Showing 594001 words to 597000 words out of 641791 words
tafi Nenne" Nenne tace "To a gaida mutan gidan" Yace "Za su ji in sha Allah" Kofa ya nufa Ajay ya bi sa da kallo, Nenn
e tace "Bari in ma Zahra'u magana ta fito ku gaisa Yarima" Daga haka ta nufi dakin Umma..... Bayan minti ashirin da zuwan Ajay gidan Khaleesat ta fito parlor nan ma Nenne ce ta takurata sai ta fito, tana fitowa taga baya parlon, ta fita compound har zuwa k
ofar gida taga babu motarsa, ta fi minti biyu tsaye bakin gate din, ta juya a hankali ta koma cikin gidan, wayarta ta tafi dakin Nenne ta dauka sannan ta shiga parlon Babanta ta kulle kofar ta zauna kan kujera tayi dialing numbersa. Sai da ya kusa katsewa
ya daga, a hankali tace "Why did you leave?" Yayi shiru at first, sai kuma yace "Kamar ya?" Bata kara cewa komai ba, hawaye suka ciko idonta, after few seconds yace "Good evening Jeeddah" Da kyar tace "Ka dawo ka daukeni, na gama zaman da zan yi" Yace "A'a
ni ban ce zan dauke ki ba, you can spend as much time as you want to spend, in dai kina bukatar wani abu ki gaya min" Bata ce komai ba, yace "Hello" Nan ma taki cewa komai, after some seconds ya katse wayar, sake kira yayi ta goge hawayen idonta tayi sile
ncing wayar ta mike ta fita daga parlon taki picking call din. Wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta fito kofar gida bayan Mai gadi ya je yace ana sallama da ita, kuma a gaban Nenne da Ummanta ya bada sakon a bakin kofar parlor, da ace ba kowa Parlon da b
azata fita ba, tana tafiya kamar warce aka tilasta ta karasa gun motar ta bude front seat ta shiga ta kulle motar bata dai kallesa ba, shi kam kallonta kawai yake, can yayi kasa da murya yace "Baƙon naku ya tafi?" Sai a sannan ta kallesa tace "Is that why
you are giving me attitude?" Ya
ɗ
an bude ido yace "Ni na isa? Naga baki da lokaci na ne shi yasa na tsaya lane dina" A fusace tace "To wajena ya zo shi baƙon? Ko kuma ni ce na kirasa nace ya zo gani nan na zo gidanmu?" Masifa ta rufe sa da shi tana fadin d
uk maganganun da ya zo bakinta, shi dai yayi shiru bai ce komai ba yana sauraronta, sai da ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke numfashi, calmly yace "Allah ya baki hakuri" Bude motar tayi zata sauka ya rikota yace "Jeeddah" Ta fashe da kuka sosai, ya b
i unguwan da kallo ganin babu kowa ya jawota jikinsa a hankali yace "Na fa ce kiyi hakuri" Cikin kuka tace "Ni ka kyaleni kawai" Yace "To wa zan rike idan na kyale ki?" Shesshekan kuka ta dinga yi yana bata hakuri har tayi shiru, ta hade rai tace "Sai kace
wajena yake zuwa a gidan" calmly yace "Nasan wajen Noor yake zuwa ai" Tace "To da ka sani kake nuna min attitude?" Ya
ɗ
an yi murmushi yace "Jiya fa mance ni kika yi a kofar gida, daxu kuma da na zo kika ki fitowa kika bar ni a parlor" Tace "Ni kawai mu ta
fi na fasa zaman gidan, bazan zauna ba" Ya
ɗ
an bude ido don gobe za su tafi Benue da Jay kuma baya son ta sani, kwantar da murya yayi yace "A'a ki dai kara kwana biyu wife...." Don ya kauda zancen kafin ta dage sai sun koma gida yayi saurin canza maganar y
ace "So what did you think about his relationship with Noor?" Ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Nenne bata so, Ummata ma haka, duk tsoronsa suke ji" Ajay yayi shiru, calmly yace "But Abdallah have turned a new leaf long ago, kuma ina ji a raina da za
a basa ita zai riketa da amana" Khaleesat tace "Nima ina masa kyakkyawan zato amma sun ki su gane hakan, ina kuma duba alkhairan sa a gareni" Ajay yace "Ya fadi intention dinsa a kan Noor din ne?" Khaleesat tace "A'a amma kusan kullum sai ya zo gidan nan"
Ajay ya
ɗ
an yi murmushi amma bai ce komai ba, Khaleesat ta kallesa a hankali tace "Ice- cream nake son sha" Yace "To shiga gida, let me go get you the ice cream" Ta turo baki tace "Tare za mu tafi, don sai na zaba wanda nake so" Bai ce komai ba ya tada mo
