Showing 48001 words to 51000 words out of 641791 words
jefa masa wani kallo tayi hanyar dakinta, Yana kallonta da kyau yace "I will definitely deal with you" Ita dai tuni ta shige dakinta ta kulle kofar da makulli, Jay na kallonsa yace "M
e yasa zaka shigo mata gida kamar tsohon barawo?" Ajay yace "Za kayi bayanin me kake yi da mace under the same roof in America, macen ma da ka kusa haifa, i promise to report you back home, ita kuma i will teach her the lesson of her life" Yana kai wa nan
ya fixge laptop dinsa a hannun Jay, Jay dake murmushi yace "Babu abinda ka isa kayi mata don ta gaya maka gaskiya Malam, kai waye da baza a gaya ma gaskiya ba" Tuni Ajay ya fice daga parlon, Jay ya zauna kan kujera ya dafe kansa yana dariya, the incident w
as just funny to him, kallon kofar dakinta yayi yana mamakin dama wai haka yarinyar nan take amma take ma saurayinta kuka? Mikewa yayi ya nufi dakin nata yayi knocking kofar yace "Halysaah" sai da ya kirata sau uku sannan ta bude kofar a hankali tana leka
parlon kana ganinta kasan a tsorace take, dariya yayi yace "Kinsan waye shi da kika masa rashin kunya Halysaah?" Ta wani turo baki tace "To ni ina ruwana da koma wanene shi, saboda me zai shigo min gida kamar wani barawo, where is it done that way? Ni dai
wallahi kar ya sake zuwa min gidan nan in ba haka ba in kira 911" Jay dai sai sauraronta yake, can yayi murmushi yace "So dama kina da baki haka amma kike ma saurayin ki kuka?" Khaleesat ta wani kallesa ta hade rai tace "Ni bana son haka" still smiling yac
e "Ok, sorry" keeping a straight face tace "Ya tafi?" Jay ya juya zai bar wajen yace "Ya tafi mana" Da sauri tace "Plss ni dai kayi masa magana kar ya sake zuwa, if there is anything ai sai ya kira kaje can gidanku ka samesa kawai ba sai ya zo nan ba" Jay
dai murmushi kawai yake yace "Ohk" parlor taga ya tafi, ta koma dakinta ta zauna bakin gado, har sannan gabanta faduwa yake, ita kanta bata san inda ta samu courage din gaggaya masa abubuwan da ta gaya masa ba, ko don dama tana jin haushinsa ne yasa ta sam
u irin wnn courage din oho, bata fito daga dakinta ba sai da tayi sallan zuhur, a hankali take tafiya ta shigo cikin parlorn, gani take kamar zai sake dawowa gidan at anytime, ai ko wallahi yan sanda zata kira masa, Zaune taga Jay a parlon yana danna wayar
sa, tana tsaye bayan kujera tace "Did u warn him not to come back plss?" Jay yace "To ke meye damuwarki ba kin masa warning kar ya sake dawowa ba, ai bazai dawo ba" Kamar zata yi kuka tace "Wallahi zai iya dawowa, kuma in ya dawo baka nan ya zan yi?" Dariy
ar da yake dannewa ne ya taho masa yace "Ina kuwa zan san yanda za ki yi, ke wa ya aike ki yi masa rashin kunya? Da sai ki yi shiru da bakinki har in fitar da shi daga gidan, Laptop dinsa na dauko daga can gida yana bacci ban san akwai aikinsa da zai yi pu
t foward ta email ba, yana ta kiran wayana kuma ina bacci na sa wayar silent, that was what brought him here" Zaunawa tayi kan kujera tace "That doesn't still warrant him ya shigo gidan mutane kai tsaye, ko magana bai min ba ina bude kofa ya kusa bangajeni
fa ya shigo parlon, am i a joke to him?" Dariya Jay yayi yana gyada kai yace "This energy u used in attacking him Allah ya baki irin energy din kiyi using ma Boyfriend din ki" Wani kallo Khaleesat tayi masa, shi dai murmushi kawai yake still not looking a
t her yace "Naga kamar kin damu da abinda kika masa, ko in kirasa ki basa hakuri ta waya komai ya wuce?" mikewa tayi a takaice tace "Allah ya kiyaye" Daga haka tayi wucewarta kitchen, shi dai murmushi kawai yake looking at a different direction, yasan yau
da kyar Ajay yayi bacci akan abinda tayi masa. Bayan Khaleesat ta gama girkin da take ta fito parlor tana kallon Jay ganin fita zai yi don har ya shirya yana saka agogon wrist dinsa without looking at her yace "I think sai gobe zan dawo in sha Allah" Ta ma
rairaice amma bata ce masa komai ba, har cikin ranta ta fara jin tsoron kasancewarta ita kadai a gidan, ya
ɗ
an kalleta yace "Any problem?" Ta hade rai tace "Toh ka bani makullinka idan ka zo goben sai kayi knocking in bude maka kofar" Da mamaki yace "Why?"
