Showing 15001 words to 18000 words out of 641791 words
baki fito kinyi dinner ba and it's past 12, ki nemi abinda za ki ci
kar ki kwanta haka" Ita dai bata ce komai ba, yace "Hello" Daga kai tayi ta kallesa tace "Naji" Yace "Good" Kullo kofar dakin nata tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, sai da yaga ta shiga kitchen din sannan ya shiga dakinta yana bin ko ina da kall
o, after a while Khaleesat ta fito daga kitchen din with a cup of tea and some cookies, tsaye ta gansa corridor, bayan ta karaso yace "Kin ga nima Ummi na bata da lafiya amma ban zauna ina kuka ba kamar yanda kika yi" Khaleesat bata kallesa ba ta shige dak
inta ta kulle kofa, tana gama shan shayin ta koma saman gado ta kwanta, tasan yau da kyar ta iya bacci, she wish she can just see herself in Nigeria, but how?? Wasu hawaye ne suka zubo idonta ta lumshe ido, after a while ta jawo wayarta a hankali tayi dial
ing number Abdul bayan ta tuna ya kirata har sau biyu daxu bata iya tayi picking ba, har kiran ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, tasan as usual yayi fushi kenan, ko uxuri bazai mata
ba, ajiye wayar tayi ta juya zuwa daya side din ga
don. Washegari da safe Khaleesat na zaune daki tana ta kokarin kiran Aunty Farida amma baya shiga, har Sha'awa sai da ta kira ita ma wayarta baya shiga, ta rasa wa kuma zata kira, ta kalli agogon wayarta dake nuna karfe goma sha daya ta ajiye wayar tayi ta
gumi, tun daga daren jiya har yau bata da sukuni, ko schl din ma yau tasan bazata iya zuwa ba, juyawa tayi jin knocking a kofar dakinta, tana dai zaune har sai da ya kwankwasa kofar sau uku sannan ta sauka daga saman gado, walking slowly ta tafi ta bude ko
far, Yace "Good morning Halysaah, how was ur night?" Without looking at him tace "Fine" Yace "Ya jikin Mama? Kun yi communicating da su?" Kai kawai ta gyada masa bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Paper da pen din hannunsa ya mika mata yace "Can i get
ur Email Address?" Ta daga kai ta kallesa da mamaki tace "I don't understand" Yace "I mean ur Email Address" wayarsa ne ya fara ring ya mika mata takardan da pen ya daga kiran sannan ya juya ya bar wajen, ita dai ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya ta k
oma daki ta ajiye takardan da pen da ya bata, after some minutes sai gashi ya dawo yayi knocking yace "Can i get the paper" Tasowa tayi ta bude kofar bayan ta dau pen da takardan tace "Why are you asking for my Email Address?" Yace "Ki dae rubuta ki bani"
Shiru tayi, sai kuma ta jinginar da paper din jikin kofa ta rubuta sannan ta mika masa ya amsa ya juya ya bar wajen, yana fita da few minutes taji message ya shigo wayarta, ta dau wayar ganin E-mail ne ya shigo ta bude, kallon Image din da ta gani as Email
din ta dinga yi babu ko kiftawa, she look shocked and confused at the same time, ta daga kai tana kallon kofar dakinta babu ko kiftawa, dai dai sanda taji sallamarsa, kasa tashi tayi daga inda take zaune, har sai da yayi knocking sau biyu tayi karfin hali
n mikewa ta isa kofar ta bude tana kallonsa, Yace "I don't know if you find this okay and a good idea" Ita dai bata fasa kallonsa ba looking speechless, Yace "Hope they won't be Mad at this back home Halysaah?" Jin bata basa amsa ba ya gyada kai yace "I gu
ess it's a bad idea, I should have ask for ur opinion first before doing this" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta, yace "Ok it's fine, i will get the ticket cancelled" Daga kai tayi da kyar tana kallonsa hawaye na zuba idonta tace "Thank
you so much, i appreciate" Yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, u can order a Lyft that will be taking u to the airport later, ur flight is at 3pm today" Sauke idonta tayi cause she is totally speechless, ya mika mata travelling documents dinta, am
sa tayi cike da mamakin how he got them, ya juya ya bar wajen, komawa cikin daki tayi ta kulle kofar tana kallon inda take ajiye travelling doc din nata a dakin, did he come to her room to check ne, to ai throughout babu inda taje, ta karasa gefen gado har
sannan jikinta a mugun sanyaye ta zauna, kallon screen din wayarta ta sake yi tana kallon ticket din don ganin abun take kamar a mafarki, tana kara duba taga tun daren jiya ya siya ticket din and kamar yanda yace the flight is by 3pm today, ta ma rasa ko
