Godiya ta kawo mata wanda zata zuba a cikin girkin abinda Abdul ya fi so, sai da ta kori mai aikinta can compound sannan ta fara girka masa Pounded yam da Vegetable soup, cikin miy
an ta zazzage duk maganin da kyauta ta kawo har kala uku, wajen karfe bakwai ta gama ta dau abincin ta kai masa dining table ta ajiye, dama iya cin sa kawai ta girka wato malmala daya kuma ba babba ba, miyar ma
ɗ
an tsut yanda zai cinye gaba daya, sai bayan
isha Abdul ya ci abincin da Momy tayi masa, ya bar ma mai aiki ta kwashe sannan ya wuce sama zuwa dakinsa, Momy ta fito dakin Meemah kenan ta bi sa da kallo har ya shiga dakinsa sannan ta bi bayansa, tana shiga dakin tace "Wai lafiya Babana? Ko dai akwai
wani matsalan da kake boye min ne" a takaice yace "Ba komai, zan shiga wanka" Yana fadin haka ya fara cire kayan jikinsa, Momy tace "To ka ci abincin?" Yace "Na ci" Momy na murmushi tace "You like it?" Yace "Miyan yayi dadi, but it's little" Tana murmushi
tace "To maa sha Allah, amma ai ya isheka dai" Yace "Ya isa" Tace "Toh je kayi wankan ka nima bari inje in ci abinci" Fita tayi daga dakin ya shiga bandaki, Momy na zaune parlonta tana cin farfesu dake cike cikin bowl din hannunta Abdul ya shigo, kallonsa
tayi ganin yanda ya shirya sai zuba azababben kamshi yake, tace "Har zaka tafi Babana" Yace "Eh, sai da safe" Tace "To ko in zuba maka farfesun ka kai ma Mamata" A takaice yace "A'a ni ba gida zan kwana ba" Momy tayi murmushi tace "To Allah ya tsare Babana
" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga gidan. The next 10 days a gidan Abdul was a living hell for Khaleesat, gaba daya Abdul ya sauya mata a gidan ya dawo kamar wani monster, dukanta da yace ya dena sai dai bai samu slightest opportunity din yin hakan ba,
kawai ya maida ta punching bag dinsa a gidan barin in ya zo gareta bai samu biyan bukata ba, kuma bai fasa zuwa mata da bukatar tasa ba amma as usual sai dai kawai ya doketa ya fita bai cimma burinsa ba, kwata kwata ya dena cin abincin gidan, ya dena kwana
sai sanda ya ga dama, duk wani ingredients din girki ya dena siyowa sai dai tayi ta cin indomie, hatta bottle water ma da ya kare yaki siyowa, kuma ko Satchet water yaki siya ya ajiye, sai dai ta sha ruwan pampo, gaba daya Khaleesat ta fita hayyacinta a g
idan ta dawo kamar ba Khaleesat ba, ga karyewa da gashinta ya dinga yi sosai saboda tsananin damuwa, kana ganinta kasan tana cikin jarabawan rayuwa, bata da aiki sai kuka sai kuma addu'a da sallan dare, gaba daya ta maida duk lamarinta ga Allah, kullum hak
a take kwana ta tashi da zazzabi amma ina taga fuskar ce masa bata da lafiya, sai dai tayi ta daurewa a haka, in ma ta gaya masa don ya zagi iyayenta ba komai bane a wajensa, in zazza
ɓ
in ya rufeta sai dai ta kwanta har sai sanda zata ji dama dama sannan ta
daure ta tashi. Ranan Friday tana dakinta a kwance ko breakfast bata yi ba har kusan karfe sha biyu da rabi, zuwa yanxu ta gaji da cin indomie da ma tana da dakakken yaji sai ta dinga yin ko shinkafa da mai da yaji ne amma babu, indomie duk ya fita a kant
a bata iya ci ko ta dafa, gashi haka take dafasa babu yaji balle albasa, bude kofar dakin nata yayi ta mike zaune da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, kamar zai fasa mata dodon kunne taji yace "Ina Cufflinks din da na bari a parlor shekaranjiya?" Sauk
a tayi daga kan gado, ita dai ta gyara parlon ta goge ko ina jiya da yau amma bata ga wani Cufflinks dinsa ba, a hankali tace "Toh bari in duba a parlon" Wani mugun kallo yake mata hakan yasa ta ra
ɓ
a tabi ta gefensa ta fita daga dakin zuciyarta na bugawa t
a tafi parlor tana dudduba Cufflinks din, da alama masallaci zai je don yin sallan juma'a, babu ta yanda za ace iya Cufflinks din da yake tambayarta yake da shi a gidan, amma sbda neman hanyar da zai musguna mata yake shi yasa zai saka ta gaba ta fito da a
