Showing 117001 words to 120000 words out of 641791 words
zama da juna yan Citadel dina
😍
*
HALYSAAH 37
Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka
ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin
ɗ
a na ku ka yi, wallahi maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan w
ahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na
matsar kwalla da gefen ha
ɓ
ar zaninta tace "Ɗan nan ina hankalina zai kwanta
ɗ
a na na can furson? In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina
jawabi, kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min
ɗ
a na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke? Ko dai kungiyar kare haƙƙin en Adam ne"
Jay ya
ɗ
an yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai
yau kusan sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin
ɗ
a na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu labarin daurin aurenta da annoban nan Awdu
l ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban ta
ɓ
a ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi mag
ana gaban su Mama Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu shigo gobe" Nenne ta daga hannu da
sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min
ɗ
a na, don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa ma
sa albarka cikin rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kal
lo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe" Dakin Umma ta nufa tace "To ke Sa
lame kike ko wa? Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun, kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen siyo kayan abincin nan...." Maman Salam
e ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki, Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin. Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mo
ta yana zaune a kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai yayi murmushi ya fara driving mot
ar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida
ko na 30M zuwa 50M ne a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe, that house isn't heal
thy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan? This is so pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin
nata bayan har yanxu ba mu yi achieving ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most especially t
he compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya far
a ji, ya kai hannu ya rage Ac din motar, shi dai Jay
driving dinsa kawai yake. Washegari da yamma haka nan suka sake komawa gidan bayan Lauyan su yayi requesting su tambayi matan Malam Ali ko da akwai wani written debt forgiveness document kuma original on
e din da kotu ta bashi bayan masu karansa sun janye karar, cause in dai babu takardun to sai dai ayi case din biyan bashin da yake bin Alhaji Musa amma ba dai su yi karan sa ba, Bayan Ajay yayi parking ya juya yana kallon Jay yace "Zan jira ka" Er dariya J
ay yayi yace "Toh ai da baka biyo ni ba kayi zaman ka a gida kawai" Bai jira cewar Ajay ba ya sauka daga cikin motar ya nufi cikin gidan, yau ma dai kamar jiya ba su kadai suka zo unguwan ba don securities da suka biyo su har sun fi na jiya tunda basu san
ko Abdul na da Spy a unguwan ba, infact bazai ma rasa ba, definitely za a basa labarin wasu sun zo gidan su Khaleesat jiya, so they are not loosing guard by any means, and they are never going to let him take them unaware, A takaice Jay ya gaida Kishiyoyin
Umma dake zaune tsakar gidan sun yi rashe rashe da su, yau ko murhu basu kunna ba don dawowar su kenan daga wajen Malamai, tun asuban fari suka bar gida sai yanxu suke dawowa, duk suka bi Jay da kallo, Jay dai yana tafe yana kallon Islam da Noor dake ma U
mma wanke wanke a tsakar gidan don ko ba a gaya masa ba yasan siblings din Khaleesat ne duba da pheomelanin din su, a tare suka gaishesa ya sakar masu murmushi yace "How are you?" Murmushin kawai suka yi basu ce masa komai ba Islam na wanke wanke Noor na m
ata dauraya, Jay ya isa har kofar dakin Umma yayi sallama, Umma da ta gama gyara dakinta kenan ta saka turaren wuta na tsinke ta amsa sallaman sa, a kullum in zaka shigo dakin Umma a haka zaka tarar da shi fes fes, duk da ba komai bane a dakinta don ta siy
ar da komai nata amma kullum a gyara zaka same dakin da turaren tsinke, Jay ya shiga dakin Umma na kallonsa tace "Sannu da zuwa" Tabarma ta dauko ta shimfida masa don bata yi tunanin zai dawo yau kamar yanda yace mata jiya ba, Jay ya zauna yana murmushi ya
gaisheta, Umma ta zauna kan dardumanta ta amsa gaisuwar sa, har a sannan zaka ga damuwar dake tare da ita alamar karfin hali kawai take, sai kuma ta mike tace "Bari in kawo maka ruwa" Ruwa ta debo masa a cup din stainless ta karaso ta ajiye masa a gabansa
sannan ta koma ta zauna, yace "Nagode Umma" Ɗan murmushi kawai tayi, Mama Zubaida da Mama Shatu suka yi tsit a tsakar gida ko wacce ta kasa kunne ko zata ji abinda ake cewa a dakin Umma, Ajay ne ya shigo gidan duk suka zuba masa na mujiya, sau daya ya kal
lesu ya dauke kai ya nufi dakin Umma, yau dai tsakar gidan a bushe yake bai yi gaja gaja da ruwa ba da yake basu yi girkin siyarwa ba, Islam na tsaye bakin kofar dakin Umma bayan ta shiga da kayan wanke wanken da suka yi da twin sis dinta, Ita kuma Noor na
share inda suka yi wanke wanke, Idan Ajay ya kalli Noor sai ya kalli Islam, ya amsa gaisuwar da Noor ke masa tana rike da tsintsiya, yana isa bakin kofar dakin Umma ya ja dogon hancin Islam don ita ce ke mugun kama da Khaleesat har bakinsu iri daya ne, mu
rmushi tayi tana kallonsa yace "How are you?" Ta sauke idonta bata ce komai ba yanda dai Khaleesat ke yi, da sallama ya shiga dakin Umma, Jay ya daga kai yana kallonsu don bai yi tunanin zai shigo ba, Umma ta amsa sallamansa, ya zauna daga gefen Jay sannan
ya gaisheta, Umma ta amsa da murmushin karfin hali tana masa sannu da zuwa, after some seconds Jay ya fara magana a hankali yace "Umma akwai wasu takardu na yarjejeniyar kotu na yafiyan bashin da aka yi ma Mai gidan nan, Allah yasa kun san in da takardun
suke ana bukatarsu ne" Umma tayi shiru, can tace "To, amma wallahi ban sani ba sai dai ko a duba dakinsa ko suna nan" Jay yace "Eh a duba Umma, Allah ya sa a gani" Umma tace "Ameen" Mikewa Umma tayi ta fita daga dakin, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi ta
da kallo har ta shiga dakin Malam Ali, after almost 8 mins sai ga Umma ta fito da wasu takardu wanda bata san ko na menene ba dai zata kai masu su duba ko akwai wanda ake nema a ciki, a haka ta wuce Kishiyoyinta da idanuwansa duk ke kanta, ta koma dakinta
ta mika ma Jay takardun sannan ta koma kan dardumanta ta zauna, Jay ya dinga duba takardun daya bayan daya, yaga har da takardun makarantar Malam Ali, ashe har Degree garesa a Agriculture, kafin nan kuma sai da yayi diploma, yana ta dai duba tulin takardu
n har daga karshe yaga wasu takardun da yake saka rai na yarjejeniyar yafiyar da aka yi ma Malam Ali a kotu na biyan bashin Mahaifin Abdul ne, ya mika ma Ajay shi ma ya amsa yana duba takardun, Jay ya kalli Umma yace "Ina jin wannan ne takardun da muke nem
a" Umma tace "To Alhamdulillah" Jay yace "To za mu koma, duk yanda ake ciki za mu dawo in sha Allah" A hankali Umma tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai akwai wata uwar dakina da bata ji ba bata gani ba yan sanda suka tafi da ita shekaranjiya h
ar yanxu ba a ma san wani caji ofis din aka kai ta ba" Ajay dake kallonta yace "Ko Baabar nan ta Hotoro?" Cike da karfin hali Umma tace "Ita, wallahi bata ji ba bata gani ba aka je aka tafi da ita" Ajay yayi shiru yana kara mamakin stupidity din Abdul, he
don't think that guy is okay in anyway, after some seconds ya kalli Umma a hankali yace "Za mu bincika inda aka kai ta mu yi bailing dinta in sha Allah" Umma ta share hawayen da ya kawo idonta ta kasa cewa komai, Jay yace "Ki kwantar da hankalin ki Umma, i
n sha Allah komai zai wuce da izinin Allah" Cikin rawan murya Umma tace "Allah ya sa" Jay ya kalli Ajay, tsabar tausayin Umma kawai yaga gwara su gaya mata gaskiyar inda Khaleesat take ko zata
ɗ
an samu sukuni a ranta, Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Sa
nnan Umma akwai maganar da zan gaya maki yanxu, amma don Allah kar ki gaya ma kowa har zuwa sanda za mu gama abinda muke" Ajay ya juya ya wani kallesa don har ya gano maganar da Jay zai gaya ma Umma, Umma na share idonta tace "To in sha Allah" a hankali Ja
y yace "Halysaah na Lagos, amma don Allah ba ma son kowa yasan hakan Umma, ko makusantan ki kar ki gaya ma tukun....." Umma da zuciyarta ke bugawa tace "Lagos kuma? Wajen wa a Lagos?" Jay yace "Tana wajen sister din ki ne, amma mun ce mata kar ta nuna maki
tana wajenta har sai sanda komai ya dai daita, shi yasa ma har yanxu bata gaya maki ba" Umma tayi shiru, amma fa ji tayi wani nutsuwa ya zo mata, lkci daya kuma taji hankalinta ya kwanta kamar an yaye mata kashi saba'in na damuwar da take ciki, Umma tace
"In sha Allahu babu wanda zai ji hakan daga gare ni, yanda ku ka tsaya
mana ku ma Allah Ubangiji ya tsaya maku haka, Allah ya saka maku da alkhairi..." Umma ta kasa ci gaba hawaye masu zafi na sauka idonta, A haka Ajay da Jay suka fita daga dakin Umma za s
u koma Office din lauya din su da takardun hoping shi ne kotu zata bukata, yau ma dai Ajay ji yayi kamar zafi zai kashesa a dakin Umma amma haka ya dinga daurewa har suka fita daga dakin sannan ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan da yayi, ya kalli I
slam dake zaune bakin kofar dakin Umma da takardan makaranta a hannunta alamar karatu take, Noor kuma na hura gawayi a can gefe, ya saka hannu a aljihu ya ciro kudaden da bai san ko nawa bane ya mika ma Islam yana kallonta yace "Ku raba ke da er uwarki" Is
lam taki amsan kudin, ya hade rai yace "C'mon collect it" Jay dake kallonta shi ma ya sakar mata murmushi yace "Karba mana cutie" Islam ta kalli Noor amma still taki amsan kudin, Ajay ya zare mata ido yace "Kee, amsa nace" A hankali ta kai hannu ta amshi k
udin, Ajay da Jay suka fita daga compound din, Kishiyoyin Umma suka dinga kallon uban kudin da aka ba Islam kamar idanuwansu za su fito ko kiftawan kirki basa yi, Islam ta tashi ta shiga dakin Umma da kudin a hannunta, Mama Zubaida ta mike ta ma Mama Shatu
alamar su shiga daki, duk suka shiga dakin Mama Shatu sannan suka sake labule, Mama Zubaida ta rike haba tace "Anya kuwa Shatu baza mu san yanda za mu yi Abdul ya samu labarin abinda ke faruwa a gidan nan ba? Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san
inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in fa muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma d
ai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance
mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin
da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan na
wa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu? Ni fa jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a kanta, mu
ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban
sa, nasan Abdul din zai taka ma yan iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida