Showing 114001 words to 117000 words out of 641791 words
na fadi
inda take ko su harbeni" A tare Ajay da Jay suka kalli juna, Salem yace "Kashe ni suka yi niyyar yi banda Allah ya rufa min asiri kururuwan da nake yi wani soja dake kusa da gidanmu ya fito da bindiga, da wani makocina da ya fito da adda, kafin makota na s
u fito ne suka min harbi har biyu daya ya sameni a kafada daya kuma bai sameni ba ya sami gate, sojan da makoci na suna fitowa suka shige motarsu suka tsere, ni wallahi ban taba jin sunan yarinyar da suka ambata ba ma" Aunties din Salem biyu ne suka shigo
ward din da sallama, Ajay ya gaida su sannan ya fita daga ward din ya tafi haraban asibitin ya zauna, after almost 10 mins Jay ma ya fito, inda Ajay ke zaune ya nufa ya zauna bai dai ce masa komai ba, Ajay yayi breaking silence din yace "He is tracking me,
ni yake nema ba Salem ba, but tana da number Salem a wayarta ne?" Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Yawanci shi take kira ya bani waya if there is anything she wants to tell me, ko number ka ma ai Salem ne ya tura mata, instead cewa zaka yi he is trac
king the both of us tunda nima ta kira layina ai ranan, but how did he get Salem's line?" Ajay yayi murmushi yace "Definitely layinta ya sa a duba masa numbers din wa enda take waya da, and he is using that to track us" Jay ya mike yace "We need to take do
wn our sim card AJ, decidedly zai samu information mun shigo kano since we are in his list, sannan i think before anything ya kamata mu fara fighting for her innocent father's release tunda ita Halysaah yanxu bai san inda take ba and she is safe where she
is, but the Man needs help" Ajay yace "No, i don't think she is safe with her aunt, although aunt din tace bai san inda ta koma ba
amma as far as yana da number wayarta zai iya sakawa ayi tracing din inda take ita ma" Jay ya juya yana kallonsa yayi shiru,
he just realize of course hakan zai iya faruwa cause ya daina underrating Abdul yanxu, Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "That guy is something else Ajay, duk wata salon mugunta ya sani adding it to his career skills, ina jin kawai a duba mana if there
is flight zuwa Niger republic a biya masu kawai su tafi can da aunt dinta har zuwa sanda za mu gama da Case din dad dinta, in the other hand shi kuma mun yi sue dinsa requesting for divorce for her" Ajay yayi shiru, can yace "But what if she is needed in c
ourt?" Jay yace "For now her lawyer will represent her, in ma an bukace ta a court we will sort that out" Jay yace "I think that's cool, amma ya kamata mu je gidan su gun mahaifiyarta" Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "Is that necessary?" Jay yace "O
f course, kasan aunt dinta tace mana the mother is not medically fit, kada wannan damuwar yayi weighing dinta down" Ajay yace "Sai mu je a matsayin su wa?" jay ya mike yace "Human right" Abdul na tsaye rike da takardan da mahaifiyar sa ta mika masa daga sh
igowar sa parlor idonsa na kan takardar yana karanta content din jiki, Meema yayarsa ma na zaune parlon tana kallonsa fuskarta dauke da bacin rai karara, wani murmushi Abdul yayi ya cukuikuye takardar ya jefar kan kujera, Mahaifiyar sa dake ta kallonsa ta
tabe baki tace "To yanxu menene amfanin wannan tozarcin da kaskantar da kai da ake yi? Sam kace kai baza ka ji maganata ka dau shawara ta ba Abdallah?" Meema ta katse ta tana kallonta a fusace tace "Haba Momy ta yaya kike son ya ji maganarki bayan uban kud
in da ya kashe ma tsinanniyar shegiyar yarinyar? Ai jin maganar ki ba nasa bane wallahi, kuma don an kawo masa sammaci ba shi ke nufin ya hakura zai saketa ba, kotu ce kawai za a shiga ayi ta gwabzawa, kuma in sha Allahu duk inda kafafuwana za su shiga sai
na shigar da su don Abdallah yayi nasara a wannan case din, bazan ta
ɓ
a bari a tozarta min kanina ba ga mari ga tsinka jaka bazai ta
ɓ
a yiwuwa ba wallahi, alamar koma waye ya zugata ta yarda aka yi karansa zai iya biyan ko nawa aka ce ya biya a kotu, kai ja
ma'a amma yarinyar nan anyi babbar er iska butulu, dama ni tun asali ban goyi bayan da yace zai kai yarinyar nan Amurka ba ina jiye masa tsoron kar idonta ya bude, to gashi nan bayan karatun har da karuwanci ta dinga yi da manyan kasar nan tunda gashi har
ta samu wanda zai tsaya mata da lauya ya biya makudan kudin da aka kashe mata kilan yace har da miliyan 100 da ubanta ya salwantar, abun arziki dai bai amshe mu ba a family din nan, ban ga laifin ki da baki son talakawa ba Momy, shi yasa nima bana son su n
a tsane su" Momy dai girgiza kafa kawai take tsabar takaici da bakin ciki ta kasa cewa komai, Meema ta kalli Abdul daka safa da marwa a parlon yana
ɗ
an murmushi tace "Ka kwantar da hankalin ka Abdul, as far as ina numfashi kuma uwar mu na numfashi ko don k
a rama duk abinda yarinyar nan tayi maka za mu shiga mu fita har sai kotu ta baka ita, in sun san wata ai basu san wata ba, koma waye ke taka mata baya daga karshe kashe kudadensa kawai zai yi a banza don sai ta shigo gidan nan mun ci ubanta da izinin Alla
h, banda kaddara me ma zaka yi da er gagurumin barawo kuma makaryaci, daga basa dukiya ya kai Lagos yace an kwace mota" Sama Abdul ya wuce kamar zai tashi sama, Momy ta bi sa da kallo cikin bacin rai tace "Kai Allah Ubangiji ya tsine ma mutanen nan albarka
, yanda suka sa
ɗ
a na a damuwa Allah ya saka duk zuri'arsu a damuwa, ita kuma yarinya Allah ya kasheta ma duk mu huta, tun da lamarin nan ya faru ko abincin kirki Abdallah yaki ya zauna ya ci a gidan nan, in ya fita tun safe sai dare muke ganinsa gaba daya
ba shi da sukuni akan er talakawa, wannan wani irin iftila'i ne ya same mu" Meema tace "Tashi tsaye kawai za mu yi ayi abinda ya kamata Momy, gidan nan ai kamar ta shigo sa ne in sha Allahu, da bakinta zata ce ita ta hakura a kai ta gidan mijinta kawai, k
uma ta shigo nan ta same mu muna jiranta" Daga haka Meema ta mike ta bi bayan Abdallah. Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case di
n a kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san wani irin lauya bane
ɗ
an sa, don har da
written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana nan, why let them arrest the man again? Ko dai
ɗ
an nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu
meye abun yi Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt again in near future, just that za mu yi
presenting documentation of the original debt forgiveness and court records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa" Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa
zai yi a kulle, his family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is going on, they will
even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar duk
kansu suka yi tsaye jikin motar da suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba tare da Ajay ya k
allesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, J
ay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah? How is that even a name? In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na asal
i?"
Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya
ɗ
an yi murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu
samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk
suka yi daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka am
sa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz
ku shiga har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali, Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan stepmom din Khaleesat ne matan, ya ku
lle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yan
da za a shigo a fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan ta
ɓ
on da yayi gaja gaja a compound din bai fallatsar ma
sa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata, gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar
da ruwa sai ya cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin kofar ya gaida Umma da Maman Salam
e dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba
duba da yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta dau mafici ta mika masa, ya
ɗ
an yi murmushi
ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mam
a Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da ma
haifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su
yi tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa, after few seconds Ajay yayi karfin ha
lin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salam
e tace "Allah yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya
kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga g
are ku, don bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mike
wa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki
da sauri, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai ga almajirai suna shigowa gidan da buhun sh
inkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu, manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta
taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??" Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless an
d shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai ya fita daga dakin.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
👈🏻
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanci
yar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
*Hmm don't even know where to start from
🥺
Khaleesat's Citadel ku sani Billah ina yinku
💯
Nagode Nagode da abun arziki, Allah Ubangiji ya bar mu tare, Allah ya kara maku
arziki ta yanda bakwa zato, Allah ya raya maku zuri'a ya baku zaman lafiya da mazajenku, wa enda basu da auren cikin ku Allah ya fiddo maku da mazaje na gari, yanda ku ka faranta min yau ku ma Allah ya faranta maku, thank you soo much Meenah parrot for bri
nging about the idea and the wonderful Souls that supported it, Allah ya kara mana hakurin