Showing 54001 words to 57000 words out of 641791 words

Chapter 19 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

221

tayi kasa da murya tana washe baki tace "Ban gane wannan fitar da ku ke yi da Housemate dinki ba Khaleesat? Ina ku ka je?" Khaleesat tace "Abinci fa muka je ya siya min,

kuma ba wai lapiyata lau muka je ya siya min abincin ba" Khaleesat ta ajiye ledan abincin hannunta ta zauna gefen kujera tare da sauke boyayyen ajiyar zuciya, Safiyyah dake washe baki tana ma Khaleesat wani kallo tace "To ya aka yi yasan baki da lafiya, ku

ma how did he know what was wrong with you?" Khaleesat tace "Kinga Sophie wnn ba shine damuwata ba yanzu, muna gidan cin abinci Abdul ya kirani" Safiyyah ta wani yatsine fuska tace "So? Da ya kiraki sai aka yi yaya?" Cike da damuwa Khaleesat ta bata labari

n yanda aka yi da kuma call dinsa da ta ki picking tun jiya, Safiyyah tace "Haba, to ko ke fa da kika fara kokarin kwatar ma kanki 'yan ci, ni sai nake ga kamar Housemate din nan naki ne ke baki Liver kike wasu abubuwa yanzu, banda haka yaushe har kika yi

bakin gaya ma Abdul magana haka" Tana dariya ta kare maganar, Khaleesat ta dinga hararanta ganin ta ma maida abun joke, Safiyyah tace "In ni ce ke ma bazan kirasa ba wallahi, gwara kawai komai ya ruguje kowa ya huta" Khaleesat tace "Kin manta abinda yayi k

wanaki kawai muka gansa kamar an jefosa Sophie? Kinsan yanzun ma ba karamin aikinsa bane sai ya iya kamo hanya ya zo" Khaleesat ta dafe kanta tsabar she is confuse, Safiyyah tayi shiru, can kuma ta kyabe baki tace "Kuma haka ne ba kai ne da shi ba sai ya i

ya kamo hanya tunda ba su dau kudi bakin komai ba, kawai anjima ki kirasa sai ki kisa abinda zaki ce masa da zai gamsar da shi, kuma kina iya cewa baki da lafiya gantalallen ya kamo hanya, ni dama ya tafka wani tsiya America su kwace visan sa kowa ya huta"

Duk da damuwar da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya, Safiyyah tace "Allah kuwa, ban ki ba ya zo ya maki hauka da kaina zan kira masa 911 wallahi" Khaleesat dai tayi murmushin karfin hali kawai, wayar Safiyyah ne ya fara ring ta duba taga Mustapha ke ki

ranta, turo baki tayi tace wannan mutumi yana takura rayuwata a kasar nan, wai daga cewa zan kawo maki abinci ya zata yawo zani shine fa ya biyoni, kema baki ji ba wai ki dawo gidansa da zama, salon wataran matar ta saka mana guba a abinci mu ci mu mutu ga

ba daya, yanzu haka fa ko ga maciji bama yi da ita,

ɗ

an fitar nan da yayi da ni muna nan dake sai ya zamar masa matsala, tana can ta cika tayi fam tana jiransa, ko a jikina kuwa, sai na ma lallabasa ya kai ni ya siya min ice-cream ta yanda zata ga na dawo

rike da leda" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Safiyyah ta mike tace "Bari in je, sai mun hadu Monday in sha Allah" Khaleesat ta rakata bakin kofa a hankali tace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "No thanks kawata, ki ce ma Housemate din

ki na tafi" Khaleesat ta gyada mata kai, a haka Safiyyah ta fita daga gidan, Khaleesat ta kullo kofar a hankali, abincin da Safiyyah ta kawo mata ta dauka ta kai fridge da wanda Housemate dinta ya sa ayi mata takeaway. Khaleesat ta fito wanka kenan taji Ho

usemate dinta na knocking kofarta, ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, yana rike da laptop dinsa yace "Good night Halysaah, i am sleepy" Khaleesat tace "To sai da safe, thank you for the dinner" Yace "No thanks.... kin ki

ra BF din naki?" Khaleesat taki basa amsa, yace "Amma bari in tambayeki, a ina kika hadu da gayen nan ne? Don't know ko na ta

ɓ

a tambayarki kwanaki...." Khaleesat ta jingina da kofa without looking at him tace "Back home" Yana gyada kai yace "I see, ni at f

irst na zata you are not Nigerian, was thinking you are from Niger or Chad, probably Shuwa Arab" Khaleesat ta dinga kallonsa, bata san sanda tace

"Why?" Yace "Na ganki kamar Buzuwa" Khaleesat ta sauke idonta bata basa amsa ba, yace "Ok, i will be on my way

, good night" Daga haka ya juya ya bar wajen, a hankali ta sauke idonta sannan ta kulle dakinta ta jingina jikin kofar, she stood there for almost 5 mins kafin ta karasa cikin dakin ta cire hijab din jikinta ta ciro sleeping dress dinta ta saka, sanitary p

ad dinta dake gaban dressing mirror ta dinga kallo, sai kuma ta dauke daga wajen, sai da ta kwanta sannan tayi dialing number Abdul gabanta na faduwa, har ya katse bai daga ba dama tasan ba lallai ya daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, ta bude Wha

tsApp tayi masa magana ta nan, reply yayi mata yace "I don't have ur time so do not border me" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta kashe wutan dakin sannan tayi kwanciyar ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Washegari bayan Khaleesat ta gama azkar din

da take yi, ta jawo wayarta a hankali, tunda ta tashi jikinta yake a sanyaye don mafarki tayi Abdul ya zo kamar yanda ya zo wancan lkcn still kuma ya sake haduwa da Housemate dinta a gidan, ba karamin daga mata hankali mafarkin nan yayi ba, WhatsApp dinta

ta bude bayan tayi deciding zata masa message din ban hakuri duk da bata saka ran reply dinsa ba, cause it won't be funny if her dream comes true, tana shiga WhatsApp din ta ga ya turo mata hotuna kusan biyar tun 3 hours ago, bude message din tayi zuciyart

a na bugawa don bata san hotunan menene ba, nan taga har da message yayi mata kafin yayi sending hotunan, ta fara downloading hotunan at the same tana duba message din da ya rubuto mata kamar haka "So now, kina kokarin nuna min cewa i made the mistake of l

etting you go to America to study right? Kin mance wacece ke ko? kin mance daga inda kika fito, then that is so foolish and stupid of you Khaleesat, amma ina me tabbatar maki idan har kika ci gaba da daukata for granted kamar yanda kike yi kwanan nan sai n

a sa kinyi da kin sani wallahi" Lkci daya Hawaye ya cika idon Khaleesat, ta sauke idanuwanta kan hotunan da ya turo mata, daya hoto ne da shi yayi mata a bakin kofar dakin Ummanta, yana zaune kan tabarma ta duka gabansa zata ajiye masa ruwa a Cup shine ya

dauketa hoton, shekaru hudu da suka wuce kenan, she look so so young and meek a hoton, hoto na biyu kuma tana wajen debo ruwa a nan unguwansu ya zo ranan ya ganta a wajen, ita bata ma san yayi mata hoton ba ga zaninta duk a jike, hoto na uku kuma tana baƙi

n murhu a tsakar gidansu tana juye alalan siyarwan Ummanta a Cooler shi kuma ya zo gidan ranan, duk bata san ya mata hotunan nan ba sai yau da ya turo mata ta gani, hoto na hudu kuma ranan da ya kai ta zata zana Jamb ne, jamb din da bata ma yi amfani da sh

i ba daga karshe, sai kuma hoton karshe na ranan da zai kawota USA for the first time, looking at all the pictures da kuma looking at her now zaka ga banbanci me tazara sosai, infact the difference is very obvious don a yanzu she looks more beautiful, matu

red, nourished and well taken care of, yanzu skin dinta har wani glowing yake, in ma ba ka santa ba bazaka taba cewa ita ce a hotunan ba, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da pillow tana kuka sosai, but like seriously Abdul bai yi deserving

haka daga gareta ba, but did she also deserve irin abubuwan da yake mata? Kuma tun asali haka yake mata, Kuka sosai tayi babu me rarrashinta, bata ma san me take ji a zuciyarta ba a lkcn, she cried profusely for almost 30 mins, daga karshe tayi karfin hali

n mikewa zaune ta dau wayarta, she don't even know where to start from, Voice note ta fara masa muryarta na rawa trying to tell him she is sorry, amma bata kai ko ina a basa hakurin ba ta fashe da kuka sosai, cikin kuka ta ci gaba da basa hakurin, sai da t

ayi masa Voice note uku sannan ta ajiye wayar still crying....

07087865788✍

🏻

✨✨

HALYSAAH✨✨

By _Khaleesat Haiydar_✍

🏻

18.....

Wajen karfe goma na safe Khaleesat na kwance dakinta idonta rufe duk da ba bacci take ba, ji tayi ana kwankwasa kofa, kamar

bazata iya tashi ba daga karshe dai ta mike ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka, tana tafiya a hankali ta fito parlor, ta tagar parlon ta duba ta ga Housemate dinta ne, ta karasa ta bude kofar, Yace "Sorry na tashe ki kina bacci, i forgot th

e key at home" Ita dai bata yarda sun hada ido ba a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how are you feeling now?" Ta juya going back to the parlor tace "Alhamdulillah" Ya bi ta da kallo sannan ya shiga parlorn, dakinta ya ga zata koma yace "Halysaa

h" Ta tsaya, after few seconds ta juyo but couldn't let her eyes contact his, shi dai kallonta kawai yake, ya karasa inda take tsaye yace "What happened?" Girgiza masa kai kawai tayi, lkci daya hawaye ya fara sauka idonta, ya dauke kai na 'yan dakiku kafin

ya sake juyowa ya nuna mata kujera yace "Sit" Komawa tayi ta zauna, ya zauna shima yana kallonta yace "Tell me what's wrong" Ta sunkuyar da kanta, yace "Are you sick?" Ta girgiza masa kai, yace "Wannan saurayin naki ko?" Ta kasa basa amsa wasu hawayen na

sauka idonta, sai kuma ta fashe masa da kuka, mikewa yayi yace "Waye ya hadaki da wannan mutumi ne? Why did u allow him know ur weak point? Why are you always crying because of him? Is he happy making u sad now and then?" Khaleesat dai kuka take a hankali,

yayi shiru for almost 2 mins yana jin ransa na baci, can ya kalleta yace

"Kee in zaki yi facing study dinki is better you do so, give that ur so called boyfriend space, ur exam is around the corner" Sai a sannan Khaleesat ta daga idanuwanta da suka yi ja

ta kallesa, sae kuma ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Housemate, zan dinga sa ki a addu'ata Allah ya maki mafita, i can't just intrude cause ban san sanda ku ka san juna da shi ba, ban kuma san me ya hada ku ba, i will only include you to my prayers i

promise Halysaah" Khaleesat ta gyada masa kai da kyar, sannan ta mike cikin sanyin murya tace "Nagode" Daga haka ta juya ta nufi dakinta, Jay ya koma ya zauna yana mamakin irin son da take ma gayen da har ta kasa rabuwa da shi duk da musguna mata da yake

yi a soyayya, bata da aiki sae yi masa kuka, da kanwarsa ce daga ita har saurayin zai hada ya ci ubansu, kuma ya rabata da shi na har abada, tausayinta yaji har cikin ransa don bai san wani irin so bane wannan take masa da har take iya tolerating abubuwan

da yake mata, and ya lura the guy is taking advantage of this to hurt her always, mikewa yayi ya tafi kitchen kamar yanda ya zarga yaga alamar bata yi breakfast ba har sannan don kitchen din ma bata shigo ba, fridge ya bude ganin abincin da Safiyyah ta kaw

o mata jiya yayi mata microwaving dinsa ya hada mata shayi sannan ya kai mata daki, sai da yayi knocking ta amsa sannan ya shiga dakin, tun da ya shigo Khaleesat ke kallonsa har ya ajiye mata abincin, ta sauke idonta a hankali tace "Nagode" kai kawai ya gy

ada mata, sai kuma ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, karfe sha biyu saura Khaleesat ta jawo wayarta jin yana vibrate, tana duba screen din taga Abdul ke kiranta, ta sauke idonta kasa tayi picking call din ta kai kunne amma bata ce komai ba, yace "K

haleesah...." ta kasa amsawa hawaye ya fara sauka idonta, yace "Can you hear me?" Da kyar tace "Um" Yace "How was you night" tana share hawayen dake sauka idonta tace "Alhamdulillah" Tun daga wannan rana Khaleesat ta fara avoiding duk wani abu da zai hadas

u fada da Abdul, she want just nothing but peace with him for her sanity, bin sa kawai take a yanda yake so for peace to keep reigning, in ma bala'i yake mata a waya zata yi shiru ta gama saurarensa sannan daga karshe ta basa hakuri kamar yanda take yi mas

a da, ranan da bai kirata ba kuwa ita zata kirasa, hakan kuma da tayi ya sa ta samu kwanciyar hankali har take concentrating a karatun ta, amma fa in ta tuna irin kulawar da Housemate dinta ke bata always wanting to make sure she is fine sai taji she isn't

lucky having Abdul, ana haka har exams dinsu ya rage some days, ranan Wednesday tana kitchen da safe taji ana kwankwasa kofa, ta fito daga kitchen din don dama she is expecting Safiyyah, ta bude mata kofa, Safiyyah ta shigo tace "Ai na zata zan zo in tara

r baki tashi ba?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "Aa i am in the kitchen" Safiyyah tace "Ohk, why are you lowering ur voice?" Still Whispering Khaleesat tace "My Housemate is sleeping" Safiyyah ta sake baki tana kallonta, sai kuma ta rike ha

ɓ

a tace "Ik

on Allah gadinsa kike kenan?" Khaleesat ta hade rai tace "Ban gane gadinsa ba, daxu fa ya zo, and dama bacci yake zuwa yayi da safe don yace min baya bacci da daddare" Safiyyah couldn't stop smiling tana kallon Khaleesat, Khaleesat ta wani harareta ta juya

ta koma kitchen, Safiyyah ta karasa ta zauna kan kujera har sannan bata daina murmushi ba, sai ga Khaleesat ta fito daga kitchen, still tana magana kasa kasa tace "Ko dai kawai mu je waje ki min gyaran gashin, kinga Hand dryer yana ƙara in ana using dinsa

, it's noisy" Safiyyah ta buda baki tace "Ikon Allah, to akwai socket ne a wajen?" Khaleesat tace "Zan sa Extension a kitchen sai mu fito da shi ta window ai zai yi, kuma akwai tap a garden din sai mu wanke gashin ma a nan" Safiyyah dai murmushi kawai take

bata ce mata komai ba, yanda Khaleesat tace haka din tayi duk don kar karan Hand dryer ya tada Housemate dinta or any of their noise kamar yanda tace, abinda bata sani ba ashe ba bacci yake ba aiki yake yi a Laptop dinsa a daki, bayan sun isa karamin Gard

en din dake bayan kitchen Khaleesat ta ajiye duk shampoo da Conditioner din hannunta sannan ta bude gashinta, Safiyyah na kallon gashin tace "Tab, Allah sa Shampoo din da Conditioner su isa dai" Khaleesat ta wani hade rai tace "Ban gane ba, saboda bargo za

ki wanke?" Safiyyah tayi dariya tace "To meye banbancin wannan da bargon Khaleesat? Babancinsa kawai wannan akan ki yake, ni naga ma kamar karuwa gashin yake Tabarakallah Maa sha Allah" Khaleesat tace "Ba abinda ya karu yana nan yanda yake" A haka Safiyya

h ta fara wanke mata gashin, suka dau time sosai bayan ta gama wankewa ta fara busar mata shi da Dryer, Jay ya shigo kitchen zai yi making Coffee drink ya dinga kallonsu ta window din kitchen, he was confuse seeing her hair, is all that Hair or what? long,

full and black, kawai yaji bai yarda gashinta bane, ya juya ya fara yin abinda ya kawo sa kitchen din, Khaleesat ta kasa kunne sosai jin kamar sound a kitchen, ai ko ta jawo mayafinta da sauri ta rufe kanta bayan ta hangosa a kitchen din ya juya masu baya

, Safiyyah dai sai kallonta take, Khaleesat ta mike ta isa kusa da window din kitchen din tana kallonsa tace "You woke up early today" Ya juya ya kalleta yace "This is to 12" Khaleesat ta zaro ido don bata san lkci ya wuce haka ba, ashe sun bata lkci sosai

wajen wanke gashinta, yace "Me kike yi a nan?" Tace "I am together with my frnd Safiyyah" Ya ci gaba da abinda yake yi yace "Ohk my regards" Juyawa tayi ta koma gun Safiyyah, bayan Drying har Stretching gashin sai da Safiyyah tayi mata, Safiyyah tace "You

know what Khaleesat, anjima ki zo can gida sai in maki Kalaba din, i think i can feel my period, i need to go home" Khaleesat ta juya ta kalleta tace "Da gaske?" Safiyyah tace "Wallahi, gwara in tafi gida kar ya zo" Khaleesat tace "Ohk, amma ki bari in da

fa mana indomie ki ci tukun ki tafi" Safiyyah tace "Ke bazan ci ba, bari in tafi kawai i am uncomfortable" A hankali Khaleesat tace "To shikenan" Safiyyah tace "Sannan pls Khaleesat nace ma Ya Musty ran sunday zaki zo gidan tunda kinga Monday za mu fara ex

ams, ko 2 days ne sai kiyi kafin matarsa ta fito da baƙin halinta gaba daya, kin dai ga bazai ce bamu ji maganarsa ba yace ki dawo gidansa baki dawo ba, even if it's just 2 days come and spend in his house pls" Khaleesat tace "Wallahi ba wai bana son zuwa

bane ko kuma ban ji

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login