Tace "So that baza kaje ka ajiye key din recklessly ba wannan mutumin ya gani ya dauka" Yayi dariya yace "To ya dauka yayi me da shi?" Ta nufesa tace "Bani" ba musu ya bata makullin ta amsa sannan a hankali tace "To abincin fa?" Yace "Abinci? Wani iri?" B
ata tanka sa ba ta juya ta koma kitchen din, after some minutes sai ga ta ta dawo da plate din rice and stew, ya
ɗ
an bude ido yace "Wa zai cinye duk wannan?" Tace "Kai mana" Ya zauna sannan ta mika masa abincin, yana girgiza kai yace "It's very plenty" tac
e "Should i get you water?" Yace "I will appreciate that" kitchen din ta koma ta dauko masa ruwan gora da drink din gwangwani, yace "Thank you Halysaah" dakinta ta wuce, after a while taji yayi knocking kofar dakinta, bayan ta bude yace "Zo ki bude min kof
ar zan tafi" Makulli ta dauko ta tafi ta bude masa kofar yace "Thank you, see yah tomorrow" ita dai bata ce komai ba ya fita daga parlon ya nufi garage, a hankali ta kulle kofar da makulli sannan ta tafi window ta
ɗ
an bude labulen tana kallonsa har ya bar
garage din after some minutes, Sake curtain din tayi, walking slowly ta tafi kitchen, bude abincin da ya rufe tayi taga kadan ya ci a ciki, Allah yasa yayi spoon hudu, naman ma kawai daya ya ci, kulle abincin tayi ta dawo parlor ta zauna, dai dai nan taji
anyi knocking kofar parlon mikewa tayi da sauri tana kallon kofar a tsorace, da kyar tace "Waye??" Muryar Safiyyah taji, lkci daya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tafi ta bude kofar, Safiyyah tace "Har kin gama laundry din?" Khaleesat tace "Na gama" Safiy
yah tace "Housemate din naki ya fita kenan?' Khaleesat tace "Eh" Safiyyah tace "Jiya da daddare da kika gaya min ya zo gidan ta chat wallahi nayi farin ciki, don mutumin na da kirki sosai" Khaleesat bata tanka ta ba, ta koma cikin parlon ta zauna tace "Ban
gan ki da laptop dinki ba" Safiyyah tace "Abeg i will use urs, bani da strength din dauko laptop, kin yi girki kuwa? Don yunwa nake ji, wancen er iskar matar faten wake tayi saboda tasan ba na ci,
hegiya dama bayerabiya ce ta wajen uwarta ai" Dariya kawai
Khaleesat tayi ta mike ta tafi kitchen, abincin ta zubo ma Safiyyah, ita kuma ta dau wanda Housemate dinta ya rage, ta dauko masu ruwan gora da lemon kwali daya....
07087865788✍
🏻
✨✨
HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍
🏻
16.....
Ko da wasa Kha
leesat bata ba Safiyyah labarin abinda ya faru tsakaninta da Ajay ba, amma fa bata da rest of mind gani take kamar zai iya dawowa gidan at anytime, upon all her restlessness bata ji tayi da ta sanin abinda tayi masa ba, dama haushi yake bata, Safiyyah na k
allonta tace "Ke kwana biyu shiru banji kince ga abinda Abdul yayi maki ba ko dai ya fara canzawa ne? This is so unusual, ko baki gaya min ba in dai ya maki wani abu you are always moody in school, ta haka nake ganewa" Khaleesat na powering laptop dinta ta
tabe baki tace "Ni ina naga wannan time din yanzu ga exams a gabana" Safiyyah tace "Atoh dai, wallahi naji dadin da kika fara daukar shawarata kina fita sabgarsa, sauranki abu daya yanzu" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, Safiyyah ta gyara zama tace "Saur
a ki fara mayar masa da magana, in ya gaya maki daya ki gaya masa biyar" Ita dai Khaleesat bata sake ce mata komai ba tana neman softcopy na course din da za su yi studying tare da Safiyyah. Bayan tafiyar Safiyyah... Khaleesat ta wanke utensils da suka yi
amfani da sannan ta wuce dakinta, wayarta ta dauka ta shiga WhatsApp don ganin ko Ummanta tayi mata reply din message da ta ajiye mata daxu, wajen karfe goma da rabi tana shirin kwanciya wayarta ya fara ring, dauka tayi taga Abdul ne ke kiranta, ta dinga k
allon wayar, tun sanda Ummanta tace mata tana ganin kamar lkci aka tsayar take wani jin tsanarsa a zuciyarta, gashi yaki gaya mata ko da gasken an tsaida lkcn ko ba a tsayar ba don Ummanta ba wai ta tabbatar bane ita ma a gari ta ji, dama tana Nigeria din
