Showing 459001 words to 462000 words out of 641791 words
n
an. Ummi ce ta shigo parlon Hajja ta zauna tana kallonta tace "Hajja yanxu nake samun labari wai anyi canceling din meeting din da za ayi bayan isha'i?" Hajja tace "Eh ni nace ayi haka, don duk abinda za a fada a meeting din abu ne da ya shafemu ba wasu ba
Ummi, na kuma gamsu da hujjojin da kika kawo da wanda Sarki ma ya kawo min na kan cewar a bar ma Jawwad crowned prince din, kuma abinda yayi Junaid shi yayi Jawwad, dalilin da yasa naki a ba Jawwad Yarima tun farko dama saboda uwarsa ce ba wani abu ba, ni
kaina sai bayan da kika yi magana naga rashin dacewar a sake cewa za a amshi title din a mayar ma Junaid din kuma, Allah ya sa hakan da Sarki yayi shi ne mafi alkhairi garemu baki daya, shi kuma Junaid zai iya basa wani title din daban" Ummi ta sauke wani
boyayyen ajiyar zuciya ranta fari kal don tun jiya take kokarin gamsar da uwar tata akan cewar a bar ma Jawwad title din kar abun ya dawo kamar wasan yara nan kuma for her selfish interest ta dinga yin hakan, amma jiya kwata kwata Hajja taki daukan hujjoj
inta ta dage lallai sai an maida ma Junaid title dinsa, daxu da safe kuma da Hajja suka zauna da sarki shi ma dai yayi convincing dinta da maganganun da yayi, shi ne har ta saduda da batun mayar ma Junaid title dinsa. Jay na zaune parlon Mai martaba kansa
a kasa ta dalilin kiran da yayi masa, after some minutes Mai martaba yace "Jeka ka kira min Junaid ku dawo tare" Jay ya daga kai ya kalli Sarki, sai kuma ya sauke idonsa kasa, a hankali yace "To ranka shi dade" Mikewa yayi ya nufi kofa, Mai martaba ya bi s
a da kallo har ya fita, Jay ya koma part dinsa ya zauna kan kujera ya dau waya yayi dialing number Hadiyah don bata bangaren, sai da ya katse ya sake kira sannan ta daga tace "I am coming" Daga haka ta katse wayar ba tare da ta jira taji me zai ce ba, baya
n dan lokaci sai gata ta shigo parlon tana yatsine fuska tace "Abincin fa yana ajiye a kitchen kake kirana bayan kasan ina wajen Ummi ne, kuma har yanxu baka tura min kudin ba gashi gobe Shahuda zata zo ta rakani siyayyan tunda ita ta san designers Abaya"
Without looking at her yace "Ki tafi ki gaya ma Junaid Mai martaba na kiransa" Hadiyah ta wani kallesa tace "Tabdi, wallahi bazan je ba, what is my business with him da zan je part dinsa, mutumin da ya gaggaura min mari kaki yi masa komai a kai, wallahi ba
zan je ba meye hadina da wani Junaid" Tana kai wa nan tayi tafiyarta dakinta, Jay ya bi ta da kallo, yana ta zaune bayan ya tuna Sarki na jiransa ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon.
HALYSAAH
Ajay ya karasa har kusa da gadon ya zauna kusa da ita ya
na kallonta tana bacci, hannu ya kai a hankali yana gyara mata gashinta don babu hula a kanta, murya can kasa yace "Good morning Jeeddah" He was being very careful not to wake her up ganin yanda take baccin peacefully, bayan ya gama gyara mata gashin ya ji
ngina da gadon yana ta kallonta, yafi minti goma a haka daga karshe ya mike ya nufi kofa walking slowly ya fita daga dakin. That same day da yamma Jay ya shigo bangaren Mami bayan ta kirasa a waya, da mamaki yake kallon akwatin dake gabanta tana zaune parl
or yace "Mami ina kuma za ki?" Mami tace "Gombe zan je in kwana biyu wajen Karima, ina bukatar in
ɗ
an huta Jawwad" Jay yayi shiru yana kallon akwatin, Mami ta mike tace "Ka kai min akwatin parking space driver yana jira, zan shiga bangaren Hajja in masu sa
