Showing 354001 words to 357000 words out of 641791 words
ta dawo kasa ta nufi kitchen tana yi tana waige waigen ko zata ga legen
d don ita dai a tsorace take har ta shiga kitchen din ta kulle kofa, shopping ta gani birjik a kitchen island din, tana tafiya a hankali ta tafi gun ledojin, daya bayan daya ta dinga fiddo kayan shopping din, she made sure she arranged everything a kitchen
din wanda zata jera a babban fridge duk ta zuba su ciki, cookies iri iri ta gani da kayan ciye ciye masu tsada, su ma duk ta ajiye su, bayan kusan minti talatin ta gama setting komai a mazaunin sa a kitchen din, ta zuba wasu bottled water cikin fridge, da
ga karshe taga ledan abinci biyu a kitchen din yayi masu order, she felt relieved don dama in don ta ita ne shayi kawai zata sha bazata dafa komai ba don ta gaji, ta dau leda daya ta bar ma driver daya ta juya ta fita daga kitchen din ta koma sama...... Kh
aleesat na zaune ita kadai a favourite spot din da suka saba zama da Sophie idan suka fito lectures, Safiyyah kuma taje amso masu snacks da wani frnd dinta ya masu order, it's been weeks now da suka yi resuming school don har sun fara preparing for quizzes
, har Safiyyah ta karaso Khaleesat bata san ta karaso ba don tayi nisa tunanin da take, Safiyyah ta ta
ɓ
e baki ta zauna gefenta tace "Kina nan kina aikin naki kenan" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai a hankali ta kalli Safiyyah, Safiyyah tace "Kawai ki dor
a ma kanki tunanin da bazai fisshe ki ba, ni dai ina gaya maki semester din karshe ne dai wannan in ba so kike ki samu matsala ba and you know what that means" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Even if it is once ai da sai yayi min reply yaji ko me zan ce
masa Sophie, you know how painful it is mutum yayi ta ignoring messages dinka bayan duk yana gani...." Safiyyah ta kalleta ta zaro mata ido tace "Ke... Ke fa matar aure ce yanxu Khaleesat, bar ganin auren naki da Ajay a gantale haka, to reply din me kike
son Housemate yayi maki? so kike ya biye ki ku fara chatting ko me? salon ma aga chatting din zargi ya shiga dama irin wannan gidan nasu gidan kananan zance don duk gidan sarauta gidan zance ne don haka gwara ma kar ya biye ki ya kama kansa wallahi, sannan
fa shi ma yana can da matarsa, may be ma yayi move on suna can suna cin amarci tunda babu yanda ya iya an hanasa ke kinga he will just make the available the desirable, ke kuma kina nan kin damu kanki da tunani ji yanda kika rame don Allah kamar warce bat
a cin abinci, shi dama Housemate ana zaune lafiya ma ya share mutum balle an masa laifi? Ai kar ma ki saka ran zai bi ta kan message din ki, ashe har kin mance halinsa kenan" a hankali Khaleesat ta share hawayen da taji ya kawo idonta, Safiyyah tace "Shi k
uma Ajayn ya fitar da shegen Legend din a gidan ko yana nan har yanxu? Ni rainin wayonsa ne ma yasa kika ga bana cewa zan je gidan don na lura ya karo sabon walakanci yanxu, kar wataran ya gaya min maganar banza in masa rashin kunya" Khaleesat ta ta
ɓ
e baki
tace "Ke ni fa sai mu yi kwana da kwanaki bamu hadu a gidan nan ba, kin tuna wani time da na ta
ɓ
a zama gidan sanda Aymaan ya biyoni har apartment dina?" Safiyyah tace "Eh" Khaleesat tace "Toh yanda bama haduwa da shi wancan lokacin a gidan yanxu ma haka n
e, although he is around amma sai mu yi many days bamu hadu ba tunda kinga da safe nake tahowa school kuma bana komawa gida sai yamma sosai, ko bani da lectures kinga sai na shigo school har Saturday saboda bana son zaman gidan kwata kwata, so bama haduwa
gaskiya, aikin gidan ma na dena yi because he makes sure everywhere is clean, ko nace zan yi gyara gyara da asuba sai in ga ko ina neat, kinga yana gyarawa kenan" Safiyyah ta rike ha
