Showing 525001 words to 528000 words out of 641791 words

Chapter 176 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

198

baka labarin abinda Ajay yace mata a mafarki zaka ga with seriousness take bayarwa har cikin ranta, har alkawari ta sa Khaleesat ta daukar mata na cewa zata rag

e damuwa tunda Ajay yace mata zai dawo, haka zata yi ta biyeta duk don ta dawo mutum amma sai ta dau alkawarin kwana biyu sai abu ya dawo sabo fil ta karya alkawarin, likitan ta dinga jin Khaleesat kamar kanwarta don halin da take ciki ita kanta yana damun

ta cause she is too young for this kind of cruel pain, she watch her everyday struggling to eat, struggling to sleep, struggling to do everything whereas kowa lafiya yake duk abubuwan nan da take struggling tayi, sai taji ina ma zata iya dawo mata da farin

cikinta ta dawo yanda take a da.... Sai a yanxu Khaleesat ta fara nuna jin haushin Jay da take yi a zuciyarta, tana ganin ya tafi shi ya dawo amma bai dawo mata da Ajay ba, bai yi protecting mata shi ba he only protected himself on that very day, ko ganin

sa tayi sai ta tashi ta bar wajen ta fara kuka, ta dawo abun tausayi a gidan sarauta, kowa tausayinta yake gashi taki zaman gidansu a Kano, sau uku in an kai ta take dawowa Bauchi, don har gwara zaman da take a masarauta wani lkcin zaka ganta tana hira da

Likitanta ko Mami ko Hajja kamar ba ita ba har da dariyar ta sosai, har da su Kilishi da Hajiya A'isha hira take yi tana basu labarin Ajay ko mafarkin da tayi, to a cikin hiran ne zata fashe maka da kuka just like that kamar warce aka tsikara, ko kuma in t

ana dariya ya rikide ya koma kuka, a Kano kuwa rasa gane kanta ma ake yi gaba daya, ya kai ya kawo an fara ganin abun nata is not normal anymore, still Sarki yasa aka kara kai ta asibitin ƙwaƙwalwa har kasar waje amma babu sign din ko wani ciwon ƙwaƙwalwa

tare da ita, Mai martaba ya nemi a bar ta a Masarauta ana ci gaba da yi mata Therapy har zuwa sanda zata dawo normal tayi move on tunda da lafiyarta aka rabota da gidansu don haka bazai yiwu ta koma gida cikin wannan halin ba, Dr din da take kula da ita da

ban wanda yake mata Therapy daban, Nenne kuwa duk kauyen da taji ana bada taimako haka zata shirya duk nisan sa taje nema ma jikarta taimako, tun Umma na boye damuwarta har sai da ya fito sarari, tana son masarauta su sakar mata erta ta dawo gida ta rungum

i abarta amma ana jin nauyin gaya ma Sarki haka, don da sun bada ita ma Nijar tayi niyyar tafiya da ita yanda zata yi nisa da Nigeria din gaba daya, ana haka aka yi diagnosing Khaleesat da mild ciwon zuciya, jikin likitan ta yayi sanyi sosai, ita da take t

unanin Ulcer ce ashe Heartache ne, hankalin kowa ya tashi a masarauta, ba a ma san ta yanda za a fara gaya ma iyayenta ba, Jay was very very worried don shi ne ma ya daurata kan medications, wannan dalili yasa zamansu ita da likitanta ya fi yawa yanxu a ba

bban lambun Masarauta, saboda ta dinga samun access da nature's view and greenery, haka nan za su wuni da likitanta a lambun wani lokacin sai su kai har Magrib a nan, time to time Jay kan shigo lambun dubata, tana ganinsa sau tari sai ta juya baya ta fara

kuka, wani lokacin ya karasa har inda suke wani lokacin kawai ya juya ya fice daga garden din cause he can't stand her cry, it's making him emotional too......

Abinsi Benue state riverine area....

