Showing 435001 words to 438000 words out of 641791 words

Chapter 146 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

136

ya hanya?" Safiyyah tace "Alhamdulillah" Nan Safiyyah ta fara wondering ba ance Mami bata da kirki ba gashi kuma faram faram ta ganta, Mami ta kalli Khaleesat tace "Ki shiga kitchen Halysaah zaki ga cin cin da aka kawo min daxu da dublan ki debo m

ata da drinks" Khaleesat tace "To Mami" Mikewa tayi ta tafi kitchen din, after a while ta fito da duk abubuwan da Mami tace ta ajiye ma Safiyyah, Mami ta mike ta bar masu parlon ta koma daki, Khaleesat tabi Mami daki taji ko da wani aikin da za ayi mata du

k da ko ina na part din fess fess ga kamshi dake tashi ta ko wani angle, Khaleesat sun fi minti arba'in bangaren Mami sannan tayi ma Mami sallama suka koma part dinta da Safiyyah, Safiyyah ta zauna kan kujera a Main parlor tana kallon Khaleesat tayi kasa d

a murya tace "In ji babu CCTV camera a parlon nan naki, gudun ko akwai a parlon Mami yasa na ja bakina na ƙume...." Khaleesat ta

ɗ

an yi murmushi don tayi mamakin da Safiyyah bata ce komai ba duk zaman da suka yi a bangaren Mami, dama da tayi wata maganar m

a zata yi maza ta kwabeta amma sai taga bata yi ba, Zaunawa Khaleesat tayi tace "Babu komai a nan" Safiyyah tayi mitsi mitsi da ido tace "shanye Housemate din matar tasa tayi ko me???" A takaice Khaleesat tace "Ohon masu" Safiyyah tace "Ji min er iskar yar

inya, wallahi da Mami bata fito ba da taji ko ni wacece kamar yanda ta tambaya, kaina ya fi nata hayaki wallahi, ki ji fa har da fixge wayarsa a hannuna, kan bala'i bata fa san wacece ni ba yarinyar nan" Khaleesat tace "To ranan fa shakeni tayi kawai daga

ta samu ni da mijinta a parlorn Mami" Safiyyah ta hangame baki tace "Ta shake ki? Sai aka yi yaya?" Khaleesat ta ta

ɓ

e baki bata ce komai ba don wani bakin ciki ne ya tokareta tuno hakan da tayi, dai dai sanda aka bude kofar parlon sai ga Hadiyah da Iklima

sun shigo parlon, daga Khaleesat har Safiyyah suka dinga kallonsu, Hadiyah na ma Khaleesat wani matsiyacin kallo har ta karaso tsakiyar parlon tace "Wato tun da na bi na toshe duk wata hanyar da zaki dinga bibiyan mijina da iskanci a gidan nan shi ne bari

ki gayyato kawarki kwartuwa kamarki ta zo ta dora daga inda kika tsaya...." Safiyyah ta mike ta cillar da gyalenta ta nufi Hadiyah tana huci tace "Don ubanki ni kike ce ma kwartuwa? A gidan uwarki kika san ni zaki ce min kwartuwa? So kike in maki duka blue

black a nan yanda ko mijin naki bazai gane ki ba??" Iklima na ganin haka tace "Kee hattara yarinya, kar ki ji ma kanki bala'in da baza ki iya fidda kanki ba, kin san wacece ita? So kike ki kare shegen rayuwarki a prison??" Tuni Khaleesat ta shiga tsakanin

su kafin a fara dambe ganin yanda Safiyyah ta hada Hadiyah da Iklima ta dinga kunduma masu zagi ba ji ba gani tana neman cakumosu, Khaleesat na jawo Safiyyah tace "Plss stop this Safiyyah, don Allah ki kyalesu mu shiga daki...." Hadiyah ta juya ta zabga ma