ɓ
a tana kallonta da mamaki, can tace "Tabb, to ku kuma haka naku salon aur
en yake kamar yanda ake yi a film? Ba ruwansa ma ko kina lafiya ko otherwise a matsayinsa na mijin ki? Ko kun mance mata da miji ne ke da shi?" Khaleesat tayi ma Safiyyah wani kallo sai kuma ta kauda kai, Safiyyah tayi shiru tana ta kallonta kamar dai tana
son yin tambaya amma bata san ta yanda zata fara tambayar ba, bayan few seconds kawai tace "So you mean ba ku ma ta
ɓ
a kwana daki daya ba kenan har yanxu da shi?" Khaleesat ta juya ta kalleta tace "Daki daya kamar ya? Saboda me za mu kwana daki daya?" Safi
yyah ta zuba mata ido tana kallonta, Khaleesat ta kauda kai fuska daure tace "For what reason za mu kwana daki daya?" Safiyyah tayi mata kallon gefen ido kamar dai tayi shiru sai kuma dai tace "Kin fi ni sanin reason din ai" Khaleesat taki kallonta tace "B
an san wannan reason din ba" Safiyyah tayi er dariya, bayan kusan minti daya tace "No matter yanda aka yi auren dai mijin ki ne shi ki ji in gaya maki, in ma ke kika ki yarda ku kwana daki daya nasan kin san repercussion din hakan, ba ruwan Allah da yanda
aka yi auren ko kuma abubuwan da suka janyo aka yi auren, aure dai aure ne koma yaya yake, yanxun nan sai ya kai ki wuta idan baki yi hankali ba" Khaleesat ta fara harhada kayan karatun ta without looking at Safiyyah cause she finds the conversation nasty
in her ears, a takaice tace "Zan tafi gida since we are done with today's lecture....." Safiyyah dai kallonta kawai take, can ta
ɗ
an yi murmushi bata sake cewa komai ba, har sai da Khaleesat ta mike zata bar wajen sannan Safiyyah tace "Yau kuma da wuri zak
i koma gidan kenan? ke da kike jin kamar ki dawo kwana cikin makaranta tsabar rashin son zaman gidan?" A takaice Khaleesat tace "Ehh, na gaji ne yau, bacci zan je gida in yi... Sai gobe" Daga haka tayi wucewarta tana dialing number driver dinta don yana na
n area din, Safiyyah dai ta bi ta da kallo tana murmushi a ranta ta fara tunanin banda dai abubuwan da suka faru wacce mace ce zata samu irin Ajay tayi ta claiming bata son sa? Ai sai dai shi yace baya so cause he gat everything, ilimin ne, kyan ne, asalin
ne, wayewar ne, ko kuma dukiya? uwa uba ga sarauta, ai sai dai macen ta yaudari kanta tace bata so, although tasan ita dai Khaleesat da gaske take har cikin ranta ba lallai duk wannan qualities din su yi freaking dinta ba tunda ita ga wanda zuciyarta ke s
o.... Khaleesat ta dade bata ji haushin Safiyyah ba kamar irin wannan rana, she was really angry at her cause bata yi expecting irin wannan maganar daga gareta ba, ta yaya zata gaya mata haka ita da bata ta
ɓ
a kallon Ajay a matsayin wanda za su yi wani abu
wai shi aure tare ba, status dinta da shi will remain the way it is, ba wani aure a tsakaninsu, shima kuma a wajensa tasan irin kalan tunaninta yake yi, bazai ta
ɓ
a kallonta a warce za su yi rayuwan aure ba, basu hango wani abu wai tarayyan aure between dem
ba, har ta isa gida her mood was really spoilt, ta bude motar ta sauka tayi wucewarta cikin gidan, Allah ya so gobe Saturday ba ma ta da lectures balle taje school ta hadu da Sophie taji sabon takaici, ita da kullum ke cewa an ci amanar Housemate menene z
ai kai tunaninta zuwa irin wannan tunanin da tayi yau, what came over her to think that way? wato so take a ci amanar Housemate din da gaske kenan, tsaki Khaleesat tayi ta shiga cikin parlor, as usual babu kowa parlon tayi wucewarta sama zuwa daki, wanka t
ayi ta canza kaya tayi sallah tayi kwanciyarta, sai wajen biyar da rabi ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dora girki yanxu dai kwata kwata ta dena ganin Legend, tun da ta sauko downstairs take kallon wanda ta gani zaune cikin parlon har ta karaso ins