binda bata gani ba, kuma rabonsa da gidan tun shekaranjiyan, tana cikin dube dube a parlon shi kuma yana tsaye fuskarsa a murtuke alamar he is loosing his patient aka bude kofar parlon, Momy ce ta shigo da Cousin sis din Alhaji Musa, warce suke kira da Umm
u, Yau kwanan Ummu uku a Nigeria daga Dubai inda take aure da yaranta duk a can, kuma a yau zata koma Dubai shi ne ta sa a kawota ta ga matar Abdul kafin a kai ta airport, duk da Abdul yaje ya gaisheta san da ta zo, Khaleesat da duk a rude take ta kalli Ab
dul a hankali tace "Wallahi ban gansa ba da nake gyaran parlorn jiya da yau, kilan ka sha'afa ko a daki ka bar su ne ka manta" Bata rufe baki ba ya sauke mata wani gigitattcen mari yana huci ya fixgota yace "Ni zaki gaya ma a daki na bar su?" Ta dafe kunci
nta hawaye cike idonta tana girgiza masa kai, nan da nan fuskarta yayi ja, ko minding uwar sa da Cousin sis din Babansa da suka shigo parlon bai yi ba, duk suka yi cirko cirko baki bude suna kallon ikon Allah, cikin tsawa yace "Baza ki fito min da shi ba s
ai na maki dukan tsiya a nan?" Tana shesshekan kuka tace "Nace maka ni ban ga wani links din ka ba wallahi...." Bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin, Momy da taji ranta yayi fari tass cikin kwantar da murya tace "Subhanallahi, Babana ka bi
a hankali, hakuri ake Babana" Ummu ta jefar da handbag dinta kan kujera ta nufesa cikin bacin rai tace "Abdallah?? kana hauka ne kake marin mace haka don uban ka?" Momy ta wani hade rai tana kallon Ummu, Abdul yaki ko kallon Ummu dake masa magana, ya wani
haure Khaleesat a mugun fusace har sai da ta fadi kasa, Wani Mari Ummu ta sauke masa a fuska, cikin fushi tace "Ashe kai jahili ne shashasha ban sani ba?" Juyowa yayi yana kallon Ummu da mamaki baya ko kiftawa, Momy ta dinga huci tana kallon Ummu ita ma,
nan da nan idanuwanta suka kankance don bacin dai, tunda ta haifi Abdul bata ta
ɓ
a marinsa ba haka ma ubansa sai gashi yau an maresa a gabanta, Abdul dake kallon Ummu kamar me counting din words dinsa yace "Ummu akan wannan jakar yarinyar kika mareni??" Umm
u tace "Na mare ka din, zaka rama ne? Wawa kawai mahaukaci ka saka yarinya karama haka a gaba kana duka? Tarbiyar da aka maka kenan? In na san abinda zan zo in tarar a gidan ka kenan uban me zai kawo ni?" Abdul da idanuwansa suka sauya launi ya kalli Khale
esat yace "Ki je... na sake ki" Yana fadin haka ya dau makullin motarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda yace ba, Momy ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "To Alhamdulil
lah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Ummu tace "Ke kuma Muhusina kin ci darajar Musa banda haka da babu uban da zai hanani rama ma
ɗ
a na marin da kika masa don tunda na haifesa ban ta
ɓ
a marinsa ba haka ma ubansa, kuma Abdul yayi min dai dai
hukuncin da ya dauka, dama me ake da auren er gidan talakawa er gidan matsiyata? Ai ba class din mu bace ita, kuma duk bama goyon bayan wannan tsinannen auren, kawai irin wannan rana muke ta jira gashi Allah ya kawo mu cikin ruwan sanyi, Alhamdulillah All
ah na gode maka, Allah na gode maka, yau zan yi bacci cikin farin ciki da kwanciyar hankali burina ya cika, effort dina kuma bai tashi a banza ba" Momy na kai wa nan ta nufi kofa tana tafiya gansan gansan farin ciki fal a ranta mara misaltuwa tana murmushi
ta bude kofar parlon, Khaleesat ta bi Momy da kallo with shock ko kwakkwaran motsi ta kasa tsabar mamaki, maganganun Momy suka dinga yawo a kanta kamar a mafarki, Ummu ta zauna gefen kujera ta dafe kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai a san
nan Khaleesat taji hawaye masu zafi na silalowa fuskarta, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta har kasa ta fito....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
👈🏻
, i
t's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atam
fa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....