tar yayi reverse suka bar layin, bayan sun siyo ice cream din zai maidata gida ta marairaice tace "Yanxu gida zaka kai ni?" Yace "Kin fiye rigima yarinyar nan" Kallonsa take cike da shagwaba, sosai take missing din kasancewa tare da shi ita kanta ta rasa g
ane dalilin haka, jiya ma kasa bacci tayi saboda wani urge da ta dinga ji, kamar zata yi kuka tace "To ni dai mu fara zuwa gida zan gaya maka wata magana, idan na gaya maka sai ka maida ni gidanmu" Yanda ta narke masa har ta kashe masa jiki, yayi kasa da m
urya yace "Me zaki gaya min wife?" Ta kai hannunta jikinsa ta ta
ɓ
a sa tana masa wani kallon shagwaba, zaro ido yayi ganin inda ta ta
ɓ
a masa, ta boye fuskarta da sauri tana murmushi, kawai ya tada motar direct ya nufi gida, jam'in da bai samu ba kenan na Ma
gariba da isha'i ranan, ita kuma saboda kunyan yan gida kawai ta kira Ummanta tace sun je gidan Sarki ne. Washegari babu yanda Ajay bai lallaba Khaleesat ba akan tayi zamanta a Kano su je Benue su dawo amma kememe taki, Jay dai bai ce masu komai ba at firs
t, amma da ya tuna condition dinta shi ma yayi mata magana ta zauna a Kano ba sai ta bi su ba kawai ta fashe masa da kuka kamar wanda ya fadi wani mugun abu, bai sake cewa komai ba ya kama kansa ya koma gefe ya bar ta da mijinta, haka nan suka kama hanyar
Benue tare da ita....
HALYSAAH
Suna sauka Airport din Abuja suka tarar motar da zai tafi da su Makurdi na jiran su a airport din, Ajay na zaune kusa da Khaleesat a baggage claim area yana kallonta don idanuwanta a lumshe suke, tun da suka shigo Arrival
hall din ta nemi waje ta zauna, and they've been sitting there for a while now Jay dai tuni ya fita zuwa gun motar da ke jiransu da hand luggage, wai
ɗ
an tafiyar da tayi daga bakin jirgi zuwa hall din shine take ji kamar tayi tafiyar awa daya a kafa, afte
r some more minutes Ajay yayi kasa da murya yace "Jeeddah" jin bata amsa ba ya fahimci she is sleeping ne haka, mamaki ya sa ya dinga kallonta babu ko kiftawa, Jay ya gaji da tsayuwa a waje ganin basu fito ba kuma su ba kaya suke jira ba ya doka ma Ajay ki
ra, vibration din wayar ne ya tashi Khaleesat ta bude ido, Ajay ya ciro wayar ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren Jay yace "Wai Ajay dama ka san baka shirya tafiyar nan ba ka sa muka kamo hanya?" Ajay yace "Not at all, she is having a little nap" Taka
ici yasa Jay ya rasa ma me zai ce masa, kawai ya katse wayarsa ya mayar aljihu, Khaleesat ta hade rai tana kallon Ajay tace "Me ya ce?" Ajay yace "A'a cewa yayi Driver na waje yana jiran mu" Tace "To naga kamar baya son in bi ku, ya mance wancan lokacin ha
ka ku ka tafi ya dawo shi kadai...." cikin sanyin murya ta kare maganar, Ajay ya
ɗ
an yi murmushi yana kallonta, after some seconds yayi kasa da murya yace "Yanxu dai as my security zaki bi mu kenan wife?" A hankali tace "Eh mana" Yana murmushi yace "To tas
hi mu je..." Hannu ta mika masa alamar ya dagota, ya dagota suka nufi hanyar fita daga arrival din, a hankali tace "Ina jin kamar kaina yana min ciwo...." Ajay ya juya ya kalleta yace "To bari mu fita outside of the airport a siya maki magani" Ta gyada mas
a kai, a haka suka isa inda driver yayi parking, Jay na tsaye jikin mota ya rungume hannunsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ajay ya bude ma Khaleesat back seat yana amsa gaisuwan driver, Jay bai ko kallesa ba ya bude front seat ya shiga, Ajay ya shiga ba
yan motar ya zauna kusa da Khaleesat yana kallonta, a haka suka fita daga cikin airport din, bayan sun dau hanya Ajay na kallon driver yace "Nearest pharmacy zaka fara kai mu sulaiman" Drivern yace "To ranka shi dade" Suna isa wani babban pharmacy drivern
