Showing 591001 words to 594000 words out of 641791 words

Chapter 198 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

111

today because they helped me, that village is supposed to be a second home to me, the peo

ple of the village are suppose to be my second family" a hankali Khaleesat tace "But ai kana da intention din zuwa ba wai baza kaje kwata kwata ba, beside we left for America for ur surgery, representative where sent to Benue after we left for America, kaw

ai dai basu gane inda za a samu mutanen bane cause garuruwan da yawa, You are not an Ingrate my love, nasan dole zaka koma wajen su, truly they are our family too" Ajay yace "In few days time in sha Allah zan je Benue, idan ban je ba bazan samu nutsuwa ba,

ni nasan inda zan samo su" Khaleesat ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, after some seconds tace "To kai kadai zaka je?" Yace "I am going with Jay, idan nace sai mun koma Bauchi za mu kara bata lokaci ne, kuma Mai martaba zai iya cewa za mu je tare da shi,

Kinga sai sanda yake da lokaci ne hakan zai yiwu" Khaleesat ta gyada masa kai a hankali tace "Haka ne, but ina son zan bi ka nima" Ajay yace "The only means of transportation to the village is by water Jeeddah" Tace "Ehh ni dai ina son ka je da ni plsss"

Bai ce komai ba, cause condition dinta yake dubawa, baya son wani abu ya samu karamin cikin jikinta, ta marairaice tace "Ka ji" Kawai don kar ta daga masa hankali ta daga nata hankalin yace "Na ji wife" A haka suka isa tudun Yola, Ajay yayi parking bayan w

ata mota dake gaban gidansu Khaleesat, Khaleesat dai sai kallon motar take wondering whose car it is, Ajay ya kalleta yace "Zaki kwana ko?" Ta langwabe kai a hankali tace "Sai yanda kace dear" Ya

ɗ

an yi murmushi, yace "Kiyi duk kwanakin da kike son kiyi" y

a fada haka ne don ya samu yaje Benue ya dawo ba tare da ta sani ba, Tace "To mu shiga sai ka gaisa da su Nenne" Yace "Ki fara shiga first...." Tana murmushi ta bude motar ta sauka tace "Bari in sanar masu zaka shigo" Gate din gidan ta nufa ya bi ta da kal

lo, har Khaleesat ta wuce motar dake gaban nasu sai kuma ta tsaya bayan sun hada ido da Abdul dake zaune cikin motar, don suna hada ido ya bude motarsa ya sauko, yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Hajajju, Barka da yamma" Tana

ɗ

an murmushi ita ma tac

e "Ina yini Ya Abdul" Yace "Lafiya lau, ya kwana da yawa?" Tace "Alhamdulillah" Yace "I came to see a frnd, ya mai gidan naki? Ko tare ku ke?" Khaleesat tace "Eh tare mu ke" Abdul ya kalli motar Ajay sannan yace "Bari in je mu gaisa" Yana fadin haka ya nuf

i gun motar, tunda ya sauko daga motarsa dama Ajay ke kallonsa, sai da Abdul ya iso har kusa da motarsa sannan ya bude motar ya sauka, Abdul ya mika masa hannu suka gaisa, ita dai khaleesat ta nufi gate din gidansu tana kallon mutumin dake zaune bakin gate

din alamar Mai gadi ne, gaishesa tayi ya mayar mata da gaisuwan da ladabi, ta shiga cikin gidan, bin ko ina ta dinga yi da kallo tsabar yanda gidan ya canza ya dawo kamar lokacin aka gina sa, ga flowers din gidan duk sun girma, ko ina was very neat, babu

kowa a compound din gidan ta karasa har cikin parlor nan ma taga tsadaddun furnitures da aka canza a parlon har da TV da labule da carpet duk an canza, infact komai na parlon sai da aka canza, ga dinning table sabo a dinning area, bedroom din Ummanta ta nu

fa taga bata ciki, nan taga sabbin kayan gado masu tsada sosai a dakin, ta dawo ta tafi dakin Nenne, farin ciki gun Nenne ba a cewa komai bayan Khaleesat ta rungumeta tana mata Oyoyo, Nenne tace "Ikon Allah, saukan yaushe Khaleesat?" Khaleesat na murmushi

tace "Jiya muka shigo Kano daga Abuja" Nenne sai kare mata kallo take ganin yanda take sheki, gashi duk ta cicciko, Nenne na washe baki tace "Ina mijin naki?" Khaleesat tace "Yana waje, Nenne ina mutanen gidan? Naga ba kowa" Nenne tace "Uwarki ta shiga gid

an Hajiya Zaliha dubota bata ji dadi kwana biyu ba, yara kuma gaba daya sun tafi islamiyyah, Kinsan yanxu ba a wasa da karatu daga islamiyyan har boko a gidan nan, kannenki dama shirye shiryen saukan Al-qurani suke, sun haddace Al-qurani me tsarki, nasan d

ai uwarki ta gaya maki" Khaleesat na murmushi tace "Eh ta gaya min, to ina su Mama Zubaida?" Nenne tace "Zubaida na can bangarenta yanxu dai atamfofi yake siyarwa da leshi, Shatu kuma taje kauyensu biki ita kuma craw fish take sarowa buhu buhu tana siyarwa

, duk Farida ce ta basu jari yan wahala" Khaleesat tace "To babana fa, ko yana kasuwa?" Nenne tace "Malam Ali na kasuwa, kin san yanxu shagunan sa na kayan hatsi hudu a kasuwa, sari ma yake badawa baya awo, yaran shagunansa sun fi takwas yanxu haka, bana m

a da shi za ayi aikin Hajji, duk juma'a sai mun yi sadaka kwana biyar a gidan nan da rana, da safe kuma ayi sadakan koko da kosai" Khaleesat na murmushi tace "Alhamdulillah, Umma ta gaya min, yauwa Nenne naga Ya Abdul kofar gida yace min ya zo wajen wani a

bokinsa, waye abokinsa a layin nan?" Nenne tace "Wani aboki?? Bai da wani aboki a layin nan karya yake, wani ranan juma'a ne fa da ya zo wai gaisheni sai suka hadu da

ɗ

an mijin Hajiya Zaliha yaro me hankali me sunan babanku ana ce masa Haiydar, shi ne fa s

uka gaisa suka

ɗ

an yi hira da yaron, tun daga sannan ya fake da cewa wajen Haiydar yake zuwa a unguwan nan, kuma wallahi ni na ganosa wajen Noor yake zuwa sai yace ya zo wajen Haiydar, duk yamma haka zai zo kofar gidan nan yana jiran ta dawo islamiyyah, ni

dai har yau ban yarda da Awdul ba, a tsorace nake da shi, zan ce kar ya sake zuwa Zahra'u ta hanani wai in kyalesa kawai, shi ne Haiydar ke ce min ai mahaddacin qur'ani ne ga sanin addini kaca kaca a kansa, wai idan ya fara rero karatu kai kace Shek Sudes

s din Saudiyya ne, to kin san Noor ita ma akwai kira'a kuma in dai ka shigo gidan nan ranan juma'a zaka sameta ne tana karatun ta, to in gaya maki kwana daddaya ne Awdul baya zuwa kofar gidan nan, ni dai har yau ban yarda da shi ba, lokaci kadan nake jira

na ja masa layi da zuwa unguwan nan yana tare min jikata a bakin gate idan ta dawo islamiyyah, bai san ni bane da Sarkin Bauchi zan hadasa wallahi" Khaleesat dake ta kallon Nenne ta sauke idonta a hankali tace "Ni na yarda da shi Nenne...."

HALYSAAH

Nenne ta saki baki tana kallon Khaleesat, can ta gyara zama tace "Kika yarda da wa?" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalli Nenne tace "Ya Abdul" Nenne ta riƙe ha

ɓ

a tace "Tabdi, wato saboda kin samu

ɗ

an arziki me sonki yana tarairayar ki shi yasa har kika

mance ukubar da kika sha a hannun Awdul ko?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Me yasa iya sharrin Abdul kawai ku ke gani kuma ku ke tunawa Nenne? Duk matakin da na taka a rayuwa Abdul ne sila babu wani kwaskwariman da zai canza haka, shi ne mutum n

a farko da ya fara son ganin ya inganta min rayuwata ta yanda zan zamo matar nuna ma sa'a a lokacin da ya so aurena, da Abdul ba ya so na tsakani da Allah bazai ta

ɓ

a daukar hanyar gyara min rayuwa ya bani ingantaccen ilimi har ayi sha'awata a wani wajen ba

, don haka idan iya sharrinsa ku ke tunawa ni kam alkhairinsa ya take sharrinsa a wajena, kuma har cikin raina nake kyautata masa zato yanxu, dama can a baya shi din mai ibada ne kuma yana karatun qur'ani sosai duk da halin sa, ni zan shaide sa akan haka"

Nenne ta kyabe baki tace "Shege shi ke manta alkhairi dama ai, amma kuma tsorona Allah tsorona Awdul baza ki ta

ɓ

a hanani dena tsoronsa ba bari ki ji in gaya maki, haka kawai bazan biye sintirin da yake mana ba a gidan nan in dau jikata in basa, ai Haiydar

din ya kusa komawa turai don a can yake aiki, zan ga da sunan wa zai ci gaba da zuwa layin nan, kuma fa in dai ya zo unguwan sai ya shigo ya gaisheni, saboda ya ga bana amsan kudinsa ya ma dena bani, zai dai shigo ya gaisheni, wani lokacin har ya ci abinci

, banda Zahra'u dake kwa

ɓ

a ta da tuni na koresa ni dai, ba ruwana da jaraba" Bude kofar dakin aka yi, Noor ta shigo da sallama, zaro ido tayi ta tafi ta rungume Khaleesat cike da murna tace "Aunty yaushe kika zo?" Khaleesat na murmushi tana kallonta ganin

yanda ta girma, ga shi sak ita a sanda take shekarunta, ta dago kanta tace "Not long ago, Ina Islam?" Noor na murmushi ita ma tace "Na bar su a baya da kawayenta" Juyawa tayi ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Kuna yan biyu baza ku jeru ku dawo gida tare

gwanin sha'awa ba, ni ban ta

ɓ

a ganin yan biyu masu yin haka ba sai a kan ku" Noor dai bata ce ma Nenne komai ba ta mike ta nufi fridge din dake dakin ta bude, Nenne ta hade rai tace "Lafiya?" Noor bata kalleta ba ta ciro ruwan gora tace "Ruwa zan dauka" Ne

nne tace "Kiyi min me da shi?" Noor tace "Uncle yace in kai masa...." Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace "Ai dama na sani, ke kika zuba min ruwan a firijin ko kuma shi Ankle din ne ya zuba min? kullum sai kin shigo min daki kin daukar min ruwan gora kamar

ke kike siya min, uwar me yasa baza ki kai masa piya water ba" Noor ta tura baki ta juya ta fita daga dakin tana rike da ruwan goran, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Munafuka ce fa, saboda shi ita ma take dawowa da wuri ta bar er uwar a gantale a hanyar mak

aranta, duk ina lura da qita, to uban me yake tsara mata da take Allah Allah ta dawo ta dau min ruwan gora? To ni dai ba ruwana, in maye ya manta uwar

ɗ

a dai bata manta ba..... Kar nake kallon Awdul" Khaleesat dai taki tanka mata, tunawa tayi ta bar Ajay a

waje bata san sanda ta mike da sauri ba har sai da taji kanta ya juya mata tayi saurin dafa bango jiri na dibanta, Nenne ta mike tace "Subhanallahi, lafiyar ki? Me ya faru" After some seconds a hankali Khaleesat tace "Wallahi na mance yana waje" Tana fadi

n haka ta fice daga dakin don jirin da take ji ya ragu, compound ta fita taga Abdul zaune cikin sabon Pavilion da aka gina a compound din, ga qur'anin Noor a gabansa, Noor kuma na tsaye gefensa, tana ganin Khaleesat ta ajiye bottle water din hannunta kan t

able sannan ta fita zuwa gun ta, tana kallon Khaleesat tace "Aunty wai tafiya za kiyi? Umma fa bata dawo ba" Khaleesat tace "Ba tafiya zan yi ba, karatu ku ke yi ne?" Noor tace "Muraja'ah kawai nake yi" Khaleesat tace "Ohk, kin ga mota a kofar gida da kika

dawo yanxu?" Noor ta girgiza kai tace "A'a babu mota, wai tare ku ke da Uncle ne?" Khaleesat tace "Tare mu ke, je dai ki duba ko yana waje" Noor ta juya ta nufi gate, Khaleesat kuma ta juya ta koma cikin gida, ba a dau lokaci ba Noor ta dawo ta tarar da K

haleesat zaune parlor tace "Aunty babu mota, kilan ya tafi" Lokaci daya jikin Khaleesat yayi sanyi, ta mike ta koma dakin Nenne, handbag dinta ta bude ta ciro wayarta tayi dialing numbersa, har ya katse bai daga ba, few seconds later sai gashi ya kirata, a

hankali tace "Why did you leave?" Yace "Zan dawo anjima, naga kuna da baƙo a gidan" Khaleesat tace "That doesn't mean, he isn't here because of us ai, we met him instead" Ajay yace "Haka ne, take care of ur self, zan je gidan sarki ne yanxu in gaishesa...

" Khaleesat tace "Sarkin garin nan?" Yace "Eh" Tace "To yaushe zaka dawo?" Yace "Idan ma ban dawo yau ba zan dawo gobe" Shiru Khaleesat tayi, yace "Take care" Daga haka ya katse wayar, Nenne dake ta kallonta tace "Ke dai ban san sanda zaki yi hankali ki wa

ye ba, don shashanci da hauka dama tare ku ke kika bar sa a gantale kamar

ɗ

an iska a kofar gida?" Ko kulata Khaleesat bata yi ba ta mike ta dau handbag dinta ta fice daga dakin ta tafi dakin Ummanta. Wajen karfe tara Khaleesat ta dawo daga parlon Babanta,

tun karfe takwas da ya dawo ta je gaishesa sai yanxu ta fito, tana shiga bedroom din Ummanta ta kwanta kan gado tana sauke numfashi a hankali, don duk ta gaji dadewan da tayi zaune parlon Babanta, Umma dai kallonta kawai take don ta gane ba ita kadai bace,

Noor dake dakin ta mike ta nufi Khaleesat ta duka kusa da ita tace "Aunty baki da lafiya ne?" Khaleesat tace "Lafiyata qlau, ina Islam?" Noor tace "Tana can dakin Nenne" Umma dake ta kallon Khaleesat tace "Me za ki ci?" Khaleesat ta juya ta kalleta a han

kali tace "Akwai fruits Umma?" Umma tace "Sai dai a siyo maki, bari in kira almajirina a waya ya zo ya siyo maki...." Mikewa Umma tayi ta dauko wayarta, Islam ce ta shigo dakin da waya a hannunta tana kallon Noor tace "Wannan wayar fa?" Noor ta zaro ido ta

na kallon wayar don second phone din Abdul ne da ya bata tun sanda ta dawo islamiyyah ta sa masa caji, Umma dake kallonta tace "Wayar waye?" Noor tace "Na uncle ne, ya bani in sa masa a caji kuma ni na manta, kilan shi ma ya manta" Umma dai sai kallonta ta

ke haka ma Khaleesat, Noor tace "Gobe idan Ya Haiydar ya shigo sai a basa ya ajiye masa" Islam ta ajiye wayar nan gaban madubin Umma ta fita daga dakin. Washegari da rana Khaleesat na dakin Nenne, Nenne ta cikata da hira, ita dai ba tanka ta take ba don ba

ta son magana, yarinyar Mama Zubaida ce ta shigo dakin tace "Nenne Uncle yana parlor yana gaishe ki wai" Nenne tace "Waye kuma Ankle, ke kuma shaidaniya don kar ki tafi islamiyyah kika fake da ciwo ko" Yarinyar dai ta juya ta fita, Nenne ta kalli Khaleesat

tace "Wai ya zo gaisheni, shi baya gajiya da gaisuwa ne, so da yawa har nan dakin fa suke shigowa da Haiydar su gaisheni" Sallama Abdul yayi a bakin kofar dakin, Nenne ta amsa, Khaleesat ta jawo veil dinta ta yafa, bude kofar dakin yayi ya shiga, inda ya

saba zama a dakin ya zauna ya gaida Nenne, da fara'a Nenne ta amsa tana masa sannu da zuwa ta mike ta bude fridge ta dauko masa ruwa da lemo, Khaleesat sai kallonta take, Abdul ya kalli Khaleesat yace "Ina wuni Hajajju" Khaleesat ta kallesa da sauri don ma

makin Nenne ya sa ta manta bata gaishesa ba tace "Ina yini Ya Abdul" yace "Ya gida?" Tace "Alhamdulillah, ya aiki?" Yace "Alhmdlh" Nenne ta koma ta zauna tace "Ya su maman ka kuwa Awdul, ran nan Haiydar ke ce min yaje gidan ku har ya dubata da jiki, ashe b

ata da lafiya" Abdul ya sauke kansa yace "Eh bata da lafiya" Nenne tace "Ayya, Allah Ubangiji ya bata lafiya" Yace "Ameen" Khaleesat ta kallesa tace "Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen, tana yawan tambayar ki kuwa, ta dade bata da lafiya, not too long ma ta

tambaye ki she said she wants to discuss something with you, and I told her that won't be possible cause you are a married woman" Khaleesat ta sauke idonta tace "Allah sarki, Allah Ubangiji ya bata lafiya" Yace "Ameen" Nenne ta mike ta dauko masa wayarsa

tace "Wannan yarinya kafin ta tafi islamiyyah ta bani in ajiye ko da Haiydar zai shigo in basa, wai jiya an saka maka a caji ka tafi ka mance wayar" Abdul ya amshi wayar ya

ɗ

an yi murmushi bai dai ce komai ba, yarinyar daxu ce ta sake dawowa dakin tace "Ne

nne wai anyi baƙo" Nenne tace "Baƙo kuma? In ji wa?" Yarinyar tace "Yanxu ya shigo parlor" Nenne ta mike ta yafa gyalenta tace "Bari dai in je in gani, gidan nan ai baya rabo da jama'a, duk samarin unguwan nan sukan shigo wani lokacin su gaisheni" Tana fit

a daga dakin, Khaleesat ta kalli Abdul tace "I will speak to my husband, if he permit me sai in je in duba Momy da jiki" Abdul ya gyada kai yace "Alright then" Mikewa yayi yace "Zan koma, a gaida min Umma" Khaleesat tace "Zata ji" Juyawa yayi ya fita daga

dakin, Nenne na ajiye ma Ajay uban ruwan goran da ta kwaso a parlon Malam Ali sai ga Abdul ya fito parlon, ya karasa tsakiyar parlon suka gaisa da Ajay, Nenne na washe baki tace "Kaga ashe Yarima ne ya shigo" Shi dai Ajay kansa na kasa, Nenne tace "To ina

Ahmad fa?" Ajay ya daga kai yace "Sun fita ne da matarsa" Abdul yayi ma Ajay sallama, Nenne tace "Har zaka tafi kenan Awdul" Yace "Eh zan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login