Khaleesat wani wawan mari tace "Ke ce dai dai yina ba er tashar kawarki ba...." Khaleesat ta saki baki with shock ta dafe kuncinta tana kallon Hadiyah, bata san sanda ta gaura mata nata marin ba ta fincikota a fusace, nan dambe ya kacame tsakaninsu, Iklim

a ta fita da gudu zata je kiran yan gidan yanda za ayi ma Khaleesat da Safiyyah taron dangi ayi masu duka, dama duk yan matan gidan da iyayensu suna nan don Hajja na hanya yau, Safiyyah bata ta

ɓ

a sanin Khaleesat na da karfi haka ba sai yau, don tuni ta kai

Hadiyah kasa ta dinga lakada mata duka ba ji ba gani kamar an aikota tana gaggaura mata maruka Hadiyah na ihu tana kiran Ummi, Safiyyah taki rabasu ta koma gefe tana wani tsumuwa tana kara gingering Khaleesat, sai da taga Khaleesat ta shake Hadiyah da gas

ke har idanuwanta sun fito, kuma exactly yanda Hadiyah tayi mata a parlon Mami sannan Safiyyah tayi saurin janyeta daga kan Hadiyah tace "Bar shegiya haka, bar ta haka nan kar ta suma a hannunki, gobe ko burkutun arna ta kwankwada bazata sake shigo maki ba

ngarenki ba, er iska mara tarbiyya kawai" Ihu kawai Hadiyah take tana birgima a parlon tana kiran Ummi, Khaleesat na huci tace "Don uwarki gobe ki sake wanke shegun kafufuwanki ki zo bangarena ki gani, wallahi sai na maki fiye da haka don jina jina zan mak

i, mijin ki din banza naga sanda yake tare dake tani yake ba take ba, kuma da bakinsa ya gaya min ke din zabin Maminsa ce ba zabinsa ba kawai ya rasa yanda zai yi ne da aurenki da aka kakaba maki, abinda Mijina aka so makala maki yaki shi ne aka makala ma

Jawwad din, to burgar uwar me zaki ma mutane bayan mun san komai, yaushe ma ya fara baki attention dinsa? Ina ce a rashina ne ya hakura yayi accepting dinki har yake maki kallon mace? Ke da kike matar chushe har kina da bakin magana mara kunya kawai" Hadiy

ah was more than shock, kukan ma ta kasa tana kallon Khaleesat jin abubuwan da take cewa, Hayaniyar matan gidan da 'ya yansu Khaleesat ta fara jiyo alamar sun iso bangaren nata, ai ko ta ja hannun Safiyyah da sauri suka shige parlon Ajay tun da akwai key a

jikin kofar, suna shiga ta kulle kofar da makulli, Safiyyah na zare ido jin hayaniya sosai a Main parlor tace "To kira mana Ajay ya zo ya kai ni tasha" Khaleesat ta zauna kan kujera tana huci tace "Wallahi kadan nayi mata, ni ma ai haka ta min ranan a par

lon Mami ta shakeni, babu wanda yayi kokarin stopping dinta sai Mami da Ya Junaid da ya mareta, but at the end Jawwad was questioning Ya Junaid akan me zai marar masa mata, bayan yana tsaye komai ya faru he couldn't even save me" Safiyyah ta bude baki da m

amaki tana kallon Khaleesat tace "Shi Housemate din??" Khaleesat tace "Kuma babu wanda yace inyi hakuri a gidan nan sai Mami, don haka nima yau na rama sai in ga me za a ce" Safiyyah tace "Har Mai martaban?" Khaleesat taki ce mata komai don ita Mami ce kaw

ai bata jin haushi a fadin gidan nan, mikewa tayi ta tafi dakin Ajay ta dau wayarta ta kunna sannan tayi dialing numbersa, yana fara ringing ya daga amma bai ce komai ba, ta turo baki tace "Kana ganin ina zaman zamana Hadiyah ta biyoni har part din nan ta