yayi parking, Ajay na kallon Khaleesat yace "Let me get you the medicine" Ta gyada masa kai ya bude motar ya sauka, Jay ma ya sauka daga motar, Khaleesat ta bi sa da kallo, a tare suka nufi cikin pharmacy din, Jay na kallon Ajay bayan sun yi nisa don baya
son magana gaban Khaleesat yace "Ajay idan kana son muyi tafiya irin na matafiya masu hankali to ka nemi inda zaka bar Halysaah har mu je mu dawo, ban ga ta yanda za mu yi tafiyar nan da ita tana langwabewa kamar lagwani a haka har zuwa Makurdi ba, gaskiy
a i am not ready to be stressed Ajay, da ma stress din iya kai kadai zai tsaya da sauki, but in dai tafiya za mu yi cikin tsari it's better you leave ur wife behind mu yi dropping dinta gidan Ammi" Ajay dai jin sa kawai yake yana tafiya, Jay yace "Kawai du
k ka sa yarinya ta dawo wata irin fitinanniya" Sai a sannan Ajay yace "A'a dama tun asali haka take, a haka ka bar min ita don rainon ka ce ai" Jay ya jefa masa wani kallo kamar bazai ce komai ba yace "Cikin dai da ka dirka mata ya maidata haka...." Ajay y
ayi er dariya yace "Yanxu dai idan mun koma mota sai kayi mata duk bayanin nan da kayi yanxu na cewa mu bar ta a Abuja" Jay yace "Ka tafi gaba da Makurdi da ita ma mana ina ruwana" Ajay na murmushi yace "She is been insecure akan tafiyar ne, and I sense sh
e is afraid to let me go alone, she doesn't want history to repeat it self again" Jay dai kallonsa kawai yake jin abinda yace, ya sauke idonsa bayan shi ma memories din sun dawo masa, shi fa tun da ya sa a ransa bazai dinga tuna abubuwan da suka faru a bay
a ba to kwata kwata baya barin zuciyarsa ya tuna da past, abinda ya saka ka shiga damuwar da baka ta
ɓ
a shiga irinsa ba duk tsawon rayuwar ka ai ba abu bane da zaka so ka dinga tunawa, after some seconds ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "But the journey
isn't safe for her duba da yanayin da take ciki, kai baka san yanda zaka lallabata ta hakura da tafiyar ba ne, it won't be good ace abu ya samu cikin jikinta...." Ajay yayi shiru cause he also reason with what Jay is saying but who will bell the cat? tun
da suka nufo mota bayan sun fito daga cikin pharmacy Khaleesat ta hade rai tana kallonsu, kawai ranta ya bata Jay cewa Ajay yayi kar a tafi da ita shi yasa ya fita daga motar ya bi sa, Ajay na shiga back seat ganin yanda ta sha kunu kamar warce ke jiran ki
ris ta fashe bai samu courage din ce mata ta zauna a Abuja har su dawo ba, Jay kuwa tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba cause ya ga alamar kiris take jira tayi masu kuka. The journey to Makurdi was so stressful and not fast saboda tsaye tsayen
da suka dinga yi a hanya duk dalilin Khaleesat, bini bini tace amai kuma idan an tsaya sai ta kasa yin aman, duk inda ta kyallara ido taga alamar gari sai tace a tsaya a huta don sosai ta gaji da tafiyar, gaba daya ta rasa inda zata saka kanta ta ji dadi,
idan taji zaman ya isheta sai ta kwanta a kafar Ajay, gashi in driver yayi gudu sai tace ma Ajay ya gaya masa ya rage gudu tana jin jiri, Jay dama toshe kunnensa yayi da earpod yana sauraron wa'azi wani lokacin idan yaga driver yayi parking baya ma sanin
dalilin parking din don kunnensa a toshe yake kar ma ransa yayi ta
ɓ
aci, cikin garin Makurdi suka nufa direct cause it's late evening time suka iso Benue, kuma baza su tsallaka ruwa by that time ba, Jay ya biya masu hotel da suka yi lodging a Makurdi, yayi
wucewarsa nasa room din ya bar mata da miji a reception, ya dade bai yi tafiya me cike da haushi irin wanda yayi yau ba, kawai sun yi tafiya ne kamar wasu gantalallu, da kyar Khaleesat tayi wanka tayi sallah bayan sun tafi nasu dakin, ko abinci ta kasa ci
sai tea da ta sha sannan ta sha magungunan da Ajay ya siya mata ta kwanta, Ajay dai na zaune gefenta yana kallonta, har ransa yake tausaya mata saboda yanayin da ta shiga, she was more than stressed yau, ya kai hannu forehead dinta yaji zafin jikinta babu
