Showing 315001 words to 318000 words out of 641791 words
ne Fulani, kin samu Jawwad din kuwa kin fito masa a mutum dinki? Jibi ne juma'an nan fa, kinsan halin Mai martaba a sanda ya
ga mun tubure bama son abu to a sannan yake daukar abun nan da muhimmanci" Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ana idar da Sallah daxu na tafi bangaren Jawwad din Fulani, kinsan tun da nayi wannan magana a wajen meeting ban kara saka sa a idona ba sai y
au da naje har bangarensa na jira ya dawo daga masallaci, in takaice maki dai daure ni da jijiyoyina kawai Jawwad yayi daxu da asuba, wai ai shi bai san zancen da nayi na cewa bana son auren ba tunda shi ba haka nace masa ba kuma shi yana nan a kan abinda
na fada masa da farko, wallahi Fulani kasa aiwatar da abinda ya kai ni dakinsa nayi, bana son duk wani abu da zai damesa ko ya
ɗ
aga masa hankali...." Aunty ta saki baki tana kallonta da mamaki, can ta gyada kai tace "Tabdi, ai kuwa nan gaba sai kin gwammac
e dama kin bata masa ran kin masa kaca kaca an wuce wajen da dai abinda zaki fuskanta nan gaba, don wallahi wallahi kinji rantsuwar musulmi fulani zai kai ya kawo ke da Jawwad sai gani sai hange daga nesa, ke kinsan su waye buzaye kuwa? Naga kamar kina
ɗ
au
kar wannan issue din sakwa sakwa fa, wallahi in zaki cire kulafucin yaron nan a ranki Kiyi abinda ya kamata to ki cire, su fa Buzayen nan ko Nijar din ma an san ba can ne asalinsu ba, nomads ne fa da suka yada zango a Nijar sai kuma suka ki tafiya suka yi
kaka gida a can, wallahi in har kika yi kuskuren zuba ma Jawwad ido ya auri yarinyar nan a sunan kina tausayinsa sai kin yi da kin sanin da baki ta
ɓ
a yin irinsa ba a rayuwarki, zaki san su kika haifa ma
ɗ
a, yanxun ma ai kin fara ganin haka tunda gashi gida
me tsada ya cire miliyoyin kudi babu sanin ki ya siya masu, Jawwad ya ta
ɓ
a yin abu da makudan kudi bai sanar maki ba? Ai tun daga wannan action din nasa ya kamata ki gagara bacci da daddare kuma" Mami ta dafe kai tace "Na rasa ta inda zan billo ma lamarin
nan Fulani, yanxu fa saboda gudun bacin ransa har ce masa nayi ya bari ya auri Hadiyah zuwa nan da wata biyar sannan sai ya auri ita buzuwar, wai fa nan duk dubara ce nake masa, nasan yana auren Hadiyah suka tare zai manta da wata bazawara can, kuma tunda
sun gama Phd din nasu ko Amurkan ma bazan bari ya koma ba ta yanda bazai ganta ko by mistake ba tunda a Bauchi zai zauna da Hadiyah ai, to amma kinsan me yaron nan yace min? Wallahi ba kunya ya kalli idona yace min shi wata biyar sun masa yawa in rage in
mayar sati biyu ko uku, a sannan na kara shan jinin jikina da yaron nan Fulani" Aunty tayi wani dariya tace "Kin ji ko? Ai sun shanyesa sai abinda kika gani, to ki bar sa a lokacin da yace din tunda tsoronsa kike" Mami tace "Ban gane tsoronsa nake ba" Aunt
y tace "To haka ne mana Fulani, ka haifi yaro amma kana tsoron tunkarar sa da magana, da nayi niyyar kawai in zuba maki ido tunda ke in an kawo maki shawarar da zai amfane ki sai ki yi fatali da shi ki gwale mutum, to bari zan fito maki a mutum yanxu Fulan
i in dai ba ta karkashin kasa kika bi ma Jawwad ba to kina gaff da shiga uku wallahi, kin ji kina gani mace zata rabaki da tilon
ɗ
an ki, yanxun ma me ya rage? Jawwad da na sani mai kawaici da gudun bacin ranki har ya tsaya yana ja in ja dake yace shi lalla
i sai yayi abinda bakya so, tun farkon lamarin nan nake nuna maki hanya kina kaucewa, ga abu har yayi nisa yanda bama zato, ta yanda suka bi suka juya hankalinsa mu ma ta nan din dai za mu bi mu dawo da hankalin nasa, ai ba wajen boka nace zan kai ki ba Fu
lani balle kiyi ta tsoron kauce hanya don nasan abinda kike tsoro kenan, da ilimina nima fa kin sani, to don me zan yi abinda zan kauce hanya, in dai zaki ji ta nawa ki yi shiru ki bar sa a sati ukun da yace idan ya so sai a daura auren nasa da Hadiyah wan