ide of the parlor sannan ta gaishesa, ya juya ya kalleta greeting her also, Ajay dai na zaune parlon yana danna wayarsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, sauke kanta tayi ta nufi kitchen, tana shiga kitchen din da few minutes sai ga Ajay ya shigo ta juya ta
na kallonsa ya hade rai yace "Ke baki da hankali ne da kika ga mutum a parlon baza ki koma sama to cover ur self up properly ba?" Ita dai bata ce komai ba tana dibar vegetables da zata yi amfani da shi wajen girki, ya juya ya fice daga kitchen din, kusan a
wa daya tayi a kitchen din tana girki don ba iya ita da Driver ta dora ma girkin ba har da Walid da ta gani a parlor, bayan ta gama ta fito har sannan Walid na parlon, Ajay ma na zaune and none of them is saying anything kamar kurame, shi Ajay wayarsa kawa
i yake dannawa at the same time yana operating din laptop dinsa dake gefe, shi kuma Walid kallon TV yake ya ƙishingi
ɗ
a kan 2 sitter, Khaleesat ta wuce sama Ajay ya bi ta da kallon gefen ido. Sai a sannan Ajay ya juya ya kalli Walid yace "Oxford din nan gar
in suka maido convocation din nasu na wannan shekaran kenan?" Kamar Walid bazai ce masa komai ba, sai kuma dai yace "How will that be possible?" Ajay yace "Da na ganka a nan ne nayi tunanin a nan kasar za su yi convocation din" Walid ya kallesa yace "Howev
er, su Aunty ma idan suka ga dama nan gidan za su sauka not England, cause babu inda aka ce an siya gidan nan da sunan just one or two persons...." Daga haka ya mike yaki jiran yaji me Ajay zai ce yayi wucewarsa sama ya tafi dakin da yake sauka idan ya zo
gidan, wanda rabonsa da Maryland yayi 3 years yanxu, after a while Ajay ya mike ya tafi sama shi ma ya nufi bangarensa. Khaleesat ta idar da sallan magrib ta fito sanye da hijab dinta har kasa ta sauka downstairs zuwa kitchen zata debi abinci, tana shiga k
itchen din taga an ci abincin an bar plate da mug din da aka sha Coffee a sink, tunda take gidan bata ta
ɓ
a ganin an bar used utensils unwashed a kitchen ba, sai da ta fara wanke plate din ta goge inda aka yi littering da abinci sannan ta dau plate ta fara
dibar wanda zata ci kenan aka bude kofar kitchen din ta juya, Walid ne ya shigo ya kulle kofar, ta sauke idonta ta kauda kai ta ci gaba da abinda take, yace "Akwai abincin ne?" Kai ta gyada masa without looking at him tace "Akwai...." Ya dau plate ya karas
a har inda take tsaye ya tsaya yana kallonta yace "Can i have some of it?" Bata yi tunanin zai karaso har wajenta ba hakan ya
ɗ
an sa ta daburce ta gyada masa kai da sauri tace "Ga abincin nan...." wanda ta fara zubawa a plate ya dau spoon ya diba ya kai ba
ki yana gyada kai yana kallonta kamar me kirga kalamansa yace "Waow, you are a great cook, the meal taste delicious, did you learn catering? Are you a chef?" Ita dai sai kokarin matsawa take daga kusa da shi don dab da ita ya tsaya, bata yarda ta dago kai
ba ta fara zuba wani abincin a plate with confusion, hannu ya kai ya rike plate din har hannun nasa na ta
ɓ
a nata yace "John Hopkins kema kike na gan ki big gal" Ƙin cewa komai Khaleesat tayi tsabar shock, kawai bata ankara ba taga ya kai hannu chin dinta y
a dago kanta yana kallon fuskarta yace "Hey I am asking you a question" Daburcewa tayi ta fara gyada masa kai alamar eh, sai kuma ta sakar masa plate din ta juya zata bar kitchen din yayi saurin rikota yace "Kee, are you alright? Ina maki tambaya zaki fita
" Warce hannunta tayi da sauri ta fice daga kitchen din zuciyarta na bugawa, sama ta tafi tana waigen ko ya biyota don duk ya tsorata ta, tana shiga Bedroom dinta ta kulle kofar ta tafi gefen gado ta zauna with shock tana processing abinda ya faru.