yawa, a hankali ta bude ido tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Ina yake maki ciwo?" Mikewa tayi ta shige jikinsa ya rungumeta, cikin sanyin murya tace "Kawai na gaji ne" Patting din bayanta ya dinga yi a hankali tana jikinsa, ba a dau lokaci ba bacci
ya dauketa, ya jingina da gado making her to relax fully a jikinsa ta yanda zata zama comfortable, shi ma a haka yayi baccin ko abinci bai ci ba. Washegari basu suka bar hotel din ba sai wajen karfe biyu na rana, Ajay gave Khaleesat enough time to rest, t
ayi bacci sosai ba kadan ba, kawai abinci ne taji bata son ci sai lemon kwali take sha kadai, kiris ya rage patient din Jay ya kare a hotel din, bai yi tunanin za su kai har rana suna hotel din ba don ma payment din kwana biyu yayi masu, Ajay ya ba Khalees
at Jacket dinsa ta saka don ita kadai ce bata taho da Jacket ba, ko da suka bar hotel din khaleesat taji ta samu karfin jikinta babu sauran stress a tattare da ita, amma suna isa inda za su shiga local paddle canoe din da zai kai su riverine area din da za
su je Khaleesat taji kanta ya fara juya mata saboda ruwan da ta gani babu iyakarsa, iya su uku ne a Canoe din sai Canoeist dinsu, tun da suka fara tafiya Khaleesat ta rufe fuskarta a jikin Ajay cause she was so uncomfortable, ko kallon ruwan bata son yi,
Ajay ya daga kai ya kalli Jay dake kallon ikon Allah, ta
ɓ
e baki Jay yayi alamar suna da aiki, ya ciro Nosemask dinsa ya saka, Ajay ya
ɗ
an yi murmushi ya rungumota jikinsa tayi lamo fuskarta a kirjinsa ta boye don kar ta dinga kallon ruwan, bayan wani lokac
i da fara tafiyarsu Khaleesat ta
ɗ
ago kanta da sauri daga jikin Ajay, ya rikota tun kan yace komai ta fara kwararo masa amai a jiki don yaki saketa, tas ta amaye duk lemon da ta sha daxu, Ajay na kallonta da damuwa ya dinga yi mata sannu, Jay yace "Allah y
a sauwake" Ko kallonsa Khaleesat bata yi ba, mai paddling din Canoe din ma sai sannu yake mata, Ajay ya cire shirt din jikinsa da aman ya ta
ɓ
a ya rage iya singlet a jikinsa, ya fara goge mata jikinta da inda aman bai ta
ɓ
a ba da rigar hannunsa, kallon Jay y
ayi, Jay ya dauke kai don kar ma ya sa ran zai basa Jacket din jikinsa, Ajay dai bai ce masa komai, murya can kasa Khaleesat tace "Kayi hakuri" Yana kallonta yace "It's okay Jeeddah, are you feeling relieved now?" Ta gyada masa kai, ta fara kokarin cire ja
cket din jikinta zata basa ya saka, yayi kasa da murya yace "Don't worry my love, I don't want you to catch cold" Tayi shiru tana kallonsa, Jay dai wani direction yake kallo daban, amma zuciyarsa taki barin ya hana Ajay rigarsa don shi haushinsa sai da yac
e kar su taho da Khaleesat amma yana shakkar yi mata magana gashi duk sun ma fita wahala a hanya don babu abun haushi a tafiya da ya wuce tsaye tsaye a hanya, after some minutes Jay ya kasa daurewa ya cire Jacket din jikinsa ya ba Ajay. Daga karshe suka is
a other side of the river bank, Jay ne ya fara sauka daga cikin Canoe din, sannan Ajay ma ya fita, yana stepping kafarsa kan soil din Abinsi mood dinsa ya so ya canza bayan wasu memories sun dawo masa birjik cikin kansa, hannu ya mika ma Khaleesat ta kama
hannunsa sannan ta mike, da taimakonsa ta sauka daga cikin Canoe din tana bin kauyen da fishing ne major occupation dinsu da kallo, kauyen kewaye yake da ruwa ga kwale kwale masu yawa a bank din ruwa ta every direction, Ajay ya ciro nosemask dinsa ya saka,
Khaleesat ta kallesa a hankali tace "Nima zan saka" Ya ciro wani mask din ya saka mata da kansa, tafiyar kusan minti sha biyar suka yi a kafa, duk inda suka bi kallonsu ake, Ajay yaki sauke Mask dinsa don wasu daga mutanen garin sun san shi, a haka suka i
so karamin compound din Ozhi, sai a sannan Ajay ya sauke nosemask dinsa yana kallon yarinyar dake