Showing 303001 words to 306000 words out of 641791 words

Chapter 102 - HALYSAAH COMPLETE

03 Sep 2026

236

har ma tace tana son a kawota ta gaishe ka" Mai martaba ya

ɗ

an yi murmushi yace "A nan garin kakarta take kenan?" Jay yace "A'a zuwa tayi, dama kuma tana zuwa" Mai martaba ya

ce "Shikenan, babu matsala sai ka kawo ta din, zaka iya tafiya..." Jay yayi masa sallama ba tare da ya yarda sun hada ido ba ya mike ya bar parlon, bangaren Ajay ya nufa, ya samesa zaune parlor yana dube dube a laptop, Bayan ya zauna Ajay ya kallesa, Jay y

a jinginar da kansa jikin kujera a hankali yace "Kasan Mai martaba ya sa anyi bincike a Kano? And he found out everything, when I say everything I mean Everything Ajay" Ajay ya

ɗ

an bude ido ya ajiye laptop dinsa yace "Really?" Jay ya sauke ajiyar zuciya ya

ce "Dama ai zancen duniya baya buya, but banyi expecting za a gano komai easily haka ba, yau na kara jin tsoron mutum, mutum abun tsoro ne Ajay, nasan har gidan da na siya Abba ya sani yanxu, he was angry but calm at the same time, I wish I told him all th

is before he find out himself..." Ajay was quiet for some time don shi ma ya girgiza, can yace "To yanxu me yace maka at the end?" A hankali Jay yace "He said it's fine, I told him about her Grandma da tace zata zo, gobe kenan...." Ajay yace "Ba nace ka ky

ale wannan tsohuwar ba, sai ta zo ta karasa fada masa abinda ba a fada ba a Kanon hankalin ka zai kwanta, she talks too much shi yasa nace kayi ignoring kawota da tace kayi gidan nan, but you still went ahead and told Abba" Jay ya sauke wani ajiyar zuciyan

yace "Bazata yi abinda kake tunani ba, i will bring her tomorrow in sha Allah, don Abba na contemplating asalin Baban Halysaah, an ce masa Kano aka dawo kuma aka ce Bauchi" Sosai Nenne ta nutsu tayi zaman ladabi da biyayya tun da aka shigo da ita babban p

arlon Mai martaba, don a iya saninta ba kowa ne ke da access din parlon sarki ba, ita a ganinta ba karamin karramata da mutunta ta aka yi ba haka, dama ta baza tsadadden turaren Khaleesat da suka barota a gida, sai zuba uban kamshi take abun ta ga sabon gy

ale da atamfa a jikinta kai baza ka bata shekarunta ba, zuwa sannan sun kusa minti goma kenan a parlon a zaune, Ajay ne yayi leading dinsu zuwa parlon sannan ya fita, Nenne ta saci kallon Aunty Farida da tayi picking call din da ya shigo wayarta ta hade ra

i tace "Ke Parida ba nace ki ajiye wayar nan ba, ba fa parlon gidanmu bane nan, ba fa kowa ake ma iso zuwa wannan parlon ba sai wanda ya isa, wannan wani irin kunyata ni kike son yi bayan na yarda dake na jajibo ki, Haba parida..." Ko rufe baki Nenne bata

yi ba sai ga Mai martaba ya shigo parlon walking like the king he is, Nenne ta sinne kai irin babban mutum ya shigo, Sau daya Aunty Farida ta daga kai bayan ta gansa ta ajiye wayar hannunta, ya karaso har cikin parlon ya zauna a spot din da ya saba zama ya

na kallonsu, tuni dama Nenne ta fara jero masa gaisuwa tun bai kai ga zama ba, shi ma ya gaisheta cikin girmamawa, Aunty Farida ma ta