*Haly
saah is 500 via 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH
PAGE 10
9
Da asuba Ajay ya shiga Bedroom dinsa zai dau darduma ya kunna wutan dakin mara haske sosai ya juya yana kallonta, ya kusa seconds talatin tsaye yana kallonta,
can dai ya karasa har kusa da ita ya duka to be sure of what he is seeing, ya kara kunna wutan bedside lamp still looking at her, da mamaki ya kai hannu yayi raising gashinta yana feeling texture din, can ya cire hulan kanta da kadan ya rage ya fita daga k
an nata yana kallon gashin gaba dayansa, lokaci daya Khaleesat ta bude ido jin hannu a gashinta tayi wani ƙara tana kokarin mikewa zaunewa tana kallonsa a tsorace tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Sai kuma ta dafe kirjinta ta jingina da gado feelin
g so much relieve ganin shi ne, tayi saurin daukar hulanta ta saka, da mamaki yace "Ke?? ƙarin gashi ne wannan kika yi? Are you okay??" Ta wani kallesa sai kuma ta koma ta kwanta kan pillow taki cewa komai, ya hade rai yace "Ba magana nake maki ba? A gidan
nan zaki yi ƙarin gashi ko baki da hankali ne? Take that off immediately" On a serious note ya kare maganar fuskarsa daure, ta daga idanuwanta ta kallesa bata dai ce komai ba, ya
ɗ
aka mata tsawa yace "Am i making any sense?" Mikewa zaune tayi tace "Naji"
Daga haka ta sauka daga saman gadon ta nufi bandakin dake dakin, ya bi ta da kallon mamaki don da gaske yayi zaton saka gashin tayi kuma har ya zargi Safiyyah ce ta bata gashin ta saka, ya dau pray mat dinsa ya fice daga dakin.... Karfe tara saura Ajay ya
shiga Bedroom dinsa cause he was expecting her to come out of the room and go to her room tun da asuba amma yaga bata fito ba, bacci ya sameta tana yi comfortably ta nannade cikin Farin duvet dinsa ba ma ta da alamar tashi anytime soon, ya hade rai yace "K
ee" A hankali ta bude ido ta kallesa da sleepy eyes, yace "Garin ki bai waye bane har yanxu? Zo ki fitar min a daki malama" Miƙa tayi tana kallon agogon dake dakin, sai kuma ta mike zaune tana sosa kanta, ya bude mata kofar dakin yana nuna mata hanyar fita
yace "Come and get out" turo baki tayi ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta gefensa ta bi ta fita daga dakin ya bi ta da kallo, sai bayan da ta fito zuwa parlonsa jikinta yayi sanyi tuno incident din jiya da daddare, kasa ci gaba
da tafiya tayi ta juya a hankali ta kallesa taga kallonta yake, ta marairaice tace "Ni fa dakin tsoro yake bani yanxu ban san me yasa ba" Ya mata wani kallo yace "Kina saka gashin kanti ya baza ki dinga mafarki kina yi ma mutane ihu cikin dare ba, c'mon g
o to ur room my frnd, what do you mean? Ni zaki yi inconveniencing a nan" Juyawa tayi ta nufi kofar fita part din jiki a sanyaye, cikin rashin kuzari ta dinga tafiya gabanta na faduwa, tana isa corridor ta tsaya tana tunanin abun yi, gaba daya ta gama tsor
ata da Walid da lamarinsa ga kuma wukar da ya nuna mata wai zai kasheta, after a minute sai ga Ajay ya fito, tana jin Footsteps dinsa ta ci gaba da tafiya tana wasa da fingers dinta shi dai yana biye da ita a baya, dai dai nan sai ga Walid ya fito daga dak
insa rike da akwatinsa karami yana sanye da kananun kaya sai baza kamshi yake, sau daya ya kallesu ya dauke kai ba tare da ya kalli Ajay ba yace "I am leaving for England, na gama abinda zan yi a Maryland" Ajay yace "Safe trip" Walid ya daga kai ya kalli K
haleesat da tayi saurin sauke idonta gabanta na mugun faduwa har sannan tana wasa da hijab dinta, Gaisheta yayi yace "Ina kwana Aunty" cike da karfin hali ta mayar masa da gaisuwan tace "Ina kwana" yace "Toh sai wani lokaci kuma, ni na tafi...." Khaleesat
ta gyada kai kamar kadangariya tace "Allah ya kiyaye hanya" Yace "Ameen" Daga haka ya sauka downstairs, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta nufi kofar dakin da take ciki ta bude ta shiga tana kallon Ajay da ya bi ta da kallo, kulle kofar dakin tayi. Th
at same day da yamma Ajay na zaune parlor yana waya da Hajiya Shafa'atu wanda ba don komai ta kirasa ba sai don Khaleesat don babu wani bond na communication tsakaninsa da ita tunda yawanci a Turai take zama da Mai gidanta da yaranta kuma tana jimawa bata
shigo Nigeria ba, mikewa yayi ya nufi kitchen yace "Tana kitchen bari in Kai mata wayar" Yana shiga kitchen din Khaleesat dake yanka Salad ta juya ta kallesa, ya