Showing 612001 words to 615000 words out of 641791 words
kasan a can yake aiki, hutu ya zo, to shi ne Allah ya hadasa da Awdul, ai ko
dai tasu ta zo daya, yanda baya son hayaniya yana nan shiru shiru ga kirki shi ma Awdul haka yake, ba sa wa ba hanawa, magana ma in bai saba da kai ba bazai yi ba in dai Awdul ne, yaron kirki da shi" Dai dai nan Ajay ya shigo parlon da sallama, sai da Kha
leesat taji wainar flour din ya fita kanta jin sallamarsa, ta tura plate din daga gabanta ta kauda kai, tun da Ajay ya kalli Abdul sau daya ya dauke idonsa, ya karasa cikin parlon ya zauna kusa da Jay sannan ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da fara'a tace "As
he tare ku ke da Jawwal din na zata shi kadai ne, sannun ku da zuwa, dama na ajiye maku dambun nama da aka yi min jiya, bari in dauko maku" Tana kai wa nan ta mike da sauri z
fi
dakinta, Ajay dai bai ce komai ba, banda gansa bakin kofar da juyawa zai yi ka
wai bazai
shigo parlon ba, tun daga bakin kofar parlon yaji wani abu ya tsaya masa cak a kirji, wani karamin veil Khaleesat ta daura a iya kanta, duk wuyanta da saman shoulder dinta a bude yake, mayafin ko gama rufe dogon gashinta dake ta kyalli bai yi ba
gaba daya, gashi in dai ka kalleta sai ka kara kallonta saboda irin hasken jikinta me daukar hankali, ita kuma Hadiyah da tasan ciwon kanta ga shi ta rufe jikinta baka hango wuyanta balle shoulders dinta, da ace Jay ne kawai a parlon babu abinda zai ji a r
ansa, but seeing Abdul sitted in the parlor ji yayi kamar an soka masa mashi a kirji, yayi kamar bai ji gaisuwan da Abdul yayi masa ba ya fara danna wayarsa ya maida duk attention dinsa a kan wayar, Hadiyah ma ta gaishesa taji bai amsa ba, haka ma Noor, Ab
dul ya mike yana kallon Jay yace "Zan shiga gidan su Haiydar, naga he is wasting time bai fito ba har yanxu" Jay yace "To jira Kaka ta fito sai mu fita gaba daya mana, mu ma airport za mu tafi yanxu, we are leaving for Bauchi" Abdul yace "Alright to" Daga
haka ya koma ya zauna, Mikewa Noor tayi ta tafi ta dauko ma su Jay ruwa da drink ta dawo parlon ta ajiye, Khaleesat na kallonta tace "Ina fruit din da Ya Abdul ya kawo min?" Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat, Noor tace "Na kai kitchen Aunty" Khaleesat ta
ce "Debar min wanda zan sha ki wanke ki kawo min yanxu" Ajay dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, ko sanin yana yi Khaleesat bata yi ba tunda ba kallon inda yake tayi ba, Noor ta nufi kitchen, ba a dau lokaci ba sai gata ta dawo da Apple biyu da Grapes
sai strawberry,
ta wankesu tas, ta karaso ta ajiye ma Khaleesat fruits din, Ajay sai kallon fruits din kawai yake, Khaleesat ta dau strawberry daya ta sha taji da zaki, ta kalli Abdul tace "Ya Abdul duk sanda zaka zo irin wannan Strawberry din nake son ka
