Showing 309001 words to 312000 words out of 641791 words

Chapter 104 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

248

ba ma ni bana jin akwai er da za ayi ma wannan setin kayan dakin, ko iya su muka kai mata babu me renamu wallahi, akan dai ace mu cakalkala kudi mu siya mata tarkacen banza m

asu arha da baza a ga darajarsu ba, don haka ni dai ga dubu dari biyar ina da shi a ajiye, Parida zata kawo Miliyan daya tace, ita Zahra'u dama babu ita a lissafi in ba dogon hancinta zata kai kasuwa ta siyar ba, don haka nake baka shawara wannan gidan nan

naka na Mariri da nawa ka siyar kawai mu fita kunya, ko miliyan hudu aka samu aka siyar da gidajen kaga ai sai mu fitar da er mu kunyar gidan sarauta Ali, wallahi hankalina a tashe yake ga lokaci da aka sa ba mai tsawo ba, kan kace me zaka ga kamar gobe n

e" Malam Ali dake ta sauraronta ya idar da alwalan da yake sannan yace "Allah ya rufa asiri ya nuna yanda za ayi amma siyar da gida kam bai taso ba Nenne, shikenan fa gare mu...." A fusace Nenne tace "Baza ka raba kanka da kalman nan na shikenan gare ka ba

, shi kuma wannan da muke ciki na gwamnati ne?" Malam Ali dai bai ce mata komai ba, don su ne suke ma gidan nan kallon gidan zamansu amma banda shi, har cikin ransa ya riga ya sa cewar gida ne aka basa ya zauna na

ɗ

an wani lokaci ya tashi, Tsayuwar mota su

ka ji a kusa da gate, Nenne ta kalli gate din, can tace "Kaddai tsinannun iyayen Awdul din ne suka sake biyo ka..." Mikewa tayi ta nufi gate din fuskarta babu rahama, wasu manyan mata ta gani har su hudu cikin shiga ta alfarma, suna kallonta suka ce sannu,

Nenne ta koma gefe tace "Yauwa sannun ku, ko batan hanya ku ka yi ne" Daya daga matan tace "Ba nan ne gidan su Halysaah ba?" Nenne tace "Eh nan ne, Khaleesat ba, Malaman makarantar su ne halan?" Matar tace "To mu dai shiga daga ciki ko?" Nenne ta juya ta

koma ciki da sauri tana cewa "Bisimillan ku, sannun ku da zuwa, ai Khaleesar ma ta

ɗ

an yi tafiya bata nan, amma ku shigo ciki" Suna biye da ita har zuwa parlon gidan, shi dai Malam Ali bai ce masu komai ba kamar yanda babu wanda ya ce masa komai balle su g

aishesa, Nenne na shiga parlor ta kora yaran Mama Shatu dake zaune suna kallo, duk suka fita daga parlon, ko wacce a cikin matan ta samu kujera ta zauna a parlon, Nenne na murmushi tace "Halan kun samu labarin an sa mata rana ne, bari in kira maku uwarta t

ana ciki" Da sauri Nenne ta tafi dakin Umma ta sanar mata Khaleesat tayi baki kamar Malaman makarantar su a Amurka don ko wacce shiga tayi ta alfarma ga gwala-gwalai, a tare Umma da Aunty Farida suka fito parlor, haka kawai Umma taji gabanta ya fadi, ta da

i karaso parlon ta zauna ta gaishesu duk suka amsa, Aunty Farida ma ta gaishesu tana kallonsu, ledan pure wata guda Nenne ta kinkimo ta kawo masu tsakar parlon ta ajiye tana cewa "Wallahi yaran duk sun shanye wanda ke prij me sanyi" Matar dake tanka Nenne

tun daxu tace "Mun san duk baku san mu ba, baku kuma san daga inda muke ba" Nenne ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Ba Malaman makarantar su Khaleesah bane a Amurka?" Matar tace "Ko daya, ni sunana Hajiya Fatima, kuma ni din kanwata ce ga Mai martaba