mareni ko?" Shiru yayi for some seconds, har tayi tunanin baya kan layin, ta kalli screen din wayar taga yana kai har sannan, sai kuma taji yace "Ta mare ki? Ke kuma sai kika zauna ta mareki ko?" Khaleesat tace "A'a na rama, sannan nayi mata duka" Yace "Ki

ka mata duka?" Khaleesat ta kara turo baki tace "Ehh mana...." Yace "Good, hope kin shiga ciki kin kulle kofa?" Tace "Eh" Yace "Kuma Kawarki bata yi involving kanta ba?" Khaleesat tace "A'a ni kadai na doketa, ita ce ma ta raba mu" Yace "Good, duk me za su

ce kar ku bude kofar" Katse wayar yayi daga haka, Khaleesat ta koma parlor, Safiyyah sai zare ido take jin uban zage zagen da mata ke laftawa a parlor kamar maguzawa suna cewa sai sun yi ma ita da Khaleesat lahani, kai baka ce sun hada komai da Sarauta ba

yanda suka dinga maganganu kamar yan tasha, gashi sai Bazawara suke kiranta da shi wai aurota masarautar ma Taboo ne at the first place shi yasa daga shigowarta komai ya rikice a masarautar, maganganu marasu dadi sai wanda suka manta ne basu ma Khaleesat

da iyayenta ba, Khaleesat ta kunna TV din parlon Ajay ta kure volume yanda ma bazata dinga jin su ba, kuma zuciyarta ko

ɗ

ar, as far as Ajay bai yi blaming dinta kan abinda tayi ba.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via

07087865788*

HALYSAAH

Sai da ko ina yayi tsit bayan kusan minti talatin alamar sun bar parlon sannan Safiyyah ta kalli Khaleesat dake ta kallon TV abun ta as if nothing happened, a hankali Safiyyah tace "Na ji shiru, kamar fa sun gaji sun tafi" Khalees

at ta ta

ɓ

e baki tace "A'a da su yi ta tsayawa mana suna displaying madness dinsu, ni sanda ta shakeni waye yace don me a gidan nan?" Cike da mamaki Safiyyah ta rike ha

ɓ

a tace "Ajay ne ya tsammaki wannan liver din haka Khaleesat? Dama kin iya dambe? Eh lall

ai yau na yarda da wannan karin maganar da ake cewa zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai" Khaleesat tace "Kina nufin da ta mareni da sai in kyaleta kawai?" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Da ba sai na tsine maki kin bi duniya ba takalmi ba, ai da

i dai kika yi mata wallahi, shegiyar ko a hall way ta ganki a gidan nan daga yanxu zata canza hanya, ni dai ki kara kiransa ya zo ya kai ni tashar mota dama kwana

ɗ

aya da rabi aka bani kacal" Knocking kofa suka ji anyi duk suka juya da sauri kamar wa enda

suka lafta ma sarki karya, Safiyyah dake zare ido tayi kasa da murya tace "Dawowa suka sake yi? Anya baza ki ciro mana wanduna ba Khaleesat, kaddai Spare key suka je nemowa su shammace mu, gwara in cire doguwar rigar nan ki ban wando in zauna da shiri na d

on babu shegiyar da zan zuba ido ta dokeni a banza" Muryar Mami Khaleesat taji tana kiranta bayan ta sake kwankwasa kofar, sai da Khaleesat ta sauke ajiyar zuciyar relieve don ita kanta tayi zaton su ne suka dawo, ta kalli Safiyyah dake kokarin cire kayan

jikinta a bata dogon wando tace "Ke Mami ce fa" Daga haka ta mike ta nufi kofar ta bude ta koma gefe bayan sun hada ido da Mami ta sunkuyar da kanta, Mami tace "Me ya faru Halysaah?" A hankali Khaleesat tace "Kawai zuwa tayi Mami ta fara zagin Safiyyah, ni

kuma ta mareni ban mata komai ba, shi ne na rama, muka fara fada" Mami tayi shiru tana kallon Khaleesat, can tace "Har nan ta biyo ku?" Khaleesat tace "Eh muna can parlon a zaune suka shigo ita da Iklima" Mami tace "To mu koma can bangarena ku zauna a can