nan Juma'an tunda haka Mai martaba ya tsara, ana daura auren mu kuma muna abinda ya kamata a gefe, wallahi wallahi sai kinyi mamakin yanda Jawwad zai mance da wata buzuwar bazawara can, wai ke baki yi mamakin yanda Walid ya nutsu ba ya dena abubuwan nan da
yake har da su
ɗ
aga kwalba? Bazan boye maki ba taimako ake ta nema masa shi yasa kika ga Walid a haka yanxu, don haka shi ma Jawwad taimakon za mu nema masa don wannan halaka yake son fadawa Fulani" Mami dai tayi shiru ta rasa abinda zata ce, amma da alam
a maganar Aunty ya fara tasiri a zuciyarta, Aunty tace "Don haka in ma ke kina dar a zuciyarki har yanxu to kawai ki bar min wuka da nama, kawai magana ce ta kudi kuma in sha Allahu sai kin gode min wallahi, sati daya yayi yawa zaki ga aiki da cikawa" Mami
ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ni fa na zata maganganun da na gaya ma Mai martaba zai yi zuciya ya aura ma
ɗ
an sa bazawarar sai naga ba haka ba kuma, wallahi da ni muguwa ce tsaf zan san yanda zanyi in juya auren ya koma kan Junaid shi ya auri bazawara
n dama ai kince tare kika ganta da Junaid din a Amurka" Aunty ta
ɗ
an bude ido jin abinda Mami tace, da sauri tace "A'a ba sai an kai ga haka ba Fulani, kin ga wannan ai babban magana zai zama a masarautar nan da ma garin Bauchi baki daya, mu dai bakinmu al
ekum mu yi abinda ya kamata hankalin Jawwad ya dawo jikinsa ya mance da wata bazawara" Mami tace "To shikenan Fulani, Nagode kwarai da gaske" Aunty tace "Haba ai yi ma kai ne, banda ma yan zugi sun shiga tsakaninmu a masarautar nan ai ke din mutuniyata ce
a shekarun baya, yanxu dai ki nuna ma Jawwad kin ji kin amince sati ukun da yace sai yaje yayi ma ubansa Mai martaba magana a
ɗ
aga auren" Mami tace "Zan sanar masa in sha Allah, bari in je ko breakfast ban yi ba" Daga haka Mami ta mike ta nufi kofa ta fita
, Aunty ta kyabe baki murya can kasa tace "In bari a juya aure kan Junaid? Ashe ina ma son sa da alkhairi in har na bari aka yi haka, ai sai dai in sa a aura masa warce zata zamo ajalinsa in ma na bari yayi auren kenan...." Shiru Mai martaba yayi yana kall
on Jawwad bayan ya gama sauraronsa, after a while ya sauke ajiyar zuciya yace "Fulani ce tayi maka wannan tsarin ko?" Jay ya sauke idonsa yayi shiru don bayan sun gama magana da Mami few hours ago sai da ta jaddada masa kar ma yace ma Mai martaba yayi maga
na da ita, Mai martaba yace "Nasan duk tsarinta ne wannan, so kana nufin yanxu in sake turawa a sanar masu na canza maganar da nayi shekaranjiya kenan?" A hankali Jay yace "Ai ba sai an tura ba ranka shi dade, ta waya ma idan aka sanar masu ina ga ya wadat
ar" Mai martaba dai yayi shiru yana kallonsa, bayan wasu mintoci yace "Baza a
ɗ
aga daurin auren nan ba Jawwad, ranan Juma'ah kamar yanda na tsara za a daura auren, nothing is going to change that" Jay ya daga kai yana kallonsa a sanyaye bai iya yace komai
ba.... Ko da ya koma bangaren Mami ya sanar mata yanda suka yi da Mai martaba kuka ta sakar masa tace "Ni kuma in dai ba nan da sati hudun da muka shirya da kai ba wallahi Ahmad kayi aure ne ba da yawu na ba, ba kuma da amincewata ba, kuma bazan ta
ɓ
a saka
maka albarka a wannan aure ba" Sosai jikin Jay yayi sanyi yace "Don Allah Mami ki yi hakuri, ni nasan yanda zan yi convincing Mai martaba zuwa lokacin da kika ce kina son ayi auren" Cikin kuka Mami tace "Da dai yafi maka, duk da bana son auren nan haka na
kai zuciya nesa na amince amma nace ga yanda nake son ayi min a matsayina na mahaifiyarka nan ma sai a tauye ni a nuna ban isa ba?" A hankali Jay yace "Kiyi hakuri, yanda kike so in sha Allah haka za ayi" Ba karamin Courage Jay yayi gathering ba ya sake ko