Sarkin Bauchi..." Ƙabbara Nenne ta saki ta mike tsaye tana tafe hannu tace "Lale lale, lale marhaba, sannun ku da zuwa, ashe manyan baƙi muka yi bamu sani ba, wallahi ba a sanar mana kuna hanya ba" Hajiya Fatima tace "Yana da kyau dai ki fara sauraronmu ki

ji me ke tafe da mu tsohuwa" Nenne ta zauna kan Carpet tana kara masu sannu da zuwa baki har kunne, Hajiya Fatima ta nuna warce ke zaune gefenta tace "Fulani Asiya kenan, matar yayanmu Marigayi sarki Ahmadu Yusuf, mahaifiya ga Ahmad Jawwad...." Nenne tayi

shiru tana kallon Mami da idanuwanta kamar za su fito, haka ma Umma da Aunty Farida da duk jikinsu yayi sanyi tun Hajiya Fatima bata fara introduction ba, suna ganinsu sun san babu alkhairi a tattare da zuwan su dama, Hajiya Fatima ta ci gaba da magana ci

ke da isa da gadara tana nuna warce ke zaune 2 seater tace "Wancan Hajiya A'isha kenan kanwar Fulani Asiya, ta kusa da ita kuma Hajiya Nafisah kanwar matan Mai martaba Sarkin yanxu...." Nenne tayi karfin halin cewa "To Allah Ubangiji dai yasa lafiya, don n

i ban gane kan wannan zuwan naku ba kuma" Hajiya Fatima tace "Gaskiya ba lafiya ya kawo mu ba tsohuwa, duk da zuwa muka yi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba" Nenne ta

ɗ

aga kai ta kalleta baki bude, cikin nutsuwa Mami ta fara magana tace "Ni ce

Mahaifiyar Jawwad, kuma Jawwad shi kadai Allah ya bani a duniya, a burikan da nake da shi kan Jawwad a duniya babu auren bazawara ciki, ko kuma auren wata kabila can baya ga cikakkiyar Hausa Fulani, tun daga neman auren da aka zo aka yi na

ɗ

a na har saka

rana bani da masaniya akan ko daya, sannan duk wani bautatawa da kashe uban dukiya da Jawwad ya dinga yi akan er ku da ma ku kanku babu wanda ban sani ba, amma duk ba wannan ne damuwata ba, kuma bazan ce zan amshi duk wani abu na alkhairi da yayi maku ba,

kamar yanda nace maku mun zo cikin aminci ne babu tashin tashina, don haka tun da girma da arziki ku cire ran auren er ku da

ɗ

a na Jawwad idan ba haka ba wallahi duk wani mummunan matakin da na dauka a kanku ku kuka siya, er ku ba sa'ar auren Jawwad bace d

on shi din

ɗ

an gidan sarauta ne,

ɗ

an sarki jikan sarki babu abinda zai yi da er ku bazawara, kai ko da ba bazawara bace wallahi babu abinda zai yi da wata kabila warce ba ma na kasar nan ba, ina sake jaddada maku tun da girma da arziki ku janye batun auren

er ku da

ɗ

a na...." Cousin sister din Aunty me suna Aunty Nafisa tace "Iya tatsarsa da ku ka dinga yi ma ya isa haka, don hidimar da yayi maku in muka ce yafi na miliyan dari biyu tsaf bamu yi karya ba, da ace tsiya ya kawo mu hatta gidan nan wallahi sai

mun kwace amma mun zo maku cikin lumana don mu din ba kananun mutane bane kuma mun fi karfin dukiyar da Jawwad ya kashe maku, kawai abinda za ku yi a zauna lafiya shi ne ku janye batun auren nan cikin ruwan sanyi tun kan tijara ya biyo baya" Har sannan Nen

ne ta kasa rufe bakin da ta hangame zaune kan Carpet with shock, Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallonsu daya bayan daya tace "Mu janye batun aure sai kace mu muka je neman auren Jawwad din? Ina ce wa enda suka zo neman aure su za su dawo su janye sa

nnan su amshi kudin da suka kawo, kuma ni a iya sanina ba mata bane suka zo neman auren Khaleesat, mazan nan dai da suka zo neman auren su nake tunanin za su sake dawowa su ce sun janye a maido masu da kudin