dinga siyo min pls" Shi dai Abdul dan murmushi kawai yayi bai ce komai ba yana danna wayarsa, Jay dai kallon ikon Allah kawai yake, don ba karamin dariya Khaleesat ta basa ba, Jay ya dan kalli Ajay da gaba daya yanayinsa ya gama canzawa a parlon, Khaleesa
t ta mike ta dau bowl din fruits din tana kallon Jay tace "Ya Jawwad zan je daki, na gaji" Jay yana murmushi yace "To je ki huta" Juyawa tayi ta bar parton tayi tafiyarta dakin Nenne, Hadiyah dai ta bi ta da ido don babu irin maganar da bata yi mata ba tun
daga jiya har zuwa yau ashe duk bata dau ko daya ba, Khaleesat na shiga daki taga Nenne ta dibar ma Jay da Ajay isassun dambun nama, sai kuma ta juya tana kallon Khaleesat tace "Ni dai gaskiya bazan ba Awdul ba, dambuna ba na sadaka bane wallahi, ta yaya
ma zaka ba mutumin da baka yarda da shi ba abun hannun ka, har yau a tsorace nake da mutumin nan, haka kawai bazan kwashi dambun nama in ba tubabben dan daba ba" Khaleesat dake ta kallon Nenne ta juya ta dauko nata dambun da Nenne ta bata daxu, ta dungurar
kusa da wanda Nenne ta debar ma su Jay tace "Sai ki basa nawa, baki yarda da shi ba amma kike zama kiyi hira me tsayi da shi" Nenne tace "A'a to meye kuma hira wanda iyakarsa fatar baki, a nan inda aka yi hiran fa nake zubarwa in tashi, zaman duniyar nan
fa duu siyasa ce tunda kin ce a basa naki kason ai sai a basa sha min kai, dadin abun dai baza ki zo ki ce in baki
wani ba...." Ko tankata Khaleesat bata yi ba ta tafi ta zauna tana shan fruits dinta. Khaleesat sai da taji babu dadi sanda Hadiyah zasu tafi
da Jay, tana kwance dakin Nenne bayan tafiyarsu, Nenne ta shigo dakin tana kallonta tace "Ke ya naga kamar sanda kika je yi ma facalarki rakiya mijin ki ya maki magana kin yi banza da shi, ko ba dake yake bane lokacin?" Khaleesat kamar bazata ce komai ba
sai kuma tace "A'a ba da ni yake ba" Nenne tace "To amma ai ina daga gefe fa naji kamar ya tambayeki ko kina da bukatar wani abu, amma sai naji kin yi shiru" Khaleesat tace "A'a mun yi waya kuma nace masa bana bukatar komai, da Hadiyah yake ba ni ba" Tana
fadin haka ta rufe ido alamar bacci zata yi, Nenne tace "Dama can Jay ya fi sa faram faram da mutane yafi sa iya mu'amala, wani lokaci rasa gane kan mijin nan naki nake, yau dai yayi kicin kicin da fuska kamar wanda ke cikin kuncin rayuwa, ranan da aka kai
ki asibiti ma ni kamar ko gaisheni bai yi ba, ranan ma duk babu fara'a tare da shi, likitocin ma yaki masu magana balle nas, miskilin bala'i ne mijin naki, don ma an masa cuwa cuwa an kwace masa rawaninsa na magajin sarki, koma wanene ya kwace masa yarima
ya tanadi abinda zai gaya ma Ubangiji don wannan zalunci ne" Khaleesat dai taki tanka Nenne.... Tun bayan tafiyar su Jay kullum sai Ajay ya je gidansu Khaleesat amma firrr bata yarda ya ganta don tana jin kamshin turarensa take pretending kamar tana bacci
, tashin duniya Nenne zata mata amma baza ta tashi ba, sai dai Ng ta
koma ta ce masa bacci take yi ko zai shiga
