Showing 501001 words to 504000 words out of 641791 words
ajiyar zuciya yace "Wa yace maka ana saki a gidan nan? Me yasa zaka yi creating room na kananun zance a masarautar nan?" Jay yace "Tuba nake Mai martaba" Sarki yace "Tun maganar nan bai fita ba ka maida Hadiyah dakinta, na
san tayi learning lessons dinta yanxu dai" Jay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace "A gafarce ni ranka shi dade, amma...." Kasa ci gaba yayi, Sarki yace "Amma me?" Yayi kasa da murya yace "Ina son a bani lokaci Mai martaba, bana son ya kasance ba
da son raina na maidata ba tursasa ni aka yi nayi hakan...." Sarki dai kallonsa kawai yake, sam baya son forcing Jawwad on anything yanxu, duk abinda yake so in dai bai sa
ɓ
a addini ba ya dau alwashin barin sa yayi abun nan without hindrance, Sarki ya sauke
ajiyar zuciya yace "Take ur time, but ka duba zumunci Jawwad, kar ka mance Hadiyah er uwarka ce ta kusa, it's a big slap to this Emirate ace maganar abin nan da ya faru ya fita...." Jay dai bai ce komai ba kansa a kasa, Sarki yace "Sai ka toshe kunnen ka
da duk wani magana da zai biyo baya most especially from ur Grandmother" Jay ya gyada masa kai kawai don shi kam sai dai su masa duk abinda za su yi babu niyyar maida Hadiyah a zuciyarsa, dama last week Mai martaba yace masa zai je Nijar to check on his ne
w company, yana zuwa kasar zamansa zai yi a can har sai ta fita iddah sannan ya dawo, Mai martaba ya kalli Ajay yace "Jeeddah kuma gobe za aje daukota a dawo da ita gidan nan, don mun yi maganar hakan da Hajja, Allah ubangiji ya bata lafiya" Ajay ya sauke
idonsa yayi shiru, Walid ne ya shigo parlon da sallama, ya zauna kasan carpet ya gaida Mai martaba, Sarki ya amsa sannan ya kalli Jay yace "Da Walid za ku tafi Nijar sati me zuwa, kafin nan ina son kai da Junaid za ku fara zuwa Calabar....." Ko numfasawa S
arki bai yi ba Walid yayi saurin gyara zama yace "Zan bi su can din ma ranka shi dade, ai yanxu duk wani harkar kasuwanci ina son a dinga yi da ni saboda in samu experience ta yanda zan tafiyar da wanda zaka dora ni a kai smoothly" Ajay ya daga kai ya kall
i Walid, Walid ya jefa masa wani kallon tsana ya murtuke fuska, Mai martaba yace "You have a point Walid, sai ka shirya ka bi su ku je gaba daya....." Ɗan murmushi Walid yayi, sai kuma yayi ma Sarki sai da safe ya mike ya fita daga parlon yana murmushi....
Aunty na kallon Walid dake zaune dakinta tayi kasa da murya tace "To ni ka ki gaya min menene shirin naka Walid, wallahi ina fargaban kar a kamaka duk da nasan you are very wise, amma Junaid is brave and smart gashi da shi kace za ayi tafiyar, kar ya zarg
eka shi ne damuwata...." Walid yayi wani murmushi yace "Momy ni fa ba sabon abu bane wannan a wajena, ko kin ta
ɓ
a jin an zargeni ko kuma an kama ni akan wani laifi makamancin haka? Ai sai dai kawai ace an kamani da kwaya, kuma ba wai bana manyan lefukan ba
ne amma nasan move dina don da kwararru nake aiki, Ba ruwana da wani
ɗ
an iskan Junaid can, na yi farin cikin da za aje Calaban nan don hanyar nan ne dai dai wajen aiwatar da duk abinda mutum ke so" Aunty tayi tagumi tayi shiru, can tace "Ko dai kawai a kir
kiro wani abu da zai hana tafiyar nan da Junaid, don gaskiya tsoron yaron nan nake" Da sauri Walid yace "A'a ba wani a hanasa tafiya Momy, dole ma da shi za aje ne, ki kwantar da hankalinki na fa san ta kan aikina" A hankali Aunty tace "To shikenan, ka ji
kuma ya saki Hadiyar ma daxu ko? Tun fa da aka nadasa Yariman nan yake wani ji da kansa ya dau girman kai da iskanci ya dora ma kansa a gidan nan, baya saurara ma kowa, har gwara Junaid yanxu a kansa, don munafurci uwarsa ta tattara ta bar gidan dama munaf
urcin ne yasa ta dawo take zaman gidan ai, i can't wait all this to come to an end wallahi, idan na fara lissafo maka kamfanonin Mahaifinku wanda Jawwad ke jagoranta a kasar nan sai kayi mamaki, wasu ma ban san su ba sai dai a kawo min tsegumi, ku da ubank
u amma duk yayi kane kane kan abinda ku ya kamata a dora a kai, ga dukiyar ubansa da ya mutu ya bar masa shi da uwarsa suna yanda suka so suna facaka da shi sai zuba uban investment suke basa shawara da kowa, ace kuma Mai martaba shima idan ya tashi sai ya
dorasa kan nasa dukiyoyin saboda neman suna da son a sani, kai da Junaid da kuke 'ya yansa kuma ko oho" Walid na huci yace "Wai yaushe kika fara tsaya ma wannan shegen Junaid din ne komai kice ni da Junaid, meye hadinmu da shi ne? Ko kin mance abinda yayi
min ne ko gama warkewa ban yi ba?" Aunty tace "Ban manta ba Walid, amma a yanxu kam Jawwad ne babban kalubalen gabanmu ba Junaid ba, Junaid din da ba wani damuwa da shi da lamarinsa ake yi ba a masarautar nan kana gani saboda rashin gata kwace title dinsa
aka yi babu wanda ya iya convincing sarki ya maida masa har ita Hajja, sai kace ba
ɗ
an sa ba, ai Jawwad ne babban challenge dinmu a yanxu" Walid ya mike yana ta
ɓ
e baki yace "Ke kike ganin haka" Daga haka ya nufi kofa yace "Ni zan je mu ci gaba da shirin d
a muke da mutane na" Aunty tace "To kayi ta addu'a dai Walid, nima zan dinga taya ka a nan, Allah yasa komai ya tafi yanda aka tsara" Walid yayi wani murmushi kawai ya fita daga dakin a ransa yace "You don't know nothing Mom" Har ya kagu ranan da za su yi
tafiyar nan ya iso, this is a day he have been waiting for, kusan wata daya da sati biyu kenan yake neman privilege irin wannan sai gashi ya samu cikin ruwan sanyi... Da safe Hajja ta taho masarauta da kanta don ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda
bakin ciki, haka ma Hadiyah da ta kwana tana kuka, tun a jiya Hajja ta sa Ummi ta kira Mami ta gaggaya mata bakaken maganganu masu zafi, bayan sarki yaje har parlonta ya gaisheta tace "Yusuf zuwa nayi inji yanda aka kwana da yaron nan Jawwad, ya maida aur
en ko bai maida ba har yanxu?" Sarki yayi shiru, can ya kwantar da murya yace "Mun yi magana da shi Hajja, kuma zai maidata in sha Allah" A fusace Hajja tace "Ohh ba umartarsa kayi ba kenan dama Yusuf? Ni da na kira na sanar maka abinda ke faruwa dama ce m
aka nayi ka zaunar da shi ku yi wata magana da ta wuce kayi masa umarnin maida auren nan cikin gaggawa ba tare da kowa yaji ba?" Sarki ya
ɗ
an yi murmushi yace "Hajja, ki kwantar da hankalin ki, zai yi hakan in sha Allahu" Hajja tace "Allah wadaran Aseeyah,
Allah ya kwashe mata, in sha Allahu sai taga irin karshen da zata yi, dai dai da rana daya ban ta
ɓ
a takurata ba a sanda uban Jawwad ke da rai suke zaman auren, shi ne a yanxu zata takura jikata ta hanata zaman aure saboda son zuciya, to wallahi koran kare
zan mata duk ranan da tayi kuskuren dawowa gidan nan, sannan in ma ka kirata akan taje gidansu Jiddah to maza ka kirata ka gaya mata ba a bukata, don har nayi waya a Kano za aje da motoci gidansu Jiddah a daukota, mu da muke da alfarma ta ko ina a kasar n
an" Shi dai Mai martaba yayi shiru yana ta sauraron Hajja.... A fusace Nenne ta shiga dakin Umma tana cewa "A kira min Junaidun ta waya, haka muka yi da shi? Rimi rimi mu yi magana ya amince sai kuma daga baya su turo motoci har uku a dau Khaleesat sai kac
e har mu za a kwashe? to a kai ta ina tana fama da jikinta, haka suke a masarautar tasu dama?" Mikewa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, Umma tayi kasa da murya tace "Nenne don Allah tunda suka aiko kiyi hakuri kawai ki bari ta tafi" Nenne tace "To da m
u da su sai mu ga wa yafi iko da ita, ni da na haifi ubanta Ali nace bazata bi su ba maganata kuma tamkar ta Ali ce" Umma tayi shiru bata sake cewa komai ba a dakin, Aunty Farida na fita dama dakin Nenne ta tafi, tana kallon Khaleesat dake kwance tayi kasa
da murya tace "To Nenne na shigowa yanxu ki bude baki da kanki ki ce mata zaki bi dangin mijinki da suka zo daukar ki, ko zaman me zaki mana a nan bayan duk abinda za mu yi maki a can ma mijinki zai maki?" Khaleesat tayi shiru, don ko Aunty Farida bata ga
ya mata haka ba dama jira take Nenne ta shigo ta gaya mata ita zata bi su, don taji gaba daya zaman gidan ya isheta ta rasa dalili, ji take kamar akan kaya take a gidan tun daga jiya har yau, Aunty Farida na fita Nenne ta shigo dakin tana huci tace "Mu za
a gaya ma sarauta, bayan kakana nima yayi Sarkin pawa...." Mikewa zaune Khaleesat tayi tana kallon Nenne, sai kuma tayi kasa da kai a hankali tace "Ni zan bi su Nenne, ai can din ma zai kula da ni....," Nenne ta saki baki tana kallonta babu ko kiftawa.
H
ALYSAAH
P
A
GE 169
..
.
*I dedicate this whole page to my able Admin Hajiya Rabi'ah
💖🥰
and Anty Kulthum mutan Saudi
💖😍
, Khaleesat Haiydar na yin ku fisabilillahi, i appreciate meeting with such beautiful souls that turn sisters
💖
, su din ma dai yan Ethio
pia ne iyayen Ajay maraya, Allah ya bar mu tare ya albarkaci zuri'ar ku*
😍🥰
*Bakin ciki kashe parrot yau*
😂
Khaleesat na zaune kan carpet din parlon Hajja ta kwantar da kanta jikin kujeran parlon, isowarsu kenan daga Kano tare da matan da suka taho
da ita, duk da
ɓ
acin ran dake tare da Hajja tuni ta watsake ganin visitors din nata, da fara'a take welcoming mata hudun da suka taho tare da Khaleesat tun daga Kano, Hajja tace "Ku karasa can parlon ciki Raliyah gani nan zuwa" Duk suka karasa can cikin pa
rlon, Hadiyah na kwance parlon abun duniya ya isheta ko kumallo taki yi tun da gari ya waye don ma Hajja na ta lallabata tana bata assurance kan cewar aure kamar an maida sa an gama, Mikewa zaune tayi ta murtuke fuska tana hararan Khaleesat da bata ma san
tana yi ba, Hajja ta karasa kusa da Khaleesat ta dafa ta tace "Sannu Jiddah, ya jikin?" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata don ba karamin wahala ta sha a hanyarsu ta zuwa ba duk ta jigata, Hajja ta kira mai aikinta da sauri tace "Suwaiba zo ki kai ta dakin
da ku ka gyara mata, ki hada mata ruwan wanka a bandaki sai ki ji me take son ci, duk ta wahala a hanya" Suwaiba ta karaso da ladabi tace "To Hajja" Khaleesat ta daure ta mike ta bi Suwaiba zuwa dakin tana jan kafa da kyar, Hadiyah ta wani kalli Hajja tace
"Saboda zata dawo daga Kano shi ne sai an mata irin wannan rakiyar Hajja? Kuma na menene zata saukar ma mutane a gidan nan?" Hajja tace "Bata da lafiya ne, shi kuma da yake wawa ne sai ya bar ta wai a gidansu, shi ne na aika aje a daukota don bamu gaji ha
ka ba a gidan sarauta" Hadiyah dake ta kallon Hajja tace "Me ya sameta?" Hajja tace "Juna biyu gareta" Kallon Hajja Hadiyah ta dinga yi babu ko kiftawa with shock, Hajja tace "Bari in je mu gaisa da baƙin nan, su Hajiya Raliya ne baki gane su ba?" Daga hak
a Hajja ta wuce parlon can ciki, Hadiyah ta ciji finger dinta, can ta mike tsaye ta fara zaga parlon a hankali tace "Juna biyu? To wallahi bazai yiwu ba" hawaye taji sun taru idonta bayan ta tuna ita an ma saketa, ta dau wayarta tana goge idonta ta tafi da
kinta da sauri. Da yamma Hajja ta fito dakin Hadiyah don tun da ta shiga ciki har yanxu taki fitowa, Hajja ta zauna kan kujera ranta a dagule, har ta gaji da fama da ita kan ta ci abinci, da ba don a gabanta aka haifi Jawwad ba da sai tace canza ma Ahmadu
shi aka yi a asibiti, amma ba komai tasan duk uwarsa ce ta sa yayi wannan abun, kuma sai tayi da ta sani, Hajiya A'isha da Kilishi ne suka shigo parlon da sallama cikin shiga ta alfarma, Hajja ta daga kai ta amsa sallamar su, suka karaso cikin parlon duk s
uka zauna kan carpet suna gaida Hajja, Hajja ta amsa tace "Sannun ku da zuwa" Kilishi tayi kasa da murya tace "Hajja wani labari muka ji mara dadi yana ta yawo a masarauta" Sosai gaban Hajja ya fadi ta fara addu'an Allah ya sa ba maganar sakin Hadiyah bane
ya fita yake yawo, cikin natsuwa tace "Wani magana ne wannan Kilishi?" Kilishi tace "Wai Jawwad ya saki Hadiyah" Hajja tayi saurin kallon hanyar dakin da ta sauke baƙinta, Kilishi tayi kasa da murya tace "Kina da baki ne halan Hajja?" Hajja ta mike tace "
Mu tafi parlor na" Duk suka mike suka bi bayanta, ko zama Hajja bata yi ba tace "Ina ku ka ji wannan magana Kilishi?" Hajiya A'isha ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajja ai maganar nan ta gama karade masarauta yanxu, Khadijah ce ta gaya ma Iklima ta waya..."
Hajja tayi shiru tana jin wani sabon
ɓ
acin rai, can tace "Khadijah?" Hajiya A'isha tace "Kwarai kuwa Hajja, don sai da ma na amshi wayar nayi mata fada nace wa ya tambayeta don muna tare da Iklima lokacin da ta kira" Kilishi tace "Ba kowa zai sa Jawwad yay
i wannan danyen aikin ba sai uwarsa, nima wallahi daga masarauta aka kirani ake gaya min wannan mummunan labarin, duk na gigice na taho nan, a bakin gate din gidan nan muka hadu da A'isha wallahi" Hajiya A'isha tace "To kasa sukuni nayi shi ne kawai na shi
rya taho nan, gwara a dakatar da yayada wannan magana haka, ai komai na son sirri" Hajja tace "Allah ya kyauta, amma kuma ai ya maidata a yau, kuma kun san baza a zuba ido a kyale lamarin haka ba, komai ya dai daita yanxu kam" Kusan a tare Hajiya A'isha da
Kilishi suka ce "To Alhamdulillah, ai haka ake so...." Hajja ta mike tace "Ina da baƙi, bari in je wajensu" Fita tayi daga parlon nata zata tafi dakin Hadiyah, su Kilishi suka kalli juna, Hadiyah na zaune tsakiyar gado waya kare a kunnenta tana sauraron u
warta, a hankali tace "Wallahi sai ma kin ga yanda take taraiyarta tana lallabata Ummi, convoy guda fa aka taho da ita daga Kano, sai wani
ɗ
aga min hanci take ita me ciki, ai ko yanxu zan shirya in fita zuwa pharmacy din...." Ummi tace "A'a kar ki fita gud
un zargi, gwara ki kira wannan kawar taki da ta karanci likita, ki nuna mata ke zaki yi amfani da shi cause you are not ready, za ku yi tafiya" Hadiyah tace "Kuma haka ne fa Ummi kin kawo shawara, bari in kira Amina yanxu kuwa zaki ga ta kawo min" Ummi tac
e "Duk yanda ake ciki ki kirani ki sanar min" Hadiyah tace "To Ummi" Katse wayar tayi ta fara kiran kawarta, bayan sun gaisa tace "Amina wani alfarma nake son ki min don Allah, nasan babu me min wannan abun sai ke" Amina tace "Ina jin ki kawata, anything f
or you" Hadiyah tayi kasa da murya tace "I just found out I am pregnant Amina, don Allah abortion pills nake so don ban shirya ba wallahi, kuma fa tafiya za mu yi da shi" Amina ta zaro ido tace "Ke Gimbiya haka kawai ki sa Yarima ya daureni?" Hadiyah tace
"C'mon ta ya zai sani, har yanxu bai ma san da cikin ba, don Allah I need it today Ina gidan Grandma kafin in koma gidan Sarki" Amina tace "Gaskiya kam it's too early, duka duka yaushe aka yi auren har za ayi ciki, ko amarcin ba a gama ci ba" Hadiyah tace
"Shi yasa nake son ki Amina don akwai ki da ganewa..." Hajja ce ta shigo dakin Hadiyah tayi saurin katse wayar ta ajiye, Hajja ta kulle kofar cikin fada tace "Ke Hadiyah gaya ma Khadijah kika yi Jawwad ya sake ki bayan duk kwabar da na maki kan cewar kar k
i gaya ma kowa wannan mummunan maganar?" Hadiyah ta juya tana kallon Hajja tace "A ina na ganta zan gaya mata, ko kuma meye hadina da ita da zan gaya mata, wato har an fara yamadidi da ni a masarauta kenan?" Sai kuma ta fashe da kuka sosai tace "Ni wallahi
wajen dangin babana zan wuce tunda Jawwad ya fi karfin kowa, wallahi bazan zauna garin nan ba gwara inje inda za a amsar min yancina...." Hajja tace "Ikon Allah, to shi Yusuf fulani ya sanar ma wannan maganar har ta gaya ma 'ya yanta suke yamadidi da