All at affordable prices
Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.
whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM
HALYSAAH 51
Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace "Zo ki zauna tukun
na diyata" Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan c
arpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, s
annan yayi gyaran murya yace "Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don't think it's proper kiyi involving kanki sama ta ka, it's not done that way, alright? kuma tu
nda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce f
light din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?" Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa,
a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba
ɗ
an uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru
ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat
tace "In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko yaya?" Ummu ta kalli Momy
tana girgiza kai cike da takaici tace "Ki ji tsoron Allah Hajiya, ki ji tsoron haduwar ki da Allah, ke ma fa kina da yaran nan mata...." A mugun fusace Momy ta karaso cikin parlon ta dakatar da ita tana nunata da
ɗ
an yatsa tace "Kin ga wannan family issue
ne ki cire bakin ki a abinda bai shafeki ba Muhusina don ke bare ce a wannan
ɓ
angaren, kuma ba ke kika haifar min Abdul din ba da kike neman cusa kai abinda ya shafi rayuwarsa, who are you to even interfere? Ko Musa kin zata ya isa ya hana Abdul abinda ya
yi niyyar zai yi ne? To wallahi ki cire bakin ki da idonki akan abinda ya shafi zuri'ata, 'ya ya mata kuma dama ko wani shege ya haifa ai, meye a ciki" Momy na kai wa nan ta kalli Khaleesat cikin daga murya tace "Baza ki tashi ki san inda dare yayi maki ba
ko sai na kira su Meemah sun fitar min da ke daga gidan nan??" Mikewa Khaleesat tayi bata bari sun hada ido da Momy ba ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ummu ta kasa cewa komai tana kallon Momy tana girgiza kai, sai da Khaleesat ta fita daga compound di
n gidan gaba daya sannan ta fara share hawayen dake sauka idonta, tunanin yanda zata koma gida bata da ko sisi ta fara yi, tafiya me nisa tayi har ta iso titin da zata samu abun hawa, daga karshe bayan jiran kusan minti sha biyar ta samu wani adaidaita sah
un da zai kai ta Mariri a dubu biyu da dari biyar, in taje gida sai ta basa kudinsa, har Khaleesat ta isa gida hawaye ya ki tsaya mata a ido, ita kanta bata san yanda take ji a ranta ba game da abinda Abdul yayi mata, farin ciki take ko akasin haka har san
nan ta kasa ganewa a zuciyarta, but she was deeply hurt and pained, daurewa kawai take kar ta fashe da kuka a adaidaita sahun, bayan ya tsaya dai dai kofar gidansu ta sauka tace "Za a kawo maka kudin yanxu, nagode" Daga haka ta shiga cikin gidansu, a tsaka
r gida ta tarar da kishiyoyin Ummanta sun gama abincin siyarwansu na yamma yara za su fita da shi talla, ta gaishesu ba tare da ta bari sun hada ido da su ba direct ta nufi dakin Ummanta, duk suka bi ta da kallo, Aunty Farida da fitowar ta daga bandaki ken
an zata yi alwala don lokacin sallan La'asar yayi ta ajiye butan hannunta