mawa gun Mai martaba bayan Magrib, ya risina kai cikin ladabi yace "Ka gafarce ni ranka shi dade, i don't mean to disobey or disagree with you in any way, amma kayi hakuri ranka shi dade ka
ɗ
aga wannan aure zuwa nan da wata daya kafin nan nayi shirye shiry
en da zan yi a tsanake" Mai martaba ya
ɗ
an yi murmushi ya jinjina kai bai dai ce masa komai ba, shigowar Aunty Parlon yasa Mai martaba yace "Zaka iya tafiya Ahmad, I've heard you" Jawwad ya mike yayi ma Aunty barka da yamma sannan ya fita daga parlon. Waje
n karfe tara Ajay ya shiga Bedroom din Jay yana kallonsa yace "Don me zaka samu Mai martaba kace a
ɗ
aga auren?" Jay yace "I have no Choice Ajay, haka Mami tace take so" Ajay yace "Must you listen to everything?" Calmly Jay yace "C'mon Ajay, she is my mothe
r, ta yaya zan yi aure babu blessings dinta? Yanxu ba cewa tayi bata son auren kwata kwata ba kamar yanda tace few days ago, kawai so take sai na fara auren Hadiyah da 4 weeks sannan in auri Halysaah, idan ina son ganin dai dai ai abinda tace take so shi z
an yi" Ajay ya girgiza kai yace "Ina me tabbatar maka wannan wani plan ne nasu suka hada ita da Aunty cause ita ke zugata...." Jay yace "What ever, ni dai nasan wata dayan da tace bazai cika ba ta canza min magana, shi yasa ban damu ba" Ajay ya sauke ajiya
r zuciya yace "Abba isn't happy with this, he wasn't expecting this from you, considering the fact that he supported you from the onset..." Jay yace "I have no choice kamar yanda nace maka Ajay, Mami ce ta sa inyi haka and I did that for peace to reign" Aj
ay ya
ɗ
an yi murmushi yace "At the end ina ga fa sai dai tayi hakuri ta saka albarkan nan da tace bazata saka ba daga baya cause I am assuring you come Friday sai Abba yayi abinda ya tsara, saboda wani reason mara ma'ana bazai canza maganarsa ba a maida sh
i karamin mutum, come Friday you will be groom to 2 bride...." Jay na kallonsa da damuwa yace "Haka Abba yace maka?" Ajay ya
ɗ
aga kafada bai ce komai ba ya juya ya fita daga dakin, Jay ya rasa ma me zai yi ko kadan bai son bacin ran Maminsa gashi har da ku
ka tayi saboda shi, nazarin maganganun da zai sake samun Mai martaba da shi ya fara yi, ya fi minti ashirin pondering on what to say to the king for the third time, daga karshe ya mike ya fita with the hope that wannan karan Sarki zai janye batun auren zuw
a nan da wata daya. Karfe goma saura Jay ya tafi bangaren Ajay, a parlor ya samesa yana kallon kwallo, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana kallonsa yace "Daga wajen Mai martaba nake" Ajay ya
ɗ
an kallesa, sai kuma yace "Ya ku ka yi da shi?" Jay yace "I
am just hoping he consider all what I said"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788
HALYSAAH 9
8
Washegari da safe Jay ya tafi bangaren Maminsa don gaisheta, bayan ta amsa gaisuwarsa tana kallonsa tace "Ya ku ka yi da Sar
ki?" Jay ya sauke idonsa yace "Mami sau uku ina yi masa magana...." Mami tace "Ba sau nawa kayi masa magana nake tambayarka ba Jawwad, cewa nayi ya ya ku ka yi da shi daga karshe?" A hankali Jay yace "Kinsan bazai yi magana me tsayi ba Mami, he was quiet a
t the end kuma yace min ya ji, i am just hoping he is convinced kuma zai yi considering duk abun da na gaya masa, don haka ko da zaki ga wani abu daban Mami ki sani i tried my best in maki yanda kike so, duk yanda nake jin nauyin Mai martaba i confronted h
im thrice just to please you Mami" Sallaman Aunty yasa Jay yayi shiru ya daga kai yana kallonta, Aunty ta karaso cikin parlon tace "Fatan mun wayi gari lafiya Fulani" Mami tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ya kwanan su Zuwaira?" Aunty ta nemi kujera ta zauna