ne ta san gun warce zata je taji ko hakan ne ko ba haka ba,
ɗ
aga kiran tayi kafin ya katse ta kai kunne, muryarta kamar me bacci ta gaishesa, ya amsa, a hankali tace "Ya aiki?" Yace "Lafiya lau" Shiru tayi bata sake cewa komai ba, yayi ƙasa da murya yace "
I don't know, kawai ina missing din ki ne yau, i want to be with you Baby" Ta kauda kai kamar irin yana kusa da ita din nan tace "Um" Yace "Yaushe za ku fara jarabawan?" Tace "Nan da wata daya" A hankali yace "Ohk, sai da safe, naga kamar kin fara bacci" T
ace "Um, ina son tashi inyi karatu ne anjima shi sa na kwanta da wuri" Yace "To ci gaba da baccinki, sai mun yi magana" Daga haka ya katse wayar, ta jefar gefenta ta ci gaba da chatting da take da Ummanta. Washegari lahadi Khaleesat na zaune dakinta tana m
orning Supplications dinta taji ana kwankwasa kofar parlor, wayarta ta jawo tana duba agogo taga bakwai ya wuce, ta daure ta mike tana tafiya a hankali ta fito parlor, bayan ta karasa bakin kofar with calmness tace "Waye?" Taji muryar Housemate dinta yace
"Good morning" bude kofar tayi ta koma gefe ya shigo, sau daya ya kalleta yace "How was ur night" Ta kulle kofar tace "Alhmdlh" Materials din hannunsa ya ajiye saman 1 seater sannan ya kwanta kan doguwar kujera, ita dai bin sa tayi da kallo taga har ya kul
le idonsa yana gyara kwanciyarsa alamar bacci zae yi, tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ta karasa azkar dinta sannan ta kwanta. Har wajen karfe daya na rana Khaleesat bata fito dakinta ba, ta
ɗ
an juya daga kwancen da take tana kallon kofar dakinta jin
ana knocking, kiranta taji Housemate dinta ke yi, mikewa zaune tayi still tana kallon kofar amma bata sauka daga kan gadon ba, Calmly tace "I can hear you" Yace "Are you alright? Naga kamar baki yi breakfast ba ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, bude kofar
taga yayi, ta gyara blanket din jikinta tana kallonsa, ya tsaya daga bakin kofar dakin yace "Hope nothing?" Ta langwabar da kai tace "Nothing" Yace "To me yasa baki fito kinyi breakfast ba or are you fasting? Beside today is sunday" Ta kauda idonta tace "
Kawai dai..." Sai kuma tayi shiru, ya karasa cikin dakin yace "Kawai dai me?" Kamar baza tace komai ba sai kuma dai tace "Ina jin ciwo a kafana ne" Yace "Ciwo a kafa kuma? Yana maki haka ne?" A hankali tace "Once a while" Shiru yayi jin abinda tace, can ya
ce "Then what is the cause?" Ta
ɗ
an kallesa, sai kuma ta bude hannu alamar bata sani ba, yace "Kun ta
ɓ
a zuwa hospital a kan hakan?" Ta dai yi shiru without looking at him, sai kuma tace "It's fine, i will get better before evening in sha Allah" Ya juya as
if trying to diagnose without examination the cause of her leg pain at her age, sau
daya ya kalli gaban dressing mirror dinta sai kuma ya juyo yana kallonta yace "Ok i get, Allah ya sauwake..." Ta
ɗ
an kallesa, yace "Try getting a hot shower, you will feel
better" Juyawa yayi ya fita daga dakin, a hankali Khaleesat ta koma ta jingina da pillow, ko tashi tsaye bata jin zata iya a yanzu dai, kilan zuwa can anjima ta
ɗ
an ji relieve before she can stand up and do anything, kiran Abdul ne ya shigo wayarta ta kife
wayar taki dagawa don ko magana bata so, after some minutes ta kalli kofarta jin knocking at the same time ya bude kofar dakin ya shigo ciki rike da cup din hot chocolate, sauke idonta tayi daga kallonsa ya karasa har side din da take ya duka yana mika ma
ta Mug din hot chocolate din yace "Try drinking this, will get u pain reliever now" Ta amshi Mug din without looking at him a hankali tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, yana fita kiran Ab
dul ya sake shigowa wayarta still taki dagawa daga karshe ma tayi silencing wayar, khaleesat na gama shan hot chocolate din ta ajiye cup din a bedside drawer sannan ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, kamar zata kira Safiyyah daxu wajen karfe sha biyu
sai kuma ta fasa hoping the ache will subside, har ta fara bacci Housemate dinta yayi knocking wajen karfe biyu almost 20 mins bayan fitarsa daxu, sai da ta amsa sannan ya bude kofar, ita dai bata juyo ba, ya zaga ta inda take calmly yace "Are you sleeping
Halysaah?" Ta bude ido tana girgiza kai, ya ajiye ledan abincin hannunsa da pain reliever da ya siyo mata yace "Baki yi hot shower da nace kiyi ba?" Tace "Zan yi" Yace "Ohk ga maganin sai ki ci abinci ki sha" Ta mike zaune without looking at him, a hankal
i tace "Thank you" Yace "Zan fita but i will come back around 6pm in sha Allah" Tana kallonsa tace "Toh makullin gidan fa?" Ɗan murmushi yayi yace "Ai a jikin kofar kika bar sa daxu da kika bude min da safe" Tace "Amma baza ka tafi da shi ba ai" Yace "To t
aso ki kulle kofar" Ta wani kallesa, er dariya yayi yace "Shi fa Ajay nasan yanxu kuma ya mance abinda ya faru tsakanin ku, may be sai ranan da ya kara ganinki zai tuna, but for now i am assuring you ya mance wallahi he is even busy with his upcoming defen
se, beside you misperceived him, Ajay is more than nice and calm, ba shi da matsala, kawai dai shaidan ne ya saka rashin jituwa tsakaninku tun a ranan da ku ka hadu" Khaleesat dai ta kyabe baki don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata ta
ɓ
a yarda da abinda yake
fadi ba, Jay yace "Baki yarda ba ko?" Ta buda ido sosai tace "To dama saboda me zan yarda?" Dariya kawai yayi yace "Take care of ur self Halysaah, in kin ci abincin ki sha magani, let me get you bottled water" Daga haka ya nufi kofa ita dai ta bi sa da ka
llo har ya fita, sai gashi ya dawo mata da ruwan gora mara sanyi ya ajiye a inda ya ajiye mata ledan abinci da magani wato bedside drawer, yace "See yah later" a hankali tace "Thank you, and pls do not mishandle the key" Murmushi kawai yayi ya gyada mata k
ai ya fita daga dakin ya kullo mata kofar, ta sauke idonta kasa, after some minutes ta dau ledan abincin da ya ajiye mata a hankali tana budewa don ganin abinda ya siyo mata. Karfe shidda saura Khaleesat na zaune kasan dakinta ta kwantar da kanta jikin gad
o tana voice note da Ummanta, zuwa sannan she is feeling very much better don har ta gyara dakinta ta wanke bandaki tayi wanka, parlor ne dai taji bazata iya gyarawa ba, wajen karfe hudu suka yi chatting da Safiyyah tace mata zata zo karfe bakwai, Khaleesa
t ta dan yi jim bayan taji kamar an bude kofar gidan, gabanta ne ya fadi bayan Ajay ya fado mata, ta ajiye wayar hannunta a hankali tana kallon kofar dakinta, after few minutes taji an yi knocking kofar dakin, she felt a bit relieved, with calmness tace "I
can hear you" Taji muryar Housemate dinta yace "Can i open the door?" Tace "Okay" bude kofar dakin yayi yana daga bakin kofar a tsaye yace "Good evening Housemate, how are you feeling?" Tace "Da sauki" Yace "Are you sure?" Sai a sannan ta daga kai ta kall
esa, ta dan kwantar da kanta gefen gado tace "It's better than before" Yace "To Allah ya sauwake, where you able to go to the kitchen?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk" Har zai kulle mata kofar sai kuma ya tsaya yace "Ko mu dan yi strolling as exercise, aroun
d the neighborhood, it will help you feel much better too" Khaleesat ta daga ido ta kallesa, yace "I will be waiting for you at the parlor, make sure to put on ur jacket cause it's freaking cold outside" Yana fadin haka ya fita daga dakin, Khaleesat dai na
ta zaune kamar me nazari, it took her almost 5 mins of deciding kafin ta mike a hankali, veil dinta kawai ta dauka ta yafa ta dau wayarta tana tafiya a hankali ta fito daga cikin dakin, tsaye ta gansa ya jingina jikin pillar dake kusa da study area