ɗ

aga karamin Nikab din da ta dora kan Abayan jikinta ta gaishesa kanta a kasa, ya kalleta ya amsa sannan ya kalli Nenne ya

ce "Kun zo lafiya Baaba" Nenne tace "Wallahi lafiya lau ranka shi dade, na ce ni dai yau a kawo ni in gaishe ka in sa maka albarka don kai din mutumin kirki ne kowa ya shaida, Allah Ubangiji yayi maka albarka ya kare gaban ka da bayan ka, ya rufa maka asir

i duniya da lahira, Allah ya albarkaci zuri'ar ka, ya ja da ranka, ya kara maka lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya taya ka riko..." Ya gyada kai with calmness yace "Ameen Baaba, Ameen, dama albarkan irin ku abun so ne gare mu, muna godiya kwarai, Allah

ya kara girma, madallah" Nenne tace "Ni dai nayi farin ciki da ganin ka, nace duk yanda za ayi yau dai a kawo ni wajen sarki mu gaisa, shi ne na saka Parida kanwar surkata ta rakoni muka taho tare" Mai martaba yace "Madallah, ai ba a jima ba aka kirani ake

sanar min wakilan da na tura sun isa can gidan Alhaji Aliyu, kuma anyi komai lafiya har an tsaida lokaci ban san ko sun sanar maki daga Kanon ba" Nenne da ta bude ido sosai tana sauraron abinda Sarki ke cewa tayi kasa da murya tace "Wallahi ba a sanar min

ba, kilan Aliyun zai ce a jira in dawo kafin a sanar min, amma nayi farin ciki da wannan abun arziki haka, ai hada zuri'a da kai Mai martaba abun alfahari ne abun farin ciki ne, nayi murna sosai, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi..." Maganar da Umma ta kir

a Aunty Farida zata yi mata kenan kafin shigowar Mai martaba da Nenne ke tayi mata bala'i, Aunty Farida ta dade bata ji farin ciki irin na wannan lokaci ba, she is finding it hard to believe it, yanxu har an aika neman auren Khaleesah kenan amma ko da wasa

daga Jay har Ajay babu wanda yace masu komai all this while, kuma kullum sai sun je can gidan Aunty Murja, Nenne ta nuna masa Aunty Farida tace "Kanwar uwar yarinyar kenan uwar su daya uban su daya, ita kanta bata sani ba banda yanxu da muke ji tare..." S

arki ya jinjina kai yana kallon Aunty Farida yace "To Madallah, ke ya sunan ki..." Nenne ta gyara zama tace "Parida, sunanta Parida Isuhu, tun tana er shekara goma Aliyu ya daukota daga gaban iyayenta a Nijar ya kawota gaban yayarta wato uwar wannan jikar

tawa da aka je neman aurenta yau, to Ali ne yayi mata auren fari aka zo zaman babu dadi kuma gashi abokinsa ne mutumin saboda ya yarda da shi ya basa ita ga manema kaca kaca ya hanasu, to daga karshe dai da kansa ya amso mata takardarta ya raba auren ganin

tana cutuwa gashi ita ba me baki bane sai dai kuka, to tun sannan har yau tana gaban Ali, duk wanda ya zo neman aurenta sai taki basa hadin kai yau shekara bakwai kenan, duk bayan wasu shekaru za su shirya su je gaida iyayensu ita da yayarta a Nijar, iyay

en nasu buzaye ne mutanen kirki wallahi, aure me hada mutanen arziki ga shi ya hada zumunci tsakanin Nijar da Najeriya" Mai martaba yace "Wannan gaskiya ne Baaba" Nenne tace "To tun da har mun samu ganin ka har mun gaisa, to ina ga mu za mu zo mu koma Rank

a shi dade kar mu shiga lokacin ka" Mai martaba yace "A'a, ku bari a karasa da ku bangaren fulani ku samu ku ci wani abun kafin ku tafi Baaba, bazai yiwu ku tafi baku sha ko ruwa ba a masarautar nan..." Nenne zata yi declining offer din nasa sai ga kanwar

