Showing 102001 words to 105000 words out of 641791 words
hawayen dake zuba ido
nta, Jay that was shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty Farida na share idonta ta ci gaba tace "A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa ma mahaifin Khaleesat ankwa a
na jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai, duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka,
mun shiga tashin hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali, da kuma mutanen da ya taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja aka nufa da shi, bayan dogon binki
ce aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda
babu sa hannun Mahaifin Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota daya ko biyu, nan aka yi ta z
uga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi don ya ta
ɓ
a yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai
cucesa yace an sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake ba, bai cin kayan wani baya ta
ɓ
a abu in ba nasa bane, beside bai ta
ɓ
a sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai da iftila'in ya faru sannan yaga
me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince tunda sana'ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutu
nci bashi da kirki, sai da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan duk bamu yi bacci ba bayan
mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa don tun dauke mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda
ɗ
an jarin da nake da shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano
sau uku muna zuwa gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu Matarsa ranan ta rako baƙinta ta gan m
u tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore mu, na uku kuma
ɗ
an cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a 'ya yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka
kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ra
nan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara
tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari'ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotu
n tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke,
Alhaji Musa babban mutum ne kuma
me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani
ɗ
an jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a
nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ƙara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu
Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu
gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abind
a za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida,
bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci s
una ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shig
o gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari,
Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa d
on shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat"
*Halysaah is 500
via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
👈🏻
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Al
hamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai bu
ɗ
e a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!
😍
‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya bu
ɗ
e da kwalliya, tsafta d
a ƙamshi irin na sarauniyar zamani!
Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai
ɗ
aukar ido
Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-tu
rai, humra, incense da ƙamshi masu da
ɗ
i
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji da
ɗ
in wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.
Adireshi: Blo
ck 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.
Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki – ki ji da
ɗ
in sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG &
TikTok: @MGsBeautyLounge
*Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga me kasuwar garin Dutse Hajiya Aunty Zahrah da Hajjaju Sadiya Chamo Ex in-law, Hajiya Nafeesah Mom twins da Ummu Zainab Maman Ramla, Aunty Maryam Dan Ladi nasidi kema na gaisheki da katon murya, H
ajiya Zainurah Boss Lady, Hajiya Jumare da Hajiya Asmy me kayan amare, Oum Nabeelah, Mardiyyah, Uwar Janan, Halysah Garba
😂
i hail you all with respect yan Palace*
Manyan Membobin _❤
🩹
Khaleesat's Citadel_❤
🩹
*Su Meenah parrot
🐔
, Oum Noor, Nafeesah Jawwa
d, Rukayya, Fidomashi, Siyam, M manal, Mrs Barrister, Shanono Esq, Ummilos, Na'imatu, Zulaiha, Ummu Abdrhm, Khaleesat Haiydar is saying a big thank you to you all for ur support always, Allah ya bar min ku*
🥰
HALYSAAH 33
Aunty Farida ta numfasa a hank
ali tace "Da yake Abdul shi kadai ne namiji gun mahaifinsa, mahaifin ya dauki son duniya ya dora masa kuma bai jin maganar kowa sai nasa, duk abinda Abdul yake so shi mahaifinsa ke so, bayan yaga Khaleesat a kotu babu tantama zuwa yayi ya samu uban ya nuna
yana sonta zai kuma aureta, wannan dalili yasa babu bata lokaci suka janye kara a kotu suka bar maganar miliyan dari da sharadin Malam Ali zai ba Abdul auren er sa Khaleesat, mu dai har yau bamu san ko da wata yarjejeniya da aka yi a kotun ba ko babu, mun
dai san an janye kara kawai kuma duk muka yi farin ciki sosai da hakan, burin mu kawai Malam Ali ya dawo gare mu ko da bazai tsinana mu da komai ba amma mu dinga ganinsa a tare da mu a matsayin kantangar gida, balle duk mun san yayi ma iyalansa hidima dai
dai gwargwado ya kuma kyautata masu yanda ya kamata, jarabawa ce kawai ta fada masa, bana mantawa Khaleesat ta shiga damuwa sosai a lkcn tana ta koke koke wai ita bata son Abdul tun ma bata san kalansa ba bata gansa ba tace bata sonsa bazata iya aurensa b
a, mu kam idonmu duk ya rufe da son ganin an wanke Malam Ali daga laifin da ake zarginsa da shi, ni da uwarta muka yi ta bata baki muna kwantar mata da hankali muka ce ko tafi son a maida mahaifinta prison ne, ko don mahaifinta bazata hakura ba ta amince d
a bukatar Abdul na son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata baki, a haka dai muka samu muka la
llabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da baƙin cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata sab
oda
ɗ
an mai kudi ya ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan uwar ta lallabata ta shirya t
a saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata wae
c dinta tunda ba mu da yanda za mu yi, a kaf tarihi ban ta
ɓ
a jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin da motarsa ba,
watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida ya
na shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda mahaifinta,
rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sany
i shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi
kan lamarin har ta samu Mai gida
nta ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana da
ya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin ba
mu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan kara
tu, in haka ne kawai a daura auren mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya dora m
a Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya
ɗ
an samu matsala a kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali
ba, a lokacin duk ya gigice yayi ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat har sai da ta
bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta,
a hankali tace "Tun daga sannan shi yake sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta WhatsApp
, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace
yau er su budurwa bata gabansu, kusan kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata, ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya dora ma
su sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da