llama" Daga haka ta fita daga parlon Jay ya bi ta da kallo, Mami na shiga Parlon Hajja ta sameta zaune tare da Hadiyah da ta dora kanta a kafar Hajja, Hajja ta hade rai tana ci gaba da maganar da take ma Hadiyah, Mami ta zauna tace "Hajja zan je Gombe, shi
ne nace in zo in maki sallama" a takaice Hajja tace "Allah ya tsare" Mami tace "Ameen" Mikewa tayi ta wuce dakin da Khaleesat take, zaune ta sameta kan pillow a kasa Yakumbo na oiling din mata gashinta tana combing dinsa, Mami na ta kallon dogon gashin da
ke ta sheƙi ga cika, tace "Gyaran gashi ku ke" Yakumbo ta gaida Mami da ladabi bayan ta sake gashin Khaleesat tace "Ai kam gyara muke Fulani, kwana biyu tace bata shafa ma gashin Mai ba shine nake shafa mata yanxu, barka da shigowa ranki shi dade" Mami tac
e "Maa sha Allah, ina Noor?" Yakumbo tace "Babu jimawan nan Yarima Junaid ya fita da ita...." Mami tace "Ohk, zan je Gombe Halysaah, ki maida hankali ki kula da kanki kinji, ki ci gaba da shiga ruwan dumi, sannan kar kiyi wasa da cin abinci, duk sanda Hajj
a ta bada umarnin ki koma bangarenki sai ku koma can din tare da Yakumbo ta ci gaba da kula da ke...." Khaleesat dake ta kallon Mami a hankali tace "To yaushe za ki dawo Mami?" Mami ta
ɗ
an yi murmushi tace "In sha Allah idan na gama abinda naje yi zan dawo
Halysaah" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don Mami kadai take gani a gidan nan ta samu relieve, ita kadai take sakin jiki idan ta ganta, shi Ajay yanxu haushinsa na musamman take ji yanxu don ko idonta biyu ya shigo daki yi take kamar tana bacci har sai
ya fita, Hajja kuma ta kasa sakin jiki da ita har yanxu duk da kulan da take nuna mata, Mami da ta lura da yanayin da ta shiga tayi murmushi tace "Do not worry dear, I will be back soon in sha Allah, take care of ur self" Tana kai wa nan tayi ma Yakumbo sa
llama ta juya ta nufi kofa Yakumbo nayi mata Allah ya kiyaye hanya. Mai martaba na zaune parlonsa da daddare ya sauke kansa yana sauraron maganganun da Hajja ke yi, Hajja ta kare da cewa "Don haka nace dole ta bar gidan nan Yusuf, zamanta babu alkhairi a m
asarautar nan, Jawwad bai da wayon rufe ma matarsa kofa, in dai ba ita ta dorasa akan yayi hakan ba, don makirci bayan ta san abinda ta hada shine zata shirya akwati tace ta tafi Gombe, to kuwa sai dai ta dauwama a Gomben" Tana kai wa nan tayi shiru fuskar
ta a daure, Mai martaba ya daga kai ya kalli Ummi dake zaune parlon ita ma, bai dai ce komai ba don yana jiran isowar Jay ne, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo da sallama, Ummi ta hade rai don bata san Sarki ya aika kiransa ba, ita kanta Hajja b
ata sani ba, ya karaso har cikin parlon kansa a kasa ya zauna kan Carpet, Hajja ya fara gaidawa sannan ya gaida Ummi, Mai martaba yace "Jawwad me ya hadaka da matarka?" Jay ya girgiza kai a hankali yace "Na ce ta je gida ne sai na nemeta ranka shi dade" Ma
i martaba yace "Haka kawai baza kace ta tafi gida babu dalili ba ai, meye dalilin ka?" Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Saboda bata min biyayya ranka shi dade, and they are so many things that i don't want to talk about here, I have been enduring all th
is for months...." Hajja tace "Biyayya wani iri kake nufi bayan wanda take maka Jawwad? Kuma meye shi wannan abun that you don't want to talk about idan ba sharri kake son kala mata ba?" Ummi dai sai wani hararansa take, Sarki yayi shiru yana kallon Jay, c
ause he could hear the pain in his voice as he speaks, Calmly yace "Kamar zuwa yaushe kenan zaka neme ta?" Hajja ta ma sarki wani kallo tace "Haba Mai martaba, wannan wani irin tambaya ne kake masa? Wato ka goyi bayan ya aika Hadiyah gida kenan kake nufi?
Sannan naga ai nan din ma gidansu ne ko kai da shi kun manta ne? yanda Hadiyah take bala'in sonsa har ya isa yace ta masa wani laifin da bazai jure ba sai yace ta tafi gida? yarinyar da ko nesa bata son suna yi da juna" Mai martaba yace "Hajja baza ki yi j
udging base on that ba, definitely akwai abinda tayi da har yayi triggering action dinsa, kuma yace bazai fada a nan ba, we have to reason with him...." A fusace Hajja tace "Me tayi kuwa, ba abinda tayi kawai uwarsa ce ta sa yayi haka, shi ne ita ma ta had
a akwatinta ta bar gidan tun ba a waiwayo ta ba...." Mai martaba ya sake kallon Jay yace "Yanxu zuwa yaushe zaka nemeta din idan ta tafi, shi nake son sani Jawwad" A hankali Jay yace "Zuwa sanda na shirya zan nemeta ranka shi dade" Mai martaba ya kalli Umm
i yace "Ki tafi da Hadiyah in zaki tafi, duk yanda ake ciki zan tuntube ki ta waya" Ummi ta saki baki tana kallon sarki, Hajja ma dai haka tayi tana kallonsa, can Hajja tace "To babu inda zata tafi sai dai ta zauna bangarena tunda nan ma gidansu ne, meye s
hi abinda bazai fada ba in ba sharri yake mata ba? Kawai uwarsa ta masa umarnin ya kora Hadiyah gida tunda naje na sameta na nuna mata
ɓ
acin rai na akan abinda take ma jikata, amma in ta san wata ai bata san wata ba" Mai martaba ya kalli Jay yace "Kana gan
in zaka iya gaya ma Hajja abubuwan da Hadiyah ke maka wanda baza ka fadi a nan ba?" Jay ya daga kai yace "Zan iya gaya mata ranka shi dade" Mai martaba yace "To idan ta koma sashinta sai kaje can ka sameta ku yi magana" Daga nan Parlon Sarki Hajja ta tisa
keyan Jay zuwa bangarenta tana cewa "In ma kaurace ma shimfidarka take yi naga dai yarinya ce Hadiyah, iya laifin da zata yi kenan ka kasa hakuri, kuma duk yarinta ce ba wani abu ba, kazanta kuwa nasan sam bata da shi, bar ta dai da son jiki da rashin son
aiki amma bata da kazanta, kuma wannan ba wani abu bane tunda ga masu aiki kaca kaca duk za su yi aikin, ta taso cikin gata ne da sarauta shi yasa baza ta so aiki ba kamar jaka...." Shi dai Jay bai ce ma Hajja komai ba har suka isa part dinta, Khaleesat na
zaune parlon Hajja tare da Yakumbo dake ta bata labari, yanxu kam she is very much okay tana jin sauki sosai and she is healing very fast, Hajja ta shigo parlon Jay na biye da ita a baya, Khaleesat ta sauke kanta bayan sun hada ido da shi, ya zauna kan ku
jera yace "Good evening Halysaah, ya jikin?" Khaleesat ta mayar masa da gaisuwan sannan tace "Da sauki" Yace "Allah ya kara lafiya" Amsa gaisuwan Yakumbo yayi sannan ya mike ya wuce Bedroom din Hajja, ya sameta zaune tana jiransa, ya zauna kan kujera, Hajj
a tace "Ina jin ka...." Jay yace "I wish kaurace min take a shimfida akan tace sai an siya mata abu kaza kafin ayi mu'amala kuma ta tubure akan hakan, tun da taga matar Junaid da designers during her convocation kullum bata da aiki sai demand na designers
now and then, kuma demand din nata baya tashi sai za ayi mu'amala, it's always like this for almost 3 months now, har na hakura na zuba mata ido......" Tun da ya fara magana Hajja ta bude baki tana kallonsa with shock, can tayi kasa da murya tace "Innalill
ahi wa Inna ilaihi raji'un, Kar ka kuskura kaje ka fadi maganar nan a wani waje Jawwad, ko Mai martaba kada ka bari yaji wannan batu, gwara da ka gaya min ni kadai, zan kuma yi maganinta, ashe Hadiyah mutuniyar banza ce ban sani ba, Innalillahi wa Inna ila
ihi raji'un" Jay yace "That aside, few days ago naga wasu abubuwa a bedroom dinmu da ban gane kansu ba...." Hajja ta kara gwalo ido da sauri tace "Abubuwa kamar me?" Yace "I don't even know how to put it, but suna nan na ajiye su, kamar dai abubuwan shirka
or something like that" Hajja ta saki wani salatin tace "Ta shi mu je bangaren naka, tashi mu je, wannan ba maganar da kowa zai ji bane Jawwad gwara a rufa asiri ko uwarka da Sarki kar ka gaya ma wannan abu, nasan kai ba me surutu bane, Hadiyah jinin ka c
e idan baka rufa mata asiri ba wa zai rufa mata, dariya za ayi mana a masarautar nan idan magana ta fita, ta shi mu je" Mikewa yayi ya nufi kofa Hajja ta bi bayansa suka fita, har Bedroom dinsu Hajja ta shiga, Jay ya dauko abubuwan da ya nannade a karamin
towel har sannan kuma Hadiyah bata san ya gani ba, ya bude towel din ya ajiye kasa Hajja ta dinga kallon layun da aka nannade da jan zare, ga wani shi ma an nannade da baƙin zare, sai wasu tarkace su ma duk akan towel din, har da layan da aka garkame da kw
ado, Hajja ta daga kai ta kallesa cikin firgici tace "A ina kaga wannan Jawwad?" Ya rungume hannunsa yace "A dakin nan na gani ina gyare gyare, don tun da muka yi aure bata ta
ɓ
a gyaran dakin nan ba sai dai ni inyi, banda ke babu wanda na nuna ma abun nan h
ar yanxu" Hajja ta saki salati ta nemi kujera ta zauna tana kallon abubuwan kan towel din ta rasa abun cewa, Jay yace "All this not enough, Hadiyah bata respecting Mamina, ko gaisheta bata yi a gidan nan, always saying ill about Mami in my presence" Hajja
ta hade rai tace "A'a ita ma Mamin tana da nata, ka bar maganar wata Mami yanxu mu ji da wannan bala'in dake kan tawul, a ina Hadiyah ta samo abubuwan nan ni Fatsuma? Su waye kawayenta don dai uwarta bazata ta
ɓ
a dorata kan wannan kazamin hanyar ba tunda ba
haka ta taso taga ina yi ba a gidan nan nima, ba irin wahalan da ban sha ba a gidan sarauta har sai da na kusa samun ta
ɓ
in hankali, jifana ake ta ko wani bangare amma kwata kwata basu samu galaba a kaina ba, why because na rike Allah daya, babu ruwana da
harkan tsibbu kamar yanda su suke yi, amma fa na sha wahala ainun daga karshe kuma gashi ni na ci riba, ni ce a saman su, to kuwa lallai zan je in kira Hadiyah yanxu ta gaya mana inda ta samo wannan abubuwan sa
ɓ
on Allahn, don ba halina bane kuma ba halin u
warta bane" Shi dai Jay kallon Hajja kawai yake, Hajja ta mike ta fita daga dakin rai bace, yana zaune parlonsa bayan kusan minti arba'in sai ga Hajja ta dawo, ta zauna kan kujera tace "To wallahi tace wata kawarta ce wai ta kawo mata su, ita kanta bata sa
n ko na menene ba kawai ta ajiye su Jawwad, ni dama nasan sai dai in sharrin kawaye amma ina Hadiyah tasan wani bin boka ko malamai, ka dauko min su yanxu aje a zubar kawai cikin rufin asiri, kuma don Allah komai ya wuce wannan bai kai dalilin da zaka ce t
a bi Maimuna Lagos ba, na kuma yi mata fada sosai, har Maimuna na taya ni, batun kwanciya ma duk nayi mata fada wallahi, in sha Allahu zata dena, yarinta ce kawai ke damunta" Jay yace "Hajja it's better ta bi Ummi su tafi ta huta nima in huta, bazan boye m
aki ba on a serious note haushinta nake ji a yanzu, so ta bani space for now pls" Hajja tayi shiru tana kallonsa, can tace "Wannan dai ba kowa ya tsara maka ba sai uwarka, ita ce zata ce kace Hadiyah ta bi Maimuna, kuma babu inda Hadiyah zata tafi tana gid
an nan zata zauna a bangarena tunda baka isa ka koreta a can ba...." Tana kai wa nan ta fita daga parlon. Tunda Hadiyah ta dawo part din Hajja Khaleesat taji part din ya isheta gaba daya, gashi Hadiyah ta dau karan tsana ta dora ma Noor ba gaira babu dalil
i, har sai da Noor ta dena zama parlor sai dai daki wajen Khaleesat, Bayan Magrib Noor na idar da sallah ta tafi kusa da Khaleesat dake shan fruit salad ta zauna, a hankali tace "Aunty ina son komawa gidan Aunty Murja" Khaleesat tayi shiru tana kallonta, c
an tace "Idan ya shigo anjima ki gaya masa" Noor tace "Ohk" Khaleesat ta gama duk abinda zata yi kafin a idar da sallan isha'i ta kwanta don dai dai lokacin Ajay ke shigowa dubata, kuma kullum ya shigo zai ganta kamar me bacci, karfe takwas da few minutes
ya bude kofar dakin ya shigo da sallama, tuni dama tayi kwanciyarta ta rufe ido kamar warce ta dade da bacci, Noor kanta tayi zaton tayi bacci, Noor ta gaishesa, ya zauna kan kujera ya amsa yace "Have u eaten?" Kai ta gyada masa, sai kuma ta sunkuyar da ka
i tace "Yaya ina son zan koma gidan Aunty Murja" Yace "Why?" Murmushi tayi tana wasa da hijab dinta bata ce komai ba, yace "Ohk gobe zan sa driver ya kai ki sai ku dawo tare ko?" Still dai tayi murmushi bata ce komai ba amma a ranta tasan bazata dawo ba id
an ta tafi, ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin kamar