ɗ

an su, ko kuma mafi sauki in kin isa da

ɗ

an ki

ai tun daga gida zaki masa umarnin ya janye ba sai kin zo mana nan ba, a yanxu mu dai bamu da sauran magana da ku sai dai iyayenmu maza su saurari wakilan Mai martaba, duk da dai ban san ko gidan sarautar taku har dankwali da dankwali na zama batun neman a

ure ba" A tare Hajiya Fatima da Hajiya Nafisah suka mike suka daka mata wani tsawa suna nunata da

ɗ

an yatsa, Hajiya Nafisah tace "Ke karamar er iska mu kike gaya ma magana? Kin san su waye mu? Who the hell do u think you are?" Aunty Farida ta ja wani dogon

tsaki ta juya ta bar parlon alamar bata da lokacin ci gaba da basu amsa, Cikin azama Aunty Nafisa ta bi ta a fusace, Mami tayi saurin dakatar da ita tace "Dawo Nafisah, dawo, kyaleta kawai" Umma dake hawaye ta dinga basu hakuri a rikice tana cewa "In sha

Allahu duk bazai kai ga haka ba, in dai ta bangaren mu ne babu batun wannan auren da izinin Allah, mu mun janye ba wannan batun in sha Allah, don Allah ku yi hakuri" Mikewa Mami tayi tana kallon Umma cikin nutsuwa tace "Da ya fi maku, don in baku janye ci

kin lumana ba za ku janye saboda tashin hankali, bana hada

ɗ

a na da kowa, kuma ba don ko wace irin mace na haifo ma

ɗ

a na a duniya ba, in ma wani abu ku ka yi ma Jawwad irin naku na yan kabilar ku to tun wuri ku warwaresa tunda kun tatsi arziki son ranku d

aga jikinsa har da siya maku gida, to duk nafi karfin abinda yayi maku bazan kuma ce zan amshe ba, kawai dai ina me maku gargadi da babban murya ku raba kanku da

ɗ

a na, ku nisanta er ku daga

ɗ

a na" Mami na kai wa nan ta nufi kofa, sauran matan suka bi baya

nta suna yatsine yatsine, rabon Nenne da shiga irin wannan shock din tun da Motar yan sanda suka zo tafiya da Malam Ali farkon case dinsa da Baban Abdul, Umma ta zauna kan kujera ta dafe kanta ta dinga kuka, Mama Shatu dake makale bakin kofar dakinta sai z

azzare ido take taki karasowa cikin parlon, Sai a sannan Nenne ta samu bakin sakin salati ta rushe da matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma da mutuwa, Duk wannan abun da aka yi Malam Ali dake zaune Balcony yana ji, har su Mami suka fito basu ce masa kom

ai ba suka nufi gate. Sai bayan Magrib Aunty Farida ta samu Ajay a waya, he was shock an speechless bayan ta sanar masa abinda ya faru don sai da ya mike tsaye daga zaunen da yake, gaba daya ya ma rasa me zai ce, after some seconds ya dake yace "Zan kira k

i Aunty" Yana katse wayar ya fita zuwa bangaren Mai martaba, Sarki ya fi minti biyar bai ce komai ba bayan Ajay ya sanar masa abinda Aunty Farida ta gaya masa, kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai, after another 2 minutes ya numfasa cikin nutsuwa yace "D