dubata, kawai sai dai yace ma Nenne ta kyaleta kar a tasheta, wani lokaci kuma tana daidaitan sanda yake zuwa sai ta shige makota Nenne ta rasa
gidan da ta shiga, gashi daga ita sai Nenne ne a gida don Umma na tafiya islamiyya, haka ma su Mama Shatu da gorin Nenne yasa su ma duk suka koma islamiyyah ana koya masu tun daga huruful hijaiyah, yaran gidan kuwa idan basa boko to suna islamiyyah.... Yau
da yamma Khaleesat ta fito daga dakin Nenne da mayafinta a hannun tana son fakan idon Nenne ta shige makota don Ikcn da Ajay ke zuwa gidan ya kusa, Abdul ne yayi sallama, Khaleesat ta warware veil dinta ta yafa a saman kanta sannan ta zauna a parlon, Nenn
e dake zaune ta amsa sallamar Abdul tace "Lallai ka cika dan halak Awdul, daxun nan fa na gama cigiyar ka nace kuma Awdul shikenan don Haiydar ya koma Ingila sai ya dena leko mu, wallahi duk mun yi kewar ka, don Allah ka dinga zuwa tunda an saba, gashi bab
u Haiydar babu kai, ai unguwan bazai mana dadi ba kuma" Khaleesat ta dinga kallon Nenne don daxun nan ta gama hamdalan Abdul ya dena zuwa masu sun huta da fargaba, Abdul ya karasa cikin parlon ya zauna ya gaida Nenne yana dan murmushi, Nenne ta amsa da far
a'a tace "Don Allah ko jifa jifa ne ka dinga leko mu ka ji" Abdul yace "Na zo wucewa ne nace in shigo mu gaisa Nenne" Nenne tace "Gaskiya ka kyauta sosai, bari in kawo maka mantina da ruwa" Tashi tayi ta tafi dakinta, Khaleesat ta dan yi murmushi tace "Ya
Abdul ina yini?" Yace "Lafiya lau Hajiya, ya kike?" Tace "I am good, ya jikin Momy fa?" Abdul yace "Da sauki, she will be flown
d
next week in sha Allah" Duk da kamshin tura Khaleesat ta fara ji hakan bai hanata ci gaba da maganar da take ba, cike da damuw
a tace "Wai har yanxu jikin nata?" Abdul yace "Eh har yanxu, ya naki jikin?" Tana murmushi tace "Naji sauki tuntuni, zan ma Nenne magana sai mu je tare da ita mu dubo Momy in sha Allah" Abdul yace "To Allah ya kai mu, ina Dr Ahmad Jawwad?" Khaleesat tace "
Ya Jawwad yana Bauchi, a nan Kano kake aiki yanxu?" Abdul ya dan yi murmushi yace "Yeah, but I have something doing in Tanzania, once a while nake practicing discipline dina...." Khaleesat tace "Ohk, business kake a Tanzania?" Yace "Yea, i am managing my d
ad's business there" Khaleesat tace
"Maa sha Allah, where are your friends? I think akwai Umar da Maska" Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yayi murmushi yace "Ai bani da friends yanxu, duk bana mu'amala da su, da Haiydar kawai nake mu'amala mostly now" Mur
yar Nenne suka ji tace "A'a Junaid, ya baka shigo ba ka tsaya bakin kofa kuma?" All this while duk Ajay na tsaye bakin kofar parlon yana jin conversation dinsu, ya sauke idonsa ya cire takalmansa kansa a kasa ya karasa cikin parlon duk da bai yi niyyar shi
ga ba sai gashi Nenne ta gansa, Mikewa Abdul yayi, Khaleesat tace
"Har zaka tafi ya Abdul?" Yace "Yeah, zan koma" Nenne tace "To ga Mantinan, har ina son zubo maka abinci kuma" Abdul yace "A'a Nagode Nenne" Bottle water kawai ya amsa sannan ya gaisa da Aja
y ya fita daga parlon, Mikewa Khaleesat tayi zata bar parlon Nenne tace "Ina kuma za ki ga mijin ki ya zo, jiya ma da ya zo kina ta bacci, shekaranjiya kuma kin shiga makota ke da babu ruwanki da shiga gidan n tane"
Bata juyo ba tace "Zan je bandaki ne" Aj
ay y
la
kan kujera ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da rara'a tace "Bara in kawo maka Lemon kwali" Shi dai bai ce komai ba ta juya ta tafi dakinta da sauri, ba a dau lokaci ba sai gata ta fito da Kwalin tsadadden lemo da ruwan gora biyu ta ajiye masa a gabans
a, ta koma daki, bubbuga kofar bandaki da Khaleesat ta shiga ta fara yi tana cewa "Wai lafiyar ki kuwa Khaleesat, ni fa sai yanxun nan na kula kamar gudun mijin ki kike yi, Yau kwanaki nawa kenan ya jera yana zuwa gidan nan amma sai dai ya tarar kin shiga
makota ko kina bacci, to wa ma ya sani ko baccin sharri kike yi, to wallahi bara in kira Malam Ali, don ban san me ke faruwa ba gaskiya, ban san komai ba" Khaleesat ta hade rai tace "To ce maki aka yi wani abu ya faru ne?" Nenne tace "Fito ki tafi gun miji
n ki, ko kuma in kira Malam Ali da Zahra'u su dawo yanxun nan ince masu gida ba lafiya, don ban san ma'anar wannan abu da kike yi ba, ina ma wayar tawa take" Bude kofar bandakin Khaleesat tayi tana kallon Nenne tace "Shikenan kuma don ya zo kar in shiga ba
ndaki inyi abinda zan yi Nenne?" Nenne tace "Oho dai fitar min daga kara, tun da can baki san kina da uxuri ba sai da ya shigo alhalin zama kika yi kina ta hira da Awdul ko tsoron mutumin baki ji bayan babu wanda yafi ki sanin halinsa" Ficewa Khaleesat tay
i daga dakin, Nenne ta nemi gefen gado ta zauna cike da damuwa tace "Anya kuwa lafiya, ko dai jefe ta aka yi ta dinga gudun mijin?" da gaske sai yanxu Nenne ta kula da cewa haduwa ce Khaleesat bata son yi da Ajay shi yasa take kirkiran bacci idan ya zo ko
kuma ta fice daga gidan tun kan ya zo, to ko dai cikin ne yasa take haka, in dai iki
bane to gaskiya babu lafiya akwai lauje cik Nenne ta girgiza kai tace "Ban ga ta zama ba
Tun
lafiya akwai lauje cikin nadi, Nenne ta girgiza kai tace "Ban ga ta zama ba" t
un da Khaleesat ta fito parlor Ajay ke bin ta da kallo yana juya counter din hannunsa, ta tafi kitchen ta dauko Apple ta dawo parlon ta kwanta kan kujera tana cin Apple din tana canza channel fuskarta babu yabo babu fallasa, shi dai kallonta kawai yake wit
h different thoughts running his mind, bayan kusan minti biyar Nenne ta fito parlon amma sai da ta leko taga ko hira suke amma sai taga akasin haka, nan jikinta ya kara sanyi ta kara tabbatar da cewa lallai da wani abu a kasa, ta karasa cikin parlon tace "
Bari a zubo maka abinci Yarima, abinci ne me kyau Zahra'u ta girka daxu* Sauke idonsa yayi yace "A'a na ci abinci Kaka, dama za mu tafi asibiti na yau, akwai gwaje-gwajen da za ayi mata..."
HALYSAAH PAGE 213...
Khaleesat ta juya ta wani kalli Ajay jin a
binda yace, mikewa yayi ba tare da ya kalli inda take ba, yana kallon Nenne yace "Sai anjima Kaka" Nenne tace "To zaka jira ta a waje kenan ko?" Yace "Eh zan jira a waje" Daga haka ya juya ya fita daga parlon, Nenne ta kalli Khaleesat ganin gyara kwanciyar
ta ma tayi tace "Ba gyara kwanciya za kiyi ba baiwar Allah, tashi za kiyi ki tafi ki shirya kar ki
ɓ
ata masa lokaci yana jiran ki a kofar gida" Khaleesat ta hade rai tace "To ai naga ba sau goma ake zuwa asibiti ba Nenne, ko ba tare da ke muka je asibiti b
a har aka bani gado, to wani asibiti kuma za aje bayan ga magunguna sun bani ko gama sha ban yi ba, ni babu inda zan je gaskiya" Nenne ta saki baki tana kallonta a tsorace, kujera ta nema ta zauna cikin kidimewa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, n
a shiga uku jama'a, to ko dai ƙwaƙwalwarki ya ta
ɓ
u ne Khaleesat? Shi mijin da kika dinga mana hauka akan sa shekaru biyu da suka wuce kike walakantawa haka kamar wani yaron gidan ki? Na shiga uku na lalace zargina ya tabbata" Khaleesat taki ce ma Nenne kom
ai, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Nenne ta mike da sauri ta daga hannu biyu sama tace "Gwara da Allah Ubangiji ya dawo dake gidan nan Zahra'u, yau gidan ba lafiya, kin hadu da Yarima a kofar gida ai?" Umma da sai da gabanta ya fadi tace "Eh mun hadu
har mun gaisa, lafiya Nenne?" Nenne tace "A'a babu lafiya wallahi, Yarima dai ya fi awa daya a gidan nan zancen da nake maki yanxu haka, ya zo ne zai kai gantalalliyar yarinyar can asibiti a duba lafiyar
ɗ
an cikinta ta ki fita tace babu inda zata je, kuma
babu uban da ya isa yasa taje, banda bakaken maganganu babu abinda take jefa min tun daxu a parlon nan, ta dai ce babu wanda ya isa ya sa ta bi sa koma wanene" Umma ta juya tana kallon Khaleesat da mamaki, mikewa zaune Khaleesat tayi ta marairaice tana kal
lon Nenne, Nenne ta nemi waje ta zauna ta dafe kanta tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati, Wallahi a yanda naga tana magana kamar ko son ganin mijin bata yi, anya bamu shiga uku ba Zahra'u, wannan abu gaskiya ba lafiya ban
e, akwai wani abu karkashin kasa, ita da ke son mijinta kamar ta mutu rana daya mu ga wannan abu, yanda kika san makiyin ta ne ya zo fa, ko gaishesa bata yi ba wallahi" Khaleesat ta mike ganin irin kallon da Umma ke yi mata
ɓ
acin rai ƙarara a fuskarta, cik
in fushi Umma tace "Zo ki fita kar in yi mummunan sa
ɓ
a maki, dama ke mahaukaciya ce ban sani ba" Nenne tace "A'a mahaukaciya ce wallahi, babu wani dama, kawai kirata mahaukaciyarta kai tsaye, ta dauko hijabinta kawai ta rufa mana asiri ta fitar mana daga g
ida lami lafiya" Lokaci daya hawaye suka ciko idon Khaleesat ta juya ta tafi daki, Nenne tace "Mu dai kar ma ta dawo mana gidan nan tunda ta zama abar tsoro, daga asibitin ya tafi duk inda zai tafi da ita ba ruwan mu gaskiya, kar ma yayi zaton mu muka zuge
ta tunda dai lafiya suka sauka garin nan, sai yanxu ma na gane rashin walwalan da yaron yake yi duk kwanan nan yana da alaka da ita, kullum in ya zo fa sai dai in ce tana bacci duk zatona baccin Allah da annabi take, ashe ba haka ba Zahra'u, kinga ai sai y
a fara min kallon tsohuwar banza, gashi sai tayi ta tadi da Abdul a gabansa, anya ba Abdul din bane yayi mata asiri kuwa Zahra'u" Umma dai ta kasa cewa komai ta nemi waje ta zauna don gaba daya jikinta yayi sanyi, duk bata san wannan abun ba sai yanxu da N
enne ke gaya mata, bayan wasu mintuna Khaleesat ta fito daga daki tana sanye da hijab har kasa, fuskarta a daure kamar zata yi kuka, Nenne ta dinga yi mata wani shegen kallo, Umma kawai Khaleesat tayi ma sallama ta nufi kofa, Umma ko amsa ta bata yi ba ta
bi ta da harara har ta fita daga parlon, Nenne