Wata yarinya ce da bazata wuce shekaru ashirin ba durku

she gaban murhu tana ta fifita wutan murhun, komawa tayi ta zauna kan kujera karama tana jiran dahuwar abinda ta daura kan wuta, daga gefenta kuma wata matashiya ce dake ta weaving din tabarma da kaba ita ma daure da zani, bayan wani lokaci yarinyar ta bud

e tukunyar dake kan murhun ta juye tulin manyan kifin da aka yi ma farfesu yana ta tafarfasa a clay bowl babba dake gefenta, ta mike ta gyara daurin zaninta tana yi ma matashiyar matar dake zaune magana da Yarensu na Jukun Wanu, warce da alama mahaifiyarta

ce, dukawa tayi ta dau bowl din kifin dake ta tafarfasa a clay bowl din ta nufi wani thatched roof hut, ta duka ta shiga cikin dakin sannan ta durkusa ta ajiye bowl din hannunta tana kallonsa, yana zaune kan tabarma a hut din ya jingina jikin ginin kasan,

tayi masa alama da hannu cewar tana zuwa ta dauko masa ruwan da zai wanke hannu, ya gyada mata kai, mikewa tayi ta fita daga hut din, tana fita waje da yarensu take gaya ma uwarta ya tashi zaune, uwar ta ajiye kaban hannunta sannan ta mike ta shiga bukkan

ita ma, murmushi tayi da jagulallen Hausanta take ce masa sannu fa, ya gyada mata kai yana mayar mata da murmushin ta juya ta fita daga Bukkan, yarinyar ta koma ciki da ruwan wanke hannu da kwaryan palm wine, ta ajiye ruwan wanke hannun da Palm wine din a

kusa da shi, hannunsa ya hade waje daya alamar godiya, tayi murmushi kawai, ya wanke hannunsa cikin ruwan da ta kawo, sannan yayi mata alamar ta tafi da Palm wine din bazai sha ba yana girgiza mata kai, daukar kwaryan palm wine din tayi ta fita, ya kalli

kifin dake ta tiriri ya kai hannu ciki ya yanki kadan ya kai baki ya fara ci a hankali......

HALYSAAH

Ajay ya wanke hannunsa bayan ya gama cin kifi daya ya mike ya dau sauran kifin da bowl din ruwan wanke hannu ya fita daga Bukkan, matar da 'yar ta s

uka daga kai suna kallonsa, yarinyar ta mike ta nufesa ta amshi Clay bowl din hannunsa da roba taje ta ajiye sannan ta dawo tana kallonsa ta bude masa palm dinta alamar me yake so, ya girgiza mata kai, ta juya ta koma ta zauna tana kallonsa, walking slowly

ya nufi river din dake nesa da inda Huts dinsu yake, ta baya yaji an ta

ɓ

o sa ya juya yarinyar ta nuna masa takalmin hannunta sannan ta ajiye masa kusa da ƙafarsa don babu takalmi kafarsa, yayi murmushi ya saka takalman sannan ya ci gaba da tafiyarsa zuwa

bakin ruwan, yana isa ya zauna kan wani ƙaramin rock a bakin wajen yana kallon ruwan da bai hango iyakarsa ba, ko minti sha biyar bai yi zaune a wajen ba yaji taku a bayansa ya juya, wani magidanci ne da bazai wuce Shekaru arba'in da biyar ba ya nufosa yan

a murmushi da Hausan sa that is not fluent yace "Sannu abokina, jiki yayi kyau yau ko?" Ajay ya gyada masa kai yana mayar masa da murmushin yace "Da sauki" Mutumin yace "Toh muna godiya ma Allah, yanxu za mu tafi za a baka maganin ka na yau, za mu je wajen

Mai magani din baza mu jira ya zo ba yau, ai kana iya tafiya" Ajay yace "Zan iya...." Mikewa mutumin yayi Ajay ma ya mike ya bi bayansa suka bar bank din river din, suna komawa inda Huts dinsu yake mutumin yayi ma matarsa magana da yare, hannu ta daga ma

Ajay alamar su dawo lafiya, ya gyada mata kai yana murmushi, daga nan ya bi bayan mutumin suka tafi, da ido yake ta bin karamin garin wanda ke bakin ruwa, duk inda ka wuce zaka ga babban river din garin daga gefe da kwale kwalen fishermen a bakin ruwan, Ba

yan tafiyar minti talatin da kafa suka iso wani Bukka, shi ma dai a kusa da ruwa yake, mutumin yayi yarensu sannan ya shiga cikin bukkan, shi dai Ajay na tsaye gefen Bukkan yana bin ko ina da kallo, sai ga mutumin da ake kira da Ozhi ya leko yace masa "Shi

go ciki aboki" dukawa Ajay yayi ya shiga Hut din, ya zauna kan tabarman dake shimfide yana kallon wanda ke zaune ya bar gemu kaca kaca a fuska ya daga masa hannu yace "Barka dai" Mutumin yace "Kana tuna tun yaushe ne baka da lafiya?" Ajay ya sauke idonsa b

ai ce komai ba, Ozhi yace "Shekara biyu kenan ba shi lafiya...." Mutumin yayi dariya yace "Ozhi ina son shi ya fada da bakinsa ne" Ozhi yace "To Dochu yaya shi zai sani yana kwance sai barci...." Mutumin yace "Amma yana jin kowa ai, ko baka ji?" Ajay ya sa

uke idonsa, Ozhi ya gyara zama yace "Mun gode ma Yesu kawai" Mutumin ya mike ya fita daga Bukkan, Ozhi yace "Allah mu ke godiya ma" Ajay ya

ɗ

an yi murmushi yana bin Bukkan da kallo, kullin magunguna ne ƙashi ƙashi a dakin da tarkace irin dai na tsibbu, har

da abubuwan da aka rataye a sama suna ta reto, Ozhi yace "Kana tuna sunan ka yanxu abokina?" Ajay ya daga kai ya kallesa yace "Sunana Ahmad" Mutumin na murmushi ya gyada kai alamar jin dadi, zai yi magana sai ga mutumin ya shigo dakin da clay bowl dauke d

a wani ruwa ya mika ma Ajay yace "Zaka shanye wannan zuwa cikin ka yanxu" Ajay ya kalli Clay bowl din sannan ya amsa yana kallon ruwan ciki da wasu particles ke ta yawo a ciki, Ozhi yace "Ka shanye, shi ne yana maka magani ai" Ajay ya lumshe idonsa ya kai

clay bowl din baki ya fara shan ruwan cikin, Ozhi sai murmushi yake har ya shanye sannan ya ajiye Bowl din, mutumin ya mike ya debo wani ruwa ya shafa masa a kai da fuska yace "Saura gobe zaka sha kuma" Ozhi yayi masa godiya da yarensu sannan ya mike yana

kallon Ajay yace "Za mu ta tafiya yanxu" Ajay ya mike shi ma yayi ma mutumin godiya sannan ya bi bayan Ozhi suka fita daga Bukkan suka dau hanyar gida, kamar dai sanda suka fito yanxu ma dai duk inda suka bi a garin kallon Ajay ake ana

ɗ

aga masa hannu, shi

ma yana masu haka, bayan sun yi nisa Ajay na kallonsa yace "A ina zan samu Banki?" Ozhi ya bude ido ya kallesa yace "Bankin kudi?" Ajay ya gyada masa kai, Ozhi yace "Sai anyi tafiya zuwa Makurdi" Ajay yace "Awa nawa ne tafiyar?" Ozhi ya girgiza kai yace "

Minti arba'in yayi yawa zuwa Makurdi" Ajay yace "Gobe ina son mu je Bankin" Ozhi yace "To sai mu tafi sassafe" Ajay ya gyada masa kai suna ci gaba da tafiya, sai kuma ya kallesa yace "Amma baza ka je fishing ba gobe?" Ozhi yace "Cikin dare ne zan je yau" A

jay ya gyada masa kai kawai.....

Tana tsaye ta jingina da trunk din bishiya a babban lambun dake dauke da shukoki iri iri da suka kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound as the sun set slowly, the view was so b

eautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view din da ido gaba daya hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take, likitan ta dake gefenta ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da mury

a tace "Magariba ya gabato mu je kiyi alwala ko" Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda take cewa ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali, likitar ta kama hannunta ta jawota jikinta calmly tace "C'

mon sweet heart, are you breaking another promise already?" ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe ido tana patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a lambun, ya tsaya daga inda yak

e bai karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame jikinta tayi daga na likitan ta juya masa baya alamar bata son ganinsa hawaye na zuba idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka

ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi, ta fara kokarin zaunar da ita akan lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down t

ace "Haba kanwata, me yasa baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?" Muryarta na rawa tace "Kiyi hakuri bazan iya ba wallahi" Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta na shigarta, tayi attending to different case

s in her career as a medical Doctor amma babu wanda ya ta

ɓ

a daga mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she can take away her pains, she wish she can make her happy once more, she wish she can make her forget the past and face

the present, a hankali likitar tace "Halysaah...." khaleesat ta daga rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace "Kiyi hakuri Halysaah, kiyi hakuri" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba hawaye na sauka idonta, likitan ta daga ta tana rike da h

annunta suka bar lambun zuwa babban compound din gidan, yana tsaye jikin bango ya daga kai yana kallon faduwar rana babu ko kiftawa, ashe ba tafiya yayi ba bayan fitar sa daga garden din, har suka iso inda yake tsaye bai sani ba, Likitan na kallonsa tace "