Aunty ta shigo parlon da sallama tana rike da bowl din fresh fruits, tare da Auntyn suke amma ita tana can baya tana tafe tana waya don wani lkcn in har Aunty zata kawo ma Mai martaba abun ci ko sha kanwarta ke rike mata har zuwa parlonsa in ta ajiye sai t

a fita, Sarki na kallon Zuwaira yace "Ki shiga da baƙin nan cikin gida Zuwaira, ayi masu duk abinda ya kamata" Zuwaira ta kalli Nenne sai kuma ta kalli Aunty Farida dake kallon direction daban hakan yasa bata ga fuskarta da kyau ba kawai dai tasan fara ce

kamar za a latsa ta jini ya fito, kallon Mai martaba tayi da ladabi tace "To ranka shi dade" Ta kalli Nenne ta gaisheta a takaice sannan tace "Mu je" Nenne ta mike bayan ta amsa gaisuwanta, Aunty Farida ta sauke Nikab dinta sannan ta tashi ita ma, hada ido

suka yi da Mai martaba, tayi masa sallama ta bi bayan Nenne dake biye da Zuwaira, sun fita daga parlon kenan sai ga Aunty cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai tana taƙu dai dai, daga sama har kasa take kallon Nenne da Aunty Farida dake sanye da Nika

b, Aunty ta kalli Zuwaira tana yatsine fuska tace "Su waye wannan kuma Zuwaira?" Zuwaira ta ta

ɓ

e baki tace "Oho, Mai martaba ne yace in shiga da su cikin gida, a parlonsa na same su" Nenne ta kwantar da murya tace "Ina wuni Pulani, baƙi ne daga Gombe...."

Ko amsa gaisuwan Nenne Aunty bata yi ba ta shiga parlon Mai martaba, Zuwaira tana kallonsu a walakance tace "Mu je don Allah ina da abinda zan yi ni kam...." Bata jira cewarsu ba ta ci gaba da tafiyarta, Nenne ta kalli Aunty Farida, sai da taga Zuwaira tay

i nisa sannan tayi kasa da murya tace "Parida kira mana Ahamad kice mun gana da Sarki ya fito ya maida mu gida" Ko Nenne bata ce haka ba dama Aunty Farida bata yi niyyar bin Zuwaira ba, haka nan suka canza hanyar da zai sada su da Compound Aunty Farida na

kokarin kiran Ajay ta wayarta... Aunty na shiga parlon Mai martaba tana kallonsa tace "Ranka shi dade, wasu baƙi ne wannan aka kawo su har cikin parlon ka? Kuma ni ban ta

ɓ

a ganinsu ba alamar babu abinda aka hada da su, ita dayar Nikab ma ta saka balle in g

a fuskarta, su waye ne su da za su shigo har wannan parlon bayan ga can inda ake sauke baƙi?" Calmly Mai martaba yace "Ina ce kin gaisa da su ai?" Aunty ta

ɗ

an hade rai tace "Eh, wai daga Gombe suke in ji tsohuwar" Mai martaba yace "To haka ne" Mikewa yayi

yace "An sanar min ina da baƙi a fada yanxu, zan je in same su Fulani"

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788

Bear with me pls, I am not well

H

ALYSAAH 94

Calmly Ajay ke driving bayan sun baro masarautar, yana ta sauraro

n Nenne da tun fitowar su take fadin irin kirkin Mai martaba tana sa masa albarka, shi dai ba abinda yace don kawai gani yake ba a tare su da kyau ba, yasan dai Abbansa zai sake masu kamar yanda ya saba yi ma kowa amma mutanen cikin masarautar will never d

o so, ita dai Aunty Farida hankalinta na kan wayarta, Sai duk yaji bai ji dadi ba don ya fahimci ko ruwa basu sha ba balle har a basu wani abinci, ko da gangan Aunty zata iya hanasu barin ace ta samu labarin shi ya kawo su gidan, Nenne tace "Toh wai Ina Ah

amad din, ko a masarautar ma fa bamu gansa ba" Sai a sannan Ajay yace "Ya je ajiye Baabarsa unguwa" Nenne tace "Allah sarki, iya sarki kawai mu ka samu muka gaisa da, kai ma kaga ko Baabar ka bamu gani ba" Ya