au waya ka saka min Number Mahaifin yarinyar" A hankali Ajay yace "Bani da numbersa ranka shi dade" Mai martaba yace "Sa min Number Faridan" Mikewa Ajay yayi ya dau wayar Mai martaba ya saka masa number Aunty Farida sannan ya mika masa, Mai martaba ya amsh

i wayar yace "Wannan karan zan yi maganin Aseeyah, i have tolerated her for so long for the sake of my late brother, amma zan nuna mata na fi ta iko da Ahmad, kuma juma'an nan mai zuwa in sha Allahu za a daura auren nan" Murya can kasa Ajay ya fara basa ha

kuri don har ya mance rabon yaga bacin ran Abbansa haka, Mai martaba ya mike yana rike da wayarsa ya shiga dakinsa, ashe duk wannan abun Aunty na tsaye bakin kofa tun da taga Ajay ya taho parlon Abban nasa ta biyosa ta tsaya bakin kofar duk tana sauraron s

u, mikewa Ajay yayi zai fita yaga Aunty tsaye bakin kofar tana masa wani matsiyacin kallo, sauke idonsa yayi ya canza wata hanyar don kofa biyu ne a parlon.

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788

HALYSAAH 9

6

Aunty fari

na na zaune tsakar gida da umma da malam Ali,umma dai tayi tagumi ko bakin magana bata dashi idanuwanta duk sun kumbura saboda kuka,Aunty farida sai jira take malam Ali yace masu ga yanda sukayi da maimartaba a waya amma yaki cewa komi,Nenne ta fito daga

cikin gida tana rike da wayar aunty farida Don har ita sai da maimartaba yayi magana da ita,Nenne tace," inba adalin sarki ba waye zaiyi haka sai kunga yanda ya ajiye izza da girman kai irin ta sarakuna yana ban hakuri,har saida kunya ta kamani wallahi,ya

na bani hakuri ina basa hakuri,to ni ai inba shegiya bace ai dole In hakura,Amma zance na gaskiya na tsorata da lamarin uwar Ahamad,taban tsoro sosai banga alamar akwai abun arziki a tattare da itaba,naji kuma ina tsoron auren nan,ace khaleesat tayi auren

farko bataji dadi ba nabiyu ma yazo mata a haka? Kunga ai bazamu bari ayi na biyu ba yarinya da karancin shekarunta tayi ta walagigi gidan aure har sai wani cutar yaje ya sameta,gaskiya nidai nasha jinin jikina gaskiya da auren nan gara kawai duk a haku

ra dan babu alamar alkhairi a cikinsa,tunda har uwar sa ta nuna bata sonta bazata taba sontaba har abada kuwa, sannan fa duk a yau mukejin ashe ba ita daya ma ashe zai aura ba,harda yar uwarsa budurwa itama jinin sarauta kuma duk a rana daya za a daur

a auren,Ina khaleesah ina kishi da jinin sarauta inba dai hallaka akeson jefa yarinyar ba ga uwar miji tun baayi auren ba ta nuna bata sonta gaskiya jikina ya mutu,akan abun duniya bazamu sake salwantar da rayuwar er mu ba" Cikin sanyin murya umma tace" D

amani auren ya fice man arai gaba daya Nenne,Hakura zatayi Allah ya fiddo mata da wani mijin kawai Don babu Alkhairi a wannan auren dama aikowa tayi akazo da sauki akan ta tako da kanta tazo gidannan tayi abinda tayi gwara a hakura kawai.....Nenne ta kats

eta da sauri tace"Ai bazamu bari wannan ya fito daga bangaren mu ba Zahara'u duba da yanda sarki duk yabimu yayi mana magana ta waya, in bama shi dinba wane sarkin ne zaiyi haka? Ai iyaka saidai yasa na kusa dashi su kiramu su bamu hakuri a gantale Amma

badai yayi waya damu muji muryarsa ba,Ki duba lokacin daya dauka yana waya da farida,Sannan yayi waya da malam Ali ma,nima kuma yayi magana dani duk yana kokarin sanyaya mana zuciya akan tijarar da er iskar mata tazo har gida ta mana,kinga ko Don wannan

bazamu yarda ace daga wujen mu mukace mun fasa bada yarinya ba,nasan kuma wannan matar er bariki ba hakura zatayi ba gwara ace ita ta ruguza zancen Auren da kanta da dai ace mu muka ruguza,Sam Ahamad baiyi dacen uwa ba gashi yaro mai hankali da nutsuwa ga

kirki amma uwa er duniya,mu bazamuce komai ba Albarkacin mai martaba saidai in su suka ce sun janye batun auren shikenan yazo ma kowa gidan sauki ,Aunty farida ta sauke ajiyar zuciya tace"hakane Nenne" Nenne tace Atoh,kai meye shawararka malam Ali?Ana mag

ana sai kayi shiru kamar wani bare a cikin mu,sai a sannan malam Ali ya daka kai a karo na farko yace" Shawara ta shine zuwa gobe ko jibi mu tattara mu koma mariri tunda har an kusan gama gyaran da akeyi gidana baaba,idan mun koma to koma me zai biyo ba

ya me sauki ne..... A mugun fusace Nenne tace "Toka tattara ka koma mana Ali wani ya rike ka ne? Mudai muna nan babu inda zamuje tunda bamu bude baki mun roki yaron nan ya siya mana gida ba,kuma takardun gida na hannun mu balle ace zaa kwace gidan,ko kum

a mu siyar da gidan mu tashi mu koma wani wajen mu siya ba shikenan ba,Amma wallahi babu shegen daya isa ya rabamu da gidannan,ko shi Ahamad din bazai fara tunkarar mu da zancen gida ba tunda saboda Allah yayi kuma jinin marigayi sarki Ahmadu na yawo a ji

kinsa,mahaifinsa kuwa kowa ya shaida mutumin arziki ne "Nenne na kaiwa nan ta Mike rai bace tana kallon Aunty farida tace" Taso mu shiga ciki muyi shawara parida " Ali da matarsa in kace zaka zauna cikinsu kayi maganar Arziki ranka ne kawai zai baci a banz

a,ban taba ganin sumbudaddu matsorata irin su ba "washegari har gida maimartaba ya tura akaje ba malam Ali hakuri akan abinda mami taje tayi,Shidai malam Ali Allah ya sani he is not longer comfortable with his daughter getting married to the royal family,

Sam hankalinsa bai kwanta da auren ba amma nauyin me martaba yasa ya kasa nuna hakan,gashi wanda sukazo basa hakurin sunce ranar jumaar nan zaa daura auren,shi kansa me martaba ya sanar masa da hakan a maganar da sukayi jiya,gaba daya ya rasa ta inda zai

bullo ma lamarin gashi yasan nenne bazata taba tsayawa ta fahimcesa ba balle suyi abinda ya kamata dan ceto rayuwar Khaleesat,baya fatan abinda ya samu ersa a baya ya sake samun ta yanzu,bayan wakilan me martaba sun bar gidan wajen karfe takwas da rabi n

a dare ya dau wayarsa ya zauna tsakar gida yayi dialing number khaleesat,yana fara ringing khaleesat dake shafe shafe bayan tayi wanka ta daga Kiran,bayan ta gaishesa ya amsa yace "yaushe zaki dawo jiddah"?a hankali khaleesat tace Nenne tace kada su bari i

n dawo yanxu amma ni ina son ranar Friday indawo ,malam Ali ya danyi shiru sai kuma yace"kina jina jiddah?tace inaji baba,yace farida sun fada maki abinda ke faruwa kuwa?Sosai khaleesat taji gabanta ya fadi ,ta ajiye kwalbar turaren hannunta tayi shiru ta

kasa cewa komai,Har saida babanta yace "hello ta kifta ido cike da karfin hali tace "inaji baba,baa gaya min komi ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login