Ashe kana nan ranka shi dade, barka da yamma" Jay ya juya ya amsa mata a hankali, Ita dai Khaleesat bata kallesa ba ta zame hannunta daga na likitan ta bar wajen zuwa cikin gida, yana kallon likitan yace "Ya jikin nata yau Dr?" Likitan na murmushi tace "Ya

u kam Alhamdulillah da sauki, ba wani complication, kwata kwata bata yi kuka ba sai yanxun nan abun ya motsa mata, kuma anyi hira da ita sosai yau da su Kilishi, daxu da rana ma da Kilishi zata je gidan Hajja tare suka tafi har da Hadiyah, amma suna isa gi

dan Hajjan kuma tace zata dawo gida, shi ne aka sa driver ya maidota tare da Hadiyah, to da ta dawo bacci tayi don magungunan da ka rubuta mata last suna sa ta bacci sosai gaskiya, dab da la'asar ta tashi naga tana ta gyaran daki har da canza zanin Gado sa

nnan ta wanke bandaki nace mata ai duk anyi da safe, shi ne take gaya min mafarkin da tayi...." Jay ya katse likitan don bai ma son jin mafarkin don it is always the same sad dream everyday, cikin sanyin murya yace "But did she complain of chest pain today

?" Likitan ta girgiza masa kai tace "A'a ta kwana biyu ma bata yi complain ba gaskiya, duk kwana biyun nan ma akwai improvement fa" Yace "Ohk" Da damuwa likitan tace "Amma ranka shi dade an fito da

ɗ

an uwan naka da theatre din kuwa? And I am hoping the ope

ration was successful" Jay yace "Mu ma bamu samu wani feedback ba tukunna, i don't think an fito da shi" Likitan tace "To Allah Ubangiji ya sa mu ji alkhairi, Allah ya tashi kafadunsa, Allah yasa karshen wahalan kenan" Jay yace "Ameen" Daga haka ya juya ya

bar wajen, Likitan ta bi bayansa tana girgiza kai cike da tausayin Walid a ranta, operation a spinal cord kusan na hudu kenan duk babu success sai kara tabarbarewa abun yake, asibiti yafi uku da aka canza masa in different countries, ana kuma tunanin wann

an operation din ne na karshe idan kuma ba ayi nasara ba shikenan a haka zai dawwama with complete paralysis for life, even though the success rate of the operation is just 5 percent dama, gashi baya iya rikon fitsari don complications din Surgery din yayi

affecting bladder function dinsa, Aunty duk ta fita hayyacinta saboda ita da Jakadiyarta da Mukhtar ke tare da shi a asibiti, sai dai ta dawo gida Nigeria ta huta kwana biyu sannan ta koma, duk mutanen da take harka da su babu wanda yace bari ya tayata ji

nya ko na rana daya, har aminiyarta Hajiya Nafisah warce sau daya taje dubo Walid a sanda suke India shi ma kwana biyu tayi ta juya kamar ana koranta, daga haka kuma bata sake komawa ba, ko kiran waya bata yi ba, a dangin Aunty ma babu wanda yaje tunda ba

harka take da su ba tun bayan da tayi aure gidan Sarauta ta dinga walakanta su, shi ne kowa ya kama kansa aka kyaleta, tafi shekara ashirin rabonta da garinsu bata kuma neman kowa har wa enda suke uwa daya uba daya, a masarauta kuwa sai dai su je dubiya je

fi jefi su yi kwana daya zuwa biyu su dawo, Mami ce kadai ke yin kwana biyar zuwa sati daya in dai taje, ita ma saboda Khaleesat ne yasa zaman nata baya wuce haka, sai Ummi warce ita dama kwana uku take cewa mijinta yace tayi, su Kilishi kuwa idan suka je

to yawon bude ido suke yi a gari su gama kwanakinsu su koma Nigeria, Hajja rashin lafiya ya sakota gaba sai dai kiran waya, kullum sai ta kirasu video call don duba jikin Walid, duniyar tayi ma Aunty zafi, ta rasa me ke mata dadi taga kamar kowa ya juya ma

ta baya, Mai martaba duk karshen wata yake zuwa duba Walid yayi kwanaki uku ya dawo Nigeria, haka Aunty ke raya dare tana sallah tana kuka tana addu'an Allah ya tashi

ɗ

an ta, duk ta rame saboda damuwa..... Likitan Khaleesat na komawa ta zauna Main parlor b

ayan wani tunani ya zo mata rai, da ace ba iya aikin likitanci aka dauketa for Khaleesat ba da zata yi karambanin bada shawaran

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login