" A hankali Khaleesat tace "To Mami" Juyawa tayi ta dau gyalenta da wayarta, Safiyyah ma ta dau nata gyalen sannan ta mike suka bi bayan Mami suka koma bangarenta.... Suna isa bangaren Mami da few minutes sai ga kiran Ajay ya shigo wayarta, ta

ɗ

an kalli Sa

fiyyah da yunwan cikinta ya isheta don sai yanxu ta tuna ko breakfast bata yi ba bayan ƙura ya lafa, mikewa Khaleesat tayi kamar zata dauko abu a kitchen din Mami, tana shiga kitchen din tayi picking call din ta kai kunne ta hade rai taki cewa komai, daga

daya bangaren yace "Are they still at the parlor?" kamar zata yi kuka tace "Shi ne baza ka dawo ba har yanxu?" Yace "Ba dai kin mata duka ba?" Tace "Eh" Yace "Kuma kun kulle kofar inda ku ke ai?" Ta turo baki tace "Mami ta zo, shi ne tace mu dawo bangarent

a" Ya

ɗ

an yi shiru, sai kuma yace "Ke ban ce maki kar ki bude kofar ba??" Tace "To Mami ce fa, kuma da muka dawo bangarenta ai kulle kofar parlonta tayi da key" Yayi shiru bai ce komai ba don bai so sun fito daga part dinsa ba, can yace "In suka bi ki can

suka rama mata dukan da kika yi mata i will only get you paracetamol tunda baki jin magana" Daga haka ya katse wayarsa, turo baki tayi tana kallon screen din wayar, bayan kusan minti biyu ta juya a hankali ta fita daga kitchen din, Safiyyah ta marairaice t

ayi mata nuni da cikinta alamar yunwa, Khaleesat bata san sanda ta fara dariya ba har da durkusawa, Safiyyah ta hade rai tana kallonta, Khaleesat ta nufi Bedroom din Mami, sallama tayi Mami tace ta shigo, ta shiga dakin ta tafi har inda Mami ke zaune ta du

rkusa tace "Mami dama Safiyyah bata yi breakfast bane..." Mami ta kalli agogo tace "Har ke ma dai baki yi ba kenan?" Khaleesat dai tayi shiru tana

ɗ

an murmushi, Mami dake kallonta tace "Ki je ki hada maku shayi a kitchen, akwai kawai da komai a can sai ku

soya, yau nace kar su kawo min komai daga can cikin gida so there is nothing much, amma in da wani abu da za ku yi sai kuyi ku ci everything is available in the kitchen" Khaleesat tace "To Mami, mun gode?" Mikewa tayi Mami ta bi ta da kallo har ta fita dag

a dakin ta kullo mata kofar, sai kuma Mami ta sauke kanta kasa tana jin hawaye na taruwa idonta..... Baƙin ciki kamar ya kashe Safiyyah ta dinga kallon shayi da bread da kwai da Khaleesat ta kawo masu, bayan ga can uban breakfast da ta bari a bangaren Ajay

, kasa daurewa tayi, tayi kasa da murya tace "Anya bazan bude kofar in lallaba in koma in dauko breakfast din dazu da aka kai mana bangaren Ajay ba, ai dai zuwa yanxu ko wace er iska ta tafi dakinta tunda ba dogariya bace" Khaleesat ta dinga kokarin ganin

bata fashe da dariya ba don bata san ko an maida Cctv din parlon Mami ba ganin how serious Safiyyah is, Safiyyah ta hade rai tace "Ai ba zancen dariya bane, wannan