tace "Alhamdulillah" Jay ya sauke idonsa ya gaida Aunty ta amsa sannan ya mike yana kallon Mami yace "Zan
ɗ
an fita Mami, sai na dawo" Aunty tace "Zaka
ɗ
an fita ko dai za ku fita, Boss din naka na can naga ai ya shirya yana jiran ka kaje ka ja maku mota" K
o kallonta Jay bai yi ba har ya fita daga parlon, Aunty ta ta
ɓ
e baki tana kallon Mami tace "Tare fa za su fita da Junaid don naga Junaid din ya fito yana rike da makullin mota" Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta daban a ranta, ba kadan maganar
auren nan ya tsaya mata a rai ba, Aunty ta gyara zama tace "To yanxu yaya ake ciki? Mai martaban ya yarda a
ɗ
aga daurin auren ko kuwa?" Mami ta girgiza kai tace "Ina tantama Fulani, don sau uku Jawwad din ke samunsa da maganar amma yaki ce masa komai, kin
ga kuwa bai amince ba kenan" Aunty tace "Sai kace ba Sarki ba, ai ni nasan ko don ya nuna mana iyakar mu fa sai yayi abin nan da yaga ba ma so, ga abu ya zo a kurarren lokaci balle a bi ta kasa a lalata, amma dai kin san abinda zai faru?" Mami na kallonta
tace "A'a sai kin fada" Aunty ta mike ta koma gefenta ta zauna tana kallonta.... Ko kallon Jay Ajay bai yarda yayi ba ya nufi motarsa, Jay ya bi sa da kallo yace "Ni zaka walakanta?" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Since when did I become ur dri
ver Jay, if you are not too fine to drive ga drebobi sai wanda ka zaba a gidan nan, why do I have to drive you, on a serious note bazan je unguwan nan me nisa ba da daddaren nan, gwara ma ace hanyar Kano na kama in san tafiya me nisa dama zan yi kawai, hab
a ai unguwan yayi nisa sosai ga hanyar babu kyau ga dare yayi, throughout the day time me yasa baka ce in raka ka ba sai da daddaren nan, beside i told you i am meeting a friend yana jirana, you met me already prepared to go out balle kace kirkiro fitan na
yi" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay yace "Zaka je wajen budurwar ka sai kace sai an raka ka, idan nace bazan je ba kuma ya zama issue, kaje for once kai kadai mana, haba you are stressing me wallahi" Kallonsa kawai Jay yake yaki tanka sa, Jin Jay yaki ce
wa komai kuma bai fasa kallonsa ba yace "To in har zan je sai ka min full tank, sannan akwai shopping da zan yi online the bill is on you, agreed?" Jay ya wani kallesa, haka nan babu yanda Ajay ya iya suka bar gidan a cikin motarsa yana mita, Jay dai ko ka
llonsa bai yi ba, karfe tara saura mintuna Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Aunty Murja, Jay ya ciro wayarsa after some seconds ya kai kunne duk da ba kira yake ba don yasan ko ya kirata ba lallai ta
ɗ
aga ba, he tried calling her once yesterday bata
yi picking ba kuma bata biyo sa ba, can ya kalli Ajay yace "Can you pls call Halysaah's line, I can't reach her" Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma yace "You can't reach her? To ni ne zan iya reaching dinta kenan, ina ce same network muke using, in baka sa
meta ba ai nima haka, better still ka aika yaro cikin gidan ya kirata mana" Jay ya dau wayar Ajay dake ajiye, shi dai Ajay kallonsa kawai yake, number Khaleesat yayi dailing sai ga suna ya fito anyi saving as Jay's girl, Jay ya daga kai ya kallesa, dariya
Ajay yayi, shi kansa bai ma san me ya basa dariya ba, May be the way he saved the contact, can dai ya fixge wayar yayi sending kiran, Jay yace "Sunanta ne baka sani ba?" Ajay yace "Oho, Haseenah kake ce mata ko Haseelah" kiran na shiga bayan
ɗ
an lokaci Kha
leesat ta
ɗ
aga amma tayi shiru, Ajay yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru Malama?" A hankali tace "Good evening" Yace "Ana jiran ki a waje" Tace "Wa?" Yace "Kar ki bata ma mutane lokaci Malama" Daga haka ya katse wayarsa ya daga kai ya