ɗ

an yi shiru, sai kuma yace "Ni Mahaifiyata ta

rasu" Nenne tace "Allahu Akbar, Allah sarki, Allah ya ji ƙan ta, ya gafarta mata, to ko dai kishiyar baabar taka muka gani za mu fito parlon Mai martaba, wata tana nan ita ba fara ba, sannan tana

ɗ

an da narkeken jiki ba can can ba, tana da matsakaicin tsay

i" Ajay yace "Eh..." Nenne tace "Amma dai bata da kirki kwata kwata, saura kadan ta walakanta mu in gaya maka" Ajay ya kalli Nenne ta madubi yace "Ta maku magana ne?" Nenne tace "Ina fa, ina gaisheta ko amsawa bata yi ba ta sha gwala-gwalai, ni na zata ma

uwarka ce shi yasa na ja bakina nayi shiru ban gaya maka ba" Ajay yayi shiru, kuma bai yi mamaki ba kwata kwata, after a while yace "Ku yi hakuri, yawanci bata son baƙi dama" Nenne tace "To er sarkin wani gari ce take wannan uban girman kan haka da rashin

son talakawa?" Ajay ya

ɗ

an yi murmushi bai dai ce komai ba, sun yi tafiyar kusan minti talatin kiran Mai martaba ya shigo wayarsa, dagawa yayi ya kai kunne tare da sallama, after some seconds yace "Eh muna hanya ne yanxu zan maida su, na zata kun yi sallam

a ranka shi dade...." After few more seconds ya ajiye wayar ya kalli Nenne yace "Dama baku yi sallama da Sarki ba?" Nenne tace "Cewa yayi a shiga damu a bamu abun sha, da naga ba arziki yasa muka ki bin yarinyar tana nan wata kiti

ɓ

ir kiti

ɓ

ir da ita, dama P

arida da nasani ba zuwa zata yi ba don bata son rainin wayo" Ajay yace "Ohk, yanxu yake gaya min ai baku yi sallama ba" Nenne tace "Tun da mun gansa ai an wuce wajen kawai, wataran za a sake haduwa in sha Allah" Suna kusa gidan Aunty Murja after 40 Mins ri

de Ajay ya ajiye wayarsa da yake driving yana dannawa, bayan sun shigo unguwan ya kalli Aunty Farida yace "Mai martaba ya bada sako a baku, na tura a account din Jiddah" Aunty Farida ta

ɗ

an yi shiru, sai kuma tace "To mun gode Allah ya saka da alkhairi" Ne

nne tace "Wallahi mu ba don ya bamu komai muka je gaishesa ba, banda shi din babba ne ai da nace kawai a maida masa, amma dai babu laifi, don Allah kayi masa godiya in ka koma gida tunda bamu da wata hanyar yi masa godiya" Ajay yace "In sha Allah" Suna sha

n kwanan gidansu Aunty Murja, Nenne ta fara hango Khaleesat karkashin bishiyar mangwaro dake gaba da gidan Aunty Murja da dogon sanda a hannunta ita da yaran gidansu Aunty Murja tana tsalle tana plucking Mangwaro, tsohon zanin Aunty Murja ta daura sai er k

aramar Hijab da slippers a kafarta, Nenne taji kunya ya lullubeta ta rike ha

ɓ

a tace "Kwance fa muka baro ta sheme sheme daxu ba lafiya, yanxu meye wannan take yi cikin 'ya yan cikinta fisabilillahi?" Khaleesat bata hangosu da wuri ba don da suna shan kwana