farin ciki zata yi ko kuma wani reaction zata yi, amma da ta tuna she is going back home to see her Mom which was her wish since yesterday sai taji wani farin cikin da tunda take bata ta
ɓ
a jin irinsa ba a rayuwarta, 80% a cikin dari na damuwarta ya ragu ci
kin lokaci kankani, kallon agogo tayi taga sha daya ya wuce sosai, the weakness she is been feeling since this morning immediately vanished, mikewa tayi tana share hawayenta ta dau medium box din kayanta.... Karfe biyu Khaleesat ta gama duk abinda take, ha
r sallan zuhur tayi, Lyft din da tayi ordering kawai take jira, tana zaune gefen gado xuciyarta fal da tunani kala kala, babban burinta a yanzu bai wuce ta ganta kusa da mahaifiyarta ba, in yaso koma me zai faru daga baya sai ya faru, kallon wayarta tayi t
aga Safiyyah ce ke kiranta, tun daxu da safe ta kirata amma sbda damuwar da take ciki ko picking bata iya tayi ba, Khaleesat ta daga kiran ta kai kunne, Safiyyah tace "Khalee me yasa baki shigo schl ba yau? Are you okay?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar
zuciya tace "Ummanmu ce bata da lafiya Sophie" Safiyyah tace "Subhanallah, amma ya jikin yanzu?" Khaleesat tace "Da sauki" Safiyyah tace "To Allah ya bata lafiya, plss nasan ki kar ki sa ma kanki damuwa kawata addu'a kawai zaki dinga mata, nasan kilan kin
a nan kina ta kuka ko?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "In sha Allah in mun gama lectures zan taho" Khaleesat tace "I am sorry ban kira ki na gaya maki ba i will be leaving for Nigeria by 3pm" Da mamaki Safiyyah tace "Zaki tafi Ni
geria? Abdul ne ya siya maki flight ticket?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Uhm" Safiyyah tace "Is it that critical Khaleesat?" Khaleesat tace "To da sauki dai, amma kinsan bazan samu rest of mind ba in ban je ba" Safiyyah tace "To kina airport yanzu ne?"
Khaleesat tace "Aa ina jiran Lyft ne yanzu zan tafi" Safiyyah tace "Toh shikenan mu hadu a can kawai sai mu yi sallama, bari in nemi Uber nima" Khaleesat tace "To nagode Sophie" Da haka suka gama wayar, Khaleesat ta mike bayan Lyft dinta ya iso, tana rike
da trolley dinta da handbag ta fito daga dakin ta kulle kofa, sanye take da Maroon Abaya sai veil dinta, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlorn, ya ajiye wayar da yake yace "Kin shirya?" Without looking at him tace "Eh" yace "Kin yi ordering ride a
i?" Tace "Eh" yace "Ohk" Mikewa yayi ya ciro 1000 Dollars ya mika mata yace "Sort ur self out with this" Girgiza masa kai tayi tace "Aa Nagode" Yace "C'mon, u didn't beg me Halysaah" Ƙin kallonsa tayi kuma taki amsan kudin, ya dau handbag dinta da ta ajiye
saman trolley din gabanta ya bude zip din jakar ya sa mata kudin tare da wani farin takarda, ta
ɗ
aga kai tana kallonsa, ya koma ya zauna yace "Allah ya tsare, my regards to ur Mom and everyone back home, Allah ya bata lafiya" Da kyar tace "Ameen nagode" Y
ace "Zaki ga digit na rubuta maki a takarda, idan kun sauka Airport sai ki kira number kice masa kun sauka" Ta kasa cewa komai, after few seconds ta dau handbag dinta cikin sanyin murya tace "Nagode " Yace "U are welcome, wishing u a Safe trip" Tana jan tr
olley dinta a hankali ta nufi kofa, tana bude kofar ta fita ta daga kai tana kallonsa taga Idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, kulle kofar parlon tayi, taga Lyft din dake jiranta ta nufi wajensa. A Airport Khaleesat suka hadu da Safiyyah, Safiyyah na ri
ke da hannunta tace "Tun yaushe ne Umman bata da lafiya?" Khaleesat tace "Jiya Aunty sha'awa ke gaya min" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya
tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Safiyyah tace "Lallai Abdul ya fara hankali da yayi tun
anin biya maki jirgi kije ki duba Umma, nayi mamaki sosai wallahi" Khaleesat ta
ɗ
an yi murmushi da iyakarsa lips, Safiyyah tace "Yanzu kwana nawa za ki yi?" Khaleesat tayi shiru at first, sai kuma tace "Sai dai naje tukunna in sha Allah" Safiyyah tace "Toh
Allah ya kai ku lafiya, don Allah ki gaida min Umma da jiki" Safiyyah na fadin haka ta jawo handbag din Khaleesat ta saka mata dala dari tace "Plss manage this kawata" Khaleesat ta
ɗ
an bude baki tace "Haba meye haka Sophie" Sophie bata tsaya ta saurareta
ba ta daga mata hannu tana murmushi ta bar ta tsaye wajen, Khaleesat dai ta bi ta da kallo. Khaleesat was more than shock bayan ta amshi boarding pass dinta ganin ticket din Business Class ya siya mata, Business class fa? Kikkifta ido tayi ta sake kallon t
icket din sosai to confirm, taga Business class din dai ne still, sosai jikinta yayi sanyi, tana jan kafa da kyar ta shiga jirgin, this is the first time she will be traveling Business class, wata Flight Attendant that gave her all the maximum attention ta
yi leading dinta har zuwa Seat dinta a cikin jirgin da fara'a tana welcoming dinta, bayan wani
ɗ
an lokaci jirgin ya tashi, Khaleesat ta ajiye Amenity kit da aka bata ko duba abinda ke ciki bata yi ba tana bin ko ina na Business class din da ido, the Fligh
t from Baltimore Washington International to Amsterdam Schiphol Airport in North Holland for Layover was smooth and comfortable, duk zuwanta Amurka bata ta
ɓ
a tafiya feeling so comfortable like this ba, bayan few hours aka sauya masu jirgi zuwa Nigeria a na
n North Holland, Khaleesat tayi shiru da mamaki jin announcement na cewar Lagos Nigeria jirgin ya nufa, ticket dinta ta sake dubawa taga ashe haka ne a jiki, bayan tafiyar kusan awa bakwai jirgin nasu ya sauka a MMI Airport Lagos.
07087865788✍
🏻
✨✨
HALYS
AAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍
🏻
6.....
Bayan Khaleesat ta dau trolley dinta a cikin airport after going through custom ta tsaya cikin airport din tana tunanin yanda zata yi cause karfe shidda saura ne na asuba, should she check for available fl
ight to Kano? To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance, ta bude handbag dinta ta ciro kudin tan
a kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa, ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din, masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan
asuba, tana ta zaune cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta dinga yi jiki a sanyay
e don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallam
a ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace "Ohk
to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci
sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport, yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zu
wa karfe daya na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya karasa ya amshi trolley dinta ya tafi
ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace "Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka
tana tafiya a hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me
tsada sosai that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai Khaleesat ba um bare um um,
gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau Shower gel zata yi wanka. Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawot
a Hotel ne, ta mike zaune sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace "Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "T
oh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana han
gota a Reception din hotel din ya tafi da sauri ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI A
irport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah... We will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh
Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju, nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly, bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano. Suna sauka kano Khaleesat ta fito
daga cikin airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da faduwa, wata lamba ce ke kirant
a tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida, kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutum
in yayi zuwa inda take tsaye bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku lafiya" Tace "Ameen
Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta
ɗ
an yi shiru kamar me nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu
lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin gida
n da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta
ɗ
an sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace "Khaleesatu? Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duk
a nan gabanta har sannan tana
ɗ
an murmushi tace "Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat