Showing 480001 words to 483000 words out of 641791 words

Chapter 161 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

126

other, komai tare suke yi, they were always clung to each o

ther ko cikin dare ma suna makale da juna suke bacci, ranan da za su bar Zanzibar kuwa tana zaune da sassafe tana kallonsa yana rufe mata box dinta bayan ya gama shirya mata kayanta don suna isa Tanzania za su yi boarding flight zuwa Abuja Nigeria duk a ra

nan, ya mike yana kallonta ganin yanayinta yace "Are you okay?" Ta sauke idonta a hankali tace "I am surly going to miss here" Ya

ɗ

an yi murmushi ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yace "Ana kan processing maki Maldives visa din ki, can za mu je

for our next trip in sha Allah my queen...." Ta

ɗ

an yi murmushi a hankali tace "Da gaske?" Yace "Sure in sha Allah, in few months time" Mikewa yayi ya dagota yace "We have a flight to catch by 9 wife...." Ta dau handbag dinta a sanyaye, a ranta tana ji har

ta fara kewan Zanzibar and the beautiful things it gat, she wish they will be there forever, the peace of mind in Zanzibar was top-notch, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, mood dinta ya canza bayan da ta tuna wannan Emirate din nasu fa za su koma yanx

u, hannunsa ta kamo cikin sanyin murya tace "We still have time Mi Vida, please Ina son in maka wata magana...." Ya kalleta yace "Alright My Lady" Zaunawa yayi kan kujera ta zauna kusa da shi tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta babu ko kiftawa,

jawota yayi jikinsa murya can kasa yace "Maganar me za ki min wife? Kina son wani abu ne?" Ta sauke idonta a hankali tace "Don Allah kar mu koma gidan Sarki wallahi bana son zama gidan, pls we should stay far away from the Emir's palace, do this for me my

prince" Ajay yayi shiru yana kallonta yana jin ina ma hakan zai zama possible don bata kai sa rashin son zaman masarautar nan ba, ta daga idonta jin yayi shiru, ya kamo hannunta calmly yace "Nima bana son zaman gidan Jeeddah but i have no choice because of

my father, Mai martaba bai son mu yi nisa da Emirate din, but idan mun koma yanxu i will try speaking to him ko zan yi convincing dinsa" Ta marairaice masa tace "Plss do...." ya gyada mata kai yace "I will in sha Allah" Bayan sun fita daga Le Mersenne Bea

ch resort Khaleesat ta juya ta kalli resort din for the last time, she will surely miss all their beautiful moment that started here, she will never forget all that happened here, cause it is the best thing that have happened to her so far, har suka isa ai

rport bata sani ba don tayi nisa tunanin da take duk da kanta na kwance ne saman shoulder dinsa suna zaune kamar zata shiga jikinsa a cikin motar, damuwarta yanxu bata san kuma what next za su je Emirate din nan su tarar ba, a haka suka shiga cikin Airport

din yana rike da hannunta. Bayan magrib Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat, basu jima da sauka Kano ba ya karbi mota wajen driver ya kawota gida ta gaisa da su Umma, sosai Khaleesat ta ji dadin kawota gida da yayi don tana son amsan maganin

nan wajen Nenne cause har suka baro Zanzibar bai yi komai da ita ba tunda yaga da gaske bazata iya dauka ba, amma kullum sai ta samar masa nutsuwa ta hanyoyi daban daban, Khaleesat na kallonsa a hankali tace "Minti nawa zan yi a ciki?" Ya

ɗ

an yi murmushi

ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yace "You can spend the night here Milady, gobe da rana sai mu tafi Bauchi, Ko kina son ki kwana biyu a nan kafin mu koma Bauchin?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a, yanda kace haka za ayi" Yace "Alright Milady ki

shiga, bari in je masallaci inyi sallah tunda nayi alwala...." Khaleesat ta gyada masa kai sannan ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidansu, da sallama Khaleesat ta shiga parlonsu, nan ta tarar da su Mama Shatu da Mama Zubaida d

a wata makociyarsu ana kallo a parlon ga yara zazzaune kan carpet, yaran suka mike da gudu suna mata Oyoyo, duk ta rungumesu sannan ta zauna kan kujera ta gaida su Mama Shatu dake ta kallonta da makociyarsu, daga haka ta mike ta karasa dakin Ummanta, tunda

ta shigo Umma da Aunty Farida ke kallonta, tana murmushi ta karasa har inda suke ta zauna kasa ta rufe fuskarta a kafar Umma tace "Ummana" sai kuma ta dago ta kalli Aunty Farida har sannan tana murmushi tace "Aunty" Mamaki yasa Umma sai kallonta take, wai

Khaleesat ce yau ta shigo masu a nutse ba a guje ba, Aunty Farida ita ma mamaki ne ya cikata, Umma tace "Ikon Allah, daga ina haka Khaleesat?" Khaleesat na murmushi tace "Yau muka dawo Umma" Gaishesu tayi, duk suka amsa, Aunty Farida tace "Ke da shi ne?"

Khaleesat ta gyada kai tace "Ya shiga masallaci ne, Umma ina su Islam?" Umma tace "Suna dakin Nenne" Khaleesat ta mike tace "Bari in je in gaisheta" Suka Bi ta da kallo har ta fita daga dakin, Umma ta kalli Aunty Farida tace "Ikon Allah"

HALYSAAH PAGE 16

1...

Khaleesat na shiga dakin Nenne siblings dinta suka taso da gudu suka rungumeta cike da murnan ganinta, Khaleesat ta ja kunnen Islam tana murmushi tace "Shi ne kika ki zuwa Bauchi ko" Dariya Islam tayi tace "Umma ce tace kar in bar ta ita kadai fa" N

enne dake ta kallon Khaleesat tace "A'a karya take, ina ruwan wata Umma da ita tunda ba nono zata bata ba" Khaleesat na murmushi ta karasa kusa da Nenne ta zauna tace "Ina yini Nenne?" Nenne tace "Lafiya qlau Khaleesat, Alhamdulillahi hankali ya samu, har

kun dawo daga tafiyar?" Khaleesat ta wani kalleta tace "To da bani da hankali?" Nenne tace "Atoh, naga a nutse kika shigo ne ai shi yasa, ko da yake tun a Bauchi ina ta mamakin nutsuwarki da muka je lokacin" Khaleesat dai murmushi kawai take, Nenne tace "I

na Yariman?" Khaleesat na wasa da gyalenta tace "Yana masallaci" Nenne tace "Maa sha Allah, wani kasar ku ka je halan? Ko da yake ni da kika yaudara za a tafi Amurka da ni ashe karya kika tsula min, Allah ya so ban gaya ma kowa ba balle aga ban tafi ba ayi

min dariya inji kunya" Dariya Khaleesat tayi tace "To wa yace maki wataran baza aje da ke ba? Kin fiye azarbabi ne" Nenne tace "To Allah ya kawo wannan lokacin dai" Khaleesat tace "Baba na parlonsa ne Nenne?" Nenne tace "A'a sun kai kaya Lakwaja, wani bab

ban mutum ne da ya saba aiki da shi da dadewa ya damka masa kayan ya taimaka ya kai masa Lakwaja don kayan kudi ne ba kadan ba...." Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Amma ni bana son Baba ya ci gaba da wannan sana'ar fa Nenne" Nenne tace "To h

auka ake Khaleesat? Taimako kawai yayi wannan saboda an yarda da shi aka basa kayan ya kai, kuma yana matukar jin kunyan mutumin, bai ma dade da dawowa kasar ba mutumin, da yana nan kilan da ya tsaya ma Ali a sanda aka dauresa, to ko sisi baban naki ma yak

i karba a kyauta zai kai masa kayan, mu kam yanxu ai kuma Alhamdulillahi babu abinda za mu ce ma Allah sai godiya, ba mu rasa komai ba, muna cikin wadata sosai wallahi kamar ba ayi rayuwar talauci ba, Allah yayi ma Ahmad da mijinki albarka don duk su suka

fiddo mu daga kangin talauci, sannan sarki ma ya taba ba Ali miliyan goma ya ja jari, duk fa ba a dade ba Ali ke fada mana, kin san sa da zurfin ciki" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "To Allah ya saka da alkhairi" Nenne tace "Ameen, ke kam kin kaw

o mana arziki gidan nan, Allah ya maki albarka Hauwa, Allah ya baku zaman lafıya da mijinki ya azurta ku da yara masu albarka" Cikin sanyin Khaleesat tace "Ameen" Nenne tace "kinsan an kawo kudin auren er uwarki Lamisa kuwa?" Khaleesat ta bude ido tace "Ha

ba dai?" Nenne tace "Wallahi kuwa in gaya maki, yaron abokin babanku Salihu ne ya fito yana sonta, da naga nutsattse ne kuma ya samu karatu babu laifi nace to a basa kawai, nan da wata shidda biki, sunan yaron Kallamu" Khaleesat tace "Maa sha Allah, Allah

Ubangiji ya kai mu lokacin lafiya" Nenne tace "Ameen, sannan uwar Ahmad ta zo gidan nan yau kwana uku in gaya maki" Khaleesat ta dan yi shiru sai kuma tace "Wani Ahmad kuma?" Nenne tace "Jewe ku ke ce masa ko me, Ahmad dai dan uwan mijin ki, Ahmad dan alba

rka yaron kirki" Khaleesat ta dan bude ido da mamaki tace "Da gaske Nenne?" Nenne ta gyara zama tace "Wallahi in gaya maki, ta zo har nan ta bamu hakuri gwanin ban tausayi har da hawayenta, har sai da ta sa ni kuka nima, gaskiya matar nan mutum ce...." Kha

leesat ta sauke idonta lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, sanda suke Tanzania sau biyu Ajay ya kira Mami kuma duk sai da tace ya bata wayan, Nenne tace "Ta ce tayi da ta sanin abinda ta aikata mana ayi hakuri a yafe mata, da yake kusan magariba aka kawo

ta a katuwar motar har Malam Ali sai da suka gaisa shi ma ta basa hakuri baiwar Allah, ai haka ake son mutum yayi kuskure ya gane kuskurensa ya nemi gafara tun a duniya, lallai ta cika musulmar kwarai, kuma nasan ba komai bane sharrin shaidan ne abinda tay

i da kuma zugan yan masarautar nan, ko matar sarkin nan ma ta isa ta zugeta ta kai ta ta baro" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya, Nenne tace "Ga kuma wani abu da ake ta boye maki, duk da lokacin kin koma Amurka bayan aurenku da Yarima, Awdul dai zuwansa biy

u gidan nan yana gaishe mu in gaya maki, mu dai a tsorace muke Ummanki ce kadai ke basa fuska, ranan farko da ya zo ya ba yan biyu dubu hamsin su raba, zuwansa na karshe ma haka, kudaden na nan mun ajiye babu ruwanmu wallahi, amma kuma sai naga kamar shiri

yar Allah ce fa ta samesa, don ya dawo wani nutsattse wallahi, amma kuma sai naga kamar shiriyar Allah ce fa ta samesa, don ya dawo wani nutsattse wallahi, tausayi ma yake ban" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, bayan few seconds ta mike tace "Ina

zuwa Nenne tace "Ina kuma za ki?" Khaleesat tace "Zan duba ko ya idar ne" Nenne tace "To yi maza ki tafi gaskiya" Nenne ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta rike haba cike da mamaki tace "Ikon Allah, to Allah mun gode maka da ka saita mana er nan ta

yi hankali tasan ciwon kanta" Mikewa Nenne tayi ta fita parlor don ganin su waye a parlor ta korasu tace bako zai shigo, a Parlon ta tarar da Aunty Farida ta kunna turaren wuta ta kunna Ac bata dai ce ma su Mama Zubaida komai ba, don yanxu magana daya biyu

sai su fashe da kuka wai ana masu gori ana hantarar su, Nenne tace "To ke Parida ba sai kice su fita daga parlon ba bako zai shigo a gaisa?" Nenne bata rufe baki ba su Mama Zubaida suka mike duk suka bar parlon, Nenne tace "Don ma dai sanyi ya fara shigow

a banda haka ai da parlon nan ya dume yanxu da warin mata, haka kawai mu ji kunya tunda bakon kunya ne Ita dai Aunty Farida bata tanka Nenne ba ta tafi ta ajiye kaskon turaren wutan can wajen dinning area, Khaleesat na fita gate ta tarar da Ajay tsaye jiki

n mota yana danna wayarsa, ta karasa kusa da shi tace "Yaushe ka fito masallacin?" Yace "Just now" Tace "Ohk na zata ka dade da fitowa Ya girgiza mata kai yace "Not at all" Tace "To ka shigo ku gaisa da yan gidan" A hankali yace "Amma bamu kawo masu komai

ba Jeeddah" Ta dan yi murmushi tace "Mu da muka dawo daga wata kasar Yayi shiru bai ce komai ba, ta dan bi unguwan da kallo ganin babu kowa ta kama hannunsa zuwa cikin gidan, Nenne na zaune parlor tare da Aunty Farida suna jiran shigowar Ajay, ga lemo da r

uwa ta jido masa daga dakinta don har da Fridge gareta a dakin, tun bai karaso ya zauna kasan carpet ba Nenne tayi saurin cewa "Don Allah ka zauna kan kujera kar kace zaka zauna kasa Yarima" Ya dan yi murmushi bai dago kansa ba yana karasawa ciki, Khaleesa

t a dan zaman da tayi da Ajay ta lura yana da kunya a inda ya kamata, kuma tasan bazai zauna kan kujeran ba saboda Nenne, hakan yasa ta dau darduman da Aunty Farida ta ajiye a parlon ta shimfida masa ya zauna a kai sannan ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da f

ara'a tana masa sannu da zuwa, ya maida dubansa kan Aunty Farida suka gaisa ita ma da fara'arta, ba a dau lokaci ba Umma ta fito parlon ita ma suka gaisa da shi ta juya ta koma daki, su Islam da Stepsisters dinta duk suka fito su ma suka gaishesa, su Mama

Zubaida ma duk suka leko a gaisa, Khaleesat dai sai kallonsa take don gaba daya he is uncomfortable, Nenne tace "To ki kai sa parlon Ali a zubo masa abinci" Ajay ya daga kai yace "A'a kaka mun ci abinci, yanxu zan koma gida ne, sai gobe in sha Allah zan zo

" Nenne tace "To ko ruwa baza ka sha ba Yarima" Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Nenne tace "To Allah ya kai mu goben Yarima, Allah ya huce gajiya" Sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Ki dauko jakarki ku tafi ko" Khaleesat ta sauke idonta sai kuma ta mik

e ta tafi dakin Nenne ta dauko handbag dinta, sai da ta fara shiga dakin Ummanta, Umma tace "Za ku tafi Khaleesat?" Khaleesat ta sauke ido tace "Eh sai gobe da safe in sha Allah Umma" Umma tace "To Allah Ubangiji ya kai mu, amma abinci fa? Ko zaki tafi mak

u da shi?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Akwai abinci a can Umma" Umma tace "To Allah ya tashe mu lafiya" Juyawa Khaleesat tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta tarar har Ajay ya fita, tayi ma Nenne da Aunty Farida sallama, Nenne na cewa "Maza ki tafi

kin bar sa a waje" Khaleesat ta leka dakin Mama Shatu ganin bata nan ta fita daga parlon tana daga ma Aunty Farida hannu, Aunty Farida dai ta kasa daina mamakin Khaleesat. Khaleesat na fita kofar gida ta tarar da Ajay cikin mota har ya tada motar, ta bude

front seat ta shiga tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "But nace ai ki kwana fa Jeeddah" Tayi shiru tana kallonsa, ya sauke idonsa yace "It's somehow mu koma tare ai yanxu" Ta jingina da kujeran motar ta tura baki tace "To bayan duk na masu sallama sa

i aga na koma" Murmushi yayi yace "Naga alama dai ke baki jin kunya" A hankali tace "To kunyan me zan ji? Bayan an san mijina zan bi" He couldn't stop smiling yana kallonta yace "To ke idan baza ki ji kunyan ba ni dai zan ji" Ta wani kallesa tace "To ba ka

ce za mu dawo gobe ba?" Yace "In sha Allah" Tace "Idan muka dawo sai in kwana tunda kace za mu yi kwana biyu" Yace "Ohk then Milady" Reverse yayi suka bar unguwan, sannan yace "Kaka tace min Baba ya tafi Lokoja da kaya ko?" Khaleesat ta gyada kai, yayi kas

a da murya yace "Amma da baba ya hakura da driving haka yayi concentrating a business dinsa, ko ya kika ga?" Khaleesat tace "Ba aiki yaje ba, kawai kaya ya kai ma wani mutum da suka saba, amma ai baya driving yanxu, kyauta ma ya kai masa kayan Lokoja" Ajay

ya gyada kai yace "Ohk na gane, but still dai it's best yayi ignoring driving idan ba within Kano ba" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, after almost 10 mins of silence ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Me za ka ci? Nasan ba lallai ka ci abin

ci a can gidan ba shi yasa ban taho da shi ba" Murmushi yayi yace "Ke zan tambaya me zan siya maki for dinner Milady?" Tace "Hotel za mu je?" Yace "A'a, gida za mu je" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Ban fiye zaman hotel a Kano ba since akwai gida a nan

, although wani lokacin ina lodging hotel din, but for now gida za mu je, masu aiki ne kawai a gidan in ba wani occasion ake yi a Kano ba a hankali Khaleesat tace "Ohk...." A wani eatry ya tsaya ya siya mata abinci ya fito, tana ganin leda daya bayan ya sh

igo motar tace "Tare za mu ci ko?" Yace "A'a, ni tea zan sha" Bata kara cewa komai ba, wajen karfe tara da yan mintuna suka iso gidan, gida ne babba with many rooms, Ajay yayi parking a parking space, yana kara amsa gaisuwan Mai gadi da masu share sharen g

idan dake gaishesa a compound, tuni suka sauke boxes din dake booth suka yi cikin gidan da su, Ajay na rike da ledan takeaway din da yayi ma Khaleesat ya nufi entrance din shiga gidan tana biye da shi a baya, ya tura kofar parlon ya shiga Khaleesat na biye

da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login