ɗ

an abinda kika kawo me zai min, ba sai in hada har naki ban koshi ba" Khaleesat dai taki ta

nka ta ta fara shan shayinta tana murmushi, sai da Safiyyah taga ba sarki sai Allah ta jawo kofin shayin tana cika tana batsewa tana tuna tulin Farfesun da ta bari a daki, ko gama breakfast din basu yi ba aka fara kwankwasa kofar parlon Mami, daga Khaleesa

t har Safiyyah suka kalli juna, nan abinda Ajay yace ma Khaleesat ya fado mata, kaddai biyota din suka yi su ce za su rama ma Hadiyah, Safiyyah dai ta ci gaba da tuttura breakfast dinta da sauri don babu wanda zai sake cutarta ya katse mata breakfast, don

daga nan bata san kuma inda suka nufa ba, ko inda za a sake tarkata su, Mami ce ta fito daga dakinta ta nufi kofar tana tambayar wanene, muryar Aunty taji tace "Fulani ce" Mami ta bude kofar, Aunty ta shigo Jakadiyarta na biye da ita a baya rike da wayoyin

ta, Khaleesat dai tunda ta kalleta sau daya ta sunkuyar da kanta, bayan Aunty ta zauna parlon Khaleesat ta gaisheta cikin Ladabi Safiyyah ma tayi haka don sau daya ta kalleta ta gane Matar Sarki ce duba da yanda take tafiya cike da isa da gadara gashi ana

biye da ita da waya, ga wani arnen doguwar riga da ta saka yatsunta duk gwala-gwalai da wuyanta da kunne, tana zaunawa kan kujera kuma Jakadiya ta zube kasa

ɗ

an nesa da ita, Khaleesat ta mike zata bar wajen, a takaice Aunty tace "A'a yi zaman ki" Khaleesat

ta koma ta zauna cike da mamaki, ita dai Mami na zaune kan kujera tayi shiru, Aunty na kallon Mami tace "Fulani Aseeya wai me ke faruwa gidan nan ne daxu naji kamar hayaniya sai yanxu na samu fitowa" A takaice Mami tace "Nima da ke nan ina zan sani Fulani

" Aunty ta kalli Khaleesat tace "Me ya faru a gidan nan daxu?" Khaleesat bata dago kanta ba cikin sanyin murya ta fara gaya ma Aunty abinda ya faru tsananinta da Hadiyah, Aunty ta girgiza kai tace "Sam yarinyar nan Hadiyah bata da mutunci bata da tarbiyya

ta karo wasu kalan raini yanxu a gidan nan uwarta na goya mata baya duk bayan sati biyu ta baro Lagos tace ta zo masarauta bayan ba haka take ba da, tunda incident din nan ya faru na sauke Junaid a gidan nan ta dena ganin kowa da gashi, hatta ni yau kwanan

ta uku bata gaisheni a gidan nan ba ta hade kai da su Hajiya A'isha da Kilishi da Fauziyya, kuma ni a ganina tunda har ita ta kai kafarta bangaren Matar Junaid duk ma me tayi mata ita ta siya kuma dai dai ne, daxun nan da safe sai da ta nemi fada da Khadij

ah a gidan nan" Mami dai taki tanka Aunty sai kallonta kawai take, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo, duk suka daga kai suna kallonsa, gun Safiyyah ya nufa direct kana ganinsa kasan daga aiki aka kirasa ya dawo a lkcn, yana kallonta fuska daure

yace "Safiyyah, me matata tayi maku ku ka doketa??" Safiyyah ta gwalo ido tace "Muka doketa kuma? A'a warce ta lafta ma mari ba sididi ba sadada ta rama marin ta hanyar dukanta" Ya juya ya wani kalli Khaleesat da taki kallon inda yake tsaye, tun bai ce kom

ai ba Mami ta nuna masa kofa fuskarta a murtuke tace "Fita ka bar min parlor" Ya juya ya kalli Mami, tsawa tayi masa tace "Ka fita nace ka ban waje" Ya juya ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Aunty da ta saki baki tace "Ikon Allah...." Mami bata sak

e cewa komai ba, bayan minti kusan biyar Aunty ta mike tayi ma Mami sallama ta nufi kofa tana

ɗ

an murmushi Jakadiyarta na biye da ita

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login