taga motar zata gudu ta shige gida tun basu karaso ba, sai kawai yara taji suna Nenne Oyoyo bayan sun ga motar, ta juya suka hada ido da Ajay dake kallonta a gaban motar, sai yanxu ya kara tabbatar da ashe yarinya ce er karama sae rashin kunya idan ta sam

u waje, Tuni Nenne ta sauka daga motar tana kara yi ma Ajay godiya, Khaleesat ta bi bayan Nenne da sauri zata shige cikin gida, Nenne ta hade rai tace "Baki da kai ne, baza ki je ki gaishesa ba tunda kin riga kin kunyata mu, meye hadin ki da bishiyar mangw

aro kamar mayya, yanxu da tare muke da Ahamad din shi ma haka zae ganki kamar almajira" Khaleesat ta wani turo baki tace "To haka zan je, ai ba sai na gaishesa ba" Nenne tace "Ina ruwan sa dake idan kin je a hakan? Wannan ai ba sa'an yin ki bane, kina gani

n mutum kamili ga nutsuwa wanda magana ma sai ya ga dama, ai ke Ahamad din shi ne dai dai ke shi zai dau ko wani kalar shirmenki da wauta tunda shi faram faram yake, yanxu banda shirme godai godai dake ki shige cikin yara kina tsalle zaki tsinko Mangwaro d

a kodadden zanin Murja" Khaleesat tace "Wallahi bazan je ba, ai ba wajena ya zo ba" Nenne tace "Ni zaki kunyata? Mutumi ya gan ki kice baza kije ki gaishesa ba dubi yanda yayi ta sintirin zuwa unguwan nan da Ahamad suna zuwa duba ki, sannan ya zo yau ya da

uke mu ya kai mu har gaban ubansa yau, ni dai ki rufan asiri ki je ki gaishesa, ai babu dadi haka Khaleesah, dama bai ganki bane wannan daban" Khaleesat ta kalli Aunty Farida dake tsaye jikin motar suna magana da Ajay, can ta fara tafiya zuwa wajen, tana i

sowa Aunty Farida ta wani kalleta sai kuma tayi ma Ajay sallama ta bi bayan Nenne zuwa cikin gida, Khaleesat ta jingina jikin motar tana kallon wani direction daban, dama tun shekaranjiya take jin haushinsa baya ce mata ya jiki duk ciwon da take ta yi, sai

dai kawai ya zo yayi ta kallonta, tada motarsa yayi ita dai bata matsa jiki ba kuma bata kallesa ba, taji yace "Baza ki bar nan ba??" Sai a sannan ta juya ta kallesa, yana kallonta da kyau yace "In kika samu waje ba karamar kazama bace ke, i am telling yo

u this for free...." Ita kanta bata san me yasa ta fara dariya ba kamar warce ake yi ma cakulkuli, reverse ya fara yi ta zaro ido ta koma baya tana kallonsa tace "Buge ni kake son yi?" ko kallonta bai yi ba a haka ya juya ya bar unguwan, kallon kanta tayi

daga sama har kasa, sai kuma ta ta

ɓ

e baki tayi wucewarta cikin gida yara na biye da ita da Mango din da suka tsinko... Da daddare Ajay na zaune parlon Abbansa yana saurarensa kansa a kasa, Mai martaba yace "To amma ku menene dalilin ku na boye min gaskiyar

lamarin gaba daya? Ko kai ka basa shawaran kar ya gaya min gaskiya? Sannan duk saboda yana son ya aureta ne duk yayi mata wannan hidima?" Ajay yayi kasa da murya yace "Ko daya Abba, need din fadin gaskiyar ne bai yi arising ba sai yanxu ranka shi dade, ta

imako kuma kai muka yi kwaikwayo don da haka muka san ka, nasan Jawwad duk abinda yayi mata ba yayi mata bane saboda yana sonta da aure